Showing 78001 words to 81000 words out of 123508 words

Chapter 27 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

710

gefe.

"Harara kuma..... Meya faru?"

"Au tambaya kake yi me ma ya faru? Kan babban bala'in can."

Wayar sa ya ajiye a gefe ya koma ku sa da ita ya zauna. Hade da janyo hannuwanta cikin nasa yana matsawa. Yayin da idanun sa ya narkar da su akanta. Duk janye janyen ta sai da ta hakura ta sallama.

Rungume ta yayi a jikin sa yana shafa gadon bayan ta da hannun sa.

"Meya faru .... Uhm?" Ya rada mata acikin kofar kunnenta.

"Ni ka rabu da ni....." Ta shiga tirjewa.

"Sssshhh... Calm down! Ahlam, Yanzu abubuwan da ke faruwa da mu. Bakya ganin maslaha shine mu zauna mu biyu mu kamo bakin zaren? Ba ruwan third party....ki ce wani abu mana... Banason wannan kawar ta ki tana shiga al'amuran mu. Kinji dear wifey.?"

"Kawata ce ta rai da rai... Wani baren na gayawa? Kai ma kasan kai ne mara gaskiya. Kana treating dina kaman wata baare. "

"Ahlam... Meyasa ba zaki amince ke me laifi ba ce.? Okay fine! Ni na yadda nima me lefi ne. Allah ya baki hakuri. To me zai hana ke ma ki fito ki bada hakurin? Ki sauya halayen ki. Ki rungumi igiyoyin auren da ke tsakanin mu? Eh Ahlam... Why ?"

Ya ki ce jikin ta tayi daga nasa. Tana hura hanci.

"Ni babu wani laifi da na ke da shi. Kai ne me laifi. Don haka kai zaka canza. Ba ni ba. Atoh."

"Haka kika ce?"

"Eh..."

"Okay fine..." Ya fada hade da mikewa ya koma cikin dakin sa ya janyowani dan box ya dauki abunda zai dauka ya zura a aljihu.

Har zai sauka sai kuma ya juya ya dube ta,

"Akwai wani abun da kike bukata babu? Ko na abinci haka?"

"Subscription dina na Netflix za kayi renewing. Sannan data plan dina ma has exhausted ... Sai ka mun renewing. "

Wayar sa ya duba ya yi renewing mata dukkanin abunda ta fada. Sai kuma ya zaro dubu biyu ya ajiye agaban ta.

"Gashi ko zaki bukaci wani abun daban. Na fita aiki "

Ba godiya baare Allah ya dawo da kai gidah lapia. Ta cigaba da danna wayar hannun ta. Girgiza kai kawai ya yi. Ya karasa sauka .

Su kayi kicibus da Waheedah da ke gyara zaman sandal din kafarta zata fita

"Ina kwana...?" Ta gayshe da shi cikin zazzakar muryar ta mai dadin sauraro da dimbin ladabi.

"Alhamdulillah... Kina lapia?" Ya amsa. Ya kuma ji dadin gayshe da shi da take yi. Ya manta yaushe rabon da Ahlam ta gayshe shi tun satin biyu farko na auren su.

"Alhamdulillah....." Ta amsa shi. Hade da bude kofar.

Ya fita. Ita ma ta fice. Cikin zuciyar ta tanata kwarara adduar Allah yasa ba zai dauke ta ba. Bata karasa adduar ba tajiyo shi yana cewa,

"Muje ko? Motar awaje nayi parking tun asubah."

Ta kasa cewa komai. Tamkar ta fasa ihu saboda takaici. Ta daga hannu tana nuni da yatsan ta cikin gidan.

"A...an..abincin safe." Ta samu kanta da amsa shi da haka.

"Oh abinci ko. Ko zaki mun packaging ?sai na tafi dashi office. "

"Toh.." Ta fada, Hade da juyawa ta koma cikin gidan.

Ta harhada komai ta saka acikin kwando . Komai tsaf tsaf. Kamshi sai tashi yake yi.

Already ya fita yana jikin motar sa awajen .

"Gashi .."

"Alright... Thank you! "

Ya shiga motar ya tashe ta.

"Shigo mana..."

"Okay .."

Shiga tayi . Kanta a kàsa sai murda yatsunta take. Ta rasa madafa.

Har sun hau kan titi ya juya ya kalleta. Kafin ya zaro wayar da ke aljihun gaban rigar sa.

"Rike.... Naga ba ki da waya ko?"

Ta daga kai alamun eh. Kafin ta danyi jim kuma. Can ta ce,

"A'a ka bar shi.."

Ya danyi murmushi. Kwarai matuka yana kaunar halayen Waheedah. Yarinya mai nutsuwa da cikar kamala. Ga ladabi da biyayya.

"Ni ba yayan ki ba ne?"

"Shi ne..."

"Tohm dan Yayan ki ya baki waya wani abune?"

"A'ah."

"To saboda emergency issues haka dai bama fata. Amma ai ya kamata ace da waya a hannun ki. Ko dan saboda pdfs na books da assignment haka na school. Ko?"

"Eh..."

"Yauwa to rike."

Karba tayi da hannu biyu. Waya ce Samsung mai kyau purple color. Daga gani kuma sabuwa ce.

"Nagode Allah ya saka da alkhairi ya kara yalwar arziki."

"Aamin Amin. Ban kuma ce kije kina yadawa ba kan na baki waya da sauran su. Ga wani charger nan idan kin bude wajen nan zaki ganta type c ce. Akwai sabon sim aciki. Allah ya bada sa'a ."

Sai jujjuya wayar ta ke. Ba kadan ba wayar ta tafi da ita. Ga ta da kyawu kuma sam babu nauyi.

Ta janyo charger ta rike hade da wayar. Gaba daya dimbin farin ciki ya mamaye mata zuciya da duk wasu gabobi na jikin ta.

"Nagode.... Nagode Allah ya saka da alkhairi. Allah ya kara budi. Nagode "

Yadda fuskar ta ta mamaye da farin ciki ne ya samu kansa shi ma da yin murmushin.

Har suka karasa layin su fannah sam Waheedah hankalin ta na kan wayar ta. Sai danne danne ta ke. Zayn ya yi parking a kofar gidan . Ya zuba mata idanu

"Banda dai kule kulen samari. Ki tsayda hankalin ki akan karatu kinji ko? "

"Insha Allah..." Tana daga kai taga ai har sun karaso

"Laaa" ta fada da sauri ta fice. Ta shige gidan su Basira suka biyawa Fannah.

Waheedah ta zaro wayar tana nuna musu. Suka shiga tsalle suna masu tayata murna sosai suma.

Nan take taji kaso goma sha biyar acikin tsanar da tayi masa ya goge a zuciyar ta.

Suka shige motar ya ja su sai school of nursing.

Har kofar twin theatre da za suyi lectures din ranar ya kai su. Waheedah ta shiga rudani mai tattare da mamakin Zayn .

Ta kasa gane kan yadda yasan komai na daga harkar karatun su .

"Suna jiran ki fa..." Ya fada yana nuna mata su Basira da ke tsaye suna jiran tafuto daga mota su tafi aji.

Ta kasa ce masa komai. Ta fita daga cikin motar tana waiwayon sa. Murmushi ya sa ki kawai. Ya ja motar sa ya fita daga cikin harabar makarantar. Ya yin da su kuma suka shige ajin da zasu dauki darussan ranar.

××××

Sannu a hankali haka kwanaki ke ta tsere mana. Waheedah sunyi sabo kwarai matuka da Zayn. Ta dauke shi tamkar madadin yayanta Kamal.

A nasa bangaren kuwa dakon jidalin kaunar ta ne kullum ke dada tasiri a zuciyar sa da gangar jikin sa.

Yana kaunar Waheedah fiye da yadda alƙaluma zasu rubuta. Zuciyar sa na begen samun Waheedah a matsayin matar aure.

Gangar jikin sa na ingiza da kwadaituwar kasancewar Waheedah a tattare da shi.

Amman gaba daya ya kasa sanar mata. Ta kuma kasa gane inda ya nufa. Ta riga da ta dauke shi a matsayin dan uwan ta na jini. Tamkar babu aure a tsakanin su.

Ganin yadda kullum ya ke dada karewa a tsaitsaye. Gashi Maa ta ki zama ta fuskanci maganar. Ranar da ya sake zubewa ya nemi rokon alfarmar samun Waheedah. Ta wanke fuskar sa da gigitaccen marruka a dama da hagu na gafen fuskar sa.

Bai sake bi ta kanta ba da maganar. Kai tsaye ya samu mahaifin sa ya sanar da shi. Alokacin kuma Ummimi mahaifiyar mahaifin su ta zo .

Zayn ya kasa cigaba da boye maganar. Daman Ahlam ta karasa kai shi karshe da halayen ta. Tamkar zaman haya haka suke yi a gidan na su. Ta tattara shi ta watsar a gefe.

Hakki na rayuwar aure ma sai ya ta rokon ta zata bashi dama. Idan kuwa bataga dama ba sam bata bari ya kusance ta.

Dukkanin abubuwan da ke faruwa daman dangi sun sani. Don haka zuwan da Ummimi tayi ta kirawo dukkanin sauran yaran nata da ke kusa da matayen su. Ciki har da mahaifiyar Ahlam.

Ummimin tace gwara ayi me yiwuwa. Ta yanke ta gille. Ahlam dinma Ummimi ta sa Zayn ya kawo ta gidan na The Adams Family.

A babban parlorn gidan duk suke a zazzaune. Ahlam sai wani fiffika ta ke yi. Ummimi tayi gyaran murya ta fadi komai a takaice. Kasancewar kowa ya san masaniyar tsakanin Zayn da Ahlam .

"To ni Ummimi menene laifi na? Shi ne tun farko dama ai ba kauna ta yake ba. Bayan munyi aure halayen sa suka fito " Ahlam ta fada tana hararar Zayn.

"To naji mu dauka ace hakanne. Ke menene yasa kike tauye masa hakkokin auren sa da ke kan ki? Eh? Tsinke wannan bakya dauke wa karya nayi?"

"A'a..."

"Toh kadan kenan daga cikin sakacin wasu matan akan bai wa yan aiki ragamar komai na rayuwar aurensu......🤸


_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_


_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
           
         💞

_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:56_


_____

   Ahlam ta daga idanu da sauri ta dora akan Ummimi. Kafin cikin bacin rai da takaici tace,

"Bangane ba Ummimi.... Sakacin me nayi?"

"Da fari kafin ma a samo miki me tayaki aiyukan. Ba almajirai kika dauka har biyu ba yara suke gudanar da aikace aikacen gidan baki daya?"

Ba tare da ta ce komai ba. Ta zumbura baki gaba tana mai yatsina fuska. Ummimi ta sake zare mata idanu,

"Tambayar ki na ke kinyi shiru. Haka ne ko ba haka ba ne?"

"To ai aiyukan ne sunyi yawa ba zan iya ba ."

"Haba Ahlam, To menene ladan da zaki samu na rayuwar auren idan har bakya aikace aikacen gidan da mijin ki zai sanya miki albarka? Kullum kina kwance kamar ruwa lamama. Da waya a hannun ki hannu bibiyu. Tunda na ke ban taba ganin me danna waya a duniya irin ki ba Ahlam. Na hane ki tun kafin auren nan ashe baki dai na ba? Kinyi uwar watsi da zance na.... "

"Ummimi please ... Abar zancen nan."

"Ba za'a bari ba. Ummimin kike kalla kina abar zancen nan? Wacece ke? Shashasha, sakarya. " Cewar alhaji nouh mahaifin na Ahlam kuma da ga Ummimi.

"Yi hakuri Baba. Kiyi hakuri Ummimi." Ahlam ta basu hakuri. Kanta a kàsa. Ya yinda kasan zuciyar ta ke mata zugi.

"A mata afuwa Ummimi..." Farfesa Adams ya fada yana murmushi

"Ai ni baki daya ba ni da tace wa... Sai fatan shiriya. Allah ya kuma ya huci zukatan dukkanin mu Amin."

"Amin Ummimi."

"Amin."

"Zayn wane hukunci ka yanke akai eh.?" Alhaji Nouh mahaifin Ahlam ya tambaye shi.

Kan Zayn a kàsa cikin ladabi yace,

"Duk hukuncin da kuka zartar ya yi."

"A'ah ai ba zamu tauye maka hakki ba son. Kuma magana ta gaskia duk wanda ya zauna ya auna rayuwar da kukayi da Ahlam zai ga kana cutuwa aciki sosai. Ba bu kuma iyayen da zasu so haka ya faru da dan su. Dan haka ni de a nawa ra'ayin. Rabuwa da Ahlam shine mafi alkhairi a tattare da kai."

Da sauri Ahlam ta daga idanu ta sauke akan mahaifin ta jin abunda ya ke cewa. Saboda bata taba zato ko tsammanin haka daga gare shi ba.

"No kar ka ce ha ka dan uwa. Ni tunanin da na ke ma Allah yasa laifin ba daga Zayn ba ne. Saboda yanada zurfin ciki matuka." Farfesa Adams ya fada yana kallon Zayn

Shi dai Zayn kanzil bai ce ba. Alhaji Nouh ya girgiza kai kafin cika daga yatsa ya nuna Ahlam yace,

"A'ah zancen nan fa ba sabo bane. Anyi fadan Anja kunnen yarinyar nan yafu a kirga. Ni da kai na gata ba karya nake ba wallahi sai da na kirata waya video call lokacin ina Cappadocia. Na ja kunnenta sosai tace mun ta dai na . Ashe ashe labarin kanzon kurege ne. Don haka babu ruwan Zayn wallahi. Ai dama na sha jiyota da mahaifiyar ta ga tanan tana mata fada akan yin aiki da dai na sangarci saboda aure zatayi. Amman taki yi. Ga banzan halayen data tsira na gayawa kawa komai. Da turawa bloggers neman shawara duk fadin dangin da muke da shi ba mu isheta ba mu sai iyayenta na waya. Na karanta writeups dinnan ba adadi wallahi. Ina mamaki wanda ko a mafarki ban taba zato ko tsammanin haka ba. Kuma wallahi wallahi yarinyar nan ba ta kaunar Zayn."

Baki daya sai akayi masa caaaa jin abunda ya fada a karshe kan Ahlam din bata kaunar Zayn.

"Zancen ka na karshe da gyara ...." Ummimi ta fada tana murmushi.

Alhaji Nouh ya girgiza kansa kafin ya cigaba da cewa,

"To bata kaunar tara iyali da shi. Wai kamar Ahlam har ta san ta dinga shan contraceptive pills? Kuma guzurin su tayi ta tafi su da gidan. To Ummimi bata kaunar karuwa da shi ai bata kaunar shi wallahi. "

"Eh to da wannan gaskia..."

"Yauwa ..Ni dai idan ana neman shawara ne.  Shawara daya zan bayar itace ta rabuwar su. A raba auren nan dubi yadda yaron nan ya zama fisabilillahi. Tamkar ba Zayn ba. Ita kuma dubi yadda take hawa kamar farashi. Idan aka bar shi ya cigaba da zama da ita tabbas an cuce shi. A cire batun zumunci a dubi hanyar gaskiya. Idan ya cigaba da zama da ita Allah karasa illata shi zata yi. Tunda dukkanin abubuwan da suke faruwa ma ba shi yake fada ba tursashi ake idan an ga damuwa a tattare da shi. Kuma ace kaman Ahlam kuna garin nan unguwa ma kusan daya amman bata san ta zo nan gidan ta gayshe da surukan ta ba? Kafin ku zama surukan natan dan uban ta ai iyayen ta ne ku. Kullum 24/7 yarinyar nan tana online tana chatting. Gaba daya rayuwar auren a wasa ta dauke ta da kuma shiririta. Saboda haka gwara a kawowa tufkar hanci. Dan Allah Ummimi.. ko kuwa Yaya?" Ya juya saitin Yayan su mahaifin su Zaid . Alhaji Nouruh.

Alhaji Nouruh ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ya dubi Ummimi can ya ce,

"A duk sanda akayi saki al'arshin ubangiji na girgiza. Aure martaba ne raya sunnah ce ta manzo SAW. Sannan rabuwar sa kuma ba'aso idan har ba da wani kwakkwaran dalili ba. Sannan wannan aure dai na zumunci ne akayi. Ba kuma a kansu aka fara ba. Ba kuma zaa dena a kan su ba. Insha Allah, Sai dai zance na gaskiya auren Zayn da Ahlam zamantakewar su tazo da tangarda. Kamar da cutuwa acikin sa. Kada rayuka su zo suna baci gaskia. Ba fata muke ba. Kada alakar su ta janyo barakar rabuwar zumunci." Cewar Alhaji Nouruh

"Haba haba su din banza. Mu muka haife su fa ba su suka haife mu ba dan uban su. Aure kuma ma dena zancen rabuwar sa. Haka zasuyita zama dole su hakura." Farfesa Adams ya karasa fada cikin fushi a hasale.

Ummimi da ke gefe tana sauraron dukkanin su. Har suka karaci hayagagar su kafin tace,

"Duk naji bayanan ku..... Kusan wannan shine karo na farko da muka fara samun sabani a aurarrakin zumuncin da muke hadawa. In dai ban manta ba ko?"

"Zancen ki haka yake Ummimi."

"Hakane Ummimi."

"Tabbas..."

Baki daya suka shiga amsa ta. Ta gyada kai kafin ta cigaba da cewa,

"Ya ku ke ganin zamu shawo kan wannan matsalar iye?"

Alhaji Nouh ya numfasa kafin cikin matsa hannuwan sa biyu yace,

"Tunda abun ya fara zuwa da haka, Ummimi me zai hana ..." Sai kuma yayi shiru bai cigaba da fada ba.

"Ina sauraron ka ... Me zai hana me?"

Hannun sa ya daga tamkar zai yi nuni da wani abun sai kuma yace

"Me zai hana abar hadakar auren nan da akeyi. A dan dakata haka. Tunda 'baraaka ta fara shigowa ciki . Ko kuwa?"

Alhaji Nouruh ya kada kai da jin abunda dan uwan na su ya fada. Kafin shima yace,

"Gaskia hakan ya kamata. A dakata din. Allah sa hakane yafu alkhairi."

Farfesa Adams yayi shiru bai ce komai ba. Fyace muzurai da yake ta faman yi. Domin bayasan rabuwar auren nan na su Zayn. 

Cikin kufulewa yace,

"Ga Jannat nan da Zaid suna zaman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login