Showing 90001 words to 93000 words out of 123508 words
Abunda takardar ta kunsa shine, Assalamu alaikum bayan gaisuwa da kuma fatan alkhairi ga zainabu a gaba. Ni Bashari na saki zainabu saki 3. Allah ya gyara mata halayen da zasu sauya ta ta dawo ta kwarai. Idan ta gyaru Allah ya dube ta ya bata miji nagari amin. Ina karasa karantawa inna saadatu ta yanke jiki ta fadi. Hakama zainabu data zube a kΓ sa tana shure shure kamar sabuwar tabi. Marka kuwa ta sankare a tsaye... Gidah dai ya hautsine... Sai awajen raude nake jin wai zainabun ashe sau 3 . Daniel likita na cire mata ciki. Wai an gaggays masa bai yadda ba. Sai da yaje aka tabbatar masa... "
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun..... Ke duniya!!" Gwaggo haule ta fada cikin mamaki da kambama zancen da Basira ta fada
"SubhanAllahi.. SubhanAllah." Gwaggo Hadiza ta shiga maimaitawa.
Baki daya jikin su yayi sanyi. Cikin haka sai ga shigowar su Haj Aisha abokiyar zaman Haj Hameedah mahaifiyar su Zayn.Da Haj Hameedah Bayan ta kuma su Nadra ne da wasu maza ciki harda Nassem dauke da akwatuna manya manya masu sheki. Irin customized boxes dinnan masu hashtag na #ItWasAlwaysYou:Wπ
Da sauran dangin su carpets, Kayan shayi, Gishi da sugar buhu da sauran kayan masarufi ciki harda su indomie da cartons na kayan bacci. Umma Hadiza ta mike da sauri ta shige daki. Ya yinda gwaggo haule ta mayar da hijabi daman tana da alwala ta dubi gabas ta zuba sujjadar godia ga Allah. Hawayen farin ciki daya na bin daya
Najan Isubu ta tare da fara'a da wasa da dariya. Ya yin da Basira da fannah suka shimfida tabarmu baki daya suka zazzauna akai.
Daga nan aka shiga gayshe gayshen juna. Fannah da Basira sai murna suke suna bin kayan auren Waheedahn da kallo. Kaya ne wanda alkalami yayi kadan wajen zayyano tsaruwar su. Komai na kayan me tsada ne da kuma daraja.
"Kaman Hadiza na gani ta tashi ko?" Haj Hameedah ta tambaya tana dariya.
"Itace... Kunya take ji."
"Kunya kuma? Ai an zama daya. Dabi'ar hausawa ce ai wannan na iyaye su buya ranar karbar kayan auren su. Bayan rana ce ta farin ciki ."
"Gaskiya kam." Gwaggo haule ta amsa ta tana dariya.
Da kanta ta mike ta kirawo Umma Hadiza da ke cikin daki. Umman ta fito tana sunkuyar da kai. Ta tsugunna suka gaysa baki dayan su.
Haj Hameedah sai tsokanar ta take. Fanna da Basira suka shiga dakko kayayyakin da aka tanadar wa zuwan su Haj Hameedah. Dai dai iya karfin su. Da cartons na ruwa da lemuka.
Haj Hameedah bata ji dadin kashe kudin da Umma Hadiza tayi ba . Na yin toye toyen kaji da su meat pie. Sun karba da hannu biyu. Sannan aka fara bude akwatuna ana bin kayan da kallo
Alokacin Haj Hameedah ke tambayar ko an sanar wa Waheedah wanda aka aura mata? Su Gwaggon suka amsa mata da a'ah... Alokacin da sukayi niyyar fada kuma zazzabi yaci karfin ta don har tasha panadol ta kwanta bacci tun dazu.
Haj Hameedah da kanta ta mike ta shiga daki wajen Waheedah ta tattaba jikin ta zafin ya ragu. Don haka ta dan tashi waheedan. Dakyar ta iya gayshe ta saboda yadda kanta ke sara mata. Ta dauke MacLean da brush dinta ta nufi bandaki tayo brush. Ta gayshe da mutanen tsakar gidan tana bin su su da kayan da kallon madaukakin mamaki.
Ta koma daki ta sake gayshe da Haj Hameedah . Sannan ta zauna tana matsa yatsun hannuwan ta. Maa ta leka da kanta ta kira su Gwaggo da Umma Hadiza.
Tsakar gidah ya zama sai su Najan Isubu dake kirga kaya. Ta dora dan karamun kit din da sakar gold ke ciki dauke da zobuna da awawwaraye manya manya...
"Waheedah ya jikin naki?"
"Da sauki Maa."
"Akwai inda ke miki ciwo?"
"Babu sai kai na kawai da ke sarawa kadan kadan.."
"Masha Allahu. Sannu kinji?"
"Yauwa.. Maa"
"Waheedah Ina son ki bamu aron hankalin ki. Ki kuma tsayar da shi waje daya. Ki kuma ajiye zantukan da zamuyi a mizanin hankali . Kinji?"
"Insha Allah Maa."
"Ki sani har gaban abadan ba zamu miki zabi da zai cutar da ke ba. Ina nufin ba zamu zaba miki abokin zama wanda ba nagari ba ne. A har kullum adduoin akan ki basa wuce Allah ya hada ki da abokin zama na gari. Inda zaki je ki huta wani naki ya huta. Ki samu nutsuwar kwanciyar hankali. Kina fahimta?"
"Eh..."
"A baya kinsan mahaifin ki ya karbi kudin auren wanda ke neman ki amatsayin abokiyar rayuwa ta aure ko?"
"Eh...."
"Bakisan waye ba kika amince ko? Saboda biyayyar iyaye da amincewa da zabin su da yafi son rai ko?"
"Eh Maa " Ta amsa gabanta na tsananta bugawa ..
"Tohmmm... A yau an daura aure ke da yan uwan ki ku uku idan har ban manta ba.... Ko Hadiza?"
Waheedah da sauri ta daga kai ta dubi Haj Hameedah. Tabbas tasan an karbu kudin auren ta don har ciwo tayi amman ta hakura ta amince . Ko dan farin cikin mahaifiyar ta. Amman bata taba zaton da ita aka hada aka aurar yau ba...
"Kiyi hakuri Waheedah..." Umma Hadiza ta fada kanta a gefe.
Waheedah gabanta ya sake bugawa. Ta mayar da kallon ta kan Maa data daga mata kai ta sauke itama,
"Yadda kika bi umarnin mahaifan ki. Kikayi hakuri da sa hannu biyu ki ka karbi zabin da suka yi miki. Ina fatan Allah yasa wannan shine matakin farko na shiga sabuwar rayuwar ki mai tattare da FARHATAL QALB!! (FARIN CIKIN ZUCIYA...) Daga yau kin dinga samun FARIN CIKI a ZUCIYAr ki har ya zuwa ranar da zaki koma ga mahaliccin ki Waheeda.. Allah ya saka miki da alkhairi ya hade kawunan ku. Amin"
Hawaye ne suka shiga reto a kyakkyawar fuskar Waheedah masu dumi. Hakika dukkanin wanda ke jiyo sautin kukan Waheedah dole zuciyar sa ta karaya. Da tausayi matuka ga dukkanin wanda ya samu kansa a halin da Waheedah ke ciki. Hawaye ne mai dauke da labarai masu tsuma zuciya acikin sa...
Wanda take so da kauna daban ... An raba su ta hanyar auren dolen da akayi mata da wanda batasan awacce nahiyar yake ba. Ta karbi kaddarar ta da hannu dubu duk kuwa da bata da tabbacin hannun da zata faada. Ta samu FARHATAL QALB da Dawood wanda suka yiwa junan su alkawarin aure don cigaba da gina soyayyar da suka fara... Duk kuwa da bata haduwa da shi ba tun bayan bikin su Zayn amman kaunar sa tayi tasiri a zuciyar ta alokacin da suka fara magana ta WhatsApp har suka dai-daita kan su. (Garaπ€£)
Ta saka kasan hijabin ta ta share hawayen da ke tsiyaya daga fuskar ta. Sai shessheka kawai da take yi.
"Kiyi hakuri Umma. Na kasa tsayar da hawayen ne" Ta fada ahankali don kada ta raunata ran mahaifiyar ta. Zatayi zaman auren ne kawai saboda farin ciki ya wanzu a zuciyar mahaifiyar ta ta dama sauran yan uwa da masoyan su
"Ki yafe ni Waheedah. Ki yafe mana baki daya kinji?" Umma Hadizan ta fada itama muryar ta a raunace.
"Ba abunda kuka mun Umma.... Allah ya yafe mana baki daya."
"Amin Allah ya miki albarka. Allah ya saka miki da mafificin alkhairi. Allah ya shiga lamuran ki baki daya."
"Amin Umma."
Haj Hameedah ta janyo Waheedah jikin ta tana mai shafa bayan ta. Har cikin magudanar jininta take jin kaunar Waheedah. Can ta nisa kafin tace,
"Waheedah..."
"Naam Maa."
"Kiyi hakuri da abunda labbana zasu furta...Don bamuyi wannan hadi dan munantawa rayuwar ki ba."
"Tohm Umma... Au Maa "
"Zayn shine wanda aka daura miki aure da shi yau. Kinji Waheedah.."
Ai baki daya.... Ji da ganin ta ne suka dauke na yan wasu dakikai ta zama tamkar mutum mutumi....
#DESTINED LOVE...
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
πππππππ
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
Β Β Β Β Β Β Β Β Β Β Β π
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
______
_PG:60_
"Kinyi shiru Waheedah.... " Cewar Haj Hameedah. Ta dan jijjiga waheedan.
Umma Hadiza ta sake dukar da kanta a kΓ sa. Tausayin tilon yar ta ta mace ya kamata kwarai matuka
"Waheedah... Diyar albarka." Gwaggo haule ta fada itama gabanta na harbawa.
Waheedah ta daga kai. Ta sauke numfashi da kyar tana jijjiga kanta da sauri
"Menene Waheedah?" Maa ta sake tambayar ta cikin kulawa.
"Maa, Umma, Gwaggo. Kuyi hakuri amman ba zan iya zaman aure da Ya Zayn ba."
"Meyasa Waheedah... Why?" Maa ta tambaye ta cikin fargaba.
"Bar cewa haka Waheedah.... Kinji?" Cewar Gwaggo haule.
"Ya Zayn tamkar marigayi Ya Kamal na dauke shi. Na dauke shi tamkar wanda muka fito ciki daya. Yaya Ahlam itama tamkar Yaya ce awaje na. Ta dauke ni kamar kanwar ta da suka fito ciki daya.... Ya zata ji idan har taji ni da ya Zayn an daura mana aure? Zata dauka naci amanar ta ne. Dan Allah kuyi hakuri amman ba zan iya zaman aure da ya Zayn ba. Na amince a auramun koma wanene amman banda ya Zayn.. Dan Allah...Zuciyata zugi ta ke Maa. Kasan zuciya ta tamkar zai ballo saboda radadi.."
"Dan Allah Waheedah ki bar cewa haka kinji? Wannan aure Allah ne ya hada. Da kuma rokon da Zayn ya dukufa yanayi a sujjada har Allah ya karbi adduoin sa. Zayn ya dade yana dauke da kaunar ki a zuciyar sa Waheedah. Ke ce FARIN CIKIN ZUCIYAr Zayn ... Yana kaunar ki tun kafin a daura auren su da Ahlam Waheedah. Zan iya tabbatar miki cewar kece first love din Zayn kamar yarda ya sanar da mu. Ya fara kaunar ki tun kafin ki zama yadda kike a yanzu. Maana tun kina karama... Ki sani auren ku da Zayn ba kici amanar Ahlam ba. Hakama Zayn bai ci amanar Ahlam ba. Zaki fi dukkanin mu masaniyar komai saboda kece kike zaune a tare dasu... Kinsan irin zaman da suke yi. Wanda maslahar sa aure ce. Na karkare miki zance har satin bikin Zayn bai dai na roko na a fasa auren nan ba don yanada wacce zuciyar sa ke muradin kauna., Bamu amince da auren ki da Zayn ba don mu muzanta miki. ko dan muci amanar ki mu kuma tauye miki hakki.. No! Auren ki da Zayn alheri ne. Auren ki da Zayn zukata da yawa sunyi farin ciki. Auren ki da Zayn abubuwa da yawa zasu gyaru. Domin ke din wani haske ce a tattare da rayuwar mu baki daya Waheedah. Kaunar da na ke miki ta sa na amince da auren ku. Na kuma yi farin ciki marar misaltuwa da kasancewar hakan Waheedah.. Ki dau wannan auren a matsayin taki kaddarar. Ki kuma yafe mana da zartar da hukuncin auren ku batare da an shawarce ki ba. Kauna ce ta kawo hakan.., Idan kuma kina kan bakan ki na rabuwar ku... Ba zan shiga hakkin ki ba. Zan samu Zayn ya sawwake miki a yau ba sai an ja da nisa ba. Kinji Waheedah? Kiyi hakuri bazan takura ki ba wallahi. Wannan auren ba zai ruguza zumuncin mu da ke ba. Zaa warware shi da yardar Allah.... Bar kuka."
Haj Hameedah ta karasa fada muryarta na rawa. Yayin da itama hawayen ke tsiyaya a fuskar ta.
Gwaggo haule da Umma Hadiza suka shiga basu hakuri duka. Haj Hameedah ta zame jikin ta daga na waheedah ahankali ta mike. Soro ta nufa ta kira Zayn a waya. Ta sheda masa dukkanin yadda sukayi da Waheedah. Don shi ma sai a satin daurin auren ake sanar masa da na su zaa hada. Ya yita FARIN CIKI yana azumin godia ga Allah na gwarzon sa'ar samun mallakar Waheedan .
Maa ta tilasta masa da lallai yazo wajen waheedan ya sawwake mata tunda dai ta tsaya akan bakan ta. Idan kuma ta amince to yasanar da ita yadda suka tsayar da matsaya.
Ko da Haj Hameedah ta fita daga dakin. Gwaggo haule ta shiga tausasar Waheedah. Amman sam waheedan ta ki bada kai sai ma ambaliyar hawaye da ta ke ta zubarwa. Fuskar Ahlam kawai take hangowa .. Gefe daya kuma ta Zayn da ko a baya ranar bikin sa yake sanarwa Dawood kan meze yi da Waheedah yar ficika da ba budurwa ba ce bata isa aure ba. Kuma a yanzu shi aka bata a matsayin miji? Ta girgiza kai kawai tana cije lebe tare da sake kyakkyabewa da wani sabon kukan.
Nadra ta shiga dakin. Su gwaggo haule suka basu waje. Nadran ta shiga bawa waheedan shawarwari duk kuwa da ba sauraron ta take ba kuka take mai fitar da sauti ahankali. Duk da haka Nadra bata fasa ba sai da ta karasa maganganun ta tukun sannan ta shiga tsokanar waheedan har tana mintsinin ta.
"Bakiga customized boxes dinki ba. Harda hashtag na #ItWasAlwaysYou:Wπ? Ni dai daman na san dan kumbure kumburen da Akiey yakeyi idan ya ganki duk kauna ce. Ya yita saki aiki duk wayon ya kare miki kallo ne. Shi kadai yasan labarin da ke cikin zuciyar sa . Ashe dai Waheedah itace FATHATAL-QALBin Ya Zayn.. Sai yanzu na kara amincewa da hashtag dinnan na It was always you Waheedah... Kaunar ki a zuciyar sa ta dade tana tsumuwa ke din ce always and forever dinsa. Bai taba soyayya ba sai akan ki. Ashe yar mutan shurah ce ta sace zuciyar Yayan mu har ya kasa hakuri sai da ya mallaketa? Ina muku fatan alkhairi. our newest sister in-law... Aunty Waheedah.... Mrs Zayn Adams Nasser. U r highly welcome to the Adams family... Allahumma bareek " Tana karasa fada ta sumbaci kan waheedan ta mike bayan ta mata sallama ta fice daga dakin
Tunda ta fara magana har ta karasa Waheedah bata kulata ba. Tana dai sauraron duk wata kalma data ambata.
Tana jiyo sanda suka karasa wasa da dariyar su. Kafin daga bisani su tashi su tafi . Fannah da Basira suka bi su da kayan makulashen da suka tanadar musu. Da dan tukwicin da suka bayar a matsayin su na marasa shi.
Ko bayan sun musu rakiya sun dawo. Akan Waheedah suka taru suna bata baki. Banda Umma Hadiza da ta zauna agefe kawai tana canza channel din yar rediyon da ke hannun ta.
Da suka takura mata da magana kuka ta fashe da shi. Daga karshe ma ta bi su fannah da Basira gidan su wajen Deluwa dubo yaran kamar yadda Gwaggo haule tace. Suna zuwa kuwa Waheedah adan guntun ilimin ta take sanar da su Basira ko ciwon idanun jaririyar dayar anophthalmia/microphthalmia ne?
Daga baya kuma su Gwaggon suka kai kayan lefen gidan wajen Marka. Inna Sa'adatu na asibiti bata farfado ba Ya yin da zainabu ke gadon asibiti itama batasan wanda ke kanta ba. Marka kuwa tamkar sabuwar tabi. Don kayan lefen da aka kawo mata tagani ma zugii su ka karawa zuciyar ta. Ta shiga kokawa tana bubbuga kirji. Sai hararar kayan take.
Ya yin da makota na kusa da na nesa suka debo kafafuwa don ganewa idanun su akwatunan shake da lefen Waheedah. Kaf ko a tarihi babu wanda aka taba kawowa kaya himili guda irin Waheedah. Lalle duk mai hakuri zai ci riba watan watarana.
Saboda tsabar bakin mutane. Kit da gwalagwalen ke ciki Najan Isubu kasa fitowa tayi da su. Kar abi dare a sace su tas. Ko bakuna su tsige auren . Masoya sun sanya albarka da fatan zaman lapia tsakanin Waheedah da mijin nata.
Sam marka batasan dan masu kudi Waheedah zata aura ba. Da bata amince da auren su ba. Ta hararo lefen da wutsiyar idanun ta . Hade da saka yatsanta a baka ta gartsana shi cikin tsantsar hassada da bakin ciki. Kasa jurewa tayi ta koma cikin dakin ta.
Ko da yan kallon kayan suka kammala gani. Aka mayar da su gidan gwaggo haule. Kafin washegari a mayar da su gidan na The Adams Family don gudun barayin dare masu bin