Showing 99001 words to 102000 words out of 123508 words
da zaa aura bace. Ballantana har ayi rayuwar aure ta re..."
Nan da nan Zayn ya harbo jirgin maganar ta. Ranar da kishi yasa yayi barambarama. Da event din bikin sa ne. Alokacin da Dawood abokin sa yace yana kaunar Waheedah da aure. Shine Zayn din yake bashi amsa da wannan karamar yarinyar ze aura? Kasan leben sa ya kamo ya cije. Ya sosa keyar sa yana marairaicewa,
"Allah... Ba wai har zuci maganata take ba. Na gaya miki tun kallon farko da nayi miki zuciyata ta kamu da kaunar ki... Kishin kaunar da nake miki ne. Ina burin na mallake ki ki zama a matsayin matata... Sai kuma dawood din ke nuni da yimin shigar sauri. Wallahi kishi ne da kaunar ki suka saka na fadi haka a lokacin. Ba wai har zuci da gaske nake nufi ba. Ki mun afuwa my love.... Ai laifukan da nayi da yawa .." ya karasa fada yana mai saka hannuwan sa akan kunnuwan sa alamun ban hakuri . Kafin ya cigaba da cewa,
"Rayuwata fansarki ce, Zuciyata tuni ta rikirkice, Kunnuwana sun ki karban zance, idanuwa na sun so su makance. Duk sanadin ki amshi soyayyar tawa da zaki kokarta ki amince mini, Mulkin ZUCIYAr ki shine aiki na, samun FARIN CIKIN ki jindadi nane, Murmushinki anashuwa ce ga zuciyata, Waheedah... Ni bawa ne ga zuciyar ki....."
Agogon da ke daure a wutsiyar hannun ta ta kalla. Ta mike da sauri . Ya tashi shima a tsayen yana jiran ta.
"Muje na sauke ki...."
Ba ta ce masa komai ba. Ta bude kofar da mukulli ta fice .
Tana sauka kasan ta ja ta tsaya. Ganin Maa da tayi itada Nadra . Ta kakaro murmushi ga kunya data ishe ta. Bayan ta kuma Zayn ne.
Me su Maa zasu zata. Wayyo! Inama kasa ta tsage ta fada, Haka takeji saboda yadda kunya ta dubibiyeta. Ga haushin Zayn da duk shi ya ballo wannan babban aiki.
"Maaa.." Ta fada a kunyace. Hade da tsugunnawa har kasa.
"Naam yar gidan Maaa. Har zaki tafi?"
"Eh.. Barka da safiya! An tashi lapia?"
"Alhamdulillah Waheedah .. Allah yabada sa'ar karatu."
"Aamin... Ai yanzu ya zo...."
"Wa?" Maa ta tambaya .
Hannu Waheedah tasa ta nuna bayanta. Gaba daya a kunyace ta ke.
Haj Hameedah tayi murmushi kawai. Kafin tace,
"Allah sarki... Allah ya miki albarka."
"Amin Maa."
"Aunty Waheedah nah. Barka da safiya."
"Barkan mu sis Nadra."
"Maa Ina kwana?" Ya tsugunna har kasa shi ma.
"Alhamdulillah.. Fita zakai?"
"Eh... Zaz..zan...zanje office. Na shigo zan gayshe ki ai naga ba kowa a parlorn "
"Masha Allah... Ya Ahlam din?"
"Alhamdulillah...... "
"Okay kaje ka dawo zamuyi magana."
"Okay Maa."
"Zaka ajiye Waheedah ne. Ko driver ya kai ta?"
"No! Zan kai ta"
"Alright..."
Fita suka yi.. Yana gaba tana biye da shi a baya. Suka karasa wajen motar. Nadra ta nata kallon su ta window tana murmushi.
Ya bude mata kofar ta shiga...Sannan ya koma matakin driver ya zauna . Ya tashi motar da addua suka fice daga gidan...
Akan hanyar tafiyar su. Go slow suka hadu da shi. Zayn ya saki tsaki kawai. Yana kallon waje. Dandazon yan makarantar su Waheedah ta sakandire a baya sunata wucewa.
Ya saki murmushi kafin ya juya ya kalleta. Ya kamo hannunta daya yana mai jan yatsun.
"Haduwar da nayi miki ta biyu anan ce... Kun taho ke da kawayen ki ku uku an taso ku daga makaranta.... Ina gano ki bugun ZUCIYA ta ya tsananta Waheedah...
"Ya kamo hannun ta ya saka a saitin zuciyar sa ...
"My love for you knows no borders, knows no limits, never fades, and will last forever. Insha Allah ... Waheedah, Your happiness means everything to me.I would cross a hundred oceans just to be with you and hold you in my arms. I would climb the tallest mountains just to fall asleep next to you. I would do anything for you. I love you long time ... 💕"
Waheedah ta sauke zuciya.... Kalaman sa na dada ratsa duk wasu sassa na zuciyar tah. Ba karya ya iya kalamai masu ratsa ZUCIYA da yalwatar FARIN CIKIn tah.. Mamaki ya dada mamaye ta. Ita kanta ta kasa gane wacce irin madaukakiyar kaunar da Zayn ya ke ma ta.. Kauna ce ya ke mata tacacciya marar gauraye. Ita ba yar kowan kowa ba. Gaba da baya yar talakawa ce. Batada wani usuli na manyan gidah. Ba ficacciya ba ce a gurbin karatu yanzu ta sanya kafafu. Ita ba shahararren kyau ba da zaa ce ya mato akan hakan. Duba da shi din da tsatson sa gaba da baya larabawa ne. Amman sai ita? Ita tasan ba dan sharrin soyayyah ba. Ita din ba ajin Zayn ba ce. Da har ko da yaushe sai ya roketa da ta tallafa ta amince da kokon barar soyayyar sa... Wani sashen na zuciyar ta ya hasaso mata Ahlam... Ta runtse idanun ta da sauri tana mai cije lebe. kunyar Ahlam kadai ta isa ta hanata nunawa Zayn kaunar da take masa. Duk kuwa da bata kai tasa ba.
Har an basu hannu. Don haka ya gangara gefen titi yayi parking motar. Ya mayar da nutsuwar sa da kallon sa kacokam akan ta. Hawayen dake tsiyaya ahankali. Ya janyo tissue ya goge mata. Ta kalle shi da sauri tana gogewa kafin ta mayar da zaman gilashin idanun nata... Shiru ya biyo baya. Kafin Zayn ya tada motar. Suka koma kan titi suka cigaba da tafiya.
Ya kai ta har cikin makarantar. Har kofar twin theatre inda zasuyi lectures... Zata fita taji kofar a rufe. Ta juya ta kalle shi ya daga mata gira yana murmushi. Murya kasa kasa yace,
"Kin hakura....? Maganan Dawood? Ki yafemun please.... Da maganar da nayi kan cewa ba ki isa yin aure ba. Kai na bisa wuya ki mun afuwa."
"Allah ya yafe mana baki daya..."
Ya zare seatbelt dinsa ya matsa . Ya sakar mata peck a gefen kumatun ta.
"Wannan turaren na ki kullum cikin tunanin sa na ke.... Waheedah, I am forever thankful to have met you. You are my breath and my light. You are the reason my days are filled with happiness. I love you more than I knew possible. You are my soulmate.You bring me to life! I’ve fallen in love many times – and always with you! Allah ya miki albarka... Wannan soyayyar ta mu daga Allah ce... DESTINED LOVE....💕"
Tayi murmushin jin dadin kalaman sa da adduar da yayi mata.
"Amin.... Nagode"
Ya zaro 1500 cikin aljihun sa ya zura mata a jaka. Zatayi magana ya dora yatsan sa akan labban ta
"Ayi karatu lapia..."
Ta sauka daga cikin motar. Kai tsaye ta shige cikin theatre. Ya dan jima a zaune cikin motar yanata murmushi kamar sauna. Tukun sannan ya tada motar ya wuce ofishin su kai tsaye..
#FARHATAL QALB
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:63_
_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._
_______
Dake asabar ce. Ya dan jima yana bacci tun bayan da yayi sallar asubah. Yana tashi ya faada bandaki yayo wanka. Hade da yin brush. Ya sauya kayan sa zuwa manyan kaya . Samfurin riga da wando na shadda. Amman bai saka hula ba. Ya dai taje sumar kansa data kwanta luf. Ya kuma taje ta sajen sa.
Ya bulbula turarukan kamshi ajikin sa ya sauka kasa. Babu Ahlam a duk wani daki da parlorn da ke kasa. Ba kuma ta kitchen ba ta farfajiyar waje. Hakan ya bashi damar ganowar tana sama.
Don haka ya koma saman. Tana cikin dakin ta. Ya murda ya jita a datse alamun ta saka makulli. Har zai juya sai kuma ya tsaya jiyo wayar da ta ke a handsfree ne kuma da aminiyar ta Bushra suke wayar. Don ya gano muryar. Ahlam din na kuka tana daga sautin muryar ta. Wayar sa ya janyo. Ya danna wajen recording ya seta ta.
"Wallahi ita dai Bushra... Ko a mafarki ban taba kawowa yarinyar nan itace wadda Zayn zai auro ba.. Bushra Zayn ya cuce ni.. Ya gama da rayuwa ta. A iya tsara rayuwa ta da nayi wallahi ban taba kawowa Zayn zai mun kishiya ba...Ya illata ni.. "
"Kiyi hakuri bestest ..Shawarar dana baki dai itace final solution.. Itama yarinyar ai na gaya miki ba ta zauna ba. Bare sunga gidan dadi ne. Ita da mahaifiyar ta zasu bazama bokaye su dasa soyayyar ta acikin zuciyar sa. Ina Zayn ina wannan kucakar yarinyar? Ita ba wata kyakkyawa ba . Dan wallahi kin fita kyau, Ita ba class ba. Ita ba wadataccen ilimi ba. Ba kuma daga babban dangi tafuto ba na mulki ko sarauta.. Ai ke kina ganin lamarin kinsan asiri ne ba yin kansa ba ne. Soyayyar jinnu ce. Ai shiya sa gwara da kika kaurace masa. Kika hanashi kusantar ki har sai ya dawo cikin hankulan sa..."
"Gaskiya nima nayi wannan tunanin da farko. But babes lamarin fa babba ne. Allah tun lokacin bikin mu bana gaya miki ba? Ya kira ni da Waheedah, Nace Waheedah kuma? Ko bayan auren ma. Tunda ta dawo nan gidan. Yanayin yadda yake bin ta da kallo zaki gane he's into her."
Zayn ya girgiza kai kawai. Ya sake gyara tsayuwar sa. Yana mamakin sakarci irin na Ahlam da ke bin zugar kawaye . Meyakwan tayi kokari ta gyara rayuwar auren ta dake neman tabarbarewa.
Ji yake tamkar ya dakko spare key ya bude kofar. Ya shiga ya kashe wayar ya kuma buga ta da kasa. Saboda tsananin yadda zuciyar sa ke tunzura shi. Ya dakata kawai.
"Kibar aikin bokonci Ahlam. Na ke gaya miki. Kaunar da yake miki hatsabibin bokan su ya dauke ya dasa a zuciyar Waheedah din. Shine ya mato akanta. Tsinannu. Nagaya miki na samo hanya. Sha yanzu magani yanzu. Aikin sa kamar yankan wuka yake. Idan ma so kike ya rabata da iska. Zai kashe ta. Ta hanyar mata turen ciwo. Ko ya haukata ta. Ko ya mata kurciya ta shiga duniya a nemata a rasa. Ko a saka mata mantau ta manta komai nata.... Ko"
"Noo bestest.... Duk bana kaunar wadannan abubuwan. Kar a mata ko daya daga ciki. Banda kisa, Banda hauka, Banda mantau din da kikace banda kuma kurciya din. If there's no other way.. Mu hakura kawai."
"Ke dai wani lokacin banza ce wallahi. Tazo har gidah ta shiga jikin ki.. Ta aure miki miji kice duk wadannan ba zaki iya ba? Kar ki manta ta kaudar da hankalin mijin akan ki . Ni gidan ki da tazo ta zauna ma tun farko bai kwanta mun ba... Saboda nasan da wata kulalliyar tazo. Maybe ta dauki kayan sawar ki ma ta kai da su akai amfani. Ke wasu mutanen fa mugaye ne. Da kuma na gaya miki nace mahaifiyar sa bata kaunar ki. Har da ita a masu ruwa da tsakin.."
"Ai nima da kika fada na gano haka ne. Bata kaunata. Tana wani murmushin mugunta. Daman can ita ta hada auren. Tunda agidan ta suke aiki yarinyar da mahaifiyar ta. So ni dai yanzu so na ke yarinyar nan a lalata rayuwar ta kawai taji batason zaman auren ni yafiye mun. Shi ma yatsaneta.. Kingane?"
Zayn ya kara harzuna. Gumi na keto masa na tsananin bacin rai. Ya danne ransa. Yana jiyo sanda Bushra ke ce mata,
"Zan gayawa bokan kan ya shafe gaban waheedan. Kar ma Zayn din yaga komai idan yazo auratayya da ita. Ya shafe shafin siminti (cement) Ya kuma cire kaunar sa a zuciyar Zayn din ta zama itace bakin cikin sa a rayuwa. Sannan ya kara mata da warin jaba. Ta dinga hamamin doyi. A kuma cire kaunar da yake mata . Da shi da mahaifiyar ta sa. Ke long story short shi ma a rabashi da mahaifiyar ta shi. Ya juya mata baya. Ta yadda ke kadai zai dinga jin maganar ki. Ya kuma saki Waheedah din. Ya zama ya dawo a tafun hannuwan ki. Sai yadda kikayi da shi . Koya kika ce?"
Ahlam ta kyalkyale da dariya har tana kyakyatawa tamkar ba ita ke kuka dazu ba.
"Sha kurumin ki. Ki bar zubar da hawayen ki. Hanyar gidan boka ba wanda bamu sani ba. Kede kawai dukkanin umarnin daya ketara miki kiyi . Ko sallah yace ki bari ta yan kwanaki ce kingane? "
"Nagane kawata... Na gaya miki banda kisa dai. Banda dik sauran. Kawai a shafe gaban nata a kuma saka mata doyin. A kuma cireta a ransa. Sannan yadda kikace din. Na aminta .A raba shi da mahaifiyar tasa. Daman yadda yake kaunar ta yana ci mun tuwo a kwarya . Komai Maa. Komai Maa. Sai abunda tace. Kullum yana can wajenta na tsani hakan. "
"Sha kurumin ki. Tamkar an raba su ne. Ina nan shigowa dana harhada komai zan je wajen sa. Da kai na zan biyo flight na zo. Na gaya miki aikin sa kamar yankan wuka ya ke. Zan hado miki da wanda Zayn din zai bude miki bakin aljihun sa ma. Duk kudaden sa ke zaki rika juyawa. Ki kuma mayar da shi rakumi da akala sai yadda kikayi da shi. Ta yadda idan kika ketara kara ba zai tsallaka ba. Idan kikace da bakin abu fari. To ta zauna.. kawata.. ki kokarin samun tufafin su ki aiko ko da ta tasha ne.. "
"Masha Allah tawaje na. Amanar zuciyata. Bugun numfashin senator gallauro.. Allah ya biya ki da alkhairin sa. Ya yi auren ku da sanata."
"Amin kawata.... Sai na kira ki "
"Yauwa.. Godiya na ke."
Suka katse wayar da suke yi. Yana jiyo sakin karar farin cikin da Ahlam tayi tana buga kafafu
Kasa tabuka komai yayi. Ya yin da kafafun sa suka gaza daukar sa. Ya jingina da bango yana runtse idanu. Maganganun su Ahlam sai yawo suke masa a kwakwalwa.
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Ya shiga maimaitawa yana mai dafe goshin sa da jijiyoyin sa suka daga saboda tashin hankali.
Dakyar ya iya mikewa ya sauka kasan. Kai tsaye ya wuce wajen freezer ya dakko ruwa ya zauna ya sha. Tukun sannan ya fice daga gidan bayan ya shiga mota.
Gidan su ya nufa kai tsaye. Haj Hameedah ya samu a karamin parlor tana karatun jaridah. Bayan sun gaysa ne take tambayar sa ya Ahlam da fatan dai zaman su ba matsala?
Ta lura ainun da damuwar da ya shiga don haka ta shiga tambayar sa akan me ke faruwa? Ya kasa boyewa saboda gudun faduwar abun Allah ya kyauta. Don haka ya janyo wayar sa ya kunna mata recording din da yayi na hirar Ahlam da kawarta.
Haj Hameedah ta saurara gaba daya tana kada kai. Ta tsorata da mamakin yadda suna kananun yara amman suke kokarin kulla wannan mugunta haka? Don haka bata tsayar da zancen ba.
Ta tasa Zayn agaba suka tafi sashen Abiey dinsu. Allah ya temaka ma su Ummimi sunzo tare da sauran iyalan nata. Bayan sun gaggaysa. Ummimi na tambayar Zayn Ahlam. Maa ta bashi umarmin daya kunna musu recording dinnan domin abun yafi karfin ta
Don haka aka samu babban music player aka hada ta da wayar aka kunna yadda kowa zai saurara dakyau. Hirar su tafara tiryan tiryan. Parlorn ya dauka da salati da sallallamin girman maganganun da suke futowa ta recording din.
Ummimi ta shiga girgiza kai kawai tana mai kambama mamakin zantukan. Suna karasa saurara kuwa ta sa lalle a je a dakko Ahlam . Hakan kuwa akayi. Basher aka tura ya dakko Ahlam din. Tanata tambayar sa daukowar menene? Yace su Ummimi ne zasu gaysa.
Ko da ta shiga parlorn. Hada gaisuwar tayi ta jimlanta. Suka amsa baki daya. Banda mahaifin ta. Da yake