Showing 60001 words to 63000 words out of 123508 words
. Sumar gashin ta yalwatacciya ta bayyana.
Ta kalle shi ta sake kallon sa tana langabar da kai.
"Ina zaka je haka? .. Sai wani kamshi kake "
Yayi yake kawai kafin ya ce da ita,
"Ba gaisuwa...?"
Baki ta turo gaba. Ta koma kan wata kujera ta zauna.
"Naga mun zama daya. Gida daya . Kai de kanason gaisuwar nan. Ni mantawa na ke "
"To banda abinki ai dole ne ki dinga gaishe ni. Kiyi tunani mana Ahlam.. ko ba aure a tsakanin mu ai a sama nake da ke. Ni Yaya ne a gare ki kar ki manta.."
"Ina kwana?" Ta gayshe da shi kasan maqoshi
Bakinta ya kalla ya gano gaishe shi tayi. Bai amsa ba ya wuce kai tsaye wajen dinning.
As usual ya daga tea flask ba komai aciki. Ya wuce kitchen ma kamar ko da yaushe babu abinci. Ransa ya kai kolokuwar baci. Ya danne dakyar yace da ita,
"Ba abinci ...?"
Ta daga kanta . Kafin tace,
"Akwai bread ... Ko na dama maka custard ? "
"Ahlam me na ce miki jia? Da shekaran jia waçcen? Ina ga kullum se na miki maganar nan... Amman sam kinki yi. Tun dazun me kike a kàsa?"
Ta sake yamutsa fuska tana turo bakinta gaba.
"Ai na gaya maka..... Ka dinga hada breakfast dinki. Kai picky eater ne. "
"Ahlamm... Fisabilillahi kusan kullum abincin daya ne. Indomie, sandwich , bread . Coffee. Ko fruits.. Tunda aka kawo ki gidan nan baki taba girka komai ba.."
"Ina dama maka custard mana... " Ta amsa ba tare da wata damuwa ba.
Yaja kasan lebensa yana taunawa. Yama rasa abun cewa.
Hannun sa ya saka ya gogo kitchen cabinet sai kura. Ya nuna mata.
"What is this?? Ahlam... Wannan wane irin rayuwa ce uhm? Kalli datti please."
"To aiki ya mun yawa. Ance zaa bani me aiki ka hana... Zan kashe kai na da aiki ne?"
Iskar bakinsa ya furzar mai matukar zafi. Cike da kosawa yace,
"Ina almajiran da ke miki komai??"
"Ba dai komai ba. bayan ka hana su dinga wanke duk wani plates da sauran kayan abincin dazaa zuba maka."
"Lord! To Hakan shine laifi Ahlam? Nagaya miki ba sau daya ba. Ni mutumi ne me tsantsami. Alla ya sani, Bazan iya cin abinci da plates da sauran abubuwan da suka wanke ba. Almajiran dake wari suna tsami. Komai tabawa suke da hannun su basa wankewa. Haba Ahlam..wannan wane irin rayuwa ce? Mu biyu ne fa sai baba Mai gadi. Wane abu muke batawa da harsai almajiran ne zasu wanke. Just 3 of us... Haba Ahlam..."
Qunqumi ta shiga yi bata sake ce masa komai ba. Ya gyada kai kawai yana girgiza shi cikin takaici.
"Akwai abunda kike bukata ne da babu anan din?"
"Bakomi .. sai dai ko recharge card.."
"Oh ya rabb... Ni banga abunda kike da kati ba Ahlam sai renewing data plans shi yasa na yi deactivating wifi na gidan nan. Gaba daya 300gb ke kika karar da shi cikin kwanaki .. "
"Noo. Ina kiran yan uwa mana..."
"Ba dai yan uwa ba... Harda kawaye. "
"Bushra ce kawai. Kuma ita ai bestfren dina ce."
"Ta fini muhimmanci ai awajen ki na sani... Bakya boye mata komai."
Ko ajikin ta. Da abunda ya fada sai ca tayi
"Itama bata boyemun komai. Human diary din juna ne mu."
"To ki zauna kina biye mata... Naga ba aurene da ita ba. She's much less busy than u ahlamm.. That aside yau su Maa zasu zo kinsani ai. Kuma kinga ai ba zasu zo su tafi ba ba tare da sunci abinci ba. Da snacks and drinks haka.. Me zaki dafa musu?"
Bata ce komai ba. Ta yi shiru. Idanunta akan wayar da ke hannun ta. Tanata latsawa
"Ahlam...."
"Naam..." Ta amsa da sauri tana daga kai
"Magana nake miki ... Dan Allah ki rage danna waya ... "
"Me kace?"
"Nace me zaki dafawa su Maa da zasu zo. ? Da su snacks haka da drinks?"
"Tab..."
"Pardon ...?"
"Gaskia sai dai ko babbar me aikin Maa dinnan tazo ta dafa abincin."
"Ke meyasa ba zaki ba.?"
"Ban iya ba." Ta amsa shi kaii tsaye.
Ya sake jan leban sa ya ciza. Kafin ya sake cewa da ita,
"To drinks fa akwai? Zasu isa?"
"Eh... "
"Tohm bari naje na dawo .."
"Alright...." Ta amsa shi. Ta juya ta zauna taci gaba da danna wayarta.
Haka ya shiga mota ya nufi gidan su kai tsaye. Zuciyar sa nata tafasa. Ya kasa gane kan Ahlam. Tamkar ba mace ba? Ba sirri. Ba ladabi. Ba tarairaya. Ba tsafta... Ba godiya. Hakika babun ta tayi yawa.
Haka ya karasa gidan su yanata tunani ya saka wannan ya ware. Yana karasa parking ya shiga ciki bakinsa dauke da sallama.
"Wa'alaykm Salam..."
Tsugunna wa yayi har kasa ya gayshe da mahaifiyar tasu Haj Hameedah. Ta amsa da fara'a.
Lura tayi da yanayin sa. Sannan tace,
"Ga abinci can a dinning... Ko zaka coi."
"Tohm Maa...."
Ya mike da sauri ya zauna akan dinning sai daya cika uwar kashin sa tukun sannan ya koma ya zauna akan kujera.
Ta sake tambayar sa kamar koda yaushe gamin yadda ya dan rame. Idanuwan sa tubarkaAllah sun sake manyanta.
"Akwai wani abunne?"
"A'ah Maa..." Ya bata amsa tamkar ko da yaushe
"Ya Ahlam din... Lapiar ta kalau?"
"Alhamdulillah...."
"Masha Allahu.... Yau mukace zamu kai ziyara kuwa. Amman sai an jima "
"Eh... Insha Allah " ya fada yana lankwasa hannuwan sa. Hade da shafa keyar sa.
"Akwai wani abunne?" Ta sake tambayar sa. Don tasan halin sa da zurfin ciki. Amman dai a matsayin ta na mahaifiya ta hasaso akwai yar tangarda a zaman sa da Ahlam
"Dama...Ahlam dince tace ko zaa kai me aiki ta tayata abinci..."
"Ta tayata ko ta mata?"
"Ta mata...."
"To gaskia dai kaga nan gyara suke tamun. Kuma Hadiza itace karfin aikin wallahi. Sai dai ko na tambaye ta idan Waheedah na nan sai taje.."
"Waheedah kuma Maa?"
"Eh Waheedah... Ai ta iya girke girke yarinyar nan. Sai ta mata din.."
"Tohm." Ya amsa badan ya so ba.
"Hadiza... Hadiza!! Hadiza!!"
"Naam hajiya..." Ta karasa da sauri tayi gurfane agabanta.
"Dan Allah Waheedah na nan kuwa? Wai Ahlam ai kingane ta ko?"
"Kwarai na game ta... Wadda akayi bikin su ko?"
"Yauwa ita... Idan anjima ne zamu je gidan . Har da ke ma insha Allah. To shine takeson a ara mata wadda zata mata girki. Na yaba da hankalin Waheedah da kuma fasaharta na iya girki. Ba matsala taje?"
"Babu......Hajia. Tana makaranta. Amman nasan an kusa tashin su. Tunda yau jumu'ah...."
"Yauwa masha Allahu... Ai kace kasan makarantar ko. ? Ko ku tafi da Nassem ya muku rakiya. Da Nadra na nanne sai taje . To sai watan gobe zata dawo "
"Nadra an sha hutu kam."
"Tabbas ana kan sha ma. "
"Shikenan Hadiza je ki .."
"Tohm Hajia."
Umma Hadiza ta miqe ta koma kitchen
Shi kuma suka cigaba da zaman kurmaye. Sai da Maa ta tashi ta kira Nassem .
Wajajen 11 da mintuna suka dauki hanyar makarantar su Waheedah. Ba jimawa kuwa aka tasa su
Nassem ya shiga da kansa makarantar aka nuna amsa ajin su Waheedah bayan ya tanbaya.
Suna gaban me youghurt yana yanka musu na 20 kowannen su
"Waheedah...."
"Naam..." Ta juya don ganin me kiran na ta.
Nassem ta gani a tsaye yana kare fuskar sa. Saboda ranar dake dallare shi
Karasawa tayi wajen sa tana murmushi.
"Yau kai ne a makarantar mu?"
Dan murmushin shima yayi kafin yace,
"Rakiya nayo ma.. Ni yanzu zan koma gidah. Zaku sauke ni."
"Ni da su wa?"
"Ke da akiey... Ya Zayn."
Yana karasa fada gabanta ya yanke ya fadi. Mumuguncin mutumin nan me zatayi masa.?
"Me zan masa?" Ta tanbaya batare da tasan ta fito ha.
"Kede muje... Sa ce ki zamuyi.." suna saka dariya baki dayan su .
Har mota suka isa. Nassem ya hide mata ya shiga ya zauna. Gabanta na tsananta bugawa. Juyawa yayi ya kalleta. Fuskar sa a daure.
"Ku sauke ni a kwanan layin mu. " Cewar Nassem.
"Alright....."
Har kofar layin suka sauke shi. Ya sauka har ya tafi. Zayn bai ja motar ba. Waheedah kuma bata tanka ha. Ya juya ransa a bace
"Ke waye driver din ki? Common dawo gaba ki zauna...."
Ta bude da sauri ta koma gaban ta zauna. Tana gatsina fuska. Murmushi ya so kufce masa dakyar ya danne suka dauki hanyar gidan sa.
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:45_
_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._
_
*A* wani junction da ke kusa da layin gidan sa. Suka tarar da hold off agaban su. Yaja siririn tsaki yana mai danne kasan leben sa.
Waheedah na zaune akan kujera . Yayin da fuskar ta ke kallon gefen waje. Ya dan juyar da kansa ya sauke idanun sa akan ta.
Gefen fuskarta idanun sa suka sauka. Kwantaccen gashin gefen fuskarta wajen kunnenta ya kwanta luf .
Girar ta mai cikar yalwar gashi.. Leben ta duk kuwa da gefen sa ne. Kana iya hango kalar sa. Pinkish in color. .
Kasa cigaba da kallon nata yayi. Ya juyar da kan sa gefe da sauri. Hade da saka hannu ya karo gudun air-conditioner dake busa musu sanyi.
Sannu a hankali hold off din ya ja baya. Zayn ya samu hanya ya shige cikin layin da gidan sa yake.
Baba mai gadi da ke zaune a bakin gate din akan benchi. Yana hango motar. Baba mai gadi ya mike da sauri ya bude gate din. Zayn ya shiga da matar ciki bayan ya tsaya sun gaisa.
Ya faka motar a rumfa. Ya kashe, Waheedah ta bude kofar ta fita tana dan kalle kallen gidan. Yayi mata kyau kwarai da gaske.
"Allahumma arzuqni...."
Ta fada kasan maqoshi tana bin garden din gidan da ke cike da shuke shuke da kallo
"Muje ko....?" Zayn ya ce da ita.. Yayi gaba tana biye da shi a baya.
Door bell ya danna. Sai da yayi ta dannawa wajen sau shida kafin Ahlam ta bude kofar.
Ya kare mata kallo. Kayan baccin dazu da ya barta ne. Bata canza ba . Ba sannu bare ban gajiya.
Ta janyo hannun Waheedah dake bayan Zayn. Hakan har yayi sanadiyyar gugar jikin Waheedah ana Zayn. Wani baqon yanayi ya ziyarci dukkanin su.
"Ina wuni sis...?"
"Lapia kalau my dear sweet sis... Ya kike?"
"Lapia Lau ..."
"Masha Allah.... Zo ki zauna Waheedah.."
"Tam..." Tabi bayanta . Jikinta a darare.
Gidan ya sha kayan alatu. Ya gaji da haduwa. Kayan gidan baki daya sun tsaru. Na gwanantawa da bajinta. Dangin masu kudi da farcinan susa...
Zayn ya zauna akan kujera. Hadi da janyo remote ya shiga chanza channel . From Telemundo to Alzajeera news.
Ya kwantar da kansa saboda sarawar da yaji yana yi màsa lokaci daya.
"Sis akwai abunda zaa tayaki?" Waheedah ta fada cike da biyayya.
"Ah ,.... Ya Zayn. Waheedah ce wadda zatayi girkin?" Ahlam ta tambaya. Hannunta daya akan wayarta
"Uhmmm" ya amsata da haka kawai.
"Kin iya girkuna ne?" Ta tanbayi Waheedah. Fuskarta kumshe da mamaki .
"Eh sis..."
"Okay.... To shinkafa zaki dafa da miya. Sai gashin kaza. Akwai kuma frozen snacks a freezer sai ki soya.... Da sponge cake ma sai ki yayyan ka.."
"Tam... " Waheedah ta amsa. Kafin ta sake cewa,
"Akwai zani da zan daura?"
"Ina zuwa.."
Sama ta haye bada jimawa ba ta dakko wata doguwar riga baka da dankwalinta.
"Gashi ... Ga daki can sai ki canza ko?"
"Tohm .."
Dakin ta shiga. Tana ta binsa da kallo. Komai na dakin Turkish royals ne. Ta cire kayan makarantar ta zura rigar. Tamkar dama tata ce.
Waheedah ta tsaya tana kallon kanta a mudubi. Can ta yane kanta da mayafin abayar ta fita parlorn.
Zayn na zaune a kujera daban. Hakama Ahlam tana gefe tana danna waya sai murmushi take.
"Sis .... Na gama."
Ahlam bata daga ta dubeta ba. Saboda tsananin yadda chatting din da take baki daya ya dauke mata hankali.
Ahankali Zayn ya daga wutsiyar idanun sa ya kalleta. Da sauri ya janye kallon sa. Saboda yarda zuciyar sa ke faman zillo. Daya kasa gane manufar hakan.
"Sis...."
"Na... Naam."
"Na gama...."
"Okay muje na nuna miki komai..." Tana gaba sanye da kayan bacci. Yayinda Waheedah ke biye da ita a baya. Tamkar itace matar gidan.ita kuma Ahlam din a matsayin yar aiki.
Ahlam na karasa nuna mata abubuwan. Waheedah nan da nan ta hau yin komai ba sanya.
"Bari na dan kwanta.... Kafin ki karasa "
"Toh"
Har zata fita Waheedah ta dan kirata da sauri.
"Sis...."
"Naam..."
"Ca nayi a ina zanyi gashin kajin? Da ke awajen Maa naga tanayi a irin wancen abun gashin naki..."
"Okay kiyi dashi .."
"Tam..."
Karfin ac din dake busawa kitchen din iska Ahlam ta karawa Waheedah. Yayinda ta kuma ta fi ce ta haye sama dan yin bacci. Kamar yadda ta fada.
Waheedah ta shiga aiki ka'in da na'in. Ya yin da Zayn ke zaune a parlorn shi kadai.
Ya janyo wayar sa yana duba wasu constructions site blog da yake bi a LinkedIn.
*******
Ta dau tsawon lokaci tana aiki. Kafin ta karasa komai. Ta hade dukkanin abubuwan da ta bata ta wanke su tas
Zayn da shigowar sa kenan gidan bayan yaje sallah ya dawo. Kofofin hancin sa suka shiga busa masa kamshin girkunan dake fita daga kitchen. Ya lumshe idanu ya bude ahankali. Sakamakon dadin kamshin da ke bibiyar hancin sa.
Ruwa ta tara hannunta a wajen sink din kitchen. Ta wanke fuskar ta. Har idanun ta sun sake fitowa. Ba karya tasha aiki.
Ta fita parlorn tana kalle kalle . Idanunta suka sauka akan na Zayn dake tokare a bango
"Na.... Na gama...."
"Okay... Bata tashi ba ne?"
"Bansani ba wallahi ..... " Ta bashi amsa cikin karshen gaskiyar ta.
"Okay bari na kirata...."
Wayar sace ta fara kara. Ya dauka ya kara a kunnen sa.
"Eh .. yanzu take cewa ta gama .. Tana sama.. ok bata dauka? Wai tana bacci ne... Alright. Sai kun kara so "
Yana gama amsa kiran ya mayar da wayar aljihun sa. Ya haye saman yana mai kiran sunan ta da karfi.
"Ahlam... Ahlam...."
Tamkar mushe ya hangota ta bararraje akan gado tana bacci. Ya saka hannun sa daya yana tashin ta ahankali
"Ahlam... Ahlam...."
"Um...."
"Tashi mana... Har anyi sallah. Ga su Maa nan fa ..."
"Ka kyake ni ..." Ta amsa shi cikin bacci
"Tashi mana..."
"Oh please...."
"Get up please .. Yarinya tun dazu take aiki sai yanzu ta gama. Ko kunya bakyaji kinzo kinata bacci..."
"Kai... Mts..."
"Tashi ...." Ya shiga janye kanta daga kan pillow yana tashin ta da karfi.
Ta shiga bude idanunta ahankali har ta ware su akan sa. Dai dai lokacin da motar su Maa tayi horn.. Baba Mai gadi na tura gate din...Ya bude musu. Suka shiga da motar ciki.
"Kingani ko .. ? abunda nake gaya miki. To gasunan ma sun karaso..."
Mikewa tayi da sauri ta fada bandaki. Yayinda ya grigiza kai kawai ya koma kasa.
Ba Waheedah, Amman yaji motsin ruwa a bandakin kasa.
Wucewa yayi kan kujera ya zauna yana mai sakin gwauron numfashi mai tattare da damuwa marar misaltuwa....
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN