Showing 27001 words to 30000 words out of 123508 words

Chapter 10 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

517

aiki.

Karar karnuka da tsuntsaye sai tashi suke. Haka dai Waheedah ta daure ta karasa har ya zuwa kofar gidan na The Adams family!!

Daya daga cikin masu gadin yana ganinta ya tashi yana nufar inda take

"Ina kwana?" Ta gayshe shi kanta a kàsa.

"Lapia lau...wajen wa kika zo? Ko masu kawo goron nanne na sayarwa? Na shekaran jia ko?"

"A'ah bani ba ce ..." Ta amsa shi cikin sanyayyar muryar ta

Dai dai lokacin da wasu manyan motoci masu nishi da kyawu suka danno kansu zuwa gingimemen gidan na the Adams family.

Nan da nan masu gadin suka bude musu gate. Jufa jufan su 3 suka kutsa kai cikin gidan.

Waheedah ta zubawa sarautar Allah idanu tana bin yadda motocin suka tulesu da kura da kallo.

"Yauwa ke menene ne? Sauri muke munada baki?" Mai gadin dazu da suka rufe gate ya cigaba da tanbayarta. Don tambayar farko daya mata bata kaiga sake bashi amsa ba baqin suka zo. Yabar inda take zuwa wajen baqin

"Sunana Waheedah. Nazo nan gidan ne taya su aiki."

"Akan me zaki tayasu aiki. Ko irin masu barar nan ce ke! ? Malama yi gaba. Ga ki komi fes fes kankanuwar yarinyar ki da ke saboda mutuwar zuciya shine kikazo nan din maula ko? Zaki matsa ko sai na mauje keyar ki?"

Waheedah ta girgiza kai kawai

"Mahaifiyata ce ke aiki anan gidan. To yau bata d...."

"Kyaleta Labaran..Ke yar Umma Hadiza ce?"

"Eh .." waheedan ta amsawa wata kyakkyawar budurwa data fito waje.

"Okay shigo ciki. ...." Nadra na gama fada ta karasa shiga ciki. Daman mahaifiyar ta Dr. Hameedah ce tace tazo ta ko Hadiza tazo masu gadi sun hana ta saboda baqin da zaayi. Ta shigar da ita

"Kema baki bayani ba " cewar me gadin daya hana Waheedah shiga ciki

Bata kula shi ha. Tabi bayan Nadra da sauri. Wayar Nadra ce ta shiga karaa. Da sauri ta dauka ta kara a kunnenta.

"Bata zo ba. Amma dai luckily enough na samu daughter din ta. Har ma mun shigo tare .."

Waheedah nata kalle kalle haka suka karasa shiga cikin gidan. Waheedah ta dade nutsuwar ta bata dawowa ba. Saboda madaukakiyar mamakin girman gidan da abunda ya qunsa...

"Nadssss ."

"Sis Ahlaaam....."

Nadra da wadda ta kira Ahlaam suka rungume juna cikin farin ciki. Waheedah ta tsaya tana jiran su. Kai daka gansu kasan yan uwa ne. Saboda kamar su sosai .. lamarin se godiya ga Allah. . Da dimbin yabawa da ganin daraja agare shi. Domin shi din mubuwayi ne gagara misali.

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:21_


======
     
*Waheedah* dai taja tunga a tsaye ta zubawa sarautar Allah idanu. Idanunta nata wulqitawa tana mai karade gidan da kallo. Ai gaba daya yadda Umman su ke tsara haduwar gidan. Sai taga a zahiri ma yafu kawatuwa sosai.

Ga bishiyu da suka ingattu da albarkacin ganyayyaki sunata kadawa. Wata iriyar iska mai ratsa jiki ce ke busawa ahankali

Ya yinda Ahlaam da Nadra ke gaisawa sun manne da juna suna farin ciki. Can sai lokacin da wata mata ta fara zuro kafafinta dake sanye cikin takalma masu laushi da kyawu.

Can sai ga sandar da take dogarawa nanma ta zuro ta kasa. Kafin direban ya sake wangale kofar motar. Dattjuwar ta fito cikin riga da zani na atamfa. Ya yinda mayafin ma atamfar ce tayi mayafin da shi.

Wuyan ta me dauke da wuri. Haka ma dankwalin kanta irin masu santsinnanne. Sai hannunta da yasha lalle samfurin dungulmi.

Fuskarta kuma da baqin gilashi. Wanda tun wani aiki da akai mata a idanun take saka baqin gilashin. Sakamakon hasken rana da qura kan iya dawo mata da aikin danye.

"Ummimi...!!!" Nadra ta fada da sauri. Tana mai rungumar kakarta su.

Wata dattjuwa yar kyakkyawa, Bata cika tsawo ba. Kuma sam batada jiki. Kyakkyawa ce. Kana kallonta kasan ta hada jini da fulani..

Yayin da wata mata a gefen ta ke riqe da jakar ta. Nadra ta tafi d sauri ta rungume ta tana farin ciki

"Sannun ku da zuwa Ummimi.."

"Sannu ka dai Nadra."

Ta sake rissinawa tana gayshe ta. Sannan ta miqe. Ummimin na ta sanya mata albarka.

Suka rankaya baki daya suka yi sashen Hajia Aisha. Uwargidah kuma mata ta farko ga farfesa Adams.

Waheedah na biye dasu a baya , Tafiya kawai take salolo. Zuciar ta nata rada mata kan tabbas Nadra ta manta da ita.

Ai kuwa Bata karasa tunanin ba ta tsinkayo muryar Nadra. Suna tafe itada Ahlam.

"Na'am... "

"Afuwan na bar ki. Wajen su kakar mu naje. "

"Bakomi yar uwa."

"Sunana Nadra. Ke fa?"

"Wa.... Hee...dah" Ta fada a rarrabe.

"Sunan larabawa kuma yan gayu ba. Well ni kuma sunana Ahlam . Nadra da ni first cousins ne."

"Ah masha Allah ..." Cewar Waheedah.

A tsakiyar su suka sakata. Suna tafiya a jere. Waheedah sai raba idanu take. Tana mamakin saurin sabo irin na su. Uwa uba kuma basa kyankyami na ganin ita din ba wata bace. Ba tsarar gogawar su ba ce .

Sashen Barr. Aisha suka shiga. Da sauri ta taho cikin farin ciki da girmamawa wa ta tarbe su. Ta rungume Ummimi bakinta tamkar zai wage .

Ta rissina har kasa ta gaishe da ita cikin girmamawawa. Ummimi ta amsa da fara'a. Ta zauna akan kujera mai cin mutum uku .

Nan da nan su Ahlam suma suka shiga gayshe da Barr. Aisha. Ta amsa tana kiran sunayen su. Waheedah ma ta gayshe ta .

"Ke kuma ya sunan ki?"

"Sunana Waheedah "

"Masha Allah ... "

Ma'aikata ne suka shiga kawo abubuwan motsa baki. Da lemuka da ruwan roba kala kala.

Su kayita tururuwar shigowa suna gayshe da ummimin. Cikin haka Haj Hameedah ta shiga sashen itama. Sanye cikin laffaya baqa mai kwalliyar pink

Ta tsugunna har kasa ta gayshe da ummimin. Ummimi ta amsa da fara'a lullube a fuskarta

Ta juya ta gayshe da Barr Aisha. Itama ta gayshe da ita. Kafin su Ahlam su gayshe da ita.

A kallo na farko Waheedah ta gano itace mahaifiyar Nadra. Saboda tsananin yadda suke kama.

"Maa ga Waheedan."

Suka hada idanu da ita. Ta saki tattausar murmushi .

"Sannu Waheedah. Ina Hadizan, Fatan dai komai lapia?"

"Alhamdulillah.... Eh batada lapia ne."

"SubhanAllah! Meya same ta?"

"Zazzabi take da amai."

"Wayyo. Allah bata lapia yasa kaffarane. "

"Aamin Yaa rabbi."

"Ummimi me zaa dafa muku?"

"Ko meye ma Hameedah."

"Toh . Bari na je."

"Sannu da kokari."

Fita hajiya Hameedan tayi. Nadra da Waheedah suka bi bayanta.

A kan hanyar su ta komawa sashenta ta sake cewa da Waheedah,

"Amma an kaita asibiti ko?"

"Na baro su dai me kyamis ze duba ta"

"To Allah bada lapia. Tun safe nake jiranta. Naji shiru. Na dauka ma ko tazo masu gidah basu bari ta shigo ba saboda baqin da za'ayi. Nasa Nadra taje ta dubo. Allah sarki hadiza ashe batada lapia "

"Eh ..."

"Tohm shigo ciki."

Waheedah ta shiga cikin parlorn tana raba idanu. Lalle dukiya tayi kuka. Idanunta suka sauka akan wata jirgegiyar tv da sauran kayan kallo

"Zauna mana Waheedah."

Waheedan ta dan tsakure akasan kujera kafin tace,

"Ance a nunnunamun abubuwan da zan yi kafin Umman ta mu ta samu sauki "

"To Waheedah ba matsala . Zo ki ga "

Haj Hameedan tayi gaba. Yayin da waheedan ke biye da ita. Ta nunnuna mata komai da yadda zatai amfani da su.

"Kinga abincin ta ma..." Ta nuna mata wata food flask katuwa. Kamshi sai tashi yake daga cikin ta.

"Allah sarki ....."

"Zaki iya kai mata ki dawo?"

"Toh ko zan kammala aiyukan?"

"A'a kai mata dai. Akwai kunu ma gashi can tunda zafin su ta samu ta ci."

"Tohm.."

"Yauwa Waheedah "

A cikin wani kwando ta jera mata kayan abincin kai kace wata babbar bakuwa zaa kai wa.

"Rike dakyau."

"Angode Allah ya saka da alkhairi Hajia..."

"Aamin Waheedah, Ki cemun Maa haka su Nadra ke kirana kinji ko?"

"Tohm ...Maa"

"Yauwa Waheedah. "

Daukar kwandon tayi cikin nutsuwa ta fita zuwa gate din. Ta ajiye a kasa ta bude gate din sannan ta dauka ta fice.

Kamshin soyayyan nama da na tafarnuwa na ta dukan hancin ta a haka ta karasa gidah

Bakinta dauke da sallama ta shiga cikin gidan.., Marka na zaune akan turmi tana tsintar shinkafa. Ta hararo kwandon dake hannun Waheedah tana tabe baki.

Waheedan ta shige da kwandon cikin dakin su. Umma Hadiza na kwance akan katifa. Yayin da dayan hannunta kuma daure yake da abun karin ruwa. Har ya kare wanda aka saka matan kafin me kyamis din ya koma anjima.

"Sannu Umma..."

"Yauwa Waheedah. Ya kika dawo?"

"Ca tai nayi sauri na kawo miki abinci. Nace ta bari ma na kammala aikin tace a'ah .."

"Allah sarki Hajia ... Mungode Allah ya saka da alkhairi."

"Aamin Yaa rabbi. Ki tashi ki sha kunun da abincin."

"Dakko kofi da kwano ki zubawa Marka "

Waheedah ta turo baki gaba.

"Umma da dai kin fara ci."

"Je ki dakko na ce ."

"Toh."

Da sauri ta dakko kwano da kofi wankakku ta ajiye.

"Zuba mata kunun ki zuba mata abincin a plate."

"Tohm."

Ta zuba kunun a kofi dake tashin kamshin gyada da kayan kamshi. Ta bude food flask din.

Kwai ne da dankali da soyayyan nama a gefe.

Ta zuba komai a farantin zata miqe Umma Hadiza ta ce,

"Kara mata waheedah.."

Waheedah ta sake karawa. Ta nunawa Umma Hadizan sannan tace yayi.

Ta fita ta kai wa Marka

"Gashi inji Umma. Daga gidan aikinta aka bata"

Marka ta yamutsa fuska hadi da wulqita idanu ta hango lafceciyar wainar kwai da dankali da nama. Ga kunu kuma.

"Sai da aka ci aka cinye.? Kalli dan abunda aka sammun. Aikin kawai " Ta wafta jikinta har yana rawa......

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:22_


=====

   Waheedah bata ce wa Marka kanzil ba ta koma daki abunta

"Ki tashi kici Umma."

"Dibi kici Waheedah. Ki raba mu ku da su Yayan ki da Najan Isubu. Don sai yanzu ta tafi gidah yo wanka. Zata dawo "

"Allah sarki aunty Naja. Allah yabar zumunci."

Nan da nan kuwa ta fara dibarwa Umman tasu nata. Sannan ta raba musu nasu.

"Umma ki tashi ki ci "

"Banajin yunwa .."

"Dan Allah Umma "

Umma Hadiza ta daure ta tashi daga kwanciyar da take. Taja plate din gabanta tana ci tana hadawa da kunun. Hakama Waheedah da kunnuwanta sai motsawa suke don dadi.

"Gaskia abincin nan yay dadi "

"Ai Hajia ta iya girkuna."

"Sunada kirki Ummaa. Ban baki labari ba. Da naje fa hanani shiga masu gidan su kayi daga farko "

"To pha SubhanAllah... Baki ce musu ni mahaifiyar ki bace?"

"Kwata kwata sun hanani. Saboda wai baqin da za suyi. Ina zuwa kuma bakin na zuwa su ma. A wasu manyan motoci."

"Lalle bakin na karramawa ne. To waya shiga da ke kenan?"

"Wata Nadra ."

"Okay Nadra . Yar Haj Hameedan ce ai."

"Eh na sa ni., Wai itace ma ta aikota wajen ko kinzo sun hana ki shiga. Tana zuwa ta ganni sai tai musu bayani suka kyaleni na shiga."

"Allah sarki "

"Gaskia sunada kirki Umma. Baki ga yadda suka mun ba gaba dayan su. Kamar irin tun da can dinnan sun sanni."

"Allah sarki su Hajiya. Akwai karamci

"Wadda tazo din ina kyautata zatom mahaifiyar mai gidan ce. Wata dattjuwa wai Ummimi "

"Tabbas naji sunan nan Hajia na fada."

"Eh tazo da maaikatan ta da wata budurwa . Tace mun sunanta Ahlam."

"Allah sarki. Allah ya saka musu da alkhairi."

"Wallahi sun burgeni sosai wallahi.. Ba ruwan dukkan su. Har sashen dayar matar mu kaje."

"To pha meya kai ku?"

"Anan tsohuwar ta sauka. Don naga Maa ma na tambayarta abincin da zaa dafa mata."

"Allah sarki baiwar Allah."

"Yauwa ni na manta ma ban gaya miki ba."

"Meya faru.?"

"Tace wai na dinga kiran ta da Maa"

"Allah sarki Haj Hameedah ... "

Waheedah ta gama bata labarin komai tsaf. Sannan ta kuskure bakinta ta mayar da hijabinta ta koma gidan aikin Umman su na The Adams family.

Tana zuwa ta shige ciki ba tare da masu gadi sun sake hanata ba

"Kin dawo Waheedah.?"

"Eh na dawo Maa "

"Masha Allah. To ya jikin Hadizan?"

"Ah da sauki . Na baro ta ma tana cin abincin. An gama sa mata ruwa."

"Oh Allah sarki Hadiza , Har da karin ruwa.?"

"Eh."

"To Allah bata lapia. Yasa kaffarane Amin."

"Amin , Bari na dauraye kayan "

"Tom Waheedah."

Nan da nan ta hada ruwan kumfa ta wanke kananan kayan ciki da safuna (socks) na Moha .

Ta dauraye ta shanye. Ta goggoge ko ina tamkar yadda suka koya mata. Sannan ta wanke mopping sticks din da dusters.

"Ah sannu Waheedah. Kina da saurin aiki irin na Hadiza. Masha Allah."

Dan murmushi Waheedah ta yi. Tana mai lankwasa yatsun hannuwan ta .

"Allah miki albarka."

"Aamin Maa."

"Zauna ki huta. Ga abinci nan ki ci kafin a kammala na rana."

"Wallahi na koshi Maa. Ai na ci na wajen Umma. "

"To kya sake ci anjima."

"Tohm.."

Can wajajen 12 da rabi Moha ya dawo daga makaranta.

Da gudu ya rungume mahaifiyar ta su yana tsalle.

"My little sun shine."

"Maaaa."

"A zubo abinci."

"Wannan wacece?" Ya tambaya yana nuna yatsansa akan Waheedah .

"Sunan ta Yaya Waheedah ..... "

"Yaya Waneeda."

"No Yaya wa... Hee... Dah."

"Okay Yaya Waheedah."

"Ya sunan ka?" Waheedah ta tanbaye shi tana murmushi.

"Sunana Moha. "

"Sunan sa Muhammad. Muna kiran sa da Moha."

"Allah sarki . Ajin ka nawa?"

"Maa what's Aji in english.?"

"Class/grade"

"Oh! I'm in grade one . "

"Masha Allah ..."

"Ke fa?"

"Ni ss2 zan shiga."

"Okay .. "

   Haj Hameedah ta miqe ta nufi babban kitchen din sashenta inda maaikatan ke girki. Ta dudduba kan abubuwan ta koma dayan kitchen din dake parlorn inda take gashi.

Waheedah ta miqe tabi bayanta .

"Maa akwai abunda zaa tayaki?"

"Babu komai Waheedah. Dama gashi ne nake yi anan din. Can babban kitchen din maaikata na abinci. "

"Okay. Sannu da kokari."

Haj Hameedah ta zura safar girki tana dudduba kayan hadin jikin naman kajin.

"Wannan gashi ne.?"

"Eh nayi marinating ne da kayan hadi. Se gasawa kawai."

Waheedah ta kada kai .

"Kin iya girkuna?"

Ta dan yi murmushi kafin ta ce,

"Bakomai ba. Na de fi iya wasu abubuwan . "

"Ah inde kin iya girki ai da sauki. Allah ya temaka. Kai temake ni. Kinsan na manta da tafarnuwa "

"Wai."

"Yi sauri ki dubamun cikin freezer dinnan daga kasa zaki ga tafarnuwar a wani canister."

"Tohm"

Nan da nan Waheedah ta duba ta dakko ta miqa mata. Tafarnuwar a dake take. Haj Hameedah ta diba ta zuba acikin gashin tana cakudawa .

Waheedah ta dauki wasu canisters din na spices tana dubawa. Sai kamshin abincin larabawa suke . Haj Hameedah ta janyo abun grilling din tana dudduba shi. Kafin ta sauke kallonta akan Waheedah. Cikin murmushi tace da ita,

"spices/seasonings ne na larabawa .." Ta shiga daukar kowanne dai dai tana gaya mata sunayen su,

"Wannan Sadaf mint leaves ne, Wannan, Natural sidr leave sai, Pure black seed ( Black cumin seed), Ga Nutmeg, sai cardamom, Wannan sumac, Sai hulba , Fenugreek ,Allspice
Cloves, Ginger..."

"Masha Allah.....Gaskia suna da kamshi Maa."

"Sai ma a abinci..."

"Gaskia daga jin kamshin su ma " Ta dauki duster ta shiga goge kitchen cabinets din. Duk kuwa da ba datti suka yi ba .

×××××

      A gajiye yake likis saboda gaba daya jiya bai yi wani baccin kirki ba kuma tun kafin asubah bai sake runtsawa ba ya fita. Dawowar sa kenan cargos din kayan su sun sauka a site yaje ya dubo.

Sanye yake cikin manyan kaya. Riga da wando na shadda. Rigar iya gwiwa sai wando. Kalar dark blue. Hular kalar kayan sa ta zanna bukar na hannun sa. Yayinda half covered shoe dinsa da agogon hannun sa kalar aikin kayan sa ne.

Sai kamshin turaren Calvin Klein ne da Rasasi suke tashi a jikin sa.

Yana sallama tun daga bakin kofar kitchen ya samu zuciyar sa da sauya bugu . Bugun mai duka da sauri sauri.

Kamshin turaren da bazai taba mantawa ba ya shiga yawo sosai a kofofin hancin sa.

Ya lumshe idanu ya bude. Ahankali ya saka hannu ya tura kofar kitchen din ya shiga.......



❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login