Showing 3001 words to 6000 words out of 123508 words
yan kanzagi sarkin fadi ba a tambeya ka ba. Bashi ya dawo mun da taliya ta. Dan ubanta ko ina take cin irinta da zata ce ta koshi? "
"Kiyi hakuri marka."
"Kar ki sake bani hakuri. Ki bashi ya dawo da ita. Ko kunci ban yafe ba "
Jin jaka yasa Umma hadiza ta mikawa hamisu farantin, jikinta a sanyaye ta koma gefe ta tsakure tana mai aikawa Waheedah kallon kin kyauta da abinda kikayi.
Najaatu ta miqe zata tafi. Yayinda umma hadiza tabiye mata zata mata rakiya.
"Su marka ni ba'a rabon da ni?"
"Ah haba Najaatu. Zo ga wannan ki danqa kici ai abar marmari ce."
"Wasa nake wallahi. Bari na tafi, Mu kwan lapia "
"Toh Najaatu. "
Zasu saka kai su fuce sai ga shigar malam na lado cikin gidan. Kunnen sa daya ya nana speaker din rediyo ajiki yana sauraro.
Najaatu na ganin sa ta tsaya da fitar don su gaysa.
"Sannu da zuwa Malam." Cewar umma hadiza
"Yauwa .. Ah Malama Naja."
"Na'am malam Na lado. Ina wuni?"
"Lapia kalau Najaatu. Ai rannan mun gaysa da isubu ta wayar gurere."
"Allah sarki. Suna can "
"Wallahi.. toh ya iyali. Komai qalau.?"
"Kalau. Mungode Allah." Cewar Najaatu. Suka tsaya daga soro suna sake zantawa da Hadiza.
"Ahh. Marka yau taliyar kakkaryawa ce abincin rana? Ahh yau zaa sha dabge. Bismillah." Ya shiga nannade hannu riga zai tsoma hannun sa acikin farantin gabanta da take ci. Da sauri marka ta janye farantin tana afka masa harara,
"Matsa. Sahorami mijin sahorama. Da bakasan hakkin iyalin ka ba akan ka. Kazo fankan fankan zaka tsoma hannu aciki tamkar kai ne ka bada kudin abincin. "
"Kiyi hakuri marka. Najajje wurare da dama na rasa aikin yi. Tun safe Ina kofar dakalin gidan mati "
"Shi Matin ba zuciya yayi ba ya fantsama ya nemi na kansa har ya zama abunda ya zama ba yanzu. ? Ammaa saboda mutuwar zuciya kake binsa "
"Ki gafarce ni Markaa "
Tsakanin uwa da da sai Allah. Ta janyo farantin ta saka shi agaban sa. Fuskarta a yamitse tace,
"Sirikin ka ne ya bayar aka kawo."
"Sirikina kuma marka?. Bangane ba "
"Eh miji na samawa yarinyar nan wahidin. Don ba zamu zauna da zagada zagadan yammata ba bayan sun isa auren. Jikokin lawure baki daya ta aurar su "
Shiru malam na lado yayi. Ya ciko hannun sa ya zura taliyar a baka. Sai daya hadiye tukun yace,
"Wanene sirikin ?"
"Na'Ateeku dai. Kuma kasan kaf unguwar nan idan ka tsame gidan mati ba wanda yakai Na'Ateeku samu da zuciyar nema. .”
Naja'atun Isubu dake tsaye a zaure da umma hadiza sai gata a tsakiyar su marka
"Aure fa kikace Marka.? Auren ma kira sa da wanda zaki bawa sai na ateeku . Mutumin da ya haifeta. ? Haba marka..…..
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_
_4 BOOKS 4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[11/23, 9:00 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_FREE PG:4_
××××××
Marka ta 'daga kai sheqeqe ta dubi Najan isubu hade da jan tsaki ta kaikaice kanta gefe.
Domin Marka tana cikin jerin tsofaffin nan masifaffu wanda basa ganin kowa da gashi.
Don kaf cikin sansanin su na manya tsofaffin unguwar shurah ta kere su a rashin mutunci da rashin ganin daraja. Haka takan taka duk wanda ya nemi ya kawo mata wargi. Duk girman shekarun ta wata rana sai an shigaa rabiyar fadañ su da tsofaffi kawayen ta .
"Marka magana nake miki ...." Najan Isubu ta sake cewa da marka. Cikin muryar ban lallashi da neman afuwa.
"Yo ai shiru nayi ki tsara yadda komai zai kasance tunda jikar ki ce. Ai sai yadda kika ce."
Najan Isubu ta dan kakaro yake kawai. Ta juya ta kalli umma hadiza da ke tsugunne daga gefen wata kwalla .
"Haba ni na isa? Ni din gaba da shirme, Ai abunda kika yanke dole abi shi Marka... Kawai dai so nake ki duba zancen Na'Ateeku a mizanin tunani. Sam Na'Ateeku ba tsaran auren Waheedah ba ne marka."
"Sannu. Nace sannu zabiya mai dalilin aure. Ita din wacece da har zaki ce Na'Ateeku ba tsaran aurenta bane iyye? Fin karfin sa tayi? Ko kuwa usuli ta fi sa. Allah na tuba astagfirullah Na'Ateeku kaf unguwar shurah akwai wanda ya ko kamo dan yatsan sa ne a usili? Mutimi dan mutunci da dangi masu dattako. Kar ki manta kakan sa da ya haifi gyatumin sa shine mai unguwar shurah. Sannan mahaifiyar uwa ta sa kakanta kani ne ga dagacin fandau., Sannan kanin sa da suka fito ciki daya chiyaman ne ke kanki kinsani. Sharbacecen kwaltar data miqe sambal ai shi yayi mana. Ya kuma kawo tuqa tuqa (borehole) Da haqa rijiyoyi. Bacin nan shi kansa mai rufin asiri ne. Shago shaqe da kaya na kayan masarufi. Sannan ke kanki kinsan yanada shagon chajin wayoyi da sayar da kati. Ki gayamun tsakanin shi da ita wanene ya kere wani? Na'Ateeku duk yar daya tsayar a unguwar nan yace yana so wallahi auren sa zatayi. Iyayenta Kuma su zuba ruwa a kasa su sha dan farin ciki , Aikin kawai."
Marka ta karasa fada hade da hambale taliyar da ke cikin hannun ta . Najan Isubu ta sauke katuwar ajiyar zuciya. Ta juyar da kanta ta hango Waheedah dake tsaye a bakin kofa hawaye daya na bin daya . Tausayinta ya sake dabaibaye zuciar Naja. Cikin sanyin jiki da muryar roko ta sake cewa da marka,
"Duk abunda kika fada hakan yake Marka, Ban musa ki ba. Na kuma san kauna ce tasa kikeson ki hada auren nasu. Sai dai abunda nakeson cewa shine, Na'Ateeku yayiwa Waheedah girma Marka. Wallahi zaa cuceta idan har aka aura mata shi. Dansa na biyu Hashimu fa satin baya ya kara aure. Mata ta 3. "
"Sai akayi ya ya? Ai dan arziki shi yasan abun arziki. Yadda matan sukayi yawa ai dama kamata yayi maza su ringa aure su , Su cike gurbi. "
Najan Isubu ta sake gyada kai kafin ta zauna daga gefen Marka.
"Marka.... Rayuwar auren daa da yanzu ba daya bane. Tamkar yadda kukayi rayuwar auren ku da tamu wallahi ba daya bane. Hakama yanzu wannan zamanin ba a irin auren nan Marka. Zamani yazo da sauyi."
"Ni fa ban gane abunda kike nufi ba Najaatu. Gwara ma ki dena 'babaatu. Ahto!" Ta karasa hade da nanawa cinyarta duka.
"Abun nufi yanzu zamani ya kara wayar da mu. Ciwukan yanzu a baya baa yi su ba. "
"Uhmm Hu'uhm..." Marka ta numfasa tana gatsine gatsine.
"Allah Marka. Na'Ateeku bakiga yana da yara hudu ba marasa lapia shima.?"
"Bangane ba.. Yo sai me? Ba Allah ne ya doran su ba. Ina ruwan auren su da wahidin ya hadu da gamayyar rashin lapiar yaran sa?."
"Ina nufin Na'Ateeku a dauke zancen ya haifeta da sauran su. Abunda nakeson ce miki shine. Shi ma Na'Ateekun yana dauke da kwayoyin cutar sikila. Kamar dai yadda su Kamalu da Najeeb ke fama da ita."
Marka taja dogon tsaki data saurari karshen zancen Najaatu. Cikin takaici tace,
"Banji ba, Ban kuma gani ba. Karki manta da sherri dan aike ne, Dik inda yaje zai dawowa mai shi... Sannan ni me sunan Malam (Na lado) Bayada wata cuta.. Domin idan da yana da ita da yaran wajen sa'adatu ba sa yi lapia ba. Ita kuwa uhm uhm Hadiza, Da cutar ta tayi guzuri. Aka liqa masa ita ya aure. Ashe lullube maganar cutar jikinta sukayi. ."
"Kayya Marka ki dena cewa haka dan Allah .. Banda ishasshen ilimin da zan buda miki komai yadda yake. Amman Allah ya kai mu sati na sama. Wata kungiyar wayar da kan jamaa kan hanyar da zaa kula kar a fada halin qaqanikayi na ciwon sikila zasuyi taro. Da yardar Allah kuma dukkanin mu zamuje. Saboda har gwajin jini za'a yi ko kanada cutar duk zaa sanar maka. Hakama idan baka da ita."
"Kingama?"
"Kiyi hakuri Marka."
"Baki gama ba kenan. To kici gaba idan kin gama se ki tashi ki koma inda kika fito."
"Kiyi hakuri Marka. Ni kawai so nake ki janye zancen ki..."
"Aure babu fashi..."
"Nalado ka sa baki dan Allah. " Najaatu ta dubi nalado dake gefe yana katsar ruwan dake kasan tukunya na taliya.
"Me zance Naja..?" Ya amsa ta hadi da lashe bayan hannun sa.
"Yanzu ba zaka tausashi zuciyar marka ba ta janye zancen nan? Haba dan Allah."
Malam Nalado yayi shiru bai ce komai ba.
"Aure babu fashi. Yace dama inde zuciyar sa ta aminta da ita. To fa ko kayan daki yace shi zai yi. Ita kadai za a wanke akai. Saboda Allah meya fi wannan karamci? Na'Ateeku kyakkyawa da shi , Sambalele jazur da shi . Kina ganin matansa kowacce da kayanta maya maya. Sunyi 'bundun da su.. wallahi ance ba yunwa agidan sa. Duk sallah sai ya dinkawa matan sa turame maya maya. "
Waheedah dake labe tana sauraron komai. Kasa jurewa tayi. Dan kukan da take rikewa ne ya kufce mata ya shigaa sharara a idanunta. Cikin rawar jiki da baki ta fita tsakar gidan. Ta sukwane agaban Marka tana faman rokonta.
"Dan Allah Marka kiyi hakuri. Ki barni na cigaba da karatu na. So nake na zama ma’aikaciyar lapia Marka. So nake na bawa harkar lapia gudunmawa Marka. Dan Allah kar ki mun aure ki bari na cika burina. " Ta karasa hade da riko kafafun Marka. Hawaye sai dalala yake daga idanunta.
"Matsa kafin na hamb'are ki. Me sunan Malam kana jin maganganun da tsageriyar yarinyar nan take faada....?”
"Laàa. Ke yanzu Waheedah Markan kike gayawa haka?Uhm tab. Lalle. Kokari." Cewar Inna Sa'adatu matar Nalado ta biyu, Mahaifiyar su Zainab da su ke uba d’aya da su waheedah…..
#FARHATAL QALB
#FARIN CIKIN ZUCIYA
#ZAFAFABIYAR2022
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:00 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_LAST FREE PAGE: 5_
_(SHAFIN KARSHE NA KYAUTA!)_
××××××
"Haba Sa'adatu, Wannan ba girman ki ba ne wallahi." Najan Isubu , Ta fadawa Inna Sa'adatu haka.
"Yo ai gaskia ta fada.. Me sunan Malam kana jinta ko kayi kunnen uwar watsi?"
"Kiyi hakuri Marka... Ke waheeda baa ta hakuri." Malam NaLado ya tsawatar wa Waheedah.
Ita dai Umma Hadiza bata ce komai ba. Tayi zugum a gefe kanta a kasa.
"Ummaaa kafaata, Umma kafata. Kafata ummah ..Wayyo, wayyo " Najibu ya shigaa maimaitawa yana mai dartse hakoran sa
Marka taja tsaki, Umma hadiza ta miqe da sauri ta koma cikin daki wajen su Najib.
"Haba wannan wahala har ina? Ga wannan ga wannan. Gaskia da sake " Marka ta fada tana mai hararo dakin su Najibu
"Kai Marka ki dena cewa haka. "
"Kinga Naja ki fita idanu na. Ni dama tun da na kyalla ido na hango shigowar ki, Nasan tabbas wani katsalandan dinne ya kawo ki.."
"Kiyi hakuri Marka. Da yardar Allah komai ya kusa wucewa. Lokaci ne, Idan Allah ya nuna mana wucewar da sai kiga tamkar ba'ayi wannan tashin tashinar ba." Naja ta karasa fada idanuwanta akan Marka dake faman cin magani.
Can ta sake sakin wani dogon tsaki tana karkada kafafu. Cikin kufulewa tace,
"Kin isheni da zubar lallami Najaatu. Har kina wani lankwashe kai kina jin haushin Sa'adatu. Yo ai gaskia Sa'adatu ta fadi. Yaran Sa'adatu babu abunda zamu ce da su agidan nan sai san barka da fatan samun nasarar Allah akan dukkanin lamuran su. Zainab da suke kusan sa'anni daya da wahidin ne sau uku mai nemanta ya kawo mana kayan abinci ga su nan idan karya nayi."
"Zancen ki haka yake Marka. Domin wainar yar tsalan jiya ma zainab ce ta sayo." Cewar Sa'adatu hade da kecewa da dariya.
"Wannan duk ba abun damuwa bane Marka.."
"Babbar damuwa kuwa Naja. Natsani safiya tayi dare ya maye idanuna su sake dora ganin su akan Hadiza da ahalinta. "
"Kash. Assha Marka. Ki bar cewa haka. Babu fa bawan da ya tsara rayuwar sa haka fyace wadda Allah ya rubuta. Kuma menene yan uwantakan da zumuncin idan har dan uwanka baya kyautata maka?"
"Ke Naja. Duk abubuwan da zaki fada ba tasiri zai yi a zuciyata ba don in gaya miki..."
"Kibar cewa haka Marka..."
"Dole na fada. Kinga wuya. Nan inda abu ya tokare mun yaki tafiya. ? Ba komai bane fyace bakin cikin da Hadiza da yaranta suke samun. Nagaji idan da gaban gajiya nayi..."
"Ya SubhanAllah! Ki dubi girman Allah Marka ki dena cewa haka, Dukkanin yaran nan fa jikokine. Haka kuma Allah yaso acikin jikokin naki zaa samu biyu marasa lapia "
"Marasa lapia? Nakasassu zaki ce. Masu tattare da kunci da 'dacin rayuwa."
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Marka!! Marka!! Ki dena cewa haka. Malam ka saka baki. Wannan ba dede bane."
"Ba ze saka ba Najaatu. Idan kin gaji da ji ki tattara ki fice mana daga gidah ."
"Kiyi hakuri Marka. Kawai dai gani nayi wannan maganganun dik basu taso ba."
"Dole ne ayita. Shi ya saka nace wallahi kwayar hatsi nawa hadiza dasu Najib ba zasu sake ci ba. Su dan kinibibi sunyi shabe shabe ga nakasassu da baza su fita su nemo ba. Ita kuma uwar tasu ta daure musu gaba ba zata tursasu ba. Kullum dan tsagwarar munafurci suna daka suna sakin numfarfashi. Ita kuma ta faake kullum tana gefen su ba zata fito cikin mata tayi shiqa ba ta samu kudin batarwa. Ragowar me lapiar kuma ta tsiri boko ba kakkautawa. Ba zeyiwu ba wallahi. Su tunda maza ne suje can su karata ita kuma tinda macece dole ne a aurar da ita. Baqin jini ya mata katutu maza basa zuwa. An samu kuma Na'Ateeku yace yaji ya gani zai aure akan wane dalili zamu fasa? Bayan idan ta aure shi kakarmu ta yanke sa'a . Ita kanta Hadizan sai tafu jin nutsuwa da kwanciyar hankali... Wahala zata ragu. "Marka ta karasa fada tana gyade kai.
Najan isubu ta numfasa kafin tace,
"Kowane bawa da yadda Allah ya kadarta masa rayuwar sa, Wala dadi wala akasin haka. Rayuwar hadiza da yaranta haka Allah ya rubuta mata tata jarabawar. Sai dai fatan Allah yaba su ikon cinyewa yasa jinkirin alkhairi ne Aamin . Zancen nauyin dake kanta da yardar Allah yazo karshe. Domin na samo mata aikin wankau da yan kaude kaude a layin manyan can na shurah. Saboda haka zata sauke nauyin wasu abubuwan . Haka zalika itama Waheedan akwai abunda zaa sama mata ta dingayi bayan su Najeebu sun ji saukin jikin su. Don haka Marka ki ajiye zancen Na'Ateeku agefe yanzu."
"Na ajiye na zuba mata idanu ina kallonta? Ba dan mashinshini a kusa sai zuryar boko? To bokon yaci uwatas."
"Kiyi hakuri. Insha Allah kwanannan samari zasu fara zuryaa a kofar gidan nan. Komai lokaci ne. Mijin ta na nan kusa da yardar Allah. Wanda zai share hawayen ahalin gidan nan kai dama na kusa da ku baki daya. Insha Allahu. Kice Aamin Marka.."
Umma hadiza dake daki hawaye suka shigaa zirara a idanunta. Tabbas Najan Isubu aminiyar kwarai ce data san dattako take kuma yi musu madaukakiyar kauna marar misaltuwa.
"Marka, Sa'adatu, Malam baku ce Amin ba."
"Aamin Najaatu." Malam Nalado ya fada yana sosa keyar sa.
"Uhum.... Inji me ciwon baki."Cewar Sa'adatu hadi da yin kwafa ta juyar da kanta gefe.
"Aamin inda gaske ne hakan zai kasance ba karairaki bane da wucewar zance."
"Insha Allah Marka... Na'Ateeku abunda yasa ki kaga na kauda zancen maganar sa akan irin lalurar su Najibu ce. Ta sikila da ake cewa amosanin jini."
Marka taja dogon tsaki tana kauda kai gefe.
"Ke wallahi Najaatu kin iya samun waje kiyi ta sakin ta."
"Allah ba karya nake ba Marka."
"Wohoho ni lauya zan ce ne banaso wallahi. Na'Ateeku ban taba gani ya kwanta ciwo ba. Zaki jajiba masa."
"Marka abunda nake nufi shine. Shima ai yanada iyali dake dauke da irin ciwon su Kamal. Ba wai ina nufin shine mai ciwon ba. Amman yana dauke da wasu sinadarai na ciwon wanda idan ba'ai gwaji ba kafin aure shine zakiga anata hayayyafan yara masu dauke da ciwon. Yanzu kai ya waye Marka... Sai anyi gwaji kafin ayi aure saboda gudun 'barakar ciwuka. Hakan yasa na ce miki ki bar zancen Na'Ateeku da Waheedah. Domin kulla auren su kan iya haifar da illoli da yawa astagfirullah. Ba tsumi babu dabara. Maganin kar ayi kada a so ma "
"Keda Naja kinada kale kalen balai wallahi. Allah shi kyauta "
"Wannan shine tushen gaskia Marka. Ba Na'Ateeku ba. Ko wani ne daban yazo neman auren Waheedah ko zainab dole ne kafin ayi auren suje suyi gwaji. Wannan shine babbar shawara da ma'aikatan lapia suka kafa. Don gudun bacewar rana. Azo ana danasanin auren."
Marka ta tabe baki hade da jan karamin tsaki.
"Gidan aikin da zataje ina fatan nima inada nawa kason acikin albashin nata.?"
"Duk ba zai gagara ba Marka. Kuma insha Allahu tare daku duk zamuje taron nan ayi mana gwajin."
"Uhm.." cewar Marka.
"Bari na tafi. Allah ya kiyaye gaba."
"Toh Najaatu. Agyada gidah."
"Gidah yaji."
"Ke kuma tashi kafin na hamb'are ki. "
Takarasa tana mai wurgawa Waheedah harara. Gaba daya maganganun Najaatu sai shawagi sike mata akai. Ta kaikaice kai ta hango ledar taliyar kakkaryawa da tumatirin gwangwani. Na'Ateeku ya sake fado mata arai. CikiN zafin nama ta mike ta shige kuryar daki .
Waheedah ta mike jikinta a sanyaye ta shigaa dakin su Kamal. Umma hadiza kuma ta tafi ta yowa Najaatu