Showing 105001 words to 108000 words out of 123508 words

Chapter 36 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

547

hakuri Love...Haduwarmu ta kasance ne bisa kaddara, Zamowar mu masoya ya faru ne bisa zabin Allah, na bawa son ki gurbi a cikin zuciyata, ya zama dole ne a gare ni, saboda kin zamo wani bangare na rayuwata, haka kuma tunanin ki ya zama masarrafin sarrafa akalar rayuwa da tunani na ..Ina kaunar ki irin kaunar da gangar jiki take wa ruhi. Waheedah, You are my answered prayer, My fulfilled wish, My realized dream..." Ya karasa fada yayinda hannun sa ke kan girarta yana shafawa ahankali.

Gaba daya dan mutan the Adams family ya sake kuncewa Waheedah notin da ke saisaita tunanin ta.

Yadda yake mata ne yasa ta kasa hakuri. Sassan jikinta na aminta da sakon da Zayn ke aika musu. Kasan zuciyar ta na begen bashi hadin kai. Dauriya kawai take yi bataso tabada kai bori ya hau.

Zayn ya lura da hakan. Don haka ya sake zage damtse ya shiga yin yadda yaga dama. Ita har mamaki yake bata. Yanzu yadda yake da shiru shiru da dan daga kai shine me wannan danyen aikin yana sumbatu.?

Ya birgino da ita. Ta dawo kan inda yake bukata. Waheedah ta runtse idanun ta da sauri tana sake matse su. Hade da sunkuyar da kanta kasa...

"Waheedah....."
Ya ja sunan cikin salon kauna...

"Um..."

"I want you..... All of you... This instant.. please."

Wani dadi ne ya mamaye ta. Tunawa da tayi da tana period fa. Dariya ta taho mata ta danne. Dan bata kaunar ayi abun kunya agidan Maa.

"Kinyi shiru .. should I...go on...?"

"Ina al'ada..."

Ya danne kasan leben sa da karfi. Takaici ya taso ya kudundune masa a makogaro amman ya danne kawai. Dan yaso ya gano dazun sai kuma bai tabbatar ba .

Gyara mata kwanciya yayi yana murmushi, Itama murmushin nan tayi masa irin na kwalelan ka. Ya girgiza kai kafin yace da ita,

"Farkon sallama ckin salamar samun sa'a da murnar kasantuwa a cikin dausayin ni'imar sanyin murmushin
labban bakinki. 😜Kin zarce shiga kinkai bangon kurewa acikin jerin matan da ke takama da kyau, Shiyasa idona baya gajiya da kallonki ayayinda murmushina yake bayyanuwa alokacinda nake kallonki Waheedah... A koda yaushe tun farkon haduwar mu da ke. Kika zama mamallakiyar ZUCIYA ta. Tun ban tabbatar ba Waheedah.. Ko kinsan yawan zuwan da nake sashen nan duk akan ki ne? Wani lokacin zakiga idan kin gayshe ni ina basarwa ko naki amsawa wallahi Waheedah kaunar ki ce ta mun illa acikin zuciyata. Ta mun wani irin kamun da idan banyi tozali da ke ba ranar ZUCIYA tah ba ta samun FARIN CIKI....My permanent relationship status – taken forever by the most gorgeous woman in this universe. Love ya soo much wifey.. Waheedah.."

"Uhmm"

"Wait.. Ni fa nagaji da sauraron uhm da um dinki tun dazu. Ki bude baki ki mun magana. Dan Allah ki dena azabtar da ni da rashin jin muryar ki... Waheedah "

"Na'am..." Ta amsa shi a hankali...

"Ki ce wa Maa zaki bini mu kuma gidan mu .. Kinji?"

Tayi shiru bata amsa shi ba. Don ba zata taba aikata wannan magana ta rashin kunya ba.

"Kinji?" Ya sake fada mata yana zagaye labbanta da hannun sa.

"I can't... I won't"

"Haka kikace?"

"Eh..."

"Okay fine...."


Tayi shiru bata sake cewa komai ba. Ya sake gyara mata kwanciya yana shafa gadon bayan ta . Gaba daya ya hanata komawa bacci. Ta rasa yadda zatayi.

"Kinyi shiru ..."

"Bacci nake ji dan Allah..."

"Ni mamaki kike ban. Har kina iya bacci a gidan sirikan ki. Ga gidan mu can ki zo mu koma kin ki. Itama Maa ta bani matata taki. Gaskia an kusa kai ni karshe. Hakuri na ya kusa karewa. Allah zan zo na sace ki mu gudu. Ba zasu kara ganin ki ba sai kinzo haihuwa gidah . Ko kuma mu zo mu su da jaririn ko jaririyar..."

Ita dariya ma zancen na sa yaso bata. Ta dan murmusa kawai. Wannan murmushin da tayi ya sake tabo kaunar ta dake zuciyar Zayn. Hakika Waheedah na da wani murmushi da ke kara mata kyau. Haka kawai idan tayi sai kaji ka samu nutsuwa.

Zayn ya samu kansa da dago da habarta. Ya sumbaci saman bakin ta da karan hancin ta. Ita dai ta kulle idanunta gam. Tana kambama kokarin sa da baya gajiyawa da showering dinta da kisses..

"Waheedah... So tamkar hasken rana yake da yake haske fuskar da take d'auke a jikin gangar jiki, ma'abociyar ZUCIYAr da take 'kunshe da so.
Kasantuwar so a cikin zuciya kan motsa ruhi ya kuma busar da idanuwa daga barin yin bacci a
mafi yawancin dare, So kan samar da wasu rassa a cikin ZUCIYA bayan bayyanar sa, wato bakin-ciki da kuma FARIN CIKI. Zan ci gaba da son ki a cikin kowane irin yanayi. Ina kaunar ki sosai...You fill all the emptiness in my heart. I’m so thankful to have you in my life. I love you very much...."

Daman bacci ne yake fizgar su duka. Murmushi kawai tayi jin karshen kalaman sa. Ya kundune ta tamkar itace bargon su. Dakyar ya kyaleta taja bargo ta lullaba.

Yanata neman maganar sa bata kula shi ba. Saboda baccin da ke cin ta. Nan da nan kuwa ya dauketa ba jimawa kuwa shima baccin ya sace shi.

Dukan su numfashin su na fita ahankali. Suna baccin su gwanin ban sha'awa. Zaka rantse irin masoyan nanne da sukai shekaru suna dakon kauna...

×××××


°°°°

×××××



*WAYEWAR GARI*


Waheedah ta riga Zayn tashi bayan da gari ya waye. Ta dubi yadda ya cukwikwiyeta tamkar kayan wanki. Ta shiga kokarin zame hannun ta da jikinta daga nasa. Amman ta kasa, Saboda tsananin yadda yayi mata rikon da ba na wasa ba

A dole haka ta hakura ta koma ta kwanta. Sai bayan wajen minti talatin tukun sannan Zayn ya farka. Ya kishingida yana kallon Waheedah da wani baccin ya sake dauke ta.

Kallon ta yake tamkar zai hadiyeta dajya. Kallon ta yake cikin so da kauna. Kallon ta yake cikin silar FARIN CIKIN sa. Kallon ta yake kallo na mamallakiyar ZUCIYAr sa da gangar jikin sa baki daya. Shi kansa bai san adadin kaunar da yake yi wa Waheedah ba.

A hankali ta shiga bude idanun ta har ta sauke kallon ta baki daya akan sa. Ya kai saitin bakin sa labbanta kenan aka shiga bugo kofar dakin.

Da sauri waheedan ta mike tana inda inda. Yatsanta a baki. Zayn sai murmushi yake.

"Waheedah... Kin tashi?" Muryar Maa ta doki kofofin kunnuwan su.

Zayn ya saka murmushi. Waheedah ta juya ta dankara masa harara. Ta matsa kusa da shi kasa kàsa tace,

"Kace na tafi makaranta.."

"Weekend din?" Ya bata amsa yana daga girar sa.

Sankarewa tayi a tsaye. Kafin da sauri ta shige bandaki. Shi kuma Zayn ya mike dama. Daama yake nema kuma ya samu a kusa. Ya bade idanun sa da kasa. Ya bude kofar da mukulli. Yana murmushi.

"Ah.... Maaa.! Barka da safiya" 😂ya durkusa har kasa yana gayshe ta.

Ita kanta Maa din sai kunya ta kama ta. Gefe daya kuma tasan da biyu yayi hakan. Don ya nace a bashi Waheedah taki. Shine ya biyo mata tanan. Don da daddare ita ta rufe kofar sashen don haka da asubah ya shigo .

"Alhamdulillah..... Kana lapia? Kace kanka yana ciwo jiya da safe."

"I've never been this better .... 🤭Jazaki Allah bil jannah Maa.. oh Waheedah tana wanka" Ya karasa fada yana sosa keya.

Bata sake cewa da shi komai ba. Ta sauka kasa. Shi kuma ya danne leben sa yana murmushi.

Ya koma cikin dakin ya zauna a bakin gado. Sai murmushi yake shi kadai. ZUCIYAr sa dankare ta ke da FARIN CIKI....


_____________________


Sosai Umma Hadiza kasuwancin da take ya karbe ta. Allah ya sanya mata albarka aciki. Tana ciniki sosai.

Don ta dawo da Najib ma gaban ta. Shagon da ke wajen gidan gwaggo haule anan Najib din ke kwana.

Haj Hameedah ce ta bawa Umma Hadizan jari me tsoka ta kuma kara mata da wanda farfesa Adams yake bawa maaikatan sa na zakkah.

Ranar Umma Hadiza har kukan FARIN CIKI tayi. cikin ZUCIYAr ta babu wata sauran damuwa sosai

Ta samu albarka na suturu da kayan abinci sosai alkhairi kala kala. Hajia Hameedah da danginta sukai mata.

Bataso rabuwa da ita ba. Sai dai babu yadda za'ayi tacigaba da aiki a karkashin su duba da uwnzun ta zama sirika awajen su. 'yar ta na auren 'dan su. Yanzun Najan Isubu ke mata aikin.

Duk sauran bakin cikin da ke ZUCIYAr Umma Hadiza da ahalinta ya kare. Sai FARIN CIKI da ya maye gurbin sa.

Hakika hakurin su yayi riba. Allah kuma ya karbi adduoin su. Ya dubi wankakkun zuciyoyin su ya musu zabi da mafificin alkhairin sa.

Tarin manema nata zuwa mata. Neman auren ta, Amman Umma Hadizan ta dakatar da dukkanin su. Musanman yanzun da bata fita ko'ina. Tana dai zaune tana mai kula da lapiar Najib....


*GIDAN MALAM NA LADO*

_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_


_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:65_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._

____

 
*A kwance* Marka ta ke, Ya yin da ambaliyar hawaye ke tsiyaya daga idanun ta. Jikokin ta , Yaran wajen Zahara'u na kewaye a dakin suna wasan oji-oji.

Tsakar gidan kuma yan biyun Deluwa ne akan katifa an kwantar da su. Dayar jaririyar idanunta a juye. Makauniya ce bata gani. Anyi maganin anyi sai addu'oi da ake bin ta da shi.

Shigowar Najib kenan gidan ya hangi Marka tana kokarin motsa bakin ta ta kaa sa. Ya yinda ambaliyar hawaye ke tsiyaya daga idanunta.

Da sauri ya karasa wajenta. Ya tattake ya daga ta dakyar yana sauke numfashi. Ya tokare ta da bango. Ruwan shan ta da ke kofi ya dauko yana mai mata nuni da shi.

"Ruwa?"
Ya tambayeta yana mai binta da kallon tausayi. Domin kwarai matuka Marka ma cikin halin haulai na kakanikani.

Marka rigimammiyar tsohuwa da bata ganin kan kowa da gashi. Wai itace cikin wannan halin. Da bakinta ma ta bude tayi magana ta kasa. Sai dai a kwantar a kuma tayar.

Bakin kofin ya kafa mata a baki . Ta shiga sha tamkar zata hadiye har kofin.

Cikin haka sai ga Zahara'u ta rafka sallama. Ta shiga gidan tana tafe tana taunar cingum ..

"Sai kira na ake ta wani faman yi. Kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Ni dai da wannan jinyar dama warewa kikayi yasin." Ta fada cikin ko in kula da gabatarin maganar da tayi. Ba tare da ta auna zancen ba.

Cikin yatsina ta shiga dakin ta zauna tana jan kwan cingum.

"Ina wuni anti zahara'u?"

"Lapia... Kai kuma yaushe ka zo?" Ta tambayi Najib.

Duk kuwa da ya koma gidan gwaggo haule wajen Umman su da zama. Kullum safe da rana yana gidan na su na malam na lado.

Duk kuwa da kyama tar su da muzantawa da marka tayi wa rayuwar su a baya . Hakan bai hana shi kula da ita ba. Dai dai karfin ikon sa.

"Ban dade da shigowa ba. Anti."

"Okay.,"

Zahara'u ta zauna a kàsa. Ta yage dankwalin kanta tana sosa gashin ta.

Marka na biye mata da kallo. Wani kwaro dai dai saitin marka . Zai shige jikin ta. Cikin wauta ji ka ke tas. Zahara'u ta wanke fuskar Marka da mari. Kwaron ya fadi kasa matacce.

Marka ta fashe da kukan zafin mari. Najib dariya ta so kufce masa ya danne kawai.

"La. Sattin ta ubangiji don na cire miki kwaron ne. Ashe ke zan samu . Kai Allah ya shirya ni. Yi hakuri marka ta"..

Sai da Marka ta sha kukan ta. Tukun sannan tayi shiru tana jan majina.

Marka ta kaikaice tana dan yamutsa fuska. Ji kake sirr ta iska ta fito. Zahara'u ta mike da sauri tana mai toshe hancin ta da bayan kasan hijabin ta.

"Kai Kai Kai. Haba Marka. Na gaya miki ki dai na baje duwaiwai kina bada iska. Ko kashi zaki?"

Nan ma Marka ta bude idanaun ta ta lumshe. Hakan ya bawa zahara'u damar ciccibar markan ta ajiye ta gefe.

Sannan ta dakko fo na manya ta dora marka. Najib ya fice daga gidan da sauri yabar Marka a kan fo.

Ta karasa yi. Dakin ya budade da hamamin bahayar Marka. Dakyar zahara'u ta mata tsarki ta fita da fon zuwa bandaki. Dakin ya dau tsami.

Ta dawo ta tsaya kerere a kanta.

"Zulfa'u ta zo kuwa?"

Nan ma Marka ta lumshe idanu ta bude alamun a'ah.

"Zabba'u fa?"

Nanma Marka ta mata alama da bata zo ba.

Ta dora hannunta akan cikin ta. Tana shafawa. Can ta mike bayan ta gantsare.

"Bari na tafi . Idan Malam na lado ya zo ya karasa miki wasu abubuwan."

"Ah Zahara'u.. Yanzu kika shigo?"

"Eh na zo ni Deluwa... Tafiya ma zan. Zan dora sanwa."

"Allah sarki "

Zahara'u ta fi ce. Ya yinda Deluwa ta tsugunna gaban wuta tana gyaggyara ledojin da zasu kama mata gaushin.

Ba jimawa malam na lado ya shiga gidan . Bayan sa kuma Malam Ubaliyo ne malamin masallacin arewa.

Gaishe da Marka malam Ubaliyo yayi ya tsugunna yana bin ta da kallon tausayi. Wai Marka ce a kwance bata iya daga yatsanta ma.

Ciwon ya faru ne baki daya cikin kwanaki uku. Dan ko a satin da cutar zata same ta ma. Taje bakin kasuwa ta surfawa wanzam damuna ashariya ratsa ratsa da aibace aibace.

Malam na lado ya kalli malam Ubaliyo. Malam Ubaliyo ya sauke zuciya kafin yace,

"Ubangiji Allah ya yaye miki Marka. Ya sa zakkar jiki ce. Allah yasa wannan cuta ta ki.. Kankarar zunubai ce. Amin. Yauwa kafin ki kwanta ciwo ki gafarce ni. Du bada ba zaki iya magana ba ko ambatar wani abun. Malam na lado ya sanar mun damuwar sa ta,

"Kan lalle kin tsaya kan bakan ki na cewar ya aiwatar da shika uku ga Deluwa matar sa. Dan Allah Marka kiyi hakuri ki janye zancen ki. Wannan tsauraran hukunci duk basu kamata ba. Yarinyar nan Hadiza itama ashe auren tuntuni babu kin saka ya shikata Marka. Aka dawo kan Sa'adatu itama ga abunda ya dawo akan diyar ta da ita kan ta . Na lado yace kince kar su soma dawowa gidan nan. Bayan har yanzu da aure a tsakanin saadatun da na lado. Marka kiyi hakuri da abunda labbana zasu furta. Amman bakya ganin wadannan hukunce hukuncen da kike yankewa suna tsauri da kaucewa aqidar islama Marka? Astagfirullah ki dubi zancen da zan fada da idanun Basira... Marka"

Duk kuwa da a kwancen da ta ke. Hakan bai hana Marka dankara masa harara ba. Ji take tamkar inama zata iya mikewa. Ta yi kutufo da shi.

"Marka... Dan Allah ki dubi komai yadda yake ki mayar da shi muhallin sa. Kiyi Imani da Allah da haqiqar sa Marka..Imani na gaskiya shi ne rayuwa da farin ciki. Ba a samun kwanciyar hankali sai dai imani da Allah mai girma da buwaya. Duk zuciyar da ba ta da imani za ta zauna cikin tsoro da rudani da rauni da rashin kwanciyar hankali. Imanin da ake samun tsira da shi shi ne imani da Allah, wanda ma’anarsa shi ne gaskatawa da yankewa cewa Allah shi ne Ubangijin komai, mamallakinsa, mahaliccinsa, kuma shi kadai ya cancanta a kadaita shi da ibada, ta sallah da azumi da addu’a da fata da tsoro da qasqantar da kai, kuma shi ne ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login