Showing 81001 words to 84000 words out of 123508 words
su cikin lumana da kaunar juna. Ku yarda wannan dinma ba lefin Ahlam ba ne. Sai dai Zayn. "
Haj Hameedah na daga gefe ita da sauran matan. Sai dai su saurara su kuma bi su da kallo. Su kara da Amin idan hakan ta kasance.
"A'a Adams. Dan Allah ka dai na dorawa yaron nan lefi. Wallahi kaji rantsuwar musulmai? Yarinyar nan Ahlam itace me lefi. Duk duniya kaga ba wanda zai darani saninta sama da mahaifiyar ta ko? To ga mahaifiyar ta a zaune . Wallahi ko ita ta fada lefin Ahlam ne. Wannan yarinyar da kakeji da gani batada mutunci. Akazo aka hadata da yaro mara hayaniya taketa cutar sa. Zaki dai na kallo na ko sai na zo na buge kan ki anan wajen? Shashasha, sakarai da batasan me yake mata ciwo ba. "
"Kayi hakuri ... Dan Allah kayi hakuri." Zayn ya shiga bashi hakuri .
Saboda magana yake tamkar zai tashi ya bugeta...
"Yanzu ya muke ciki ne ?" Ummimi ta sake fada .
"Duk yadda kika tsara Ummimi. "
"Abunda kika yanke shi za'ayi."
Ummimi ta daga idanu ta sauke akan Ahlam dake zaune a gefe. Ta sakala wayarta dan balai ta kasan kujera tana dannawa. Ya yin da shi kuma Zayn ke gefe ya rakube. Ya rame ainun tamkar majinyaci da yayi shekaru yana ciwo. Yayi bakikkirin da shi tamkar ba Zayn ba.
Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin tace,
"Dama wannan tsari na hada auren nan ni ce na kafa shi. Kuma Alhamdulillahi dukkanin aurarrakin da muka hada akayi har yau kowanne suna cikin zaman lapia da dadi babu dadi dai sun rungumi tasu kaddarar. An kuma samu zuri'ah mai tarin albarka ta hakan. Hakika baki yayi kadan wajen zayyano godia ta agare ku. Ubangiji Allah ya saka muku da alkhairin sa mafifici. Kun bani dama batare da gazawar ku ba. Dukkanin ku da yaran ku. Duk wadanda na hada aure sun karba basuyi musu ba. Alhamdulillahi wallahi ina alfahari da hakan. Ko bayan rai na na san zuriyata yan albarka ne. Nagode muku. Godia mai kima da dimbin fatan alkhairi da albarka."
"Amin Ummimi ."
"Amin Ummimi "
"Amin Amin"
"Allahumma Aamin.""
Dukkanin yan cikin parlorn suka hada baki wajen amsa adduoin Ummimi.
Ta kurbi ruwan da ke hannun ta. Kafin ta cigaba da cewa,
"Zayn da Ahlam suma basuyi musu ba sun bi umarnin mu. Sun amince an musu auren nan ba tare da wata husuma ta taso ba ko baraka da za'ai auren nan. Lamun lapia akayi biki aka kare. Don haka ko yanzu kasuwa ta tashi dankoli yaci riba. Alhamdulillah Allah yayi musu albarka. Wannan sabani da suke samu a tsakani. Ina fatan Allah yasa hakane yafu zaman alkhairi. Sannan kamar yadda kuka fada din. Nayi dan nazari naga hakan zai fi. Tunda yanzu komai yana tafiya ne da zamani. Kuma bazeyiwu mu dinga tauye hakkuna ba gaskia. Daga yanzu maganar auren zumunci da muke na tsakani an soke . Tunda al'adace ba jazaman ba ne. Dukkanin wanda ke raayin karo aure daga wani dangin sai ya karo. Wanda ba suyi ba dake shirin yi kuma sunada wasu daban a waje da suke so. To suma duk mun lamunce mun amunce su auro su. Wadanda kuma suke da raayin auren na gidah sai su aura. Amman ba takura. Daga yau na cire wannan takunkumin na auren dangi. Wadanda mukayi a baya idan har an shiga hakkuna muna neman gafarar Allah ya yafe mana. Kuma kuma ku yafe mana baki daya. Allah ya karawa zumuncin mu kwari da karko. Allahumma Amin."
"Amin ..." Baki dayan su suka hada baki wajen amsa ta.
"Saboda haka zancen cigaba da zaman su tare. Gaskia babu lallai babu kuma dole. Idan dukkanin su sunyi naam da cigaba da zama to sai a sake jan kunnuwan su. Idan daya baya raayi ko kuwa dukkanin su basayi. To gaskia gwara a raba din shi zai fi zama alkhairi. Sannan Zayn bazamu tauye maka hakki ba idan kanada wadda kake so ka karo aure karkaji nauyin komai ka yi magana manya su shiga ciki kaji?"
Da sauri ya samu kansa da daga mata kai alamun eh. Kafin cikin ladabi yace,
"Eh Ummimi... Tohm, In sha Allah. "
"Yauwa. .. To Allah ya muku albarka amin. Ka nada wadda kake so a tambayo maka aurenta ka auro ko?"
Nan ma ya daga kansa alamar eh. Ahlam dake gefe ta bude baki,
"Kishiya? Kishiya? Ummimi zaki bari ya karo aure? Yamun kishiya?"
"Ke ummimin ki ke fadaawa magana haka?" Zai tashi ya bugeta suka riko shi. Daman alhaji Nouh akwai saurun fishi da hawa doron zuciya.
Kuka ta saka. Tanayi tana bubbuga kafafu ita ga shafaffiya da mai da ba zaa karowa kishiya ba.
"Wallahi sai dai a raba auren . Ni ba zan zauna da kishiya ba. " Kuka take sosai harda shessheka.
Ummimj ta kalleta ta tabe baki. Ta dubi Zayn kafin tace dashi,
"Wacece?"
Ya samu kansa da yin murmushi kafin yace,
"Wata ce Ummimi... Ba yar uwa ba ce."
"Masha Allah..... Amman dai tanada hankali ai"
"Tanada hankali. Ga nutsuwa, Tanada tarbiyyah . Tanada kulawa kuma sosai. " Yanata magana yana murmushi shi kadai. Tamkar Waheedah ce agaban sa.
Ummimi tanata nazarin sa. Ta kuma tabbatar koma wacece yarinyar gasksia Zayn yana kaunarta. Sai fatan Allah yasa aurota da zaiyi ya zama alkhairi.
Haka suka cigaba da zama anata zantawa. Daga karshe dai aka tsaya akan barin auren Zayn da Ahlam bisa rokon da farfesa yai ta yi. Amman da sharadin inde Ahlam ta sake wani lefin to auren su ya kare zaa raba igiyar auren.
An kuma lamunce Zayn ya auro koma wacece yake so. Ba shi ba har sauran yan uwa na dangi kowa zai iya auro wanda yake so daga wani tsatson.
Suka ci abinci. Aka dau hotuna na tarihi. Kafin daga bisani wadan da zasu bi jirgi a ranar su kuma gidajen su duk suka tafi. Wanda zasu kwana su tafi da safe kuma suka koma cikin gidah.
×××××××××
*Yana zaune a parlorn sama shi kadai. Domin Ahlam fushi take dashi sosai bata shiga harkar sa tun da suka baro wajen su Ummimi ta kulle kanta a daki tana kuka.
Wayar sa ya janyo. Daman jikin sa sai ingiza shi yake da yayi mata magana. Ya danna button din WhatsApp ya shiga ciki.
Yana dubawa ya ganta online. Dp (display picture) dinta kuma hotan wani namiji ne da yake da tabbacin shine ya Kamal din da ya rasu. An rubuta rest in jannatul frdws. ajikin about din ta.
Sai ya danna salam sai ya goge. Ya saka hi nan ma ya goge. Sai cije labe yake yana tunanin yadda zai mata magana.
Ya daure ya cije ya danno kan number ta ta. Ya tura mata da,
"Assalamu alaikum.."
"Wa'alaykm Salam...." Ta bashi amsa
Murmushi yayi. Ya kwantar da kansa akan kujera yana wani lumshe idanu,
"Waheedah ya gidah?"
"Lapia Lou... Da wa na ke magana?"
Shiru yay ya kasa mata reply. Yanata tunanin sunan da zai fada ba. Kawai sunan Dawud abokin sa yazo masa. Ba tare da bata lokaci ba ya tura mata da,
"Dawood ne... Kin tuna ni?"
Fuskar bude baki ta tura masa
"😱"
"Kingane ni?" Ya tura mata yana gyara zaman sa. Sai wani annashuwa yake ji.
"Abokin Ya Zayn ko?"
"Yes ... Shi. Ashe kin tunani. To ya samarin ki?"
"Samari kuma? "
"Ehmanaa. Ai nasan kina da su ko?"
"Noo. Ina dai karatu tukun."
"Masha Allah... Allah yasa albarka "
"Amin... Amin"
cikin kankanin lokaci, Da haka da haka dai Zayn ya samu da wayo ya cusa sakon zuciyar sa ga Waheedah amman ta sigar Dawood. Ta kuma amsa da hannu biyu. Kullum cikin chatting suke shi da da ita. Duk a zuwan Dawood ne abokin Zayn wanda suka hadu a bikin Zayn din...,
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: *FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:57_
*GIDAN MALAM NALADO*
Zahara'u ce a tsakar gidan su tana wanke kanta da kumfan los. Marka na daga gefe akan yarkacacciyar kujerar ta.
Mikewa tayi daga zaunen da take. Ta shiga kai da kawowa tana daga hannuwa sama.
Zahara'u ta mike da jikakken diddigaggen gashin kanta. Daya zama kuda kuda duk ya gwaigwaye.
Ta ja dankwali ta daure kan nata tana gyara zaman zanin jikin ta.
"Ban hamsin Marka. "
Marka ta kalleta sama da kasa ta tabe baki.
"Ke kuma me zakiyi da hamsin?"
"Zuwa zan a kitsen kai na mana. Dan Allah bani kar na tarar da layi."
"Ah kiji ki. Ina da kudin ne? Zaki tsaya gansan gansan akai na ki ce na baki hamsin. ?"
"Na fa ga kudi a karkashin tabarmar ki."
"Wannan yarinya bansan yadda zan da halayen ki ba. Au dan uban ki caje kike mun? Ajiya kika ban?"
Zahara'u ta ture baki gaba. Tana yatsina can ta banka kasar tabarmar ta kwashe chanjin ta zura a rigar mama.
Marka ta bude baki kafin ta yo kanta tana zuba hannuwa sama.
"Bani dan uban ki. Na ki ne? Da zaki saka hannu ki dauke mun? Ajiya kika ban?"
Suka shiga kokawa kacar kacar. Zahara'u ta fincike Marka daga jikinta tana sauke numfashi.
"Sanda ina gidan Adamushe wata rana ta laraba munzo kikace a sayo miki ruwan leda . Na ciro dari biyu ta kenan na baki da niyyar kiban chanji na. Har muka tafi baki ce mun gashi ba. Alhalin ba baki nayi ba duka. Don haka dole ne na dauki abu na. "
Tana karasa fada ta fice waje da sauri. Ya yin da Marka ta shiga tafa hannuwan ta tana salati.
Bata rufe baki ba badamasi dan Zahara'u ya bugo yar randar ta ta fashe a kàsa.
Ya kwasa a guje ta bi bayan sa tana kururuwa
"Sai kaci malafar kan uban ka. Dan kwal uba da rafkeken kai. " Tana tsaki tana tattare gutsattsarin fashasshiyar randar. Sai mita take tana zundumawa sunan sa ashariya
"Randar nan jaka biyu na saye ta tun duniya na kwance. Amma saboda tsabar kiriniya da rashin ji irin na ka sai da kasa kafa ka shure mun ita.." Ta ja dogon tsaki ta shuri mayafi ta fice waje.
Daga can nesa ta hango Deluwa da malam na lado suna tahowa. Ya riko mata wata leda fara ta asibitin malam aminu kano.
Turtsetsen cikin ta ya fito tamkar zai yago ya fado. Dakyar take iya tafiya saboda cikin nata yana da girma ta kuma kusa haihuwa.
Marka ta kwasa da sauri ta isa gare su tana mai dokawa Deluwa sannu.
"Allah dai ya raba ku lapia . Sannu Deluwa."
"Amin Marka.. Sannu da kokari . Unguwa zaki je ?"
"Barka da rana Marka."
"Yauwa mai sunan Malam. Eh Deluwa fitowa nayi ko zan ga zahara'u. Yarinyar nan ta dauka mun kudi ta tafi kitso. Shi ne zanje na rutsa ta "
Deluwa tayi murmushi. Ta karbi ledar hannun malam na lado . Markan sai kallon gefen ido take yi wa Deluwa.
"Bari na ta fi." Ta fada tana tafiya.
"Kai dan Allah Marka ki kyaleta.. Har nawa ne kudin?"
"Kai Deluwa. Allah karki biya mata. Rabu da ita. Ni da ita ne."
"A'ah dai Marka dan Allah. Kawai dai ca nai ki kyaleta. Ga dan chanjin da yayi ragowa " Ta mikawa Markan nera dari biyar.
"Ayi haka? Deluwa."
"Dan Allah."
Da sauri Marka ta karbi kudin ta soke a kullin zanin ta. Ta sake dashare hakora tana murmushi tamkar zata yage bakin ta.
"Ga ruwa can na doran ki. Muje na sauke. Ki samu ki gashe jikin ki . Allah ya sauke ki lapia Deluwa. Ya kawo malam tsalha ko mai sunan Malam lapiya cikin aminci. Dan ni dai ina kan gabana. Na'urar baturen karya. Wagga ciki na ki yan biyu zaki haife. Maza. Ba guda daya ba."
Deluwa ta kakaro murmushi kawai. Kafin tace,
"Sannu da kokari Marka . Nagode da adduoin ki gare ni."
"Ba godia tsakanin mu. Mai sunan Malam yo sauri ku karasa gidah mana."
Malam na lado ya riko hannun Deluwa suka dauki hanyar shiga gidah. Ya yin da Marka ta lelleka bata hango zahara'u ba ta koma cikin gidah.
A yammacin ranar aka kawo kudi da kayan sa rana ta Zainab 'ya ga malam na lado da Inna Sa'adatu. Bashari magini zata aura .
Yan ganin kaya sai zuwa suke suna yaba kaya. Akwatuna 3 da kit. Inna Sa'adatu sai yatsine ta ke tana hura hanci yar ta tayi goshi
Haka ma Marka da ke ta sakin guda tana mai kuranta kudin kayan. Kawayen ta tsofi duk sun zo ganin kaya.
"Gaskia zainabu tayi goshi. Kaya maya maya gasu nan." Cewar lawuri kawar Marka.
"Wallahi ga bashari sharfacece dashi. Du kayan da zai saka sai ya hada da shawul kalar kayan. Zaki ga ya dora a wuyan sa🤣 Wannan yarinya zainabu na da kashin arziki. " Indodo ta fada
Marka ta mike daga zaunen da ta ke. Ta daga hannu ta saka akan hancin ta. Ta saki katuwar gud'a tana taka rawa .
Sai da ta yi mai isar ta tukun sannan ta zauna tana mai rangada wata gudar.
"Jika ta kam tayi goshi. Tun zamanin adaman badamasi baa taba kawo kayan aure irin wannan ba na Zainab. Sai ma kunga gidan. Dakuna biyu dandatsa dandatsa ga uwar falo da dakin girki. Bandakin ta fa irin na korawa dinnan ne masan. Kur'an ga rijiya tafkekiya harda murfin ta. Ga ruwan pampo. Ai zainabu ta gama da ce "
Inna Sa'adatu da ke gefe aka hura hanci ita ga uwar 'ya. Can wata cikin yan ganin kayan ta ce,
"Ina Hadiza ne. Da yarinyar wajen ta?"
Marka ta ja tsaki tana yamutsa fuskar ta,
"Waya sani ne? Yarinyar dai ta kan zo nan ta kwan. Ta zama yar kwalta. Suna fakewa da boko ta ke. Can ta matse musu."
"Na gama ta kara zama sharfaceciya "
"Yo a banza ai. Girman shirme ba namijin aure? Gansansan da ita. Sai ma kunga yad da tayi kwailin taci uwar sabada na bilicin."
Lawuri ta kece da dariya. Suka hada hannu da Marka. Ji ka ke raf sun tafa.
"Bangan su ba."
"Kayya rahanatu ni kin ishe ni da maganar gayyar tsiya wallahi. Yo ta yazasu zo? Suna bakin ciki da hassada. Ile kuma wahidin din ta sani. Don an gayan ta sanda tazo nan din kwana ki "
Matar ta jinjina kai kafin tace,
"To Allah ya kyauta ."
"Salama alaikum " Najib yayi sallama ya shigo cikin gidan hannun sa dauke da rake yana sha
Matan wajen suka amsa. Ya hanga ya gano Marka. Daman wajen ta aka aiko sa,
"Marka "
"Ya akai? Ba abinci. Ka shigo kana rurruntuma kai. "
Murmushi yayi kawai kafin yace,
"Na'Ateeku ne ya ke kiran ki awaje."
Mikewa tayi da sauri. Zanin ta saura kadan ya fadi don sauri dakyar ta gyara ta fice wajen tana dashare baki tamkar gonar auduga
"Na'Ateeku..."
Zubewa yayi a kàsa duk kuwa da shekarun sa.
"Barka da yammaci Markan mu."
"Barkan mu dai Na'Ateeku. Iyalin kalau?"
"Alhamdulillah wallahi " ya amsata yana sosa keya.
"Masha Allah "
"Allah ya sanya alkhairi zainabu na zo miki."
"Allah sarki Na'Ateeku. Godia na ke. Allah ya saka da alkhairi."
"Amin..." Ya dan sake sosa keyar sa.
"Ina sauraron ka Na'Ateeku."
"Marka .... Dama nace.... Zan... Zan zo da kai na. Domin zuwa da kai yafu sako. Dan ba na so abun yadauki lokaci ne."
Marka ta sake gyara tsayuwar da tayi kafin tace,
"Eh .. Ina sauraron ka Na'Ateeku. Allah sa muji alkhairi."
"Amin. Alkhairi ne ya kawo ni ....Magana ce akan zahara'u yar wajen ki "
"To... Ina sauraron ka dai Na'Ateeku. "
"Wato hakika banji dadin abunda Adamushe yayi mata ba. Ga yara ga wanda aka yaye ko?"
"Kwarai... Ai bashi da mutunci. Kakan sa ma haka ya dinga shikan matan sa. Gado ne."
"To Allah shi kyauta ..."
"Aamin Na'Ateeku."
Ya sake sauke zuciya ya cigaba da cewa,
"Wato idan ba damuwa... Ni ina bidar auren ta. S"
Bai karasa ba Marka ta dora hannu a hanci ta saki guda
"Na'Ateeku dagaske kunnuwa na suke jiye mun?"
"Kwarai Marka ... Ta