Showing 75001 words to 78000 words out of 168608 words
jikinta akan kujera tana jin bakinciki abubuwan da suke faruwa daita allah ya bata kyau ya bata ilimi tana da nagarta amman bata san dalilin da maza suke gutunta bayan sun kawo kansu wajenta ba , tana zaune tana tunanin taji sautin muryar aunty salma"maryama !maryama!!ke dan uwarki wannan wani irin rashin mutunci né kalmarta ta katse mata tunaninta ta dawo haiyacinta tana magana cikin bacin rai "au zama ma kikayi dan iskanci ni nawa mijin bai kwanta ya huta ba yana can neman abinda zaku ci shine ke zaki zauna saboda sakarci banza da tunanin banza daga yarinya tazo tana sakarci da munafurci sai ki nemi waje ki zauna kina tunanin iska dana banza da wofi allah dai yasa komai zai faru abanza né tunda bashi da wani amfani ana da kyau amman ya zama na banza ."
"tô ai dole ya zama na banza tunda mugun hali yayi yawa "
tarasa me ta tsarewa aunty salma acikin gidan nan zuwa yanzu bata tunanin iya kiyayya ce kawai ta fara tunani har da hassada take mata akan halittar da allah ya bata idan ba haka ba tana mata komai iya bakin gwargwado tayi mata shara tayi mata wanki idan ta kama wanke wanke duk tana yi dan dai a zauna lafiya da kuma kar ayi masu gorin ciyar dasu daake acikin gidan shiyasa sau tari bata son fita tsakar gidansu tafi son tayi zamanta a daki dan da zarar ta fita ko ita ko aunty hassana sai an samu wanda yasata aiki ko ya zageta ko mata gori ."
muryarta a sanyaye tace "yanzu ni aunty salma me nayi miki ?akwai abinda kike bukata da banyi miki ba ?ta rike baki au tambayata ma kike yi saboda yanzu kin kawo karfi an balaga an balallage an zama iyayen mata ? "
"allah yasa ba ita kadai ta balaga ta zama iyayen mata ba wadan da suka balaga suka zama iyayen mata suna da yawa " suka tsinkayi muryar habib abayansu yana harararta ta juya tana kallonsa
"zo ki fitar mana daga daki kafin na miki dukan mutuwa "uwarka da ubanka basu isa ba bare kai qaramin dan iska bazan fita ba idan kana iyawa zo ka fitar dani tattaccen d'an iska ."
Jin haka yasa cikin fusata ya nufota gadan gadan maryama ta mike da sauri ta shiga tsakani tana cewa "Uhm uhm after dad babu ruwanka daita "tô wallahi kice mata ta fita ta bar mana dakinmu "au har wani takama kake da dakin aro? "dakin aro ne a aka bawa uwarka byn kai a kusa da dakin kashi aka haifeka idan bakasani ba kasani ga dakin daaka yi cikinka ga masai Shege ma shegen girman tsiya anyi mugun gado a wajen uwa ".
Ya daga hannu zai kai mata mari maryama ta rike hannunsa a rikice cikin muryar kuka tace "haba habib ka barta mana ta fadi duk abinda take son fad'a ai bakinta ne tunda mu din ba shegu bane meye abinda zai dameka arziki kuma na allah né "kinga makira banason iskanci da munafurci ki barshi yayi min abinda ya ga dama amman gamawarsa ke da wuya zanci uwarsa da shi kansa dan wallahi duk iskanci da yayi akan uwarsa zan rama dan ita ce daidai ni ba shi qaramin dan tasha ba ,yana yawo suki suki duk yunwa ta gama cinyesa tayi maganar cikin daga murya ".
"Dan allah kiyi hakuri karki saka aunty cikin fadan nan habib yayi Kuskure amman kiyi hakuri bazai sake ba habib ka bata hakuri ".
"What!"
"Allah ya tsareni na bawa wannan matar hakuri kar allah yasa tayi hakuri ko ki fitar mana da wannan mahaukaciyar matar koni yanzu najata na fitar daita sha shar mata mara sallah mai dotti kawai hannu aunty salma ta daga zata wanke masa mari taji ya rike mata hannu sannan ya tsura mata idanunshi cikin sarkewar murya yace "kin gama ta'ba lafiyar kowa acikin gidan nan yanzu ke har yanzu a tunaninki kin kai matsayin da zaki cigaba da marena na kyaleki ? tô idan kina wannan tunanin ki daina yanzu dan zaki ya girma ya wuce wannan tozarcin dan bake ba hatta wanda ya ajiyeki acikin gidan nan kanin mahaifina kenan ba bai isa ba bare ke banza jaka dabba mai hali irin na dabbobi mara hankali ."
a fusace ta fixge hannunta tare da cewa "da uwarka kakeyi itace jaka dabba ai ,dan marasa mutunci irin tsiya irin jaraba tana fada yana maida mata ita kuwa maryama sai faman kuka take tana bawa aunty salma hakuri data gaji ma sai tayi shiru kawai tana kuka tana kallon fuskar habib dake tsine mata yana hadawa da yaranta da kaf dangin mahaifinsu da yasan basa qaunarsu a maganganunsa ta fahimci babu wanda ya tsana kamarsu aunty salma ta fice cikin fushi ta bar dakin cike da tsananin damuwa ."
Maryama ta zauna jagwaba akan kujera tana mai runtse idanunta habib ya lumshe idanunshi "shiyasa kullum suke takura miki wannan sanyin naki yayi yawa ki zama mutun ki nuna masu zamani ki nuna ma kema yar zamani ce sai ku dawo daidai dasu ba kullum ki zauna kina asarar hawayenki a banza ba .""haba after dad mutunci aunty zamu duba yanzu kasan halin matar nan sai taje tayi mana wata kullaliyar a wajen baba gali ".
"taje dan kutumar ubanta shima dan kutumar ubansa yazo daidai nake da kowa allah ya taimakesa yazo idan ban raba masa kanshi gida hudu ba kice Shege ne , anan zan jira zuwansa ya fad'a yana huci tmkr zaki ta mike ta kamo hannunsa ta zaunar dashi ta zauna kusa dashi tana shafa masa baya dan ta fahimci ya dauki zafi dayawa "kayi hakuri komai me wucewa ne wata rana sai labari abinda ya baka dariya wata shi zai saka kuka ka bar aunty salma da duk wanda zai fad'a son rashi acikin gidan nan akanmu."
ita fa aunty salma bata da laifi gani tayi yanuwan mahaifinmu suna yi mana yau da sun ga kima da darajanmu wallahi bata isa ba amman nasan wata rana idan ance tayi bazatayi ba kayi hakuri kaji danuwana rarrashinsa tayita har ya sauko tace "kaje kayi sallah nima zanje nayi kafin aunty su dawo ni na godewa allah ma da bata nan bare taga abun bakinciki kuma allah yasa kar aunty salma ta fad'a wa baba gali "ta fad'a masa mana Ke kike tsoronsa yazo ni yau a gida ma zanyi sallah ina jiran duk abinda zasu dashi bari ma naje na nemo atakobina wacce zan fellewa mutun kai dashi ."
"Dan girma Allah kayi hakuri meye hadinka da takobi kai ba dan daba ba "na zama yau "allah ya tsareni allah kiyaye bazaka zama haka ba Kiyi adduar karsu zo da hauka ya fad'a tare da shigewa dakin aunty kofar tabi da kallo kafin daga baya ta mike taje tayi alwala ta fita ta tada sallah tana cikin sallah tajiyo sallamar aunty tana kiran sunanta tana jin habib ya fita yana cewa "sallah take aunty sannu da zuwa "
"Yauwa habib a she kana gida ?nima ban jima da shigowa ba ina kika je ne ?kai habib zaka fara tambayoyinka kenan babu damar kaga na fita murmushi yay yana sake cewa "aunty ina kike je ?munje duba jikin hafsat ne ta haihu amman cs aka mata ".bai sake cewa komai ba saboda ya fahimci kowace hafsa take nufi diyar aunty fatima yayar mahaifinsu aunty ta mike ta shige dakinta domin yin sallah ."
Byn mintuna goma maryama ta fito daga dakinta zuwan dakin aunty duk jikinta a sanyaye lokacin aunty tana kan dadduma ta idar da sallah tana dai zaune "aunty sannu da zuwa "yauwa my princess ya zaman gida ?ta gyada mata kai alamun Lfy!"ya na ganki wani iri ko akwai abinda me damunki ne ?tayi shiru kawai tana jin faduwar gaba "kin dan daura mana wani abu kuwa ?ta bude bakinta ahankali tana shirin bawa aunty amsa suka jiyo hayaniya shiru tayi tare da kasa kunne muryar baba gali ne ta mike da sauri jikinta har rawa yake ta nufi kofar fita itama aunty ta biyo bayanta a tsakiyar falon suka gansa tsaye tare da aunty salma da aunty hassana sai hargagi suke tamkar wasu karnuka yayinda habib ya shiga kitchen ya dauko zabgegiyar takobinsa mai tsine ya koma bakin dakalin kofar fita ya zauna yana wasa takobinsa ,aunty hasana ta nufo inda yake shi kuwa habib kanshi na kasa yana cigaba da wasa takobinsa jira kawai yake suyi masa wata maganar banza ."
Aunty ta kalli maryama ta kalli habib tana bukatar qarin bayani cikin fusata aunty salma tace babu irin qare maku zagin da wannan tantirin yaron bai yi ba ta uwa ta uba har da ce mana dabbobi jakuna aunty hasana tace "da ubansa yake Shege dan Shegiya "da sauri ya mike yana zagayesu da takobi kiiiii kake jin tsinin bakin takobi asimintin falon basu ba hatta aunty da maryama sun tsorata "kai ko ka fara shaye shaye ne ko meye ?"da sauri ya juyo kan baba gali da yayi mgn fuskarsa a tsuke alamun bai son ya kawo masa raini "dan ubanka da kake zare masa idanu ka dauka zamu ji tsoronka ne ?"
"a'a nasan bakwa jin tsorona kamar yadda nima yanzu babu wannan tsoron duk wanda ya nemi zaman lafiya ayi wanda yace sabanin haka yake bukata bismillah ni bazan bata bakina ba sassara mutun kawai zanyi na aika sa lahira ."ya fad'a yana tsoka takobi daidai kafar baba gali ."
Da wani saurin gabadayansu suka ja baya suna kallonsa da mamaki kamar yadda aunty Ke kallonsa "tunda ku kun zama ahlin sheidan bakwa jin wani yare sai na dabbobi bismillah nima zan nuna muku akwai digon wannan dabbar ajikina ,tunaninku me zakuyi da kuka wani kwaso jiki gbdynku kuka zo ?
"To wallahi yau koni ko ku duk wanda ya zagi uwata da yaruwata sai na yanke masa harshe byn na raba kanshi gida hudu ."
zaro idanuwa sukayi suna sake ja baya dan ya daga takobin hannunsa daga aunty hassana har aunty salma suka koma bayan baba gali suka boye cikin karfin halin yace " bamu bane dabbobi da uwarka kake aiko jin haka Ke da wuya habib yayi kansa gadan gadan zai sara mata takobi aunty ta rike masa hannu tana zabga masa mari cikin muryar kuka tace "meke damunka habib ta fad'a tana kwace takobin tayi jifa dashi "zaka kasheni ne ?
"Ai da zai kashe dabba irinki da mun samu kwanciyar hankali "inji cewar aunty salma .
aunty kina jinsu ko bani takobina na sassara
shegu yan kutumar uba .."inna lillahi wa inna ilaihi rajiun allahumma ajirni fi musibatihi Waklifli khairan minha tana gama fadar haka ta durkushe kasa tana cewa "yanzu habib irin tarbiyar dana baka kenan ?maryama ta durkusa kusa daita tana mai rike hannunta tana ma habib wani irin kallo mai cike da tashin hankali ".
"Me yasa bazaka koyi danne fushinka ba ?me yasa zaka min haka habib ? me nayi maka dana cancanci haka habib ? "Kuji makira ina allonki allonki yana jahannama ,makira mata kin gama koya masa yadda zai ci mutunci mutune shine yanzu kizo kina kukan munafurci yau zamanku ya qare acikin gidan nan ku hada ina ku ina ku ku bar mana gidan nan mun gaji da ganinku daga Ke har wadan nan mataiyatan yayan naki bama bukatarku."inji cewar baba gali ."
nan da nan habib yayi kan baba gali duk da yaso ya rabu dashi ganin mahaifiyarsa tana kuka dan a duniya babu abinda ya tsana sama yaga ana cin mutunci mahaifiyarsa da yar uwarsa baya son ana zagar masa su bare a zagi qaddararta da binta da muyagun kalamai ko zubar hawayenta ,wuyan baba gali yake shirin damka ya
jiyo sautin muryar aunty cikin kuka tana cewa "wallahi habib idan ka ta'ba shi sai na tsine maka albarka "cak ya tsaya yana kallon baba gali ido cikin ido jikinsa na wani irin rawa tamkar mazari ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 16
Ahankali maryama ta mike daga cinyar umma hawaye ne sha'be sha'be akan kuncinta
ta tsurawa umma manyan idanunta wad'an da suka canza kala tana kallonta batare da tace uffan ba ,duk yadda taso ta daure ta tsaida hawayenta kasawa tayi hawaye take zubarwa sosai cikin tashin hankali mai tsanani ita kad'ai tasan halin bakinciki data tsinci kanta ciki adalilin jin labarin iyayenta ."labarinsu yayi matukar d'aga mata hankali "a she wahaalarsu da tsanar da'aka yi musu acikin family's ta samo asali ne daga soyayyar iyayensu ? haka nan taji tausayin kansu na sake shigarta . "
Koina ajikinta yayi sanyi yayinda falon ya d'auki shiru ,yadda maryama tayi shiru tana zubar da ruwan hawaye tana sake tariyo halin da iyayenta suka tsinci kansu adalilin soyayya haka ma umma bata sake cewa komai ba " ahankali wani irin so da qaunar mahaifiyarta da qaninta habib ya qara shigarta" allah sarki aunty "hakika kinga rayuwa, hakika ahlinki sun d'auki zafi dayawa akanki ."
"hukuncinsu yayi tsanani dayawa domin allah Ke had'a soyayya alokacin daya so ba dabarar mutun ba ,ba son ran mutun bane ,domin kuwa idan da dabarar mutun ne ko son ran mutu da mutanen duniya dayawa basu tsinci kansu cikn
ta ba ."
a qalla sun d'auki minti goma a haka suna kallon juna sannan maryama ta lumshe idanunta da sukai jajur alamun tarin quna da bakinciki ahankali umma ta numfasa "maryama ! ta kira sunanta a natse , ahankali ta motsa lip's dinta alamun ta amsa dan zafin da zuciyarta keyi ya danne fitowar muryarta "ki godewa allah ba kuka ya kamata kiyi ba maryama."
"ki godewa allah daya qaddara aure a tsakanin iyayenki da har aka sameku ta hanyar sunanh " "Alhmd!ta furta a can kasan makoshinta tana dafe kanta dake sara da mugun karfi "ya kai ki godewa allah ki sake gode masa ko bai kai ba ? kanta ta gyada mata alamun "eh!.
"To ki manta da duk abinda na fad'a miki muje Kiyi sallah kici abinci ki kwanta ki huta " da karfi maryama ta fizgo magana "bazan iya manta komai ba ,a halin yanzu ma ganin komai nake kamar a yanzu ya faru har nayi danasani umma nayi danasani jin wannan mummunar labarin rayuwa irin rayuwar da iyayena sukayi rayuwar kaskanci ne a wajena."
"why umma? "me yasa komai yake faruwa damu haka ?ahankali ummah ta shafa kanta
zuwa gadon bayanta tare da cewa "kiyi hakuri maryama kowa da kalar irin tasa qaddara a yanzu jajurcewa zaki qara akan wanda kikayi har kika samu cikar burinki na zamowa cikakkiyar mai ilimin lissafi ,kiyi qoqari ki tsaya bisa kafafunki domin tallafawa rayuwar mahaifiyarki daya qaninka domin ina hango tarin nasara da kwanciyar hankali atattare dake , bilkisu na bukatar farinciki ,maryama nasan da sannu zaki zamewa bilkisu sanyin idaniya amman fa sai kin manta komai maryama kin rungumi qaddarar rayuwarku ."
"Na yarda da qaddara ummah domin yana daga cikin cikar imani mutun , na yarda da qaddara amman umma aunty tayi kuskure arayuwarta bance laifi bane dan taso mahaifina amatsayin da yake amamn iyaye fa umma ? "manzon sallahu alaihi wa salam yace "ridal lahi fi ridal walidaini , wa sakad'ul lahi fi sakad'il walidai ."yarda allah yana tare da yarda iyaye, haka zalika fushin allah yana tare da fushin iyaye allah ya fifita iyaye akan komai most especially uwa ummah ,babu uwar da taza ji dadin irin rayuwar da aunty tayi ."
umma tayi shiru kawai tana sauraronta "misali na kwatantawa aunty irin abinda tayiwa iyayenta ya zataji ? na kawo mata in responsible man nace naji nagani sai shi duk tarbiyar da tayi tsawon shekaru tana bani nasa kafa na rugujeta ya zataji ?" magana ta gaskiya iyeyenta da yan' uwanta sun d'auki zafi dayawa amman aunty ta fisu laifi kuma lallai ya kamata taje ga iyayenta ta roki gafararsu sannan ta koma cikin danginta zuciyarta ta samu salama ."
"wallahi yadda nake jin habib araina bazan iya barinsa saboda wani ba bare iyayena da suka kawoni duniya ba ,abun da ciwo ummah ba kamar yadda kuka d'auka bane kema uwa ce ummah , aunty ta kona zuciyar mahaifiyarta dayawa, yanzu na gano duk aunty ce silar shigarmu cikin matsala , iyayenta na can suna fushi daita har yau ta yaya kike tunanin zataji dadi ?"ta yaya kike tunani zan iya bata farinciki byn ga inda zata samu fiyye da nawa ."?
maryama ta kalli umma cikin sarewa ta cigaba da magana " umma abun na da matukar ciwo irin ciwon dake cin zuciya da bargo ,ciwo ne da bashi da magani da mafuta har sai ka had'u da mahad'inka , shiyasa a kullum idan na kalli aunty sai naji tamkar tana boye mana wani abu mai mahimanci ga rayuwarta , ashe gsky né hakika bakinta bazai iya furta mana komai akan rayuwarta ba matsawar ita din uwa ta gari
ce , dan allah umma Kiyi min rai ki raba zuciyarta da wannnan rayuwar idan kuma baki yi ba ni zanyi ,zan rabata da nauyin dake daskare a qirjinta ."
Tana gama fadar haka ta mike a hankali tana share hawayen idanunta da suka gagara tsayawa tana jin wani zafi a qirjinta , bazata cigaba da d'aukar wannna nauyin ba , koda aunty bata amince ta koma ga yan'uwanta ba ,lallai ita zata nemosu a duk inda suke acikin garin nan ."muryarta a sanyaye tace "umma ni zan wuce sai da safe " kai kawai ummah ta gyada mata sannan maryama ta fara tafiya umma tayi shiru tabi bayanta da kallo tana kallon yadda take d'aga zara zaran yatsun kafafunta da kyar tamkar wacce bata da laka ."
" A