Showing 63001 words to 66000 words out of 123508 words
SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:46_
_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._
_
*Knocking* kofar suka fara yi. Kafin kararrawa (door bell) ta fara kara. Ya tashi ya nufi wajen kofar. Yana mai waiwayon kafar bene ko Ahlam zata sakko.
Shiru shiru ba alamun ta. Kawai yasa hannu ya bude kofar. Suka shigo ciki. Haj Hameedah da Haj Aisha sai Ummimi kakar su. Da Umma Hadiza data shiga a karshe.
"Ahh mazan fama....." Ummimi kakar su ta fada tana dashare hakoranta.
Ya saka hannu ya sosa keyar sa yana murmushi.
"Sannun ku da zuwa...." Ya fada cikin girmamawa.
Wuce shi sukayi. Suka zazzauna akan kujeru. Ya yinda Umma Hadiza ta nemi waje daga kasa ta zauna.
"Ah haba Hadiza. Dan Allah tashi ki zauna akan kujera."
"Tashi mana ..."
"Tashi 'yar nan ki zauna....."
Haj Hameedah...Haj Aisha da Ummimi suka shiga bai wa Umma Hadiza umarni kan ta tashi daga zaunen da take ta koma kan kujera.
Umma Hadizan ta zauna daga gefen wata kujera kanta a kàsa.
Ya yin da Zayn ya tsugunna ya shiga gaishe su daya bayan daya cikin girmamawa da mutuntawa.
"Ina Ahlam dinne....?"
"Ta... Tana sama yanzu zata sakko."
Waheedah ta futo daga cikin dakin da tayi sallah. Ta tsugunna ta gayshe su. Umma Hadiza sai murmushi take
"Sannu da kokari Waheedah... Allah ya saka da alkhairi."
"Amin Maa.."
Sun dan yi mintuna da zama. Shiru ba Ahlam. Sai can daga baya ta sakko daga ita sai dogon hijabi zuwa gwiwa. Kayan baccin ta na dazu ta mayar .
Mamakin hakan ya mamaye Zayn. Har ya kasa boye halin da yake ciki a fuskar sa.
Zama tayi akan kujera tanata murmushi
"Ina wunin ku??. Ummimi na, Maa da Aunty Ai..."
Suka amsa. Ya yinda ta juya ta kalli Umma Hadiza.
"Ina wuni?"
"Lapia kalau amarya."
Can dai sunata zaune jugum. Waheedah ta miqe ta shiga kitchen din. Ta shiga dakko trays da plates da cokula da serving spoons.
Ta koma ta dakko warmers na abincin ta ajiye musu akan dinning dake gefen parlorn.
Ta sake bude freezer ta debo musu ruwa da lemo ta ajiye.
"Ahh .. Har na manta ma... Sannu sis." Waheedah ta fada.
Haj Hameedah na hankalce da su. Ta dubi Zayn da ke gefe, Kan sa akan tv. Ya yin da Ahlam ke danne danne a wayarta.
"Maa ga abincin can kar ya huce."
"Toh Waheedah sannu da aiki kinji?"
"Yauwa..."
Miqewa sukayi suka nufi dinning din. Ita dai Umma Hadiza bata tashi ba.
"Zo mana Hadiza.."
"Hajia nan din ma yayi .." ta amsa ta cikin ladabi.
Kan dinning table suka nufa. Suka ja kujeru suka zazzauna.
Ahlam tayi serving dukkanin su abincin.
"Waheedah zo ki zuba... Ki zubawa Umman ku ma"
"Tohm."
Karasawa tayi dinning din. Ta janyo plate babba ta zuba musu abincin ita da Umman ta.
"Ki kara muku mana..."
"Ya ishe mu haka...."
Ta koma can inda Umman tasu ke a zaune ta ajiye plate din abincin a gaban Umman .
"Sakko muci Umma..."
"Tohm Waheedah..."
Kasan carpet suka zauna. Abincin na tsakiyar su. Su kayi basmala suka fara ci.
Zayn na kan kujera ya kurawa tv kallo.
"Ah ina naka abincin? Zuba ma sa yaci Ahlam."
"Na koshi Ummimi."
"Dan Allah ka karba ka ci ka ji?"
Zai sake cewa wani abun . Haj Hameedah ta masa kallon kar ya yi haka. Ya dan kakaro yake yace,
"Toh.."
"Yauwa... Sannu Ahlam da aiki. Abinci yayi dadi." Ummimi ta fada tana mai sake yanko loma ta saka a bakinta.
Ahlam din ta danyi yake. kafin tace,
"Ai bama ni nayi ba Ummimi."
"Ai ho to... Na wajen sayarda abinci ne?"
"Ah'ah Waheedah ce ta yi komai..." Ta karasa fada hadi da sa ka hannu ta nuna Waheedah da yatsanta.
"Ah masha Allahu... Lalle tayi kokari."
"Sosai ma. " Cewar Hajia Aisha.
Ita dai Haj Hameedah murmushi kawai ta ke.
Ahlam ta zuba abincin a plate ta kai gaban Zayn. Yana daga zaune ta tsaya akan sa kerere. Da plate din abincin tamkar zata dora akan sa
"Gashi...." Hannunta daya na kan wayarta . Dayan kuma tana miqa masa abincin saura kadan ya bare.
Ya sa ka hannu ya karbi abincin ya ajiye a gefe. Kallon abincin ya tsaya yi. Gashi dai komai tsaf tsaf. Kamshin abincin na ta dukan kofofin hancin sa.
Amma tsantsamin sa da kuma aqidar sa ta qin cin abincin da ba na Maa ba yasa ya kauda fuska kawai yana jan kasan leben sa.
Ahlam ta koma ta zauna akan kujera tanata scrolling pages a Instagram. Sai bude videos take yi tana kalla.
Waheedah ta tattare inda suka ci abincin ta kai kitchen. Su Maa na karasa ci ta gyara wajen ta kai kwanukan kitchen tana dauraye wa.
"Wai baka ci abincin ba ka barshi yanata sandarewa?"
'Zan ci....." Ya fada ahankali yana mai kallon idanun Haj Hameedah mahaifiyar su.
Cokalin ya dauka ya saka acikin abincin. Sai yamutsa fuska yake. Amman tunda ya fara taunawa sai yaji wani dadi da gardi na fita na abincin.
Ya samu kan sa da sake ciko loma ya saka a bakin sa. Tabbas gaskia ne ba mafarki yake ba. Bai taba cin abincin mutane me dadi irin wannan ba idan har ka tsame na mahaifiyar su Haj Hameedah.
Ya shiga zura loma bayan loma yanata ci. Yana korawa da lemo. Sai daya cinye tas tukun sannan ya ajiye plate din yana goge bakin sa da tissue.
"Alhamdulillah..." Ya fada yana sake shan ruwa.
Waheedah ta sake fitowa daga kitchen tanata dauke kwanukan da bata dauka ba dazu. Ta hada da wanda ke agaban Zayn . Kitchen ta kai su ta wanke su tas. Tatattare kitchen din . Ko'ina tsaf. Sai da ta tabbatar ta gyara komai sannan ta koma dakin nan ta shiga bandaki ta watsa ruwa.
Ta mayar da kayan makarantar ta. Rigar Kuma ta ninke ta dauka ta fita daga kitchen dakin ta koma parlorn. Daga gefe ta tsugunna.
"Mu tafi ko...?" Ummimi ta fada tana kallon Haj Hameedah.
"Tohm Ummimi yadda kika ce."
Mikewa suka yi baki daya. Ciki harda Waheedah dake gyara zaman rigar hannun ta.
"Sis ga kayan. Nagode."
"Wane kaya?"
"Rigar da kika bani na saka nayi aiki da ita.."
"Oh . Ni ba aro na baki ba Waheedah... Kyauta na ba ki.. kinji ko?"
"Eh. Nagode Allah ya saka da alkhairi ya kara miki arziki mai tarin albarka Amin. "
"Amin..."
Zayn yana sauraron maganganun da su ke. Yanata mamakin adduoin da Waheedah ke yi.
Ya danyi murmushi kawai kansa akan tv.
Waheedah ta matsa wajen Haj Hameedah tana gaya mata alkhairi da Ahlam ta mata na bar mata kayan da tayi.
"Tohm Ahlam godia muke... Waheedah tace na miki godia."
"Kai ba komai Maa. Ai an zama daya."
"Angode kwarai. Allah ya saka da alkhairi." Cewar Umma Hadiza dake yaba kyautar.
"Amin."
Fita sukayi dukkanin su wajen. Direban ya tashi motar. Suka shiga baki dayan su.
Ya yin da Ahlam da Zayn ke ta waje a tsaye suna musu sallama . Har suka fice daga gidan tukun sannan Ahlam ta juya ta shiga ciki.
Zayn ya bita a baya shi ma. Ko da ya shiga bata parlorn. Ba kuma ta kasan baki daya.
Saman ya haye da sassarfa. Ya bude dakin ta ya leka. Tana kwance akan gado kamar ruwa.
Tayi dai dai da ita. Hijabin na gefe. Ita kuma ta sake barrarrajewa akan gadon bayan ta tukwikwiye jikin ta da bargo.
Rufo mata kofar dakin yayi. Ya koma kasa ya zauna akan kujera. Tv nata yi. Idanun sa na kan tv. Amman zuciyar sa ta tafi duniyar tunani. .....
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:47_
_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._
___
*GIDAN MALAM NALADO*
Karar gudar shigowar mutane ce ta sa inna Sa'adatu hanzarin toshe kunnuwanta. Duk a tunanin ta amarya aka kawo a layin bayan su
Cikin bacci karar ta isheta. Ta kuma tabbatarwa kanta tabbas yar iskar rediyon Marka ce ke yi.
Don haka cikin fushi ta mike ta fita daga cikin dakin nata.
Ja tayi ta tsaya a lokacin da dandazon wasu mata suka tunkari dakinta suna sallama.
Ta bisu da idanu tana mamaki. Auren wa akeyi haka?
"Shiga da kafar dama...." Matan su kace da matar da ke lullube cikin mayafi wai ita amarya
Daurewar kai tasa inna Sa'adatu ta basu hanya suka shiga dakin nata. Suka gaysa ita dai tanata binsu da kallon mamaki
"Allah ya baku ikon zama tare da juna, Allah ya kauda fitina a tsakani..."
Cewar wata babbar mata dake tsugunen a bakin kofa.
"Eh wallahi delu batada hayaniya. Da yardar Allah zaku wanye kalau. Amatsayin ki na babba kima matar farko dan Allah kece agabanta. Ki dubi girman Allah idan tayi ba daidai ki tsawata mata..."
"Bangane ba..." Inna Sa'adatu ta tanbaye su cikin karshen gaskiyar ta.
"Wannan din abokiyar zaman ki ce."
"Abokiyar zama....?" Ta sake maimaitawa tana tauna maganar.
"Allah de ya hade kan ku ya kauda fitinah a tsakani ."
"Ah wai wace irin magana ce wannan? Idan batan kai kukayo ku tambaya a nuna muku inda zaku je. "
"Banan ne gidan malam na lado ba?"
"Nan ne...Ya akai?"
"To shine dai aka kawo masa amaryar sa. "
Inna Sa'adatu ta ja tsaki ta fice daga dakin tana mai dokawa sunan Marka kira.
"Marka .. marka... Kina Ina ne wai?"
"Ga ni nan..." Marka ta amsa ta. Tana tsakiyar sauran yan kawo amaryar sunata hira.
"Bangane ba .. waye yayi aure?"
"Mai sunan malam mana..,"
"Kan babban bala'in can .. Au me?"
"Aure ."
"Aure fa kika ce? Malam dinne zai yo aure? Meya ke da shi meya tara da hat zai karo aure.?"
Marka ta ja tsaki tana girgiza kai...
"Zancen dai kenan... Yayi aure."
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun...Muga wacce shegiyar ce ." Ta kwasa a guje tayi cikin dakin ta.
Tsakiyar mutanen taje. Ta yaye mayafin da ke jikin amaryar. Wa zata gani?
Deluwa dai wadda ta kama hayar daki. Ta Kuma ke sayarda abincin sayarwa. Wadda sukayi fada akan buta, Ta zubar mata da kwabin danwake. 🤣
'bangane ba....," Inna Sa'adatu ta fada. Hannunwanta biyu dafe da kirjin ta . Ranta amatikar razane. Duk ta firgice. Wannan shine babu zato ba tsammani.
"Kai ! Kai!i Kai... Wannan ba karamar kasurgumar munafuka ba ce ke.... Kinada hassada da tsantsar mugunta.. Na meye zaki auren miji? Akan wane dalilin?... Iyye? Daman can daya bakin ku daya. Da Markan da shi malam din. Wallahi ni daman na san wannan rawar takashin da Marka keyi akan ki na san da kwai wani abun a kàsa. Wohoho. To ta yanke ta gille dai. Ba dai kin shigo gidan ba? Mu zuba mu gani. Wuya tallan turmi."
"Allah ya baki hakuri Yaya..."
"Yaya? Na hada ki da yayar na kwarfe. Kiji Wani sabon salon munafurci. Wai Yaya.? Allah ya Yayaba miki masifa da balai."
Yan dakin suka mata caaaaa. Takaici yasa inna Sa'adatu jan hijabin ta dake jikin kofa ta fice daga gidan.
Ya yinda aka raka Deluwa dakin ta . Sannu ahankali yan uwanta da abokan arzuka suka fara watsewa . Har dai gidah yazama sai yan gidan kawai idan ka tsame inna Sa'adatu da bata nan.
Tana fita ta wuce majalisar su malam na lado. Mutane nata yi màsa Allah ya sanya alheri.
Inna Sa'adatu ta kutsa ta cikin mazan ta ta shiga ta janyo malam na lado daga cikin su . Yanata janye hannun ta dada kama masa aljihu tana jansa.
"Menene hakan wai?"
"Gaskia malam kai bakin munufiki ne."
'haba Sa'adatu. Wanmnan wace itiyar rayuwa ce haka. Zaki wulakanta ni acikin abokai na. Dubi yadda sukayi cirko cirko suna binmu da kallo. Suna kuma sauraron abunda muke fada."
"Kunyar duniya kenan ma. Kafin kaje ka hadu data azabar lahira saboda baqin halin ka da muguntarka. "
'cikani wai menene haka wai?"
"Allah ya kwashe maka albarka malam."
"Sa'adatu wai meye haka eh...?" Ya fada da karfi
Abokan sukayi kansu. Ta daga musu hannu tana nuna shi.
"Munafiki ne. Annamimi ne, Kuma bakin mugu.."
"Assha. Assha. Dan Allah ki dena fadar haka. " Cewar malam Isubu mijin naja.
"Idan ba tsabagen tsagwaren rashin mutunci da tsantsar butulci ba. Me na rage shi da zeyi aure? Kuma ze karo din be fadamun ba. Ina cikin bacci ma jiyo hayaniyar yan kawo amaryar.. Wannan ya dace.?"
"Kiyi hakuri....." Suka shiga bata baki suna bata hakuri.
Tayi kwafa kawai ta juya ta koma gidah. Tana shjga zaure ta hadu da Deluwa.
Ta gogeta zata wuce . Deluwar ta hana ta hanyar riko gyalenta.
"Cika ni...."
"Dan tsaya mana... Yayata."
"Algunguma .."
"Kash Ina ki tsaya kin ki. Bakyacin ribar zance..... Ina kwanaki da mukayi cacar baki da ke akan butar ki da Marka ta kawo?."
"Matsalar ki ce ni sau ni dalla ..."
"Ki saurara .. Idan baki mance ba . Kin kirani da shashasha matsoraciya.. Na ce miki ki jira ramuwa ta... Dan ramuwar gayya tafi ta gayya zafi... Wannan itace ramuwar da na ce ki tsumayi zuwan ta . Na aure miki mjii har gidah.. sirikar ki da mijin duk sun juya miki baya.... Gidah yazama namu gaba daya.... Daga haya na haye igiyar auren me gidan..🤣. Me yafi wannan ramuwar dadi? Uhm.... Yayasko... Yayata mai buta."
Inna Sa'adatu maganganun Deluwa sun tsaya mata a rai. Sun taba mata zuciya. Sun raunata damuwarta. Hawaye ya taho ta danne hade da cijewa tace,
"Miji ne dai ko? Gaki nan ga shi... "
"Miji, uwar miji da gidan baki daya...Ga kuma karin ki amatsayin abokiyar zama na.. Riba uku"
Inna Sa'adatu ta tattare ta fisge mayafin ta da Deluwa ta riqe tayi gaba tashige dakinta tanata mita kasan makoshi.
Baki daya tun daga ranar ta nemi farin cikin zuciyar ta ta rasa. Zuciyar ta ta rubanya da baqi mai ciwo da tsantsar na dama...
To haka rayuwar take.., sai dai fatan Allah ya yayi mana me kyau Amin...
*BAYAN SHUDEWAR WASU LOKUTA*
*Dare* ya zama safiya. Safiya ta zama rana, Ya yinda rana kan zamo yammaci. Kwanakin mu nata shudewa.