Showing 12001 words to 15000 words out of 123508 words
SubhanAllah! Haba Sa'adatu "
"Atoh ai gaskia ne. "
"To Allah ya baki hakuri."
"Matsalar ki ce."
Umma hadiza bata sake cewa komai ba. Tayi hanyar dakin Marka kai tsaye tana sallama a hankali. Shiru ba amsawa . Ta dan zura kanta kofar dakin Markan. Bata nan sai yar rediyon ta da keyi ita kadai. Nan da nan kuwa Umma Hadiza ta saka hannu ta kashe gudun kar battery din yayi sanyi.
Sannan ta fito daga ciki tayi dakin su Kamal. Sai Najib shi kadai yana fiffita da mahuci. Tayi sallama ya amsa yana dan gyara kwanciyar sa.
"Sannu da zuwa Umma..."
"Kai zan wa sannu Najib. Ina yayan na ku?"
"Bai jima da yin wanka ba ya fita. Yace na ce miki ya dan ji dadi jikin sa ya tafi kasuwa "
"Masha Allahu! Allah ya kara muku lapia . Amin"
"Amin Ummah. Nima daman jiran dawowar ku nake . Ko ke ko Waheedah "
"Ai ga ni na dawo. Wani abun ne Najib?"
"Ah babu komai wallahi. Nima so nake na fita na dan zauna ko a bakin titi ne."
"Alhamdulillah! Jiki ya yi sauki. Allah ubangiji ya kara muku lapia mai dorewa. Allah ya takaita wahala, Aamin Yaa rabbi."
"Aamin Aamin Umma. Bari na dan watsa ruwan ni ma."
"Toh Najibu. Akwai ruwa ai. Na kwallan yafi dumi."
"Tohm Umma."
Fuskarta cike da farin cikin jin dadin ganin ciwon nasu ya dan lapa. Gashi har daya ya futa ma daya kuma zai fita yanzu. Bayan dogon zangon da suka dauka suna fama da jinya. Dama haka cutar sickler/ amosanin jini yake. Ya lapa ya tashi. Sai fatan samun lapia ga dukkanin masu fama da ciwon. Allah kuma yasa hakan ya zamto musu samun rahamar Allah , Aamin. (Our warriors !! Allah ya baku lapia mai dorewa. Da dukkanin marasa lapia na gidah dana asibiti.) Aamin.
"Ummah ya naga kinata murmushi ne? Allah yasa murmushin alkhairi ne." Cewar Najib daya gama wanka ya zura kayan sa.
Umma hadiza ta sake murmusawa kafin tace,
"Murmushin farin ciki ne Najib. Babban murmushin da nake yanzu bai wuce na ganin warwarewar jikin ku yayi ba wallahi. Har a raina baka ji dadin da nake ji yana ratsa ni ba."
"Allah sarki Ummah.. Allah ya kara mana lapia ya yaye mana dukkanin matsalolin mu. Ya azurta mu muma muyi miki iyakar kokarin mu. Dan har mu koma ga Allah ba zamu iya biyan ki abunda kike mana ba Ummah. Allah ya kara miki lapia da nisan kwana..."
"Da imanin Allah."
"Ai kuwa dai da imanin Allah. Allahumma Aamin Umma."
"Sai abu na biyu. Idan kun dawo baki daya an jima na gaya muku. Amma kafin sannan dubi abun arzikin da ke gabana. Gidan da Najaatu ta sama mun aiki ne suka babba mu. "
"Masha Allah. Allah ya saka musu da mafificin alkhairin sa . Gaskia mutanen arziki ne. Yanzu du wannan abubuwan haka ? Masha Allah ."
"Wallahi kuwa Najib. Amin Aamin. Sun san abun arziki. Mutanen kirki ne."
"Toh umma me zan tayaki da shi kafin na fita?"
"Ba abunda zaka tayani dashi Najib. Kayi ficewar ka. Yanzun nan zan hada komai "
"Toh shikenan Umma. Sai mun dawo."
"Sai kun dawo Najib. Allah yayi albarka ."
Nan da nan Umma Hadiza ta shigaa harhada kayan girkin da zatayi. Ta dake kayan kamshinta waje daya saboda qarnin kajin. Ta wanke su tas bayan ta yayyanka su tsoka da yawa.
Ta hada wuta ta fara tafashen kazar da kayan kamshi. Dayan murhun kuma ta dora ruwan taliya. Tanata aikinta ita daya agidan du ba kowa. Har Allah yasa ta kammala komai ta soye naman ta zuba komai a muhallin sa tukun sannan ta kai cikin daki bayan ta kakkasafce na kowa a faranti. Taliyar da miyaar ma nanma ta zuzzuba ta ajiye.
An kira sallah kenan. Bayan tayo alwala ta tada sallar ta idar. Tana zaune tana addu'oi. Waheedah ta dawo daga makaranta ita da Zainab . Can sai ga shigowar Marka. Ba jimawa tamkar hadin baki sai ga Sa'adatu itama ta dawo. Sai malam NaLado daya dawo a karshe.
"Kamshin meye wannan haka?" Cewar malam NaLado hadi da fara dauke murafan kwanuka. Yana sake bude kofofin hancin sa.
"Marka kamshin me nake ji haka.?"
"Kai wanene ya kashe mun yar radio di ta iyye?" Cewar Marka. Ta fito daga cikin dakinta tana huci tamkar zakanya.
Sai da Umma hadiza ta shafa adduar da ta daga hannuwa sama tukun sannan ta mike ta nannade sallayar ta ajiye ta a bakin gefen katifa.
"Ni ce marka. Naga tana tayi ita kadai kada batirin yayi sanyi."
"Mts! Dama na san sai ke wallahi. Tsugudidi kashin o'o. Yanzu banda nemawa kai magana. Akan wani dalilin zaki kashemun radio bayan sarai kinsan ba kida hurumin kashewar? Tukun nama akan wane dalilin zaki ketare ki shigaa cikin daki na iyye? Nace akan wane dalili. Kuma na rantse da rantsuwar ba fashi sai kin gyaro mun radio ta. Yanzu gashi nan kinsa ta denayi baki daya. Dama joganeta nake ahankali na kunna amma saboda tsabar mugunta shine zaki lalata mun. To wallahi sai kin gyaro mun kinji Allah kuwa." Marka ta karasa fada , Hadi da ajiye rediyo din agaban Umma Hadiza dake tsaye tana sauraron Marka ta karasa abunda zata fada.
Doguwar ajiyar zuciyar ta sauke .kafin cikin muryar lallashi da ban girma tace,
"Kiyi hakuri Marka. . Wallahi ba da sani nayi miki haka ba. Wai dan kada batirin suyi sanyi tanata yi ita kadai shi yasa na kashe. Abunda yasa na shigaa tsakar dakin ki kuma dana dawo ne zan gayda ke ba kowa agidan sai Sa'adatu da na hadu da ita a zaure zata fita. Abunda ya saka na kashe kenan wallahi. . kiyi hakuri dan Allah, ki gafarce ni."
"Kinibibin banza dana wofi." Marka ta shigaa mita a kasan makoshi.
"Nace marka kamshin .."
"Dan Allah mai sunan Malam ka kyale ni. Kamshi da kakeji haka nima nake jinsa. Haba."
"Kiyi hakuri Marka. Kamshi kuma gidan dana samu aikatau ne matar gidan zatayi tafiya shine ta bamu kayan miya da taliya da kaji guda biyu. Shine ina dawowa na fara aikin su ban jima da karasawa ba. Ga sunan na zubawa kowa a mazubi."
"Wanne ne nawa?" Cewar Malam NaLado sai wulkita idanu yake yana hangen inda zai gano nasa.
"Gashi Malam naka. Marka ga naki kema. Sa'adatu ga naki ke da yaran. Ke ma Waheedah ga na ku nan."
Malam NaLado ya karba da sauri ya koma kan turmi ya zauna yana ci. Sai gyada kai yake yana lumshe idanu
Hakama marka data karbu nata sai baza hanci take tana shakar kamshin miyar dataji komai ta hadu da dadi. Dama umma hadiza akwai iya girki idan ta samu kayan abinci
Inna Sa'adatu ma data karaci hura hancin ta. Daga karshe bajewa tayi tana ci. Sai taunar kashi kake ji. Kunnuwa na motsawa.
Kamal ne ya fara dawowa. Sai Najibu daga karshe. Umma hadiza ta basu nasu abincin. Tukun sannan itama ta zuba nata tanaci.
Daga ita sai su waheedah dake gefe tana taune kashin cinyar kaza. Alokacin umma Hadiza ke sanar dasu yadda sukayi da Hajia Hameedah. Bata boye musu komai ba. Kwarai matuka sun taya Umman ta su murna. Sai farin ciki ya kara ninkuwa da annushuwa a fuskokin su da zukatan su.
Bayan sun gama cin abincin. Umma hadiza ta dakko dubu daya ta bawa Najibu kan ya siyo sabuwar rediyo ya kaiwa marka. Hakan kuwa akayi ya sayo ya kai mata. Mai makon tayi murna sai ta zo tayi wa Umma Hadizan tatas akan saboda taga ta samu aiki ne zata fara daga kai da nuna isa da izza. Dakyar ta karbi rediyon dan sai da aminiyar ta lawuri ta tausashe ta. Dakyar ta karba
Ranar kukan farin ciki Umma hadiza tayi. Tana kuma sake yiwa Allah godia akan sabuwar rayuwar da suka tsinci kansu ciki.
×××
Haka lokaci yayi ta ja.. Har ranar da za'ai taron wayar da kai akan lalurar sikila)amosanin jini.
Da wuri suka shirya. Kusan dukkanin mutanen unguwar shurah mazan su da mata. Manya da yara duk sun hallara. Kasancewar rana ce ta hutu. Dan haka kwansu da kwarkwatar su sun tumbatsa awajen taron. Wanda wani babban likita zai gudanar da shirin.....
*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*
*ZAFAFA BIYAR BACTH A*
1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*
2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*
3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*
4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*
5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*
_Duka biyar 1500_
*___________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*
1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*
2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*
3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*
4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*
5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*
1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*
2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*
3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*
4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*
5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*
1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*
2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*
3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*
4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*
5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*
1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*
2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*
4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*
5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*
_Duk biyar 1500_
*______________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*
1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*
3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*
4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*
5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*
1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)*
2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)*
3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)*
4... _INAYAH_
*(Mamu gee)*
5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)*
_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_
*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*
_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*
_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*
_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*
_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_
*_07040727902_*
_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_
*_09134848107_*
*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:11_
Tunda Marka ta kyallara idanu ita da Inna Sa'adatu akan kaji da yan kayan abincin da Umma Hadiza ta samo a gidan aikinta. Tsangwama, Kyara da tsantsar kiyayyar da suke wa Hadiza da iyalanta suka nunku cikin zukatan su.
Domin Alhamdulillah. Yan sauran canjin da sukayi ragowa awajen Hadizan. Tuni ta auno musu garin kwaki da sukari da kwanon gero. Da kanta takai wa me yar tsala. Zata dinga basu yar tsalan har na tsawon mako 2.
Gashi duk sanda Umma Hadiza zata dafa abinci daga ragowar kayan abincin da gidan Hajia Hameeda taba su. Sai ta dafa ishasshe ta zubawa Marka. Amman duk kyautatawar da takewa Markan bata gani. Sai dai ta cinye ta lashe ta kuma ture kwano tana mitar kadan aka zuba mata. Sam ba godia bare yabawa ga Umma Hadizan.
Baya ga haka kiyayya ce zazzafa ta sake shiga tsakanin Marka da Waheedah. Tunda akayi taron gwaji da kuma wayar da kai akan cutar amosanin jini ta sickle cell Marka ke jin zafin Waheedah a ranta. Musanman da gwajin Na'Ateeku ya fito da matsala.
Tashi akayi da ruwa tamkar da bakin kwarya. Gari yayi luf luf. Bishiyu se kadawa suke suna bada iska mai dadi.
Yayinda ruwan ya yi gyara masha Allah. Wasu gidajen suka cika da ruwa sai aikin kwalfacewa ake.
Gidan MalamNalado da sauran gidajen dake baki bakin unguwar ta shurah duk sun cika maqil da ruwa.
MalamNalado da kansa ya sharce ruwan dakin Marka da nasa dakin. Yayinda dakin Inna Sa'adatu dana yaranta. Su ukashatu da basher suka tsaya suka kwalfe nasu.
Dakin Umma Hadiza kuwa. Waheedah ce ke kwalfewa gwanin ban tausayi. Sai Najib dake tayata kadan kadan domun jikin nasu ya sake motsowa.
Kamal na dakin su. Umma Hadiza na gefen sa tana masa sannu. Dawowar su kenan daga asibitin cikin unguwa.
Sai numfarfashi yake saki yana dartse hakoran sa hadi da tallabo kafarsa ta hagu yana hawaye .
Marka dake wajen dakali a zaune da rediyo a gefen kunnenta tsaki taja mai tsayi tana tabe baki. Kafin cikin kufulewa tace,
"Wai menene haka? Sai wani uban numfarfashi ka ke jerawa tamkar jemammen sa. "
"Kayi hakuri kayi shiru yayan su." Umma Hadiza ta shiga lallabar sa.
"Radadi ne a cikin kasusuwanmu, Misali kafa ko hannu ko baya. Idan a kafa ne ciwon ya tashi sai ka ji kamar ana sara kafar ko ana raba ta biyu Marka, Radadi ne mai wahalar fassarawa." a cewar Najib daya leka kansa wajen Marka
"To uban yan shisshigi da kai na ke?"
"To assalamu alaikum!! Jamaar gidan nan.. wai wai wai. Lalle kuma ruwa ya muku gyara. " Cewar Najan Isubu data shiga gidan tana kwarara sallama hadi da karewa ruwan dake kwarara a gidan da kallo.
Marka na hango Najan ta sauya fuska. Hadi da juyar da kanta gefe tana kara setin rediyonta. Ai kuwa Najan ta zagaya gefen Markan tana daria
"Hajjaju makkatu."
"Najaatu."
"Naam tsohuwa mai ran karfe an buga da ke an bar ki. "
"To ya zaayi da ni.? A haka zaa ganni a bar ni."
"Wannan zance haka yake. Shakka babu. To kar na cika ki da surutu tare muke da maaikaciyar lapia wadda sukayi gwajin jinin mu."
"Ni fa banason tsurfa wallahi. Menene kuma iyye? "
"Kai Marka"
"Ah to yo ai gaskia ne. Karairakin su ne na banza da wofi."
"Dan Allah marka kiyi hakuri kar ta jiyo."
"Gafara can ni. Babu wanda ya isa yayi mum abunda Allah bemun ba."
"Hakane. To dai zan shigo da ita yanzu."
Da sauri Najan ta fita. Nan da nan kuwa sai gashi sun shiga da matar tana biye da ita a baya. Matar suka sbiga gaisawa da Marka da ke yauki kai kace Kashi tagani.
"Fito Hadiza ku koma can. Na tattare nan. Sannu Kamal. Allah ubangiji ya baku lapia."
Umma Hadiza ta share hawayenta. Hannunta daya ta kamo na Kamal suka koma can dakin da shi su Waheedah sun gama kwarfe ruwan cikin sa.
Nan da nan Najan Isubu ta daure mayafinta a kugu ta shiga kwalfe ruwan tana tsane ko'ina.
Sai data gama tukun sannan ta leka ta kirawo Inna Sa'adatu dake kwance akan gadonta tana hambadar ridi.
"Menene ne ake nema na?" Cewar Inna Sa'adatu dake yauki.
"Abunda nagani kenan, Bayan ke da yaran ki lafiyayyu ne, kinga dakta canne dakin uwar marasa lapian ato." Marka ta ce da maaikaciyar lapiar hade da miqa hannu ta nuna setin dakin Umma Hadiza.
Maaikaciyar lapiar ta girgiza kai kawaii. Kafin ta shiga cewa,
"Wato shi wannan ciwo fa Hajia abune daya kamata ace kun bada gudunmuwar lokacin ku da karfin ku kai dama aljihun ku akan wadancan yara masu fama da cutar amosanin jini."
"A saboda me zamu bayar iyye? Bayan shi kansa me sunan malam asirce shi iyayenta sukayi ya aureta. Nan ya tasamun seda na sayar da gonar mahaifin su aka masa auren. Tunda ya aurota kuma gashi nan dansu na farko shanyayye. Ta biyu gatanan kalau akansa amman itama wai seda gilashi take gani. Sai na karshen shima gashi nan a shanye. Baki daya duk abunda mai sunan malam ya mallaka ya kare akan su. Hmm! Wannan yariinya Hadiza wallahi aurota kaddara ne"
"Kash iya kidena cewa haka .. Wato ita wannan cuta, Lokaci mai gajeren zango a dan baya kadan, idan aka yi aure, aka samu juna biyu, aka haihu, bayan kwanaki ko watanni kadan sai kaga yaron ko yarinyar da aka haifa sun mutu, haka ma’auratan zasuyi ta fama da mutuwar ‘ya’yansu, sunata neman magani, je-can, je-can domin samun mafita. Kasuwar bokaye da yan bori sai ta bude, yar-mai-ganye kuwa takan samu wurin baje hajarta a irin wadannan wurare, a karshe abinda za’ace shine, ai matar mayyace, ma’ana ita ce take cinye ‘ya’yanta ta hanyar lashe musu kurwa!
"Sai dai fa, abun ba haka yake ba, “matar ba mayya bace” ba kuma ta “lashe kurwar ‘ya’yanta” Tun farko ba’a tantance kwayar halittar bane, akwai jinsin mutanen da sam bazasu haihu su bayar da da mai nisan kwana ba.Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana dauke da abubuwa iri daban–daban, kamar su kwayoyin halittar jini masu dauke da ruwa (plasma), jar kwayar halitta (Red Blood Cells, RBC), kwayoyin halittar jini masu kula da garkuwar jiki (White Blood Cells, WBCs), kurgun ruwa (Platelets) da sauransu. Iya
"Cutar sikla ko amosanin jini tana faruwa ne idan aka samu matsala a jajayen kwayoyin halittar jini (red blood cells). RBC yana dauke da sinadarin ‘Haemoglobin (Hb) a cikinsa. Haemoglobin (Hb) kala-kala ne; akwai Haemoglobin A (HbA), Haemoglobin B(HbB), Haemoglobin C (HbC), da sauransu. HbA shi ne lafiyayyen haemoglobin. Sauran Hb ɗin ba lafiyayyu bane.
"Cutar sikila tana daya daga cikin cututtukan da ake iya kauce musu kafin samuwarta. Idan kuma cutar ta samu, to tana da wahalar magani.Idan aka ce mutum na dauke da cutar sikila ana nufin mutum yana dauke da sinadaran haemoglobin guda biyu marasa kyau (ba lafiyayyu ba) a jikinsa. Ma’ana dai ya gaji gurbatattun sinadaren haemoglobin daga wurin mahaifiya da mahaifi.A yanzu haka, cutar sikila na daya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jinin AS da AS ko SS da AS....Iya Ina fatan kina ganewa?".
*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*
*ZAFAFA BIYAR BACTH A*
1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*
2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*
3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*
4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*
5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*
_Duka biyar 1500_
*___________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*
1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*
2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*
3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*
4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*
5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*
1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*
2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*
3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*
4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*
5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*
1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*
2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*
3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*
4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*
5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*
1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*
2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*
4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*
5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*
_Duk biyar 1500_
*______________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*
1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*
3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*
4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*
5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*
1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)*
2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)*
3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)*
4... _INAYAH_
*(Mamu gee)*
5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)*
_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_
*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*
_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*
_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*
_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*
_SAI