Showing 42001 words to 45000 words out of 168608 words
dari zaka gansa to da waya ne ko system yana operate "samu guri ki zauna aunty zabiba ta fad'a tana nuna mata kan kujera kasa zama tayi a Inda ta nuna mata .
a hankali ta samu guri ta zauna nesa kadan dasu a qasa dan gudun balain ATA ta kasan idanunta take qare masa kallo sanye yake da dogon wando da riga mai gajeren hannu blue da ratsin fari kayan sun yi masa kyau sosai ga gashin Kan nan nasa sai sheki yake wanda da alama yana shafa man gashi ne yasa yake fitar da sheki ko yaushe ."
"Adam ga mryam nan "inji cewar aunty shahida "naga tantiriya mara kunya mara mutunci , uhm
Ina jinki ki maimaita abinda kika fad'awa aunty a gabana ". sai da gabanta yayi wani irin mugun fad'uwa taji wani abu ya tsarga mata tun daga qirjinta har zuwa kasan mararta take taji marata ta soma murd'awa taji wani abu mai d'umi ya zubo mata wanda bata raba d'ayan biyu na tsananin tsoronsa ne."
ta d'ago kanta a hankali taga har lokacin kanshi na sunkuye yana danna wayar hannunsa "ke har kin Isa kice wai bazaki aureni ba ?tayi saurin sunkuyar da kanta kasa tana sake jin digar wani abu mai zafi na diga a pent dinta wanda babu tantana jini ne yazo mata a dalilin tashin hankalin daya risketa ne
ya cigaba da magana fuskarsa a d'aure tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa "daraja kika ci bancin haka har duniya ta nade baki Isa ba , km baki Kai matsayin da zaki zamo mata agareni ba ."
ta d'an dago kad'an ta saci kallonsa adaidai lokacin daya dago idanunshi suka tsarke cikin nata wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki wanda babu tantama na tsoro ne wani irin mugun kallo yake mata mai firgitarwa "Ina jinki fad'a min abinda kika fad'a masu ?"kaga AD ba dan ka tutsiye yarinyar mutane muka taro anan ba mufi bukatar amincewarta akan komai "no aunty shahida bari ta fad'a taga yadda zanci ubanta ".
"nace abar wannan mgn ta wuce ke mrym kin amince zaki auresa ko kuwa har yanzu baki so dan yau shine final decision domin zamu sanar da mami komai ? "muryarta na rawa tace "na ...na amince .."
"kin amince da me ya fad'a a tsawace yana zaro mata Idanunshi "na amince zan..zan aureka " you are very stupid ,useless kawai tashi ki 'bace min da ganin kafin na miki dukan mutuwa ,bana sonki kuma bazan aureki ba daman nasan baki Isa ki kalleni ki fad'a min abinda kika fada musu ba , maza tashi ki bar nan bana son kallon wannan banzar fuskartaki ya k'arasa maganar yana jan tsaki tare da runtse idanunshi ."
har ta mike zata tashi aunty shahida tace "koma ki zauna tayi saurin girgiza mata Kai tana duban Inda yake zaune tare da jujjuya hannuwanta cike da tsoro "nace ki koma ki zauna a d'ard'ar ta zauna tana kallon kasa a ranta tace "masefaffe banza kar Allah yasa ka aureni nima ai banasonka .
muryarsa a kasalance yace "muddin kuna bukatar na cigaba da zama na saurareku sai wannan yarinyar ta bar falon nan " shiru falon yayi babu wanda yace uffan gashi babu wanda ya Isa yayi mgn sai aunty shahida ko khadija da yake bi bata isa ba bare zabiba da kanwa ce ,aunty shahida ta Kalli maryam tace "mrym kin amince zaki auresa ?tayi saurin gyada mata Kai alamun "eh .!
"Okay tashi ki wuce abunki ta mike da sauri kmr iska ta bar parlour'n "a gsky Adamcy ban ji dadin abinda kayi ba ,a hankali ake bin komai Kai komai zuciya da zafin rai Allah ya sausauta mk zuciyar nan karta sa wata rana kayi nadama iska ya furzar "yanzu tunda ta amince shikenan sai mu sanar da mami aunty shahida ta fad'a tana kallon kannenta mata "eh hk ne suka hada baki gbdy .
"Da izinin wa kenan zaku sanarwa sweetheart .?
"Da fari na amince maku zan aureta amman wannan iskancin da tayi yasa na fasa aurenta har abada km komai zai faru sai dai ya faru amman na fasa "haba yayanmu dan Allah kayi hakuri karkayi haka tunda ta amince ka aureta kawai a wuce wajen tsoronka take ji shiyasa kaji ta fadi hk, cewar zabiba "ka taimakemu karka fasa auren nan kodan mami kabi komai a sannu please "ai bai ma Isa ba tunda ta yarda dole ya aureta ka godewa Allah da kasamu salahar mace mai kamewa kmrta ."
"bafa zan aureta ba I repeat it I can't marry her ,na aureta na kaita Ina da wannan rashin tarbiyar nata ?"yanzu ku baku ga rashin dacewarmu ba ?A tare suka girgiza masa Kai "mu bamu gani ba sai sam barka .Ya girgiza Kai " matar data Kalli tsabar idanunku tace bata son jininku har abar so ce agurinku ?yayi musu tmbyr a matukar fusace"
dukkaninsu kallonsa sukayi yadda jikinsa ke rawa kmr anjonasa masa shocking ."Ku bar ganinta shiru shiru irin wadan nan mutanen abun tsoro ne wallahi gara a bani masefaffiya daita juyin duniya sukayi dashi yace bai sonta km bazai aureta ba "na yarda ku nemo wasu mata ku aura min ko guda hudu ne km a rana daya na amince amman ban da wannan jakar yarinyar mara tarbiya yana gama fad'ar hk ya mike ya kama gabansa kallon junansu sukayi na second goma sannan suka numfasa "yanzu me kuka ga zamuyi ?inji cewar aunty khadeja "mu fad'awa mami kawai tasan komai dan boye boye bashi da wani amfani zan fada amnan mu bari zuwa jibi zan san yadda zan fad'a mata .
atare suka mike suka nufi d'akin hjy zulaiheart tana zaune akan kujera tana duba abubuwan da suka kawo mata suka shigo jikinsu a sanyaye tana ganinsu ta fad'ad'a fuskarta da murmushin jin dadi duk suka yiwa kansu mazauni ta kallesu daya byn daya "Allah dai ya taimakeku gbdy yayi muku albarka yadda kuke tsaye akaina da abinda kuke min dukkaninku Kuna min k'okarin gurin yin abubuwa ."
"da wanda ya bani million daya da wanda ya bani dubu dari da wanda ya bani dubu hamsim dukkaninku abu d'aya ne agurina Kuma inshallahu ladanku daya ne saboda dukkaninku abu d'aya ne
ni dai fatana Allah yayi muku albarka ,kowa yayi abinda zai iya ban da takura kai , Allah ya raya muku zuriarku yadda kuke hidima dani Allah yasa yayanku suyi muku fiyye da haka "Ameen suka had'a baki gurin fad'ar hk.
shiru sukayi babu wanda ya sake kokarin fad'a mata halin da'ake ciki ta d'ago daga duban kayan da suka kawo mata, shiru tayi tare da tsura musu Ido"ya na ga kmar bakwa cikin farinciki alhalin ba haka fuskokinku yake ba a d'azu da kuka zo ? naunayen ajiyar zuciya suka sauke "ku fad'a min idan wani abu ne ? shiru sukayi kowannensu najin tsoron mgnr ta fito daga bakinsa "Kun min shiru ku fad'a min mana Kun tasani gaba Kuna kallona da kyar aunty khadeja ta soma bayani "kiyi hakuri aunty shahida zata fada miki komai amman ba yanzu ba ."
"akan Adamcy ne ko ?ta tmby tana dubansu a tare suka girgiza mata Kai alamun "eh suka tsinci kansu da bata amsa da haka "yanzu har akwai matsalar da zaku boye min bayan bani da kowa daga Allah sai ku duk abinda ya kunno Kai cikin rayuwarmu tare muke had'uwa muke magance matsalar shine yau zaku barni cikin duhu, shikenan na gode karku fad'a dan ko Kun fada min daga baya bazan gode ba Kuna iya tashi ku kama gabanku ."
zubewa sukayi a gabanta kamar zasuyi kuka "kiyi hakuri mami zamu fad'a miki a natse aunty shahida ta zayyane mata komai tun daga ranar da suka fara magana da mrym har zuwa yau din nan "shiru hjy zulaiheart tayi tana sauraron aunty shahida da sauran yaranta mata byn ta gama Jin komai ta numfasa kafin daga bisani tace "shikenan ku barni dashi zan nuna masa ni na haifesa bashi ya haifeni ba daman na dade da sanin baya son farincikina."
nan suka cigaba da tautaunawa "Allah mami ki bud'e masa wuta idan yaga kin haukace masa zai yi abinda kike so "ku barni dashi a yau din nan zai amince ko kuma ya canza uwa aunty shahida tace "duk abun bai kai haka ba ki dai bisa a hankali kar komai ya jagule "babu wani binsa da zanyi ahankali ai shi zuma ne sai ancisa da wuta ake samun kansa daman Ina lallabasa ne na d'auka abun nasa na girma da arziki ne a she wulakanci ne tana gama fad'ar haka ta mike ta nufi d'akinta .." tana shiga aunty khadeja ta mike ta d'auki jakarta ta rataya "ni zan wuce baza'a yi wannan dramar Ina gidan nan ba ,itama zabiba ta mike jirani mu wuce tare gbdy suka mike suka fito tare ."
*******
A bangare mrym kuwa tana shiga d'akinsu ta fashe da matsanacin kuka nana hauwa'u dake zaune ta zabura ta k'araso Inda take ta rungumeta tsam tana tambayarta sai dai taki bata amsa kuka take sosai zuciyarta na zafi da qunci "me yasa ya Adam bai sona ?me yasa nana hauwa'u fada min aibuna da yasa baya Sona ? tayi mgnr hawaye na tsiyayowa daga cikin idanunta ,nan nana hauwa'u ta fahimci dalilin kukanta "Kiyi hakuri marsi baki da wani aibu illa rashin sa'a irin nasa domin sai ya aureki zai san yayi Sa'ar samu mata mai kyakkyawar zuciya."
qaruwa kukan marsi yayi ",yadda bai sona
nima bana son shi amman nayiwa kaina alkwarin zan auresa zan rayu dashi muddin rai " wani murmushin farinciki nana hauwa'u ta saki tare da sake rungumeta ajikinta tana Shirin magana qarar wayar yasa tayi shiru sannan suka saki juna a hankali ta k'arasa ta d'auka tana kokarin fita daga d'akin mrym ta shige bayi ta kulle ta jingina bayanta da kofar ta sulale zuwa kasa tare da sakin wani kuka tana toshe bakinta da sauri nana hauwa'u ta fito zuwa haraban gidan Inda ta iske yayyunta mata da mamaki take kallonsu ",ya haka har zaku wuce ?tafiyar dole ce auta dan yau bom zai tashi a gidan nan Kuma tashin babba ne gara mu san Inda dare yayi mana "daman na kiraki ne dan kisan yadda zaki kwantarwa mrym hankali tare da bata kwarin gwaiwa ."
"Ga ta can kuwa sai kuka take amman ai ta amince zata auri yaya ? " eh ta amince amnan ai shi uban gayyar yace bai yi inji cewar zabiba "Kai!
ta fad'a tare da dafe goshinta "kiyi kokari ta dawo normal inshallahu zuwa jibi zamu shigo idan munji yarda suka kare da mami juya sukayi a tare kowace ta nufi motarta tana tsaye direbobinsu suka jasu sannan ta juya da sauri ta koma ciki. koda ta koma d'akin bata ga mrym ba tana toilet ta kunnawa kanta ruwa tana kokarin daidaita natsuwarta da rarrashin zuciyarta, dole tana bukatar ta rarrashi kanta sannan ta sanyawa zuciyarta hakurin zama dashi ta kowani hali , guri nana hauwa'u ta samu ta zauna abakin gado tana jiran fitowarta ."
Rai a matukar bace hjy zulaiheart ta shiga bangaren ATA tana gama shiga ta fara zuba masa fad'a " tur da haihuwarka Adam " ya waigo a matukar firgice yana zaro Idanu lokaci guda yay fillinging da wayar dake rike a hannunsa ya zube kan gwiwowinsa kasan a gabanta cikin tsananin tashin hankali muryarsa a shake yace "sweetheart me nayi ?"dan Allah ki yafe min ,kiyi min afuwa bazan sake ba."
hjy zulaiheart ta nuna sa da yatsa "Kai Adamcy ban ta'ba sanin baka da hankali da tunani ba sai yau , yau tsawon shekaru Ina binka akan magana daya amman babu komai na rantse da girman Allah bazan sake maka magana akan batun aurenka ba ka cigaba da rayuwarka haka har mutuwa ta riskeka tunda baka san mutuncin kanka ba, ga yarinya yar mutunci yar'uwarka amman dai..."sai tayi shiru tana huci ta kasa cigaba da mgn sai lokacin ya fahimci laifinsa ."
ya sunkuyar da kansa kasa yayinda mami ta cigaba da magana cikin zafin rai "idan baka so maryam ba wa yakamata kaso?" ba dan maryam na diyar dan'uwana ba tana da nagarta da kamun kan da kowani nmj zai sota Kuma mahaifinta nada nagarta da zai zama surukinka "ai ka nuna min ban Isa da Kai ba ko ? to na gode Allah ya saka da alkhairi Allah ya biya ."
"a'a sweetheart wallahi kin Isa dani sai dai zuciyata ta kasa ..."mami tayi saurin tareshi da cewa ",aikin banza daga yau in nice na haifeka to ka fara shirin aurenka da maryam Koda yin hakan yana nufin rasa komai naka ATA ya kalleta da sauri sannan yace "to sweetheart zanyi duk yadda kike so sai dai naso ki dan saueareni kiji ita kanta yarinyar bata ..."
Mami ta juya a matukar fusace tana cewa "bazan saurari komai daga bakinka ba ni dai na fad'a maka muddin nice uwarka ka shirya rayuwar aure da mrym idan baka zo ka sameni da maganar aurenta a daren yau ba na rantse maka da girman Allah sai dai ka nemi wata uwar bani zulaiheart ba kayi abinda nake so shine zaman lafiyarka dani ta karasa fita tana magana cikin tsananin fushi da bata ta'ba yin irinsa ba ."
ATA ya rike kanshi tare da furta "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun"shikenan zuciyarsa ta sake shiga rud'ani kasa ya zame ya zauna akan capet tare da zabga tagumi tunani yake yi yanxu ya zai yi kenan?"shin ya cigaba da kafewa akan ra'ayinsa ne ko Kuma ya hakura ya aureta a wuce gurin ?cike da sanyin jikin ya mike ya nufi bangarenta Yana kokarin shiga part dinta sukayi karo da maryam itama d'akin hjy zulaiheart zata sakmakon kiranta datayi ."
wani irin gigitacen mari ya ɗauketa dashi Sanna ya rufeta da duka "kina hauka ne da zaki hada jikinki danawa ? kasa tayi dafe da kuncinta tana kallon zara zaran yatsun ka'fafunsa dake jere kowannensu dauke da kwantaccen gashi ,koina ajikinta rawa yake "mahaukaciya kawai ko ni sa'anki ne ?ta d'ago tana dubansa sai faman huci yake "Maza ki d'auke wad'an nan banzayen idanun naki akaina wallahi ban taba jin na tsani wani halitta ba kamarki har kece zaki bude baki ki fuskanci 'yan'uwana da Kalmar baki sona saboda ke din dakikya ce da bata san hallici ba yasa kafarsa d'aya ya take mata kafa yana watsa mata kallon banza ."
"ki sani bana sonki kuma har abada bazan soki ba wani abu taji ya caki zuciyarta tare da kafeshi da idanunta da suka canza kala zuwa na bacin rai yayinda wani bakinciki ya tokare mata kahon zuciya wanda yasa hawayen ya cika idanunta amman ta danne taki barin su zuba tunda take baa ta'ba mata wulakanci irin na yau ba wannan shine karo na biyu da ya daura hannunsa ajikinta ranta yayi matukar baci tana son ta bar wajen amman bazata iya ba bazata iya ba dan batasan me zai sake biyowa baya ba ,dan haka ta kife kanta akasa kuka take son tayi amman bata son tayi akan wani banza da bai san darajarta ba ..."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS
AYSHABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 11
" har tsawon wannan lokacin yana tsaye yana mata kallon kaskanci kafin daga bisani ya d'an motsa labbansa " biyayya Kawai zan yiwa mahaifiyata na aureki sai dai zakiji jiki sai kinyi da kin sanin kalmarki gareni, zakin san kin ta'boni yana gama fad'ar haka ya d'auke kafarsa tare da shure mata kafa ya nufi cikin part din mahaifiyarsa ransa a dagule .
girgiza kai mryam ta shiga yi kafin daga baya ta rarrafa ta shige parlour'nsu ta ra'be a bakin kofar d'akin tana kukan zuci , cikin yanayi na tashin hankali take furta "me na tsare maka ya adam ? "me yasa baka sona ? "me yasa ka tsaneni hk ? haka tayita jerowa kanta tambayoyin da bata da mai bata amsa sai shi shi din kuma bata isa ta tuknkaresa ba gbdy Idanunta sun canza qala tsabar tashin hankalin data tsinci kanta ."
kuka take son yi sai dai zafin da zuciyarta ke yi yasa hawayenta yaki diga sai idanuwanta gbdy sun burkice " baka sona amman ya zama dole na jurewa komai muddin ina son rabuwa da iyayena lafiya , bazata manta kalman mahaifinta ba alokacin da zata dawo daga abuja domin sun samu kyakkyawan mazauni acikin kwalkwaluwarta "maryam muddin ni ne wanda nayi sanadiyyar zuwanki duniya Kuma kina son gamawa da duniya lafiya ki auri adam bisa umarnina Kuma ki zauna dashi zama na amana bisa umarnina , yau ace ba yar'uwata ce ta nemi wannan hadin ba sam bazan takura miki ba zan barki har sanda zaki kawo min irin mijin da kike so .."
A bakin gado ya iske hjy zulaiheart ta cika tayi bam ,cikin sanyi jikin nan nashi ya k'araso ya zauna a gabanta yana neman gafararta , ko kallon Inda yake bata yi ba daga karshe ma ta kawar da fuskarta gefe al'amun bata son ganinsa ya runtse idanuwanshi sosai yana sauke numfashi ,byn kmr second biyar ya bud'e idanunshi ya fara Kame kame "uhm ammm kiyi hakuri sweetheart , afuwa sweetheart I will not do it again , inshallahu I promise you zan aureta ."
"hjy zulaiheart taji dadin jin furucinsa har cikin ranta sai dai ta share tana jan tsaki a fili. "ki yarda sweetheart duk duniya babu wanda zai soki da son farincikinki kmr ni ,kiyi hakuri bazan juri ganin 'bacin ranki ba ya fad'a yana riko hannunta , naunayen ajiyar zuciya ta sauke batare data fuskancesa ba ,duk da zuciyarta ta d'an yi sanyi dan daman fushin na dole ne yanxu kuwa ta hakura