Showing 120001 words to 123000 words out of 123508 words

Chapter 41 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

522

ta tumbatsa ta kuma gauraye ilahirin jini da tsokar su Basu da wani sauran FARIN CIKIN ZUCIYAH..

To dama hakan abun ya ke. Idan kana yiwa kaddarar wani dariya. Sai Allah ya jarabceka da irin ta ko ya ninka maka fiye da ita.

Wani tun a doron duniya yake fara ganin hukuncin Allah akan sa. Shi yasa duniyar nan kayi me kyau. Ka kyautata mu'amalar ka da kowa. Kada ka zama silar da wani zai kai kukan sa wajen Allah akan ka... Allah ya raba mu da mummunar kaddara. Yasa mu wanye kalau. Allah ka kare zukatan mu da gangar jikin mu wajen fadawa kogin aikata haramun. Ka nesanta mu da haramun ka kuma kusanta mu da aikata mekyau cikin halaliyar ka me dimbin rahama... Domin kai din mubuwayi ne gagara misali.. Allahumma Aamin.

××××

IYALAN MALAM NA LADO ME IGIYA

   Bayan sati da faruwar mutuwar auren zahara'u. Kuma wanda yayi dai dai da lokacin da Marka ta saka wanda zasu hallara da ahalin ta baki daya don neman gafarar su da yafiyar juna baki daya. ...

Hakan kuwa akayi. Ranar dukkanin su kwan su da kwarkwatar su sun taru a tsukukun gidan na Marka.

Ciki harda Umma Hadiza da nata iyalan su biyu. Waheedah da Najib.
Duk wanda ya dora idanun sa akan Umma Hadiza da iyalanta sai ya sake mayarwa ya dube su.

Gamin yadda suka yi bulbul da su. Fatar su na sheki, Gefe daya da nutsuwar zuciya. Musanman Waheedah da tayi wani irin fresh tamkar a tsaga jikinta jini ya fito.

Sanye cikin kayan alfarma. Kana ganinta kasan ta samu gidan hutu da wadatar zuciya. Dubada yadda komai na jikinta mai kyau ne da tsada. Wai ahakan ma bata kure adakar ta ba. Tayi saisa saisa. Gudun kada suyi ta yada maganganun ta zama yar karya da sauran su.

Bata zo hannu biyu ba. Ruwa leda leda na pure water. Sannan na cartons cartons na roba da lemo. Gefe daya ga kayan abinci buhun shinkafa ta dafawa data tuwo, Da kayan shayi da jarkar mai. Wannan kayan abincin Haj Hameedah ce ta bata tace ta kai gidan su.

Baki daya sai aka yayyabe ta. Kowa na yabawa da alkhairin da tayi. Marka tsabar dimaucewa kuka kawai take. Ganin wadanda ta muzantawa a rayuwa a baya. Sune a yanzun suke temakon ta da karfin su da gumin su da kuma aljihun su. Hawaye take tsiyayar wa sosai na nadama... Hakika tayi dana sani da abubuwan da ta aikata a baya...

Zuwan malam me carbi ba dadewa ... Ya bude taron da addu'oi sosai. Sannan ya shiga yin wa'azi mai ratsa jiki da fadakarwa ga dukkanin su yan wajen baki daya ....

Daga bisani kuma ya bawa malam na lado dama shima ya fara tasa maganar. Daga karshe ya shiga neman yafiya da afuwa ga dukkanin su. Da su yafe masa akan dukkanin abubuwan da ya aikata wa kowannen su na bacin rai akan sani da na rashin sani ...

Bayan ya gama nasa bayanin. Marka ta karba. Muryar ta na rawa da kakkarwa. Idanuwan ta taf da ruwan hawaye. Ta shiga bawa daya bayan dayan su hakuri akan dukkanin muzgunawa da tayiyyi musu. Hususan (musanman) Umma Hadiza da ahalin tah.

Marka ta sake fashewa da kuka... Hakuri sosai take basu. Numfashin ta na fuzga. Neman yafiyar su ta ke. Nadama sosai take yi. Ji take dama a tariyo baya . Ta goge halayen da ta aikata ta musanya wa kowannen su da alkhairi ..

Wasu daga cikin su hawayen suma suka fara, Musanman Umma Hadiza, Waheedah, Najib, Nalado, inna Sa'adatu da kuma Deluwa.

"Yanzu ba gashinan ba ? Na girbi abunda na shuka. Duk wasu sharruka dana aikata daya bayan daya sun dawo mun. Daman ance sharri dan aike ne. Duk inda ya zaga ya zagaye da aiken da ka yi ma sa. Sai ya dawo gare ka ko ga wanin ka.. Dukkanin mugayen alkaba'en dana dinga yi wa Hadiza da yaranta yanzun ba gashi nan ba. Sun dawo gare ni da na wa yaran da jikokin? Ciwon da nake musu dariya ina zunde gashi nan akan nawa jikokin na wajen Zahara'u. Makantar Wahidin... Au Waheedah da na ke aibata gashi nan Deluwa ta haifo yara daya makauniya ce. Baki daya ma ita bata gani kwata kwata. Sakin da na saka mai sunan Malam ya yiwa Hadiza gashi nan an sako tawa 'yar har sau biyu. Yara kuma dukkanin mazajen sunce basa ra'ayin su. Jikar da na fi kauna na fifitata akan Waheedah. Nake ganin Waheedah itace me budadden idanu ta iskance akan karatun da take. Sai gashi ana zaton wuta a makera... Naga aya akan wadda na zaba... Ranar daurin auren an daura nan mijin ya zo ya saketa kan zubar da cikin ta uku bata gari bace... Sa'adatu ta yanke jiki ta fadi ana fadar hakan. An kaita asibiti zaa dawo da ita nan nace ban amince ba.. kaya zata zamar mana.. Sai gashi ita Allah ya warkar da ita. Ni ce na zama kayan. Sai dai a kwantar a tayar... Nayi kurakurai da manyan laifuka da baki ba zai iya fade su duka ba. Saboda girman haramcin su .. Ni dai ku yafemun... Dan Allah ku yafe mun.."

Kuka ne yaci karfin kusan dukkanin su. Ciki harda malam me carbi da ke gefe... Daya bayan daya suka shiga cewar sun yafe

Inna Sa'adatu ta tashi daga inda take. Duk ta yamutse. Ta motse ta lalace. Kamar ba wannan saadatun me tsiwa a baya ba.. Gaban Umma Hadiza ta tsugunna ta shiga rokan gafarar ta. Hawaye suka shiga reto a jemammiyar fuskar tah.

Umma Hadiza tayi murmushin yake. Hannunta daya na kan na inna Sa'adatu.

"Na yafe ma ki Sa'adatu . Allah ya yafe mana gaba daya.. Nima ina neman yafiyar dukkanin ku. Wadanda nayi wa lefi akan sani ko akasin sa. Ni da yarana baki daya mu na neman afuwar ku. Allah ya yafe mana baki daya Amin."

Haka dai suka shiga neman afuwa da neman yafiyar junan su. Alhamdulillahi kowa ya yafewa kowa acikin su baki daya. Wannan yasa Malam me carbi sa ke jan kunne agare su .. Kafin yayi musu zai tafi

Marka ta saka aka deba masa lemuka da ruwan da Waheedah ta kawo. Da rabin kwanon kayan masarufin. Yayita godiya ya yi musu sallama ya tafi. Najib ya rike masa kayan yayi masa rakiya..

Waheedah da zainab ne suka hada wuta suka dora taliya yar kakkaryawa da miya🤸 Ranar anci an gyatse... Anyi wasa da dariya... An saada zumunci sosai. Harda hotunan tarihi suka yiyyi...

Da Waheedah ta tashi tafiya. Ta dakko yan kudaden ta na sadaki da taketa ajiyar su. Duk kuwa da tayi amfani da wani kaso daga ciki ..Ta dankawa mahaifin ta .. Don FARIN CIKI fashewa yayi da kuka. Ya rungume ta yana sanya mata albarka ,. Tace yaja jari da su.

Yana kaunar iyalin sa. Da matar sa ta baya Hadiza. Dan dai auren ya rabu ne. Ya so tayi komai . Sai aka dakatar kan dukkanin su AS ne.. Don haka kar a mayarda auren tarihi ya maimaita kansa . Kar su sake samun wasu iyalin wadanda zasu zo dauke da cutar amosanin jinin suyi ta wahala har karshen rayuwar su .. Don haka ya hakura ..

Har mota suka raka Waheedah wadda Nassem kanin Zayn ya zo daukar ta. Shima ya gayshe da su cikin girmamawa... Taro ya watse . Kowanne ya koma muhallin sa cikin FARIN CIKIN ZUCIYAH.....


××BAYAN SHUDEWAR WASU LOKUTA××


Anyi bikin Nadra an gwangwaje... Dangi zumunci ya kara bunkasa . Zuciyoyin su sun samu farin ciki da kara kusanta a tsakani..

Allah ya azurta Waheedah da karuwa. Ba karamin kyau baby bump din ya mata ba. Idan ta saka uniform din school of nursing sai kuga yayi das das ajikin ta. Gwanin ban sha'awa..

Soyayyar duniya Zayn ya dauka ya dorawa cikin Waheedah. Ta kara samun kulawa da tarairaya daga dangin ta da na sa. Ciki kuwa harda Ahlam . Domin yanzu tuni komai ya wuce sun dedeta kansu. Suna kuma ziyartar gidajen juna. Wani lokacin har tsokanar su Zayn yake .. Yana cewa suna hade masa kai bai yadda ba.

Itama Ahlam ta koma makaranta karo karatu na digiri na biyu. Ya yinda Zayn arzikin sa ya yalwata. Ya hada da aikin office da kasuwanci.

Ya mallakawa matan na sa biyu mota iri daya. Ta Ahlam fara ta Waheedah ja. Lamarin sai godiyar ubangiji.

Fannah da Basira ma lokaci daya aka saka bikin su. Ibrahim ne ya auri fannah. Ya yin da Salman lecturer dinsu na school of nursing kuma ya auri Basira. Waheedah ita ta zama uwar biki. Babbar kawar amare.

Gidan su wajen Marka ta koma ta tare har aka kammala shagalin bikin na tsawon kwanaki uku. Ya yinda gefe daya bangaren na ahalin malam na lado ma sai sam barka komai yana tafiya ahankali cikin nutsuwa da kwanciyar hankula... Da waraka ta fannoni da dama...

Don Umma Hadiza ma wani mutumi mai rufin asiri a gidan da ke kallon na gwaggo haule. Matar sa ta rasu ta bar masa yara biyu. Shekara daya kenan da wata uku bayan rasuwar ta. Ya samu mijin gwaggo haule da zancen neman auren Umma Hadizan.

Da fari Umma Hadizan ta ki. Kasancewar ga yara manya agabanta auren me zatayi? Da kyar da sudin goshi gwaggo haule ta shawo kanta.

Aka daura auren ranar wata jumu'ah. Ta tare agidan. Mai gate da dakuna uku da parlor har biyu. Kuma Alhamdulillahi yaran mutumin na kaunarta.

Ta rike su tamkar yaran data haifa daga cikin tah. Ta kance ai 'da na kowa ne.. Hakan yasa dangin sa dana marigayi ya matar sa suka sake kaunatar Umma Hadizan. Suna masu yabon ta a ko'ina...


××ZAYNUL_WAHEEDAH××
(DESTINED LOVE)💕


__
Samun karuwar da tayi ... Yazo mata da lauyi kala kala. Ciki harda kasala da bacci uwa kasa. Da tayi ishai take zubewa tayi bacci..

Kusan ko yaushe sai ya dawo da daddare ya ke tashin ta ... Taci abinci sai ta sake komawa baccin.

Yau ma hakan ta ke. Mai gadi na bude masa gate ya shiga da motar sa ya yayi parking awajen adana motoci.

Ya bude kofar da zata saadaka da cikin gidan da spare key din da ke hannun sa.

Bakinsa dauke da sallama ya shiga. Sai kamshin turaren wuta ne ke tashi . Ya sake bude kofofin hancin sa yana mai shakar niimataccen kamshin.

Hannu ya saka ya bude dakin ta. Tana kwance akan gado tana bacci. Ya danyi murmushi hadi da ajiye yar jakar da ke hannun sa a gefe .

Ya zare safar kafar sa ya isa ga gadon da take kwance. Ya yaye duvet din ahankali ya shiga ciki.

Ya shiga unbutton din maballan jikin rigar sa. Ya cireta ya ajiye a gefe. Jikin Waheedah ya shige sosai tamkar za'a kwace masa ita...

Ya saka hannuwan sa akan rassan jikin ta yana mai mata tafiyar tsutsa.. Cikin wani salo na tafiyar da soyayyah . Ya dan saka hakoran sa ahankali ya ciji kunnenta..

Ta shiga ture shi daga jikinta. Idanuwan ta a rufe. Baccin ya ki sakin ta..

"Kasa uwar bacci ....." Ya fada ahankali cikin kunnenta.... Yana mai yawo da harshen sa acikin kunnenta.

Da sauri ta farka daga baccin. Ta shiga ture sa da iya karfin ta . Ya hanata, Ta hanya sake makaleta. Yana mai shafa gadon bayan ta,

"FARHATAL QALBi nahhh, A yayin bayyana miki adadin yadda nake jin son ki a zuciyata, zan iya yin amfani da kalmomi irin su…….hmm ko dan ina ganin cewa babu wata kalma da za ta iya wakiltar matsayinki a gare ni. Sai dai a yau a kuma yanzu ina mai kara sanar da ke cewa, ina kaunar ki .. Irin son da gangar jiki ke wa zuciya. Zuciya ta ke wa rai... Kin zamo mun FARIN CIKIN da ke cikin ZUCIYAH marar misaltuwa.."

Yana magana yana zame rigar da ke jikinta a hankali. Dama ta bacci ce iya cinya. Ya sake jan bargo ya rufe su yana mai aikawa wasu rassa na jikinta sako da suke tafiyar da shi a koda yaushe.

Ta shiga ture hannuwan sa. Tana mai turo baki gaba.. Cikin kwarewa ya burkito ta .. Ya kamo bakinta ahankali ya hade da nasa waje daya . Sumbatar ta yake cikin kwarewa da nuna tsantsar kaunar sa agare ta ...

"Ka bari ....."

"Sshhhh...... Please Waheedah.... Please" Ya shiga rokonta ta hanyar sanya idanun sa cikin nata.. Baki daya ya narke mata.

Wasu zafafan sumba ya shiga aika mata tun daga tafukan kafafuntaa zuwa kirjin ta. Wanda suka haddasa mata tashin tsigar jiki. Kofofin jikin ta suka shiga budewa da son kasancewa da shi. Suna mai maraba da sakonnin da ya ke aika musu

Hakan ya sa Zayn sa ke kai mi wajen. Zare rigar tata gaba daya ya jefar. Ya kashe fitlar bedside ya sake kankame ta ajikin sa.

Duk kaucewar Waheedah sai da ta kasa hakuri. Ta bashi hadin kai. Suka shiga nunawa juna bajinta..

Bayan sun samu nutsuwa ne. Zayn ya dauki Waheedah suka shiga cikin bandaki. Ya sakar musu shower akan su.

Suka tsaya ruwan shower din na zuba ajikin su. Ya shiga kwaranya akan sumar gashin Waheedah... Zayn ya saka hannu yana shafa gashin na ta.

"Waheedah nah.. I never loved you any more than I do, right this second. And I’ll never love you any less than I do, right this second..."

Ta dago idanunta da suka jike da hawayen FARIN CIKIN kalaman sa da ke tsuma ZUCIYAr ta a koda yaushe... Ya gyarda mata kai, Ya sanya harshen sa yana mai goge mata hawayen da harshen sa, Hadi da cigaba da cewa,

“I love you and I don’t want to lose you. Because my life has been better since the day I found out..... You are my sunshine, My moon and all my stars💕"

Da wannan kalaman ya hade bakunan su waje daya .. Daga wanka kuma suka shiga bude shafin wata kaunar. Dakyar Waheedah ta yageshi daga jikin ta ... Suka shiga mayar da numfashi.

Daga karshe dai sukayi wankan me dalili dana tsarki. Kafin su sanya wasu kayan baccin su koma parlor .. Tv suka kunna suna kallon wani American film 'legally blonde..'

Rayuwar su gwanin sha'awa... Tamkar irin masoya dinnan da suka shekara dari suna bawa soyayya hakkin tah. Zaman su suke lapia kalau ba wanda ke jin kansu . Ko sun haura da kansu suke shiryawa ba tare da kai wa wanin su kara ba...


××Bayan wucewar watanni... Allah ya sauki Waheedah lafiya.. Ta haife santalelen jariri kato. Kyakkyawa tamkar Zayn ne yayi kaki ya tofar.

Kwayar idanun ce kawai irinta Waheedah... Da dan karamin bakinta masu dauke da labba jajaye .

Daga ita har jaririn suna cikin koshin lafiya. Zayn ya yiwa yaro huduba ya sanya masa sunan mahaifin sa wato farfesa Adam. Amman daman sun tsara idan mace ce sunan Maa ne zasu kira ta da Hayfa. Idan namiji ne kuma Adam za'a dinga kiran sa da Sultan ..

Asibitin ya cika makil da yan uwa da abokan arziki. Kowa ya zo yi musu barka. Ko dan bedrest ba su bari tayi ba. Saboda surutu, Likitan ya tarkata ya basu sallama.

Gidan Maa suka wuce. Sai da tayi wa zayn jan ido da ya kafa ya tsare agidan ta zata zauna baa ko'ina ba.

Ba yadda ya iya haka ya hakura. Maa tatafi da Waheedah da ke masa gwalo. Aka gyara mata daki daya.

Kan kace me ko'ina an cika sa da kayan baby da gadon baby. Umma Hadiza kuwa tunda tazo tayi barka ta tafi ko jimawa batayi ba saboda kara da take musu. Gefe daya farin ciki ya cikata na sake ganin sabuwar tarairayar da ake bawa Waheedah...

Ranar suna aka hada hadadden taron suna. Da decoration, Mai dauke da hotan baby sultan da sunan sa.

Abinci kala kala da masu hoto da kayan rabo. Nadra ma tazo sunan itama da nata kayan barkan himili guda.

Akayi hani'an da abinci da kayan rabo. An sha hotuna. Kafin baki kowa ya watse. Ahlam ma ta bada kayan barka kala kala. Gwanin ban sha'awa... Yan uwa kowa yaji dadin haduwar kawunan su.

×××

Ranar da Waheedah ta cika kwana arbain da daya... Hutu na musanman Zayn ya dauka awajen aiki. Ya murje idanu ya tafi gidan Maa.

Allan ya temaka tana asibiti. Sai Waheedah da Najan Isubu da ke tayata reno. Itama Najan tayi bulbul da ita.

Ba abunda ta nema ta rasa. Ga Isubu ya dawo daga tafiyar tashi da ya yi. Alhamdulillah kuma ya samo alkhairai. Rayuwar su ta kara bunkasa.

Najan na ganin shigowar sa ta goye baby sultan tayi sashen Haj Aisha bayan sun gaysa.

Hakan ya sake masa dadi a zuciya. Ya shige gidan wuf yayi dakin Waheedah. Tana tsaye agaban mudubi da daurin zani..

Juyawa yayi ya saka mukulli ya kashe fitila . Ya rufe labulaye. Dariya ce ta taho mata ta danne kawai ,

'ina wuni?"

"Yana wajen ki .... "

Ya karasa wajen ta . Ya janyota jokinsa na ta rawa tamkar mazari.

Ya shiga kokarin cire zanin nata ta hana shi tana turo baki gaba...

"I love and miss you soo much.... Kaman zan zauce " Ya fada yana lalubar bakin ta.

"Naga dazu ma ka zo..."

Ya lakuce mata kumatu kafin ya rada mata cikin kunnenta,

"Kinfi kowa sanin abunda nayi missing... " Ya karasa fada yana rungumar ta tsam a jikin sa.

Ba tare da bata lokaci ba... Ya kwantar da ita akan gado shima ya kwanta... Yana mai aika mata da sakonni kala kala, Sai da suka samu nutsuwa tukun sannan ya sake rungumar ta. Bayan ya sumbaci gefen fuskarta,

"If I had a flower for every time I thought of you, I could walk in my garden forever. I don’t care how hard being together is, nothing is worse than being apart. Nayi kewar ki kwanakin nan arbain da daya... In a sea of people, my eyes will always be searching for you. Waheedah.... Enta FARHATAL QALBI– Kin zamo mun FARIN CIKIN da ke mamaye da ZUCIYAH tah. Sometimes, I knock on the doors of your heart, just to make sure I still live there. Wifey.. No matter what has happened. No matter what you’ve done. No matter what you will do. I will always love you. I swear i...I’ve never had

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login