Showing 96001 words to 99000 words out of 123508 words

Chapter 33 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

543

wajanta nake, kuma Alhamdulillahi sai da na samu fiye da abinda baki san matan aure na yiwa mazajensu ba. Ke kuma ki zauna a haka kicigaba da chatting dinki har zuwa randa zamuga ribar yinsa." Yana kaiwa nan ya juya zai bar mata parlorn yaji tana cewa.

"Ai dama na gane cewa ba tun yau ta fara baka abinda bana baka ba, ni tunda naji kace ita nasan dama kun dade da mallakar juna a watse, gwarani sai da mukai aure ita kuwa fa? Yanzu na san ragowar abinda ka rage a wajanta shi kake son kwakulewa daga nan sai na fara jin kace zakai wani auran." Habawa Ahlam ta sosa

masa zuciya, metake nufi da kalamanta? Zarginsa takeyi kome? Lallai dole ya takawa Ahlam burki akan tunaninta. Juyowa yai yana sake kallanta, tana zaune a inda take tana murmushi tare da danna waya.

"Koma dai menene kekika janyo, idan ma iskancin nayi tabbas yayi min dadi tunda gashi har na aureta ta zama kishiyarki sai ki gaya min dame kika fita? Kuma bari kiji na gaya miki na dena wani lallabaki akan kiyi hakuri, kar Allah yasa ki hakura. Waheedah kuma matatace wacce tasan darajar aure tasan darajar miji, ba irinki ba da chatting kawai kika bawa duk wani lokaci naki." Yana kaiwa nan yai tafiyarsa, kalamansa kuma sun konawa Ahlam rai da zuciyarta. Afusace ta mike tabiyo bayansa, kofar ta murda taji an rufe ranta na suya take fadin.

"Wallahi karyane Waheedah ba zata taba zama matsayi irin nawa ba, Waheedah yar talakawace wacce bata san komai ba sai wahala da kauyanci. Kuma kaima nasan ka aureta ne kawai dan tazo tayi maka bauta tunda kasan ita din yar wahalace."

Kafa tasa ta buga masa kofar dakin sannan ta juya tana masifa da bala'i, ji take kamar ta tsaga kofar ta shiga cikin dakin tai masa shegen duka ko zuciyarta zatai sanyi.

Zayn kuwa yana shiga kamar yasan zata iya biyoshi ya murzawa kofar mukulli, briefcase dinshi ya ajiye akan madubi shi kuma ya karasa wajan gado, a hankali ya fada saman shi tare da rintsa idanuwa, tunani ya fada yana jin zuciyarsa tamkar wuta, sam baya cikin jin dadi saboda ta ko'ina baya samun farin ciki, duk inda yake babu farin ciki gaba kura baya sayaki, dama haka mata suke? Waheedah dan yana santa sai gwarashi takeyi yadda taga dama? Ahlam na gwarasa cikin borin kunyarta da babu gaskiya a ciki, yanzu ya zai yi? Ta ina zai fara yiwa Ahlam bayanin cewa sai ta yadda sannan Waheedah zata amince masa? Gashi yanzu yazo ya sake damula komai.

"Ya Allah." Ya furta yana rintsa idanuwa. Yana jin muryar Ahlam harta gama ta bar wajan, kansa ne yaji yana masa wani irin nauyi kamar an dora masa dala da gauran dutse.

"My love.." Ya fada yana hango hotan Waheedah acikin idanuwansa. Maimakon yaji soyayyarta na raguwa a'a sai yaji ana sake ninka masa. Wayarsa ya zaro daga cikin aljihu ya lalibo sunanta, kamar ya kira sai kuma ya fasa besani ba ko tana tare da su Maa. Online ya hau ko zai ganta yana kunnawa yaga Ahlam is online, yaja dan siririn tsaki, shi kam be taba hawa yaga bata kai ba saboda tsabar jarabar santa da chatting. Contact din Waheedah ya duba yaga ta dade bata hawa WhatsApp din, ya dan duba abinda zai iya dubawa ya sauka tare da kifa kansa akan pillow....

Zayn yayi iya yinsa wajan ganin bacci yazo masa amman ya kasa, banda juyi akan gadon babu abinda yakeyi. Yadda zai yiwa Ahlam magana akan ta amince Waheedah ta zama mallakinsa ita kawai yake nema, ya rasa dalilin da yasa Waheedah ta bashi wannan sharadin, gashi daga shigowarsa ya batawa Ahlam din rai. Juyawa ya sakeyi yana mai rintsa idanuwa tare da tunanin anya zai biyewa Waheedah? Gaskiya ba zai biye mata ba dan ya gaji da zama babu ita a tare dashi, idan kuma ba so takeyi zuciyarsa ta samu matsala ba akan soyayyarta. A ranar haka Zayn ya karaci juyi a gado, gashi ko aikin office da ya taho dashi gida kasa yi yai bare ya rage.

Tashi yai ya gabatar da sallar nafila, ya dade yana addu'o'insa kafin ya tashi, gado ya koma tare da janyo wani english novel yana karantawa, sai dai tunaninsa gabaki daya yana kan matarsa abar so da kaunarsa sannan kuma FARIN CIKIN ZUCIYAR sa. Bashi da wani buri irin yaga itama ta sakko daga dokin tsoran Ahlam da takeyi, wanda yake neman ya hanata ciki umarnin ubangiji. Har aka kira assalatu bai rintsa ba haka ya tashi ya sake yin sabuwar alwala ya fito ya tafi masallaci. Bayan sunyi sallah ya dawo yaje ya yiwa Ahlam knocking dan ta tashi itama tayi, bai jira ta bude ba ya nufi bedroom dinsa ya fara shirin fita.

Yasan dama ba wani breakfast zai samu ba a wajanta hakan yasa yana gama wanka yasa kayansa yai duk abinda ya zame masa al'ada ya feshe jikinsa da turaruka na musamman, fitowa yai kafadarsa rataye da briefcase yana danna waya. Ahlam ya gani tsaye a bakin kofar dakinta tayi kicin-kicin da ita Zayn ya kauda fuska yana nufa hanyar fita yaji tana cewa.

"Za'a fita inda aka saba zuwa?"

Ya dan yi murmushi, kallanta yai yana lumshe idanuwa yace.

"Kwarai da gaske kina da sautu ne?"

Rai a bace take yi masa wani kallo mai nuna bacin rai Ahlam Ι—in ke cewa.

"Wallahi Zayn ka badani, ni wallahi kacuceni ina jin bakin cikin irin yarinyar da zaka auro min matsayin kishiya sai Waheedah, duk yan matan dake fadin jihar Kano. Ina gaya maka ni bazan iya kishi da yarinyar nan ba wacce a gabana ta fara sanya bra, ta fara sanya kaya na alfarma, a gabana ta fara iya sanya lipstick ace kuma ita zaka kawo min a matsayin wacce zan hada miji da ita, tabbas ka yaudareni."

Zayn ya dan lashi kasan lips din shi tare da sauke numfashi yana murda handle zai fita yake cewa.

"Dama bake na aurowa Waheedah ba, na aureta ne saboda ina santa, itace zata iya bani duk wani hakki na aure ba wai kyal-kyal banza ba."

Kamar yasan zataji haushi, yana gama magana yai saurin ficewa ya rufe kofar da key din hannunsa. Yana jinta sai murda kofar take yaje ya bude mota wace tuni an gama wanketa sai sheki takeyi tana walwali. Briefcase din ya ajiye a back seat tare da jan numfashi yana girgiza kai, motar ya kunna ya fice daga gidan gaba daya. Kai tsaye gidan Maa ya wuce, a waje yai parking saboda yana son fitowa ya tafi aiki. Yana shiga mai gadi ya gaishe dashi Zayn ya amsa cikin sakin fuska ya shiga sashen Maa. A parlor ya tarar dasu Waheedah kuma tana kitchen ya gaishe da Maa kannansa suka gaishe shi.

Idanunsa na hanyar stairs yana son zuwa wajanta kawai yaji motsi ta bayansa, be juya ba har ta karaso parlorn rike da wani jug mai kyau ta ajiye a kan center table. Ido ya zuba mata yana kare mata kallo tana sanye da hijab har kasa. Bata bari sun hada ido ba ta durkusa tana gaishe shi.

"Ina kwana Ya Za.."

Ta kasa karasawa saboda kunya, Zayn ya cije lips. Muryarta yaji tana yiwa Maa magana.

"Maa an kammala kawo komai bari naje daki zan watsa ruwa."

Cikin fara'a Maa ta ce.

"Shikenan Waheedah idan kin dawo sai kiyi breakfast din."

Da sauri Waheedah ta wuce Zayn yana bin ta da kallo har ya dena ganinta. Kunun gyada ne Maa ta zuba masa dan tasan beci a gidansa ba, da awara wacce tayi irin ruwa-ruwan nan tasha eggs akai mata wata hadaddiyar sauce din kwai ga yankakkun veggies a kai. Ci ya farayi amman duk hankalinsa yana kan yadda zai shiga gurin matarsa, Maa ta mike da sauri tana cewa.

"Oh na manta Abiey yasani abu, kai Allah ya kyauta min yanzu abubuwa saurin mantasu nake." Tana fada tana wucewa wajan maigidan.

Zayn ya dire cup din da sauri ya haye wajan Waheedah. Da sauri ta juya jin yadda aka rufe kofar, ganin Zayn yasa ta ware idanuwa, batayi aune ba kawai ta ganshi a gabanta, hannu yasa yaja mata hanci ganin yadda ta kame a guri guda yana cewa.

"Zuwa nai ki gaidani."

"Gaisuwa kuma? Nafa gaida kai a parlor." Tayi maganar tana kauda fuska.

"Wata nake so kiyi min." Ya fada yana sake matsawa kusa da ita.

"Please Ya Zayn bana so, shin matarka ta amince da aure na da kayi?"

Zayn ya lumshe idanuwa yana tuno yadda ta kasance tsakanin shi da Ahlam. A hankali ya bude ido yana kallan Waheedah da idanunsa masu cike da zallar kaunarta. Hannu yakai zai kama nata tai saurin jan baya.

"Please Ya Zayn ka tafi wajan aikinka."

Rintsa ido yai yana jin wani irin babu dadi a ransa, ya gyada kai ba tare da ya iya cewa komai ba ya bar mata dakin. Ko Maa be yiwa sallama ba yabar gidan, mota ya shiga tare da figarta yana mamakin lamari irin na mace.

Koda ya dawo gida ya wuce saboda yana san ya bawa Waheedah fili karyaje ya sake sanya tsanarsa a zuciyarta. Ahlam ma bata san ya shigo gidan ba saboda be nemeta ba tana cikin daki tana bacci.

Zayn kam mazewa kawai yake yi na rashin sanya Waheedah a idanunsa yanzu. Yana kwance ya tasa laptop a gaba, shi beyi aikin ba sannan ya kasa rufewa. Har akai sallar isha yana jin zuciyarsa tana tunzura shi akan zuwa gidan Maa amman yana daurewa. A ranar dai shima be samu wani bacci mai dadi ba, ya bari kawai da safe dole zaije gidan dan ba zai cuci kansa ba akan sharadin da ta bashi......

_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_


_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β Β  πŸ’ž
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:62_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._

______

Β  *A* hankali ya fara zura fuskar sa ya leka cikin dakin. Kafin gangar jikin sa ta biyo baya.

Gabansa na tsananta bugu. Hamdala ya saki ganin babu kowa acikin dakin. Haka ma parlorn kasan. Dan haka ya murza key ya koma bakin gadon ya zauna

Motsin ruwan dake zuba a bandaki ne ya tabbatar masa tana ciki. Don haka ya gyara zaman sa. Ya janyo wayar sa a aljihu ya shiga dannawa.

Bayan ta kammala wankan. Ta sake tara ruwa ta zuba masa after bath khumrah na kamfamin turaren yerwa incense and more. Ta dauraye jikin ta da shi. Take jikinta ya fara kamshi sosai.

Ta daura bathrobe a jikinta ta fito daga cikin bandaki tana adduar fitowa daga cikin bandaki.

Kai tsaye ta wuce wajen mirror ta zauna bayan ta dauki wata kulaccam ta kamfanin turaren yerwa incense and more . Ta shafe jikin ta da shi. Lungu da sako na bayan kunnen ta da kasan maman ta da cinyoyin ta.

Zayn ya zuba mata idanu. Sam batasan yana dakin ba. Sai data tsiyayi khumra a tafun hannunta tana shafawa a jikinta. Tana daga idanuwa ta sauke akan mirror ta hango shi ya mayar da nutsuwar sa da tattaro hankalin kansa baki daya ya dora akan ta. Ta janyo glass ta zura don tabbatarwa.

Wani abu ya taso ya tokare mata a makoshin ta. Ta janyo hijabin da ke sakale a gefe ta zura.

Dan murmushi ya bi ta da shi yana mai lashe kasan leben sa.

Drawer ta bude ta dakko kayanta ta koma can karshen closet ta zura su. Ta zura hijabin ta ta rataya Jakarta a kafada.

"Ina kwana?" Ta gayshe shi kanta a gefe.

Ya mike ya isa inda take a tsaye ya riko ta. Ta shiga zillewa. Amman da ke karfin ba daya ba ne... Sai ya sake tukwikwiye ta . Sam ta kasa kwatar kan ta.

"Makaranta.....?" Ya tambayeta cikin muryar rada. Ta hanyar dora bakin sa akan kofar kunnenta .

"Uhmmmm" Tace dashi, Domin baki daya ya kashe mata jiki. Ta kasa tabuka komai.

Janyota yayi suka zauna a bakin gadon. Ya yinda ya riko hannuwanta ya saka acikin nasa. Idanuwan sa na sauke akan ta. Ta kasa hada idanu dashi saboda kwarjini da girman sa daya kamata..

"Waheedah....." Ya kira sunanta cikin kwarewa da jan haruffan karshe.

"Na'am..."

"Bazan gushe ba fa-ce na cigaba da baki hakuri .... Ko kinsan Dawood?"

Yana karasa fadar sunan Dawood gabanta ya yanke ya fadi. Daman jikin ta ya soma raya mata wani abu game da chatting dinsu da Dawood...

"Kinyi shiru .... "

"Zan makara ne a school.."

Ya dan matse hannunta da har sai da tayi yar kara. Ya kuma saka hannu ya lakuto kumatun ta. Kafin yace,

"Saura 1 hour 30 minutes ku shiga lectures... Ai inada timetable dinku. Dan Allah kiban hankalin ki nan. Ki auna zance na. Tabbas ni me lefi ne awajen ki Waheedah... Nayi miki lefuka da dama wadanda na ke neman gafara awajen ki a koda yaushe. Amman this particular one da nake jajantawa Waheedah ki yafe mun. Soyayyarki ce ta jawo haka. Na dade zuciyata na neman begen kaunar ki. Na kasa sukuni. Waheedah kece FARIN CIKIN ZUCIYA tah.. kaunar da nake miki Waheedah dadaddiya ce,.. Har hankali na ya gushe na nemi samun soyayyar ki ta hanyar fito miki a zummar ni.... Ni....ne Dawood." Yana karasa fada ya runtse idanun sa. Hawaye suka shiga kwarara daga idanun sa...

Ya zare ta daga jikin sa. Ya zube gwiwoyin sa a kΓ sa ya durkusa agabanta. Ya janyo hannuwanta duka biyun ya rike .

Ahankali cikin murya tamkar ana busa sarewa. Cikin wani salo ya shiga cewa,

"Soyayya na iya chanja mutum, domin ita soyayya ba'a ganin ta balle a koreta ko a hana ta shiga ZUCIYA. Ba'a cewa soyayyah ga yadda ake so, sai-dai kayi yadda take so. Ba'a shiryawa soyayya, ko babu shiri
Idan tazo kamar mutuwa haka zata shiga ZUCIYAr mutum. Duk wanda yayi so dan Allah to shine keda riba, Waheedah soyayyar ki ce ta dasar mun da FARIN CIKI har tayi tsiro ta yi reshe a cikin ZUCIYA tah .. Kwarjini da fargabar ki suka hana ni fitowa na nuna miki ni ke kaunar ki... Hakan yasa na fito da dabarar shiga zuciyar ki da sunan Dawood. Tabbas nayi babban lefi agareki..... Kauna ce ta haddasa hakan ba komai ba. My prayers were answered the day that I met you. Tun kallon farkon da nayi miki..."

Ya karasa fada yana murza hannunta. Hade da sunkuyawa ya sumbaci tafukan hannayen nata. Dai dai lokacin da ta daga idanu ta sauke akan fuskar sa. Ta ke ta tuno ranar da suka taba haduwa sukayi gware.. Girar sa da suke cike da gashin da suka kusa hadewa saboda yalwar su...

Ya sake daga kansa ya sauke akan idanun ta. Ta janye nata da sauri. Ya cigaba da cewa,

"Waheedah .. You are a blessing in my life, and I'm so lucky to call you my partner for the rest of our lives. Your smile is my everything. Cikin soyayyar ki babu sirki, na gani kuma na gamsu kuma na tabbatar da ke me kauna tace ta... Ko bakya mun kallon miji kina mun kallon dan uwa. Waheedah, hakika, ki sani, ni bazan taba son wata ya mace wacce bake ba, domin zuciyata bazata taba jindadin zama da wata ya sama dake ba, duk wani jin dadin duniya bai damen ba indai babu ke...."

Kalaman sa suka sata dariya. Wasu mazan iyayen karya, Sam ba ta ido.. Ta yamutsa fuska tana mai sake dunkufar da kanta gefe... Kafin tace da shi,

"Ni kuma? Ai na dauka ba zaka iya soyayyah da karamar yarinya ba .. Renon ta zakai ko? Domin karamar yarinya ai ba matar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login