Showing 69001 words to 72000 words out of 123508 words
introduction na course din da zai dauke su. Ya basu course outline. Nan ta ke ya fara lecturing din su.
Cike da kwarewa da sanin kan aikin. Turyan turyan yake yi. Daki daki da kuma tsayawa yayi bayanin inda yaga kamar ba zasu gane ba. Yanayin yadda yake koyar da su baki dayan su suna ganewa. Yanayi ana wasa da dariya. Babu bata rai na wasu malaman.
Ya kammala musu darasin ya fita. Nan take kuma wata lecturer din ta shiga. Bayan ta gaya musu sunan ta. Sai kuma ta juya allon ta rubuta sunan course din da zata musu na: Legal and ethical aspects of professional development in nursing..... Lamarin sai sam barka kawai. Domin itama suna game koyarwar ta. Ciki harda su Waheedah da ke jotting key points da take fada acikin littattafan su...
Sannu ahankali haka suka karasa duk wasu lakcoci na ranar. Sun kuma gane kowanne. Bayan an tashi suka hau dan sahu suka koma unguwar su. Kowannen su cikin zukatan su chunkushe da farin cikin kasancewara rana irin ta yau. Mai dimbin tarihin da ba zasu taba mantawa ba.
×××××××
×××××××
Fitowar sa kenan daga bandaki ya wai ga inda ya ajiye wayar hannun sa bai gani ba.
Girgiza kai kawai ya yi. Ya karasa closet dinsa ya sauya kaya. Ya feshe jikin sa da turaruka masu madaukakin kamshi .
Ya taje kwantacciyar sumar kansa da comb. Ya goga chappete na mint a leben sa.
"Ahlam.... Ahlam.... Ahlam..!!" Ya shiga kiran ta yana gyara button din jikin hannun rigar sa.
Shiru bata amsa shi ba. Ya fice daga dakin ya fara sauka kenan a bene ya jiyo muryar ta tana kuka.. Wayar da take yi kuma a speaker.
"Wallahi kinga matan da yake chats da su?.... Banda ma WhatsApp har da sauran social media apps... Baki ga mata friends din sa.."
"Kiyi hakuri Baby A .. Ai dai komai abunsa bai isa ya kara aure ba. Bakwa auren wadanda ba yan cikin dangin ku ba. Kuma dangin na ku bakwa mata biyu ballanata yace zai auri wata cousin din. Rabu da shi. Uban girman kai."
Zayn ya ja kasan leben sa yana taune wa. Yana mamakin har kawar ta tsabar guts take kiran sa da uban girman kai? Kasa karasawa yayi. Ya jingina a bango kawai ya harde kafafu
Yana sauraron su ta kammala wayar. Still wayar tasa na hannunta tana daddannawa. Dan balai ga tissue a gefenta tana goge hawayen da ke kwarara.
Shi abun ma sai ya so ya bashi dariya. Yayi ta maza kawai ya karasa sauka kasan. Alokacin ta kifa kanta a cinyar ta tana kuka. Sanye cikin kayan bacci.
Karasawa yayi ya zauna a kujerar gefen ta bayan ya dauki wayar sa. Yayi scrolling ya na duba chats dinsu da Asiye da Hazan da Leyla yan ajin su da sukayi university tare. Wanda biyu daga ciki an kawo kudin auren su ma. Dayar kuma baa kawo ba. Amman tanada wanda ta tsayar.
Cikin kakkausar murya ya dube ta yace,
"Meyasa kike son daukar waya ta ne Ahlam? Ina tunanin wannan shine karo na 7 ina ce miki ki dena dauka mun waya kina bincike. "
Ta dago ta gantsara masa harara kafin tace,
"Saboda bakada gaskiya shi yasa. Kana chats da yammata har wani hirar dramas kuke yi."
"To haramun ne dan nayi chats da su? "
"Eh tunda ba matan ka bane."
"Ke ko...kinada issues wallahi. Yanzu ke da wani banzan halin na ke zan bari ki san inda wayata take ma? Amman har password na wayata kinsa ni. Kin uzzurawa rayuwar ki akan wasu banzayen dalilai... Dan nayi hira da su haramun ne? Ko kuwa iskanci kika ga munayi? Ahlam kin fara kai ni karshe... Bakida sirri kwata kwata. Komai kankantar zance sai kin kwasa kin gayawa kawar ki. Ga abubuwan da ya kamata ki gyara kin ki."
"To ka aure su mana...Dama nasan ai ba kaunata kake ba.."
"Na taba daukar wayar ki na duba? Amman ke ba kida aiki se bincike binciken da ba zasu qare ki da komai ba. Kece bibiyar location dina. Ina hankalce da ke kyale ki kawai na yi. Sai bin diddigin wayata kina dubawa. Ban isa na danna waya ba sai ki fara lekowa kina ganin abunda zanyi. Wannan wacce iriyar rayuwa ce da kika dauka kika dorawa kan ki eh...? These should be the very last time Ahlam da zaki dauka wayata kina bincike...." Cikin fushi ya mike ya fuce daga gidan.
Ya yin da ita kuma ta dauki wayar ta tasake kiran aminiyar tata tana gaya mata abubuwan da ya fada.
××××
Haka zaman na su ya cigaba da kasancewa. Sam lamarin Ahlam kara bunkasa yake babu gyara aciki . Har yau bata abinci. Ragamar gyaren gidan ta bai wa almajirai. Kullum ba kyakkyawar shiga sai kayan bacci. Safe rana dare tana kan kujera ko gado a kwance. Kullum tana kan Whatsapp tana chatting da kawayen ta. Babu wani saurin hakki na miji da ke kanta da takeyi dai dai. Sam sam ba bu.
Hakan ya kasance har the Adams family sun fara lura da zamantakewar Zayn da Ahlam. Manya sun tsawatar amman lamarin yaci tura.
Zayn bai karasa hasala da lamarin Ahlam ba. Sai da idanuwan sa sukayi masa tozali da contraceptive pills (maganin hana daukar ciki) din da Ahlam ke sha. Kwali biyu ta gama da daya. Daya kuma sauran rabi ta karasa shanye kwalin duka.
Tsabar tsagwarar bacin rai har kuka Zayn yayi. Na ganin kullum ya kan hana idanun sa bacci yana rokon Allah ya basu albarkacin yara su ma. Amman Ahlam ashe munafurtar sa take tana shan maganin hana daukar ciki.
Ya dafe kansa da hannu biyu. Ya kuma kasa barwa kansa sanin hakan. Ya tunkari Maa yasanar mata. Nan ma manya suka sake shiga tsakanin su. Ahlam sai da tayi sati biyu tana gaba da Zayn .
A cikon sati na ukun ne dakyar da digon goshi malam na lado ya amince da zaman Waheedah agidan Zayn. Bisaga hukuncin duk karshen sati asabar da lahadi zataje gidah ta kwana.
Waheedah bata so hakan ba. Sam tafu kaunar gidan su duk kuwa da talakawa ne. Bata kaunar komawar ta can.
Amman tunda Umman su ta amince da hakan. Batada ja. Ta hada kayanta a babban akwatin da Haj Hameedah ta bata.
Ranar talata aka kaita gidan na su Zayn. Dan taya Ahlam kula da harkar gidah. Musanman abinci da sauran abubuwan da suka kamata. ...
#FARHATAL QALB
#FARIN CIKIN ZUCIYA
#ZAFAFABIYAR2022
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:51_
___
*Tsaye* take agaban dressing mirror tana mai gyara zaman rigar jikin ta ta uniform. Ta kammala duk wasu aiyuka da suka kamata.
Ta zaro dubu daya daga cikin kudin motar da Haj Hameedah ta bata ta zura acikin aljihun gaban rigar ta.
Ta dakko hadin madarorin turaren ta data saya masu dan yawa a babbar kwalba. (Arabian perfumed oils) ta shafe jikinta da su.
Ta bude kofar dakin ta leka zuwa parlorn kasa. Tana son tayiwa Ahlam sallama kafin ta tafi makarantar.
Ba kowa a parlorn . Hakan ya sa ta dubi agogon da ke wutsiyar hannun ta don kada ta makara.
Ta dan sake tsayuwar ta kafadar hannun ta daya dauke da jakar ratayawar ta . Dake dauke da notebook da handouts.
Shiru shiru ba motsin su . Haka ta hakura ta bude kofar gidan ta futa.
"Ina kwana Baba..?" Ta tsugunna ta gayshe da baba mai gadi.
"Lapia kalau 'ya ta. Makaranta za ki?"
"Eh! Baba...."
"Toh Allah ya kai ki a sa'a. Allah ya buda kwakwalwa yasa albarka a abunda ake karanta."
"Amin!! Amin... Baba. Nagode kwarai." Ta karasa fada fuskar ta ta fad'aad'a da farin cikin adduoin da yayi mata. Ta fuce daga gidan tana sa masa albarka itama.
Da ke babu nisa da unguwar su. Nan da nan ta haye adaidaita sahu ya kai ta zuwa unguwar su. Gidan su Basira ta dauke ta su ka biyawa Fannah sannan suka nufi makarantar baki daya.
"Kawata kinga yadda ki ka sake shar da ke?" Fannah ta fada tana taba kumatun Waheedah.
"Ke de karyar ki bata sallah ...." Waheedah ta amsa ta tana dariya.
"Allah ba karya na ke ba... Ko ba haka ba Basira?"
"Zancen ki haka yake fannah... Allah gidan nan ya karbe ki Waheedateey... Inji ya Ibrahim . "
Dan murmushi kawai Waheedah tayi. Tana mai girgiza kai kawai. Haka suka karasa makaranta suna ta wasa da dariya.
××××
Tashin sa kenan. Ya waiga ya dubi alarm da ke gefen bedside drawer. Kallon lokacin yayi yana mai ware idanun sa.
Da sauri ya mike ya gyara zaman bedsheet din da pillows. Ya karkade komai ya mayar da shi muhallin sa.
Bandaki ya faada yayo wanka ya sauya kayan sa zuwa manyan kaya. Samfarin riga da wando wagambari kalar toka.
Ya dora hula akan sa bayan ya gyara karin ta. Hancin sa ya shiga budawa sakamakon kamshin da ke dukan kofofin hancin sa.
"Ahlam..... Ahlam.. Ahlam...." Ya daga murya yanata kwarara mata kira.
Jin bata amsa ba. Ya feshe turare ajikin sa ya fice daga dakin bayan ya dau wayar sa.
Ba kowa a parlorn sama. Don haka ya bude kofar dakin Ahlam din tana kwance. Ya dauka ma bacci ta ke. Har ya juya zai rufe mata kofar. Sai kunnuwan sa suka jiyo masa karar waka ta video
Ya juya da sauri yana tunanin ko data ne a kunne tabar wayar. Ya tafi ahankali da niyyar ya dauka. Ganin ta baya ta juya masa baya ganin gaban ta.
Yana lallabawa a hankali don ya dakko wayar. Idanuwan sa suka sauka akan fuskar Ahlam. Hannu biyu da wayar a hannunta ta fito da kanta da hannuwa. Yayin da sauran jikin ke cikin bargo tana kallon wani biki a Instagram sai murmushi ta ke.
Can ta fita daga handle din ta koma hausaroom tana mai ci gaba da karanta sauran abubuwa tana tuntsirewa da dariya.
Girgiza kai kawai yayi. Ganin tsabar shagala da kallon da takeyi sam batasan shigowar sa ba . Ya fice daga dakin ya sauka kasa
Ko'ina tsaf. Kamshin turaren wuta sai tashi yake yi. Mamaki ne ya cika sa. Lalle ba su Waheedah da akayi ba karamun temako akayi musu ba.
Ko'ina kamshi ne ke tashi mai sanyi da kwantar da zuciya. Ya wuce kitchen nan dinma tas. Ta jere tukwane da sauran kayan amfani duk a muhallin su.
Kan dinning ya wuce. Abinci a jere a food flasks sai kamshi ne ke tashi. Ya bubbude doya soyayyiya an sakata acikin jarida saboda gumi acikin flask din
Sai soyayyyen dankali da kwai da plantain. Dayar food flask din kuma sauce ce ta hanta.
Da shayi a flask da yaji kayan kamshi. Bayaso yaci saboda aqidar sa ta abincin Maa din sa da yake kauna kawai.
Cikin sa ne ya shiga kara . Tabbas yunwa yake ji. Don haka yayi azamar zama akan kujera ya shiga zuzzuba komai a plate iya kacin cikin sa.
Ya yi basmala. Ya diba ya saka a bakin sa. Take idanuwan sa suka ware. Ji yayi tamkar abincin Maa... To ko itace ta bayar a ka kawo musu da sassafe?
Ya daga kai da tabbacin hakan. Ya karasa cinyewa tas. Ya shiga bandakin da ke corridor ya kuskure bakin sa da mouthwash. Ya dauki mukullin motar sa ya fice
"Ranka ya dade ... Sannu da fitowa."
"Sannunmu Baba... Barka da safiya."
"Barkan mu dai .. An kwan kalau?"
"Lapia kalau Baba ... " Ya sosa keyar sa da kasan mukullin motar da ke hannun sa. Kafin ya sake cewa.
"Ah... Na ce ba."
"Eh ina sauraron ka mai gidah."
"Ahh baba nace ka dinga kira da Zayn...."
"Ai sunan na ka ne mai gidah ... Na yan gayu ne "
Zayn ya saki murmushi kawai yace
"An kawo sako daga gidan mu ne?"
"Sakon me ranka ya dade?"
"Sako haka na abinci .. kulolin abinci."
"Yau kuma?"
"Eh...."
"Gaskia babu wanda ya zo. Ba re kawo sako. Tun wayewar gari na ke anan. Ba wanda ya shigo. Sai yarinyar nan data tafi makaranta ba jimawa ."
"Waheedah??"
"Eh ita....."
Kasa cewa komai ya yi. Ya wuce mota kawai. Har ya shiga ya fito ya zaro kudi ya mikawa baba mai gadi.
"Godia nake ... Yau ma? Allah ya amfana. Allah ya shi albarka "
"Aamin Aamin Baba... "
Ya koma mota ya tayar. Baban ya bude masa gate ya fita.
Kai tsaye ya wuce wajen aiki. Zuciyar sa nata tunano masa abincin da yaci. Me kama da na mahaifiyar su Haj Hameedah . Har spices din nan masu kamshi. Duk komai kaman na Maa.
Ko da ya tashi daga aiki gidah ya wuce. Ya ci saa kuwa mahaifiyar tasu na nan. Bayan sun gaysa tace da shi,
"Ya Ahlam ...?"
"Tana gidah Maa."
"Masha Allahu! Waheedah na makaranta ko?"
"Eh... Haka Me gadi yace."
"Bangane ba... Ku din bakwa nan ne baku sani ba.?"
"Bantashi da wuri ba ne. Amma dai ko'ina naga a gyare....Maa kin aika da abinci ne?"
"Akan wane dalilin zan aika muku da abinci?" Ta tambaye shi fuskar ta dauke da mamaki ..
"No na ga ..... I mean naga.."
"Kaga me?"
"Naji abincin ne kaman na ki .."
Murmushin fuskar ta ne ya fad'aad'a. Kafin ta ce,
"A'a ..... Waheedah ce tayi ko?"
Ya daga kai sannan yace,
"Amma ban sani ba gaskia .. "
"Batun kasani ko baka sani ba ma bai taso ba. Itace. Ai dama ta iya girki ... Sai kuma lokacin da suka samu hutu kafin ta karasa school tazo nan ta koya wasu abubuwan awaje na. Da su bangaren spices haka... Meya faru?"
Murmushi yayi tattausa. Cikin muryar ladabi yace,
"Naji kamshin komai kaman na abincin ki.. so na dauka ma an aika mana ne.... Masha Allah" Ya karasa fada fuskar Waheedah na masa gizo a idanun sa .
"A'ah....." Kawai taceda shi. Tana duba wasu folders a laptop din da ke gaban ta.
"Allah ya kara lapiaa Maa."
"Amin. Allah ya kara mana dika."
"Aamin."
Suna zaune ta re. Sai ga shigowar mahaifin su professor Adams Nasser . Da waya a kunnen sa yana amsa wa.
Zayn ya rissina yana gayshe shi. Ya daga masa hannu yana murmushi.
Haj Hameedah ta miqe ta nupi dinning area tana kara turaren wuta acikin electric burner.
"Abiey.... Barka da rana."
"Barkan mu dai Zayn...Ya wajen su Ahlam?"
"Alhamdulillah..."
"To masha Allah.... Akwai abunda kake bukata?"
Ya girgiza kai da sauri kafin yace,
"A'a Abiey... Akwai komai. mungode Allah ya saka da alkhairi."
"Amin Aamin Yaa rabbi... Allah ya temaka."
"Amin Abiey.."
Haj Hameedah ta tarbe shi tanata murmushi. Suka sake gaysawa. Kafin su isa wajen dinning din ta janyo masa kujera ya zauna. Ta shiga serving dinsa. Kallon su Zayn ya shiga yi cikin so da kulawa. Bai taba jin kan iyayen na sa ba. Yana alfahari da su.
Ahlam ta fado masa arai. Sam baya gabanta. Shi baki daya ya kasa gane wane irin so take masa Anya kuwa? Sam bata kula da shi. Ita kanta bata kula da lokacin kanta .. Gaskia ba son gaskiya ba ne.
Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kawai. Ya daga kansa kan saman pop ya zurfafa duniyar tunane tunane. Har mahaifin su yakammala cin abincin ya fita ta kofar gida.
Haj Hameedah ta koma parlor kujerar da ke kallon ta Zayn. Kansa a sama bai masan ta dawo ba. Sau uku tana kiran sa baya ji.
"Zayn...." Ta fada tana mai girgiza hannun kujerar da yake kai.
Ya daga kansa da sauri ya sauke akan ta ...
"Maa magana ki ke?"
"Me yake damun ka ne? Ka gayamun gaskiya har yanzu Ahlam bata canza halayen ta ba?"
"Ba komai Maa..."
"Uhm uhm... Zayn!"
"Na'am Maa..."
"Ga yamun gaskia.... "
Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Yana mai Jan kasan leben sa . Kafin ya furzar da iskar bakin sa. Ya samu kansa da fitowa ya fadaawa mahaifiyar sa gaskia akan dukkanin abubuwan da suke faruwa acikin gidan.
Tayi mamaki kwarai matuka . Domin