Showing 84001 words to 87000 words out of 168608 words

Chapter 29 - Mar'adam's Book 1 Hausa Novel Complete

masa baya, bai tsaya akoina ba sai abakin wani makeken kofar glas wanda ya kasance anan ake ajiye duk wasu ayyukansu masu mahimanci ya zura duka hannuwansa acikin aljihun wondonsa yana kallon wajen yana bukatar a bude masa ya shiga tare da qarin bayani ."


Ahankali ta danna madan nan bude waje suka shiga gabadaya a natse ta shiga yi masa bayani tana nuna masa kayayyakin dake ciki da kuma wanda aka fitar kudinsu basu shigo ba duk abinda take fad'a yana jinta kuma yana fahimtarta , amman ko tari bai yi bai yi ba ."
runtse idanuwanshi yayi sosai domin ransa ya gama kololuwar 'baci , daga nan wani bangaren suka nufa inda suka dinga wuce maikata da masu zuwa sarin kaya ,ba qaramin barna akayi masu ba ,yaya Ibrahim "yanzu kuna kallo akayiwa kamfani barna mai girma haka ? ya fad'a yana sake runtse idanushi dan baya ganin komai sai wani irin azababen duhu na 'bacin rai ."


Yayi shiru na kusan second goma sannan ya sake motsa lip's dinsa "yanzu har kunnuwanka sun manta abinda dady ya fad'a mana kafin rasuwarsa .?" Ka manta umarninsa akan wannsn kamfani ?" duk wannan maganr da yayi Idanunshi na runtse sannan cikin tsadadden turancinsa yayita " ban manta komai ba adam "ban manta umarnin dady ba amman bani
da yadda zanyi ne kai kasan halin sultan da sauran yanuwansa kowa abinda yaga dama zaiyi yanzu dai tunda kazo Komi dawo daidai amman kuma kabi komai a hankali kar asamu damuwar da zata haifar da matsala a tsakaninmu wani irin azaban ciwo yaji yana saukar masa har cikin kahon zuciyarsa yana sukarsa zuciya tazo masa wuya , baya jin zai d'agawa duk wanda yake da saka hannu acikin 'barnar dakayiwa kamfanin kafa ba ,bai sake cewa komai ba ya juya da sauri suka rufa masa baya ."


conference room ."d'akin ne da'aka tanada domin tautauna mahiman abubuwa masu matukar mahimanci , dogon table ne zagaye da kujeru bakake na alfarma yayinda jikin bangon d'akin ke manne da hoton mr president na lokacin da gwanar jahar lagos ,sai hotonsa dake tsakiyar hotonsu da certificate dinsa na kasuwancinsa ."mafi yawan mutanen dake zaune aciki room din yan'uwansa ne dake aiki akarkashin kamfanin ,a natse ya shiga d'akin taron ya yana shan kamshi tsit baka jin motsin kowa sai ac dake aiki da kuma na mutane dake fita a hankali , bai kalli inda suke zaune ba ya qarasa kujerarsa wanda ya kasance mallakin mahaifinsa ne ada ya zauna cikin nuna isa."


ido sultun ya runtse da karfi saboda bakinciki ganin yadda mr ata yayi wani irin zauna akan kujera na nuna isa da jarumta da kamala duk da cikin yanayi na bacin rai yake amman hakan bai hana ainihin sahihin kyawunsa fitowa ba daman kuma shi haka yake fushi ko damuwa baya hana aga kyawunsa hasalima kyau yake qara masa."
wani dogon tsaki sultan yaja wanda bai san a fili yayisa ba sai daya ga gabdaya mutanen dake gurin sun juya suna kallonsa banda uban gayya mr ata wanda ya sake daure fuska alamun babu wasa ,sai dai zuciyarsa banda tafasa babu abinda take ahankali ya runtse tsumammun idanuwanshi domin saisaita kanshi daga aikata abinda ke taso masa ahankali ya motsa lip's dinsa ya soma magan a natse tamkar baya son magana sai dai jin maganar kasan magana ce ta masu hankali ce ."

"The journey of thousands miles begings with a step as you all know ,ya numfasa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya cigaba d'an lokacin da muka dauka bamu ziyarci wannan kamfanin ba yasa kowa yayi abinda ya ga dama "hakika anyi mana barna mai girman da bazamu iya bari ba , bayan acikinmu kowa yasan adadin wahalar daaka sha kafin wannan kamfanin ya samu kar'buwa a idanun duniya gabadaya ,but what's more important is that duk wanda yasan yana da hannun acikinku wajen danne kwandala acikin dukiyarmu ya gaugauta dawo dashi a yanzu kafin na dauki mataki akan kowa ye acikinmu dan bazan ragawa kowa ba ,bayanin mr ata yayiwa wasu daga cikin yanuwa dadi most especially mukhtar wanda Ke rike da wayarsa yana daukar vedio tautaunawa da'ake wanda kusan duk lokacin da zaa gudanar taro haka ana yi wani lokaci a daurashi a social media wani lokaci kuma baa daurawa ."


"Ina jiranku wad'an da sukayi taadanci da fashiwa kamfani domin su san kansa ba sai na fadesu ba sannan sun san number asusun kawasuwancinmu mintuna shabiyar kacal na bayar a maida kudaden daaka hamdame cikin asusu "malam ka dinga sanin yadda zakayi ma mutum magana yaji dadi (Al kalimatu dayyibat sadaqat)kazo kana wa mutane magana cike da isa da izza wa kaajie anan ? sannan su waye suka yiwa kamfani taadanci da fashi da hamdame kudin kamfani ?"sun san kansu !mr ata yayi mgnr tmkr ba daga bakinsa mgnr ta fito ba ,ya cigaba da sauraron some ."

D'akin taron ya sake yin shiru babu wanda ya sake magana hatta yaya Ibrahim bai tofa albarkacin bakinsa ba illa ya zuba tagumi yana ji kuma kallonsa kuma hukuncin adam yayi masa daidai muryarsa a dake mr ata yace " ina jiranku rashin dawo da kudad'an nan fa daidai yake da bari aiki acikin wannan ma'aikatan ya fad'a yana kallon gefensa inda some Ke zaune tana qara masa bayanin wasu a abubuwa" idan haka ake son mutun yasan kuskurensa har gyara da mutane dayawa basu gyara kuskurensu ba sannan dan haka malamanmu suke koyar damu wallahi da babu wanda ze juri zaman islamiyya ba kafi fili ka fad'a mana su waye masu laifi musani ba ka tsaya jin kai da girman kai ba ,dan anan babu wanda ka ajiye , yadda kake iko da wannan kamfanin haka muke..."


"Enough ! ya fad'a a matukar fusace yana dukan table "ka shiga hankalinka ,su waye mahamdama macuta yan fashi daya wuce ku " sam gaku nan tamkar. mutane amman baku da bambamci da dabbobi ,sam babu jin tsoron allah acikin zuciyarku , sultan ,fahad , hamid a wani goma sha biyu kawai na baku ku dawo da komai idan ba haka ba..... "me zakayi ?sultan ya katseshi cikin zafin rai "me ka isa kayi ?babu abinda ka isa kayi "
"kunsan su dabbobi basu gane yaren biladam sai na dabbobi yan'uwansu dan Allah karku dawo da kudaden nan alokacin da nace "yana gama fadar haka ya mike tsaye ya tura kujerar daya tashi baya ya fice ."nan hayaniya ta kaure kowa na fad'ar albarkacin bakinsa kai tsaye mr ata office dinsa ya koma ."


Karfe biyu daidai na rana mami na zaune a parlour tare da yaranta maryam da nana hauwa'u suka jiyo sallamar baba qarami sai da gaban mami yayi wata irin mummunar faduwa ya qarasa shigowa yayi wa kanshi mazaunin nana hauwa'u ta gaishesa haka ma maryam ya amsa fuskarshi babu yabo babu fallasa mami ta kallesu alamun su basu waje ,bayan sun tashi sun wuce mami ta fuskancesa alokacin da shima ita yake kallo "zulai naji shiru akan maganarmu banji kin neme ni ba har gashi an saka ranar auren adamu da wacan yarinyar yana da kyau nasan inda maganarmu ta kwana abun nan zai yuwa ko kuwa ?".

mami ta numfasa gabanta na faduwa domin dai ita kam bazata iya sake kuno wa danta wata damuwar ba maryam ma da yaya ya karbeta ?gara kawai ta ari bakin adamcy tace masa a'a tunda tasan ko ta tunkaresa da batun bazai ta'ba amincewa ba cikin shakkakiyar murya tace "nayi masa magana ammm..."sai tayi shiru tana jin nauyin fitowar maganar "amman me ki fada min abinda yace "Uhm daman cewa yayi wai mace daya ta .."
shiru tayi ta qasa qarasa maganar ganin wani irin kallon da baba qarami ke mata ido cikin ido furzar da iska yayi ya lashi lebansa na kasa sannan ya hade hannunwansa still idanunshi na kan fuskarta cikin danne fushinsa dan baya son ta gane fushinsa a fili saboda abinda kan iya zuwa yazo bare su suyi zargin da hannunsu ,cikin dakewa yace "yanzu dai kin nuna min bazan iya zuwa neman alfama wajenki kiyi min ba ko ?sam sam ba haka bane kai ma kasan halin adamcy idan kuma zaka iya masa magana da kanka to kayi kamar ma haka zai fi "no ba sai nayi masa kema uwarsa da kika haifesa bai ji maganarki ba maganar ubanwa zai ji ? " iya abinda ya iya fada kenan ya tashi ya kama gabansa ya barta cikin zullumi."


Mr ata a matukar gabalaice ya qaraso gida zuciyarsa tamkar zata kama da wuta , sai dai cike da qasaita ya shigo parlour'n Mami babu kowa parlour'n sai qarar tv da motsin masu aiki a kitchen ya zauna akan doguwar kujera ya d'ora kafarsa d'aya akan d'aya yana ciza gefen lips dinsa ,ko cikakken second goma bai yi da shigowa ba sai ga hindu ta shigo dan akan danunta ya shigo tunda mahaifinta ya fad'a mata yadda sukai da Mami ta kasa tsaye ta kasa zaune , zama tayi a kujerar dake fuskartashi ta tsura masa idanunta tana kallonsa tamkar ranar ta fara ganinsa tana qoqarin bude baki tayi masa magana ya mike tsam ya kwashe wayoyinsa ya haye samansa yana jan tsaki dan shi ya tsani yawon kallo , kamar ta dakatar dashi amman ta kasa ta cigaba da zama zuciyarta na mata wani irin bugawa akanshi ."

tana nan zaune har mami ta fito sanye cikin doguwar rigar na atamfar super exclusive sabuwar bugu ,mami bata tsufa saboda tsanani tsafta da gyaran jiki fuskarta a sake tace "a'a hindu yaushe kika shigo ?ban wani jima ba mami nazo wajen yaya ne "to ai bai shigo gidan ba tukun .
ya shigo yanzu ya hau sama "to shikenan bari naje dakin nasa nazo har ta juya hindu ta kirata sunanta cike da rauni "mami !"
Cak mami ta tsaya tare da juyowa ta tsurawa hindu ido "mami da gaske kin yiwa yaya adam maganata yace miki a'a ?"shiru mami tayi shiru ta rasa me zatace mata kafin mami tayi wata magana hindu ta cigaba da mgn cikin rawar murya "dan girman allah mami karki yi min tsakani da ya adam kullum zuciyata tafasa take akan sonshi Ke kad'aice zaki iya taimakawa zuciyata idan ba haka ba zan mutu cikin rawar murya mami tace "mutuwa kuma ?"kanta ta gyada mata tare da cewa "da gaske zan kashe kaina shine fansa akan soyayyar ya adam "na shiga uku ni zulai "mami ta furta acikin zuciyarta "kiyi addua hindu ni kaina zan só adamcy ya auri mata fiyye da biyu amman raayinsa ne auren mace daya macen dayan ma da kyar ya amince amman Kiyi addua nan gaba idan rabo sai ya qara dake da sauri ta runtse idanunta kana ta koma ta jingina bayanta da kujerar da take zaune tana jin wai irin faduwar gaba mai tsanani ahankali take zubar da hawaye ganin da gaske tarasa farincikin rayuwarta "anya kuwa mami nada tausayi da imani ."Anya mami bata da son zuciya ?"Tayi wa kanta tambayar tana jin radadi acikin zuciyarta bazata iya jurar rashinsa ba ,bazata iya ganin da wata a matsayin matarsa ba, yadda bazata zama matarsa a farko ba to babu wacce zata zama "hindu bari naje naga yayanku nazo hindu ta bude idanunta da kyau tana kallon bayan mami dake taku ahankali."

Kai tsaye kitchen ta shiga ta bud'e firdge kwalin dynsimo mai sanyi ta ciro ta rufe ta qarasa inda cup's suke ta dauki daya ta daura akan qaramin tray ta fito ta wuce a parlour ta samesa zaune akan kujera yana sanye da singlet da gajeren wondo ta bude kwalin juist din ta tsiyaya a glass cup taja qaramin table din glass din dake tsakiyar dakin ta dora tray ta mika masa cup ya girgiza mata kai tace "na kawo maka ruwan sanyi ?ya sake girgiza mata kai "coffee fa ? still dai kai ya girgiza aranta tace yau dai akwai damuwa ta d'an zauna gefensa "ka daina barin damuwa na hana zuciyarka sukuni "naji sweetheart amman ba wani damuwa bane zazzabi nake ji kawai "sannu bari naje na kawo maka magani ka sha "no need sweetheart thank you "kai har yanzu bakasan ka girma bane meye abun gudu a magani ?ni dai kawai bana só né da zarar na kwanta nayi bacci zanji daidai ,tô karka kwanta yanzu magariba ta kusa ya gyada mata kai yana mai runtse idanuwanshi ta mike tana cewa "me zaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login