Showing 63001 words to 66000 words out of 168608 words
batare da ta fitar da abinda ke cikin zuciyarta ba ."sosai idanunta suka canza kala kallonta suka cigaba da yi suna jiran ta fara basu labarinta, yadda suke kallonta haka itama take kallonsu zuciyarta cike da wasi wasi tana son magana amman hakan ya faskara tana tsananin son yaranta ba zataso suji abinda zai d'aga masu hankali har da zai yi silar shigarsu damuwa ba haka zalika bazataso suji irin rayuwar da sukai da mahaifinsu kafin aure ba da irin tozarcin da mahaifinsu ya sha a wajen yan'uwanta ba ,ganinta fad'a masu wannan labarin babban kuskure ne zata aikata ko bama haka ba bata tunanin zuciyarsu zata iya d'auka , zuciyarsu ma bazata iya dauka ba , bazasu iya wannan juriyar ba."
Ahankali ta lumshe idanunta adaidai lokacin da habib ya d'auke hannunsa daga ha'barta har yau tana jin soyayyar mahaifinsu acikin ranta duk da bai duniya amman kullum ta kalli ya'yan da Allah albarkacesu da samu soyayyarsa na qara hauhawa acikin zuciyarta kuma bata jin Kuskure tayi dan ta auresa ".tana kallonsu suka mike atare suka nufi kofar fita kowannensu da abinda zuciyarsa ke tunani akanta dan daman sun san da matukar wahala mahaifiyarsu ta fad'a masu labarinta kasancewarta mace mai tsananin zurfin ciki da rashin son magana ."
bayansu tabi da kallo har suka 'bacewa ganinta bata iya d'auke kwayar idanunta akansu ba byan fitarsu ta gyara zamanta sosai tare da rafka tagumi gabad'aya kuma sai taji babu dadi aranta ji tayi kamar bata kyauta masu ba hakan yasa taji zuciyarta kmr zata kama da wuta ahankali ta mike tsaye cikin sanyin jiki ta isa bakin window falonta ta kai hannunta ta zuge labule tana kallon haraban gidan yaranta ta hango suna tafiya a natse kafad'a da kafad'a wanda kusan kansu d'aya basu tsaya akoina ba sai bakin part din umma "heartbeat ban san me yasa haka ke faruwa damu ba ? bana son ganin kanmu haka ina jin Kmr na kashe kaina na huta da wannan rayuwa ".
ya fad'a yana dafe goshinsa cikin tsananin damuwa .
"Subhanallah after dad ka daina fadar haka karka sake fad'ar wannan kalmar Allah bazai sa naga wannan ranar ba ,"ka dinga addua a duk lokacin daka tsinci kanka cikin tashin hankali ambaton sunan allah zakayi karka bari zuciyarka tafi karfinka muryarsa cike da tashin hankali
"amman me yasa anayi mana abubuwa rashin mutunci aunty ta hanani d'aukar mataki ? "daidai kenan habib ,abinda aunty tayi shine daidai shine abinda kowace uwa ta gari ya dace tayi idan suna yi muma muna yi to meye bambamci a tsakanin mai ilimi da wanda bai dashi ? kowani irin abu zaka gani a gidan nan ka d'aure ka cije ni yanzu damuwata ba matsalar Aunty hassana bace sanin inda dangin mahaifiyarmu suke shine babban damuwata ."
Ya riko hannunta cikin nashi yana dubanta "ki ciresu aranki abinda muka fi bukata sune dangin mahaifi , ace yau bamu da dangin mahaifi ko ba acikinsu muke rayuwa ba shine babban tashin hankalinmu "suma dangin mahaifiya suna da mahimanci domin zuciyarsu tafi ta dangin uba tausayi , jikina na bani akwai abinda yasa suka nisanci juna dole ina bukatar nasan haka har lokacin aunty tana kallonsu har sanda maryama
ta nufi kofar shiga bangaren umma shi kuma habib ya nufi get din gidan da alamun fita zai yi ta saki labulen tana sauke naunayen ajiyar zuciya ta koma ta zauna cikin zullumi tana tuno rayuwarta ta baya "
Maryama bata iske umma a falo ba dan haka ta samu waje ta zauna akan d'aya daga cikin kujerun falon ta runtse idanunta tana tunani "anya ba wani mummunar abu mahaifiyata ta shuka ba wanda yasa yan'uwanta suka gujeta ita kuma take jin tsoron komawa garesu ba ?"anya ma yan'uwanta su suka d'aura aurenta da mahaifinmu ? anya ma akwai gasky a zamanta da mahaifinmu ? "wad'an nan tambayoyin tayita jerowa kanta wanda bata da mai bata amsa sai mahaifiyarta ko umma ."
shiru ta sake yi tana qoqarin kawar da zarginta akan iyayenta bata san shigowar umma ba sai dai taji an girgizata sannan tayi sauri ta juyo cikin tsoro taga tana kallonta tace "maryama mai kike tunani haka ?na shiga uku ni aseeya kar dai abinda ya faru Kika zauna kina tunani ?" nan da nan ta soma girgiza mata kai alamun "a'a! tana in in nah "amm uhm Allah umma bashi bane ."umma ta girgiza ka fadanta cikin sanyin murya "kin kuwa san lokacin dana dauka ina miki magana baki sani ba ?na jima anan ina kallonki maryama kina tunanin abinda ya faru d'azu still maryama kai ta girgiza mata alamun" a'a!
Cike da nuna kulawa umma ta juya ta qarasa kitchen inda fridge yake ta isa ta bud'e ta dauko kwalin hollandia ta rufe fridge ta matsa kad'an inda d'an qaramin tray da glass cup's Ke kansa ta d'auki d'aya ta dawo inda take zaune ta janyo kujera gaban maryama ta zauna tana kallonta ta zuba mata hollandia ta mika mata tare da cewa "gashi ki sha dan nasan har yanzu baki sakawa cikinki komai ba ta kai cup bakinta tana kallon umma kad'an ta sha ta kawar da bakinta alamun ya isheta."
"karki sake tunanin abinda ya faru d'azu abinda ya rigada ya faru ya faru karki sakashi aranki yazo ya dameki wani ciwo yaje ya kamaki mu shiga uku dan sai nafi kowa shiga damuwa "Allah umma bashi bane wannan ai idan da sabo na rígada na saba "
"Wani kallo umma tabita dashi tare da sanyaya muryarta tace "idan bashi bane maryama sanar dani matsalarki dan bayan mahaifiyarki baki da wanda ya fini ina jinki tmkr ni na haifeki bancin ke kadai uwarki ta haifa da tuni na kwaceki gbdy daga hannunta , wannan soyayyar da nake miki yasa na janyoki jikina sosai karki ji komai sanar dani damuwarki ta fad'a tana kallonta ."
sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da yatsun hannunta kusan second goma sannan ta motsa labbanta "daman ba komai bane kawai ina son nasan inda dangin aunty suke, ko sanin labarinta "me yasa bata zuwa wajen yan'uwanta suma kuma me yasa basa zuwa wajenta?" laifin me tayi masu? " me ya faru daita tunda na taso nake ganinta cikin damuwa da raunin zuciya wanda har yasa nima nake jin haka atare dani ."?
Wani dogon ajiyar zuciya umma ta sauke cikin fargaba ta tashi zata wuce har ta juya maryama tayi saurin riko hannunta cikin nata "umma ! ta kira sunanta muryarta na rawa cak umma ta tsaya tare da juyowa fuskarta da tausayawa itama maryama mikewa tayi cikin tsananin tashi hanakali ta rusuna kasa ta daura hannuwanta a saman kafafun umma cikin raunin murya ta fara mgn Kmr zatayi kuka "umma nasan Kinsan komai daya faru da iyayena dan allah karki boye min gskyr dana sanki daita "
umma ta zare hannuta ta sake juyawa "umma Kodai mu din bata hanyar sunah aka haifemu bane ?"
Umma ta juyo da sauri tana dubanta qirjinta na dokawa da karfin gaske "maryama ta gyada mata kai kana ta cigaba da mgn "duk yadda muke da aunty duk shakuwarmu da soyyyar da take nuna mana ta kasa fad'a mana haka kema gashi umma zaki wuce ki barni byn kece kika bukaci kisan damuwata .
"Nasan kinsan komai daya faru ki fada min mu san matsayinmu wata killa ma shine dalilin da yasa muke ganin tasko acikin gidan nan dan girman allah umma karki boye min abinda yafi komai mahimmanci arayuwarmu ki fad'a min na rabu da nauyin dake daskare da qirjina ta qarasa mgnr cike da sheshekar kuka ."
Girgiza kai umma ta shiga yi ta dawo inda take tsaye ta kamota ta zaunar daita akan kujera tana kallonta cike da tausayawa kusan mintuna ashirin sannna ta numfasa tana cewa "ku din ba shegu bane ku din yan halak ne" naunayen ajiyar zuciya maryama ta sauke tana kamo hannu umma cikin nata "kinsan kowani d'an adam da yadda yake kar'bar gaddararsa . wasu mutane basa gane rayuwa duk yadda allah ya rubutawa bawa babu wanda ya isa ya canza maka ita,ita qaddara kuma tana fadawa bawa daidai da yadda allah ya hukunto masa qaddara bata san talaka ba bata san mai kudi ba ,qaddara ce da rabonku ta nisanta mahaifiyarku da yan'uwanta yan'uwanta sun kasa kar'ban qaddarar data fad'a mata amatsayin su na muslimai amman mgn ta gsky ku din yan halak ne sai dai akwai yan'uwanki da'aka samesu bata hanyar aure ba .."
nan take jikin maryama ya kama rawa tmkr mazari ta tsaya tana kallonta tana assessing maganarta umma ta damke mata hannu gam cikin nata tana kallonta tana jin yadda jikinta Ke rawa tamkr mazari , maryama tayi imani bancin a zaune take da ta tabbatarwa kanta kafafuwanta bazasu iya d'aukar ba, da zuwa yanzu ta zube kasa."cikin kyarrrma wasu hawaye masu zafi suka shiga turereniyar zubo mata tana jin wani zafi a qirjinta mara misaltuwa cikin ikon allah allah ya bata ikon furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shi tayita furtawa tana maimaitawa still jikinta da zuciyarta na rawa ."
Umma ta kalleta cikin sarewa ta cigaba da magana "wannan qaddara ce maryama km kowani bawa da tashi irin kalar qaddarar bata wuce Kan kowa ba , ki godewa allah da yasa ta hanyar aure aka sameku bilkisu na bani tausayi matuka kullum idan na kalleta sai na zubar mata da hawaye , da gatanta da komai tana rayuwa tmkr bata da kowa ,tana rayuwa cikin kaskanci alhalin bata cancanci haka ba tunda taji an samu wasu babu aure taji komai ya tsaya mata cak hatta shi karan kanshi labarin taji ya fita kanta ."
Mahaifiyarki haifaffiyar wannan gari ce anan aka haifeta aka haifi iyayenta ke hatta kakaninta ana aka haifesu sune asalin yan kasa "Idan mutun ya shigo jahar lagos din nan ya tmbyi family's din alhj rafi'u giwa to babu wanda bai san mahaifinta ba ."mahaifinta ko nace dangin mahaifiyarki gbdy masu arziki ne ."mahaifinta alhj rafi'u giwa yana da mata hud'u kinga kenan suna da yan uba a qalla guda talatin sai dai bazan iya kawo miki sunansu ba ina dai jin Aisha , hauwa wacce suke kira da jiddah abakinta gbdy a gidansu bilkisu ce auta a mata sai kannenta biyu maza dake binta daga kanta mahaifiyarta bata sake haihuwar mace ba haka ma sauran bangaren matan sun daina haihuwa wanda hakan yayi sanadiyar da soyayya mai karfi ya shiga tsakaninta da mahaifinta da yan'uwanta gbdy kowa yana sonta kasancewarta auta a mata "
gabadaya yan'uwan bilkisu masu kudi suka aura daga wanda yake london sai wanda yake Canadá ko American ,mafi yawa daga cikin yan'uwanta suna wata kasa daga maza har mata idan kuma anan ne zaki iske su cikin VI ita kadai ce ta auri talaka marashi ,dan gbdy asalin mahaifinki talakawa ne idan aka cire abban sadam wanda yake da d'an rufin asiri dan yana da gidan bread da kowa ya dogara dashi amman basu da komai ."
"bilkisu ta taso cikin gata da soyayya da kulawar iyaye tun daga tasowarta har zuwa girmanta duk abinda take so shi takeyi ta taso cikin soyayyar iyaye dana yan'uwa kowa yana sonta sannan ta taso da farinjin samari acikin family's dinsu kasancewarta kyakkyawa hasalima kyawun jikinta kika d'auko fuskarki ce ta mahaifinki amman km shi din ma baki dauko farinsa ba dan shi fari ne sol tmkr bature kmr yadda kike ganinsa a hoto ." kowa na sonta da nuna mata soyayya ,acikin masoyanta akwai mubarak dake mutuwar sonta, mubarak cousing dinta ne da ubansa da uwarta uwa daya uba daya kuma shima mahaifinsa mai kudin gaske ne km shi kadai suka haifa ,bilkisu na da shekara shabiyar a duniya alokacin tana ss 1 a secondary school alokacin mahaifiyarta da mahaifin mubarak sukai alkwarin aure a tsakanin yaransu dan mubarak din zai yi tafiya zuwa american qaro karatu , sun bar mgnr atsakaninsu idan ta gama karatunta na secondary sai ayi musu aure ."
mahaifinki ussein adam shima asalin haifaffen garin nan ne haka iyayensa sun kasance su takwas ne a wajen iyayensu mata hud'u maza hud'u umar ,fatima ,gali saadatu ,nazifi fadeela Kmr yadda kikasani , hassana da ussein ne auta ."
yana da shekara ashirin da takwas a duniya ya fara aiki a gidansu bilkisu ta sanadiyyar abokin abban sadam abdulwahab wanda shi gadi yake a makotansu ." mahaifinki ussein ya kasance direban ne gidansu bilkisu wanda Ke kaita school , idan lokacin tashi yayi ya koma ya d'aukota duk inda zata shike kaita hussein ya kasance mutun ne mai tsananin kirki gashi kyakkyawa aji farko illarsa dai shi din ya kasance talaka ne mai son jin dadi arayuwarsa km yana harka da yammata da shaye shaye sai dai bai ta'ba barin gidansu bilkisu sun san da zaman wannan halin nashi ba a boye yake yi saboda tsira da aikinsa ."
Maryama ta runtse idanunta tana jin wani tuttukin bakinciki a zuciyarta. ta d'aura kanta akan cinyar umma ko zata samu sausaucin zugin da zuciyarta take ,dan tun baaje koina ba ta fara datasanin jin labarin iyayenta , mahaifinta manemin mata ne ga shaye shaye a iyan nan ma kad'ai ta raina kanta ta sake yarda su din marasa gata ne ."
" tun farkon ganin bilkisu da ussein taji ya burgeta daman shi Allah yayi masa farinjin mata dan atarihinsa bai ta'ba cewa yana son mace ba dan har prouding yake , wannan yasa ya qara samun kusanci daita sosai , duk abinda taci sai ta rage masa idan zai kaita school ta bashi tun abun yana bashi mamaki har yazo ya daina bashi mamaki ya ajiye abun amatsayin ita din mai alkhairi ce , shima kma yana kulawa daita sosai dan hatta murfin mota kafin ta fito ya fito ya bude mata sannan idan sun iske an gama assembly zai tabbatar da ta shiga class akan idanunshi sannan zai juya ya koma gida ,ga iya bada labari, ussein ya iya bada labarin da zai saka mutun nishadi amman fa ga wanda yake da mahimanci a wajensa duk wannan yana cikin abinda yasa bilkisu ta sake sakewa dashi , shiyasa kullum bata da magana sai na fadar kirkinsa a wajen iyayenta wanda har hakan yasa iyayenta suke son batunsa tana sa ayi masa alkhairi na mussaman kullum da irin kyautar da take sa ayi masa ."
haka rayuwa tai ta tafiya mubarak na kiranta a waya amman sam bata bashi lokacinta yayinda wata irin shakuwa mai karfin gaske ta shiga tsakanin ussein da bilkisu lokacin da