Showing 84001 words to 87000 words out of 123508 words
kwanta mun, Ta yi mun. Don na kammala dakin da na ke ginawa acikin gidah na ma. Bani kuma da matsalar komai. Ita kawai zaa daura aure a kawo. Idan da son samu ne ma a hade da na zainabu. Ance farkon watan gobe ne ko?"
"Kai naji dadin zancen nan. Na'Ateeku da ma da tsinanniyar yarinyar nan ta ki ka har ciwon kirji nayi saboda takaici. Kai din babu macen da zata ki ka. Kuma kanta tayi wa. Yanzu bagashi ba. Ta rasa mijin auren tana yawon rariya? An gama. Zahara'u ta zama ta ka Na'Ateeku. Ba ka da shauran damuwa. Ka samu mai sunan Malam ku tsara komai."
"Godiya na ke Marka. Allah shi saka maki da alkhairi. Kifin gwangwani, Shayi da biredi mai yanka yanka, Ga tsiren kasuwar dare ba fashi zahara'u kullum idan aka yi auren nan sai taci. Ranar tuwon laraba kuwa indomi din haladu mai shayi da lafceciyar wainar kwai da lemon kwalba zata ci babu ita babu tuwo. 😂 Ga wannan kya ci goro ba yawa." Ya karasa fada hadi da ciro gudar dari biyar ya mika mata.
Tamkar Marka ta zuba ruwa a kàsa ta sha don farin ciki. Su kayi sallama da Na'Ateeku. Ta zura kudin ta a zani tanata murna.
Da guda ta koma cikin gidah. Ta kamfaci ruwa a cikin jarka ta zuba a kàsa. Tayi goho ta dukar da kan ta ta shiga shan ruwan kasan .
Ta dago bayan ta sha. Ta sake dora hannu a hanci ta saki guda.
"Menene Marka.?"
"Shafa mana Marka."
Duk matan suka shiga tambayar Marka . Fuskar ta kumshe da farin ciki marar misaltuwa ta ce,
"Zahara'u ce akazo neman auren ta. Auren kuma tare akeso a daura da na zainab. "
"Barka Marka... Barka."
Suka shiga tayata murna.
"Wanene manemin Marka?"
"Hmm abu kamar almara. Na'Ateeku dai in karkare muku zan ce. Yace wanke zahara'u zaai kawai a mika ta. Shirgegen dakin daya gina acikin gidan sa na ta ne ya ce. Baya bukatar komai daga gare mu. Ya ce, Kifin gwangwani, Shayi da biredi mai yanka yanka, Ga tsiren kasuwar dare ba fashi zahara'u kullum idan aka yi auren nan sai taci. Ranar tuwon laraba kuwa indomi din haladu mai shayi da lafceciyar wainar kwai da lemon kwalba zata ci babu ita babu tuwo... Na san kuma taliya ma yar kakkaryawa zasu dinga ci."
Baki daya sai gidah yahautsine da ife-ifen farin ciki. Zahara'u da ke daki sai murmushi ta ke. Idanuwan ta na hango mata kifin gwangwani da wainar kwai da tsiren da zata dinga ci.
Duuu yan wajen tsakar gidah suka shige daki don taya zahara'u murna.
Marka nata taka rawa da sakin guda . Hadi da tattaro tsinuwa da mugayen alkaba'i tana dorawa a sunan Adamushe mijin zahara'u na da .
"Mummunan banza mummunan wofi. Da hanci bajajje a saman fata. Baki uwa bayan tukunya. Yana tafe yana hankada kirji sama. Dan iska matsiyaci. To ga naateeku nan zai share mana kukan mu. Ahh shokeeei." Ta kwarfata hannuwa kasa ta mayar sama wai ita nan rawar shoki ta ke kwasowa.
×××××
Ba wata kwalliya tayi ba. Ta zura doguwar riga baka da dankwalin ta. Wadda Haj Hameedah ta bata.
Ta shafa man lebe da farar hoda hade da dan zizara kwalli a idanun ta
Ta dauki sabon medicated glasses din ta ta saka shi a fuska.
Ta dauki yar karamar jakar data zura kayan ta ta fita daga cikin dakin da ya ke a matsayin na ta.
Tana bude kofar parlor ta hangi Ahlam malale akan kujera hannunta rike da waya tana dannawa
"Sis..."
Sai da ta fada sau biyu sannan Ahlam ta farga.
"Naam dearest one ... Sai ina?"
Waheedah tayi murmushi kafin tace,
"Kinsan dama na gaya miki zanje gidah, za'a kawo kayan auren yayata. Ranar Monday insha Allah zan dawo nan din daga school. "
"Oh haka fa. Allah sarki, Ki gayshe su please "
"Zasu ji, In sha Allah... Sai na dawo."
"Okay dear sis "
Waheedah ta fita daga cikin gidan bayan ta kullo kofar.
Su kayi sallama da baba mai gadi ta futa don hawa dan adaidaita sahu da zai kai ta gidah
Tana tafe cikin nutsuwa akan hanya. Sai ga dosowar Zayn Adams. Tun daga mudubi yake hango ta.
Tana tafiya ahankali tamkar mai tausayin kasa. Ya samu kansa da kallon gefe. Yar majalisar mazan layin sun zuba mata idanu
Kishi ya taso ya harde masa a wuya. Tsayawa yayi chak da motar ta sa. Ya kira number dinta da dayan layin sa da yake a matsayin Zayn ba wanda suke chatting da sunan Dawood ba.
"Assalamu alaikum" sanyayyar muryar ta. Ta doki kofar kunnen sa.
"Wa'alaykm Salam.... Ina zakije haka?"
Dan daga kai tayi ta hango shi a mota
"Zanje gidan mu ne ..."
"To karaso .."
Karasawa tayi. Ya zuba mata idanu. Da har sai data janye idanun ta akan sa.
"Shigo na ajiye ki."
"Ka bar shi Ya Zayn . "
"Shigo na ce "
Bata sake musu ba. Ta bude murfin mota ta shiga tana adduar hawa abin hawa
Ya juya ya kalli jakar da ke hannun ta . Kafin ya tambaya ta yi saurin gaya masa duba da a karkashin su ta ke,
"Zanje gidah ne sai Monday zan dawo insha Allah ..."
"Meyasa?" Yayi subutar baki wajen tambayar ta.
"Zaa kawo kayan yayata ne.... "
"Okay.... Allah ya sanya alkhairi "
"Amin...."
Yaja motar suka dauki hanya. Na'urar sanyi nata busa su. Ya yin da wakar forever ta gyakie ke tashi ahankali.
Yana so yagaya mata sakon zuciyar sa amman zuciyar sa ta hana shi. Sai jan kasan leben sa ya ke yana taune shi.
A haka suka karasa har layin su wajen gidan su Basira.
"Ajiye ni anan ma .. Nagode."
"Ba gidah kika ce ba?"
"Zan karba notebook dina ne awajen Basira "
Ibrahim da ke zaune acikin yan majalisar su hangen Waheedah da yayi ya mike da sauri sai murmushi ya ke.
Zayn ya samu kan sa da sauya fuska.
"Kawai dai wajen saurayin ki kika zo."
"Haba Allah ya kiyaye ... Nagode bari na sauka. "
Zayn yaci magani,
"Shiga ki karbo na sauke ki agidah "
"Ai zan..."
"No buts .... Plz"
Ta shige gidan su Basira ba dadewa suka fito tare da ita. Ta tsaya suka gaysa da Ibrahim. Zayn na ta aika mata da sakon harara.
Suka shiga ya sauke su a kofar gidan su Waheedan.
"Mungode sosai..."
Har zasu shiga gidah yasamu kansa da cewa,
"Waheedah...."
Ta juya da sauri .
"Naam Ya Zayn..."
"Shikenan ma, Take care "
Sukayi waving ta shige gidan su dasauri. Shi kuma ya ja mota ya koma gidan sa.
Ransa duk ba dadi. Ya kara tabbatarwa kansa lalle Waheedah FARIN CIKIN ZUCIYAr sa ce. Gashi daga rabuwar su. Ya samu zuciyar sa da radadin rashin ta .....
A haka ya karasa parking a harabar gidan sa ya shiga ciki bakin sa dauke da sallama....
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: *FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:58_
___
*Ko da* ya shiga, Ja ya yayi yai turus. Ganin parlorn a hautsine. Tamkar ba gidan da mace ke ciki ba. Bayan dazun da safe kafin fitar sa ya tarar da parlorn baki daya a gyare a kuma tsaftace. Ya yin da komai ya ke muhallin sa. Har da guzurin kamsashshen turaren wuta na kamfamin turarukan yerwa incense and more.
Robar faro ta ruwa a wulle a kasan kujerar da ta ke kwance akai. Gefen robar kuma sachets ne na biskit da ledojin chocolate na maltesers sai gwangwani na Pringles.
Tana kwance akan kujera ta mike kafafun ta a tare ta dora su a hannun kujerar. Hannuwan ta duka biyu kuma ta rike wayar ta tana dannawa.
"Assalamu alaikum wa rahamatul Allah, Wa barakatuh!" Ya daga murya wajen sa ke yin sallama a karo na uku.
Ya yin da ya jingina da jikin kofar parlorn ya zuba mata idanu. Ganin sai a sannan ta daga kai ta dube shi. Wato duk sallamar da yayi bata jiyo ba. Saboda baki daya hankalin ta da nutsuwar ta na kan wayar da take dannawa. ?
Shikenan idan har Waheedah bata gidan ba sauran mutunci da gidan yake da shi? Ba gyara babu kulawa? Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ganin ta kalle shi ta mayar da kanta kan wayar hannun ta
Bai wani damu ba. Domin ya saba da shirmammakin halayen Ahlam irin na ko in kula din da take masa. Tamkar shi din ba miji bane a gare ta.
Kai tsaye ya wuce kitchen, Ko'ina a kitchen din tatas ya ke. Komai a kintse a kuma gurbin sa.
Ya dan dudduba mazuban abinci. Babu komai na abinci. Ya juya ya hango parlor Ahlam na kwance abunta tana karkada kafafu. Wato saboda Waheedah bata nan yau ba abinci kenan?
Ya girgiza kai kawai, Ya bude freezer ya dakko wata fura daya saka jiya . Ya dauki cokali ya haura sama. Kasan zuciyar sa na masa zugi da radadin halin ko'in kula da Ahlam ke nuna ma sa.
Zama ya yi a parlorn saman. Ya bude furar da basmala ya shiga sha. Dadi sosai tayi masa. Ta kuma cika masa ciki. Yana shanyewa ya shige bandaki ya wanko bakin sa.
Ya kunna tv ya lalubo tashar labarai ta BBC yana kalla. Can ya janyo wayar sa ya shiga Whatsapp.
Da status dinta ya ci karo. Ta dora hotunan akwatunan Zainab yar uwarta da aka kawo. Da caption din 'congratulations dear sis. Allah yasa albarka da alkhairi amin. '
Hoto na gaba da ta saka kuma ita da kawarta ne Basira. Dukkanin su sunyi dariya . Samun kan sa yayi da zooming din dai-dai saitin fuskar ta yana kalla.
Tun daga kan girarta cikakkiya mai dauke da gashi baki ya zuwa manyan idanun ta dake dauke da gashin ido zara zara a kanannade suna sheki. Ta saka kwalli da ya karawa idanun annuri. Har ya kan dan karamun bakinta. Da ke da labba pink. Suna sheki saboda pink lipstick din da ta sa ka.
Ya samu kansa da tsurawa hotan nata idanu tamkar yana nazarin wani abun. Can ya ajiye wayar tasa ya mike. Daki ya shiga ba jimawa ya fito ya sauka kasa bayan ya dauki wayar sa.
"Zayn...." Ahlam ta kira sunan sa. Tana zaune akan kujera. Kalba biyu ce akan ta sun mimmike.
Gata da cikar gashi amman ba kula. Ya kalleta ya kauda kansa zai fita ta sake kiran sunan sa.
"Zayn."
"Ya akai?"
Ta turo baki gaba .
"Subscription dina ne ya kare. Na ke so kayi mun renewing "
Girgiza kai kawai yayi. Ya kalleta sosai kafin yace da ita,
"Kin gama?"
"Me fa?"
"Maganar"
"Eh..."
"Toh." Ficewa kawai yayi kai tsaye ba tare da ya sake ce mata komai ba.
Baba mai gadi na zaune akan kujera . Hannun sa dauke da yar rediyon sa ya saka ta a saitin kunnen sa.
Yana hango Zayn ya tashi da sauri ya shiga tura gate.
Zayn din ya nufe shi yana murmushi,
"Sannu da kokari Baba."
"Yauwa sannun mu."
Hannu ya saka ya zaro dubu daya ya mikawa Baba mai gadin.
"Kayi mana gafara Baba. Bamu kyauta ba. Ga wannan kaci abinci yanzu da daddare ma . Dan Allah"
"Ah kar ka damu ranka ya dade. Kudin da ka bani jiya ma har yanzu da shauran su. Na ci abinci na dadewa awajen me sayar da abincin tsallaken titi , Ga kudin ka."
"A'a Baba. Ka bar su ka sake sayan me nauyi kaci sosai dan Allah. Ni zan fita "
"To shikenan. Nagode Allah ya saka da alkhairi."
"Amin Amin."
Mota ya koma ya shiga ya tayar da ita ya fita. Kai tsaye ya wuce gidan su. Dai dai kofar gate din layin ya tsaya da motar sa. Ya janyo wayar sa ya tura wa Ahlam data ta bank.
Kafin ya karasa gidan na su. Masu gadi suka bude masa gate ya shige da motar sa.
Dakin sa ya shiga da yake na kwanan sa a da kafin yayi aure. Dan lokaci zuwa lokaci ya kan je ya buda ya shiga ya kwanta.
Domin komai na nan a mazaunin sa baa cire ba. Sannan wasu kayayyakin na sa suna nan bai dauka ba.
Kwanciya yayi akan gadon sa bayan ya karkade da addu'oi. Wayar sa dake gefen sa ce ta shiga kara. Tamkar ba zai dauka ba. Sai kuma ya daga yana kallon screen din don ganin me kiran. Abiey din su ne, Don haka da sauri ya dauka ya kara a kunnen sa.
"Wa'alaykm Salam... Barka da yammaci Abiey.. Eh, Eh... Ina daki na, Okay tohm, Gani nan "
Mikewa yayi da sauri. Ya fita daga cikin dakin bayan ya kulle shi da mukulli.
Kai tsaye ya wuce sashen mahaifin na su. Bakin sa dauke da sallama ya shiga. Da ke transparent sliding door ce a babban parlorn. Ta nan ya hango har da mahaifiyar su aciki da kuma Ummimi.
Ya shiga parlorn bakin sa dauke da sallama. Ya tsugunna har kasa ya gayshe su cikin girmamawa.
Suka amsa fuskokin su a sa ke. Haj Hameedah sai kallon Zayn ta ke ta gefen idanu. Ya faada sosai tamkar wanda ya tashi daga ciwo.
"Ina Ahlam ...? Tana gidah?"
"Eh Abiey..."
"Fatan kowa da komai lapia dai ko?"
"Alhamdulillah Abiey....."
"To masha Allahu ."
"Zayn... Kasan akan meyasa na sa aka kirawo mun kai?"
"A'ah Ummimi .."
"Kayi hakuri da hadin auren ka da na saka akayi da yar uwar ka Ahlam..."
"Haba Ummimi. Hakurin me kuma? Dan Allah ki dena cewa haka. "
"Dole na fara da ba da hakuri Zayn. Domin ni ce maqasudin shigar ka wannan mawuyacin hali. Dubi yadda ka rame ka fice daga hayyacin ka. Kasancewar ka mai dimbin zurfin ciki. Baka fadin damuwar ka. sai an tasa ka agaba an maka tilas. Banyi zurfin tunanin mabambamta halayen ku ba. Na yi amfani da kasancewar ku a dangi daya. Ka gafarce ni kaji?"
Zayn yayi murmushi kawai kafin yace,
"Allah Ummimi ba komai. Kuma ba kiyi lefi ba. "
"Ka dai yi hakuri. Ka kuma yafemun. Kaji?"
"Tohm "
"Allah ya maka albarka .."
"Aamin Ummimi."
"Yauwa .. Sai batun yarinyar da kace kana so. Wacece? "
"Wata ce.." Ya fada ahankali.
Ya daga idanu ya dora akan Maa data murtuke fuskar ta. Tana cilla masa kallon kashedin kada ka kuskura ya ambaci Waheedah.
Saukar da kansa kasa yayi sosai. Gaban sa na tsananta bugawa,
"Yar gidan wacece? A'ina take? Ina fatan kuma ta fito daga tsatso masu dattako da sanin ya kamata. Sannan mai hankali ce da wadatar zuciya... Toh Alhamdulillah. " Ummimi ta karasa fada tana kallon farfesa Adams Nasser.
"Haka zancen ki yake Ummimi... Zayn kaaji dukkanin abubuwan da Ummimi ta fada. Ina fatan kamar yadda Ummimi ta fada yarinyar na da hankali da sanin ya kamata. Sannan wacece?"
Zayn yayi shiru. Rashin sanin abunda zai fada.
"Magana ake ma ka."
Kansa a kasa yace,
"Wata ce.... Ummimi"
"Budurwa ce ko bazawara.? Karka ji komai dan na tambaye ka ha ka.. Dukkanin su da za'a aura ne. Sai dai bazawara ana son aji dalilin da ya fito da ita daga gidan mijin ta na baya ka gane?"
"Eh! Ummimi."
"To masha Allahu. Waccece daga ciki?"
"Bu... Budurwa ce."
"To masha Allahu. Allah ubangiji yasa kayi zabi na kwarai. Allah kuma yasa haka ne yafu alkhairi. Kaji ko?"
"Eh..Aamin Yaa Rabbi. "
"To Insha Allahu. Manya zasu shiga cikin zancen. Sai dai har yanzu baka fadi yar gidan wacece ba "
Hannuwan sa a hade yana harhade su . Rashin sanin abunda zai fada. Ganin sun zuba masa idanu suna sauraron cewar sa . Hakan ya sa shi yanke shawara kan cewar,
"Ba .... Ba mu. ... Bamu gama... "
"Baku gama dai-daita tsakanin ku ba kakeson cewa?"
Ya daga kansa alamar eh.
"To ku dai-daita din. Kada abun ya dau lokaci. Saboda manya su shiga ciki kaji ko?"
Ya gyada kansa sama. Kafin yace da su,
"Toh! Insha Allah."
"Masha Allahu. Allah yayi muku albarka baki daya, Amin."
"Allahumma Aamin."
"Zaka iya tafiya... "
Durkusawa yayi ya musu sallama. Ya fice daga sashen. Kai tsaye