Showing 99001 words to 102000 words out of 168608 words
habib Ke mata fatan alkhairi idan wani abun farinciki ya sameta tace "na gode sosai yaya ."
Habib yace "a she dai yaya ka gane shiyasa sai na zaba mata na durje mata miji dan ita din ba kalar kowani nmj bace "kaga yaya karka kulashi mu je ciki mu qara gaisawa "wucewa sadam yayi side d'in Ummah maryama da habib na biye da shi sunata hiran duniya..."
Zama sukayi a parlour'n sadam ya fara kiran "Ummah Kina ciki ne? Eh! Ganin nan zuwa dan albarka har ka dawo ne? sadam yace" eh ! gashi na kawo miki maryamarki "ban gane ka kawo min maryama ba maryama da muke yini tare dan gulma zakace ka kawo min ita Bari dai nazo ganin nan fitowa ."
Bata wani bata lokaci ba ta fito cikin doguwar riga qaton tray ta aje a gaban sadam na fruits bismillah sannu da zuwa yau har da habib to duk sannuku "Ina yini "Habib yace " lafiya lau habib Ummah ta kalli sadam ta kalli maryama sai taga sun maseefar dacewa ina ma su kasance maaurata suna hirarsu gwanin ban shaaawa habib ya fahimci maryama kunyar sadam take ji sosai dan taki fad'ar abinda ya kawo su gashi shi yunwa yake ji ."
Maryama tace after dad ya kamata mu wuce dare nayi "a'a har zaku tafi kenan maryama to ai bakuci komai ba "karki damu Ummah "ban gane karta damu ba kinga nifa banason kunyar nan take wai ma wa Kike jin kunya anan umma ko yaya sadam ,?maryama tayi shiru tana mai sunkuyar da kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta "kinga Ummah nan ya fad'a mata abinda ya kawosu "kai maryama amman shine zaki jashi ku wuce to kuci me idan kun wuce? allah ya kyauta wannan kunyar taki kaga habib bari nazo ta fad'a tana mikewa tsaye ta nufi kitchen ".
Bata wani bata lokaci ba ta dawo hannunta d'auke da wani madaidaicin kula cike da abinci sannan da wata leda cike da su cincin wanda tayiwa sadam ta miqa ma maryama tace gashi kai km habib ka rike kula " mungode Ummah !Suka fito maryama nayi masa mitar abinda yayi dariya kawai yayi yana cewa "ina ganin gara kawai ayi yar gida mu huta da samari masu mana patrol "kai dai kasani ni nasani ko gaskiya suna tafiya suna jan juna har suka qaraso falonsu habib ya zauna yana kiran "washhhh allah maryama ta cire hijab dinta ta ajiye akan kujera tace "habib bari na kira aunty kanshi kawai ya gyada mata ."
Ahankali ta shiga d'akin sai dai abinda yayi matukar daga mata hankali shine ganin mahaifiyarta kwance rigingine akan katifa hannunta rike da wani hoto tana kallon hoton hawaye na zuba daga idanunta tana tuna irin rayuwar dadin da tayi ada kafin shigowar ussein rayuwarta ,bata haskowa kanta irin rayuwar da take ba sai data hadu da ussein soyayyarta ta gurba tunaninta ."
yayinda maryama ke kallon mahaifiyarta da ita kadai ta rage mata a duniya yanzu a natse ta qara taku biyu domin son ganin hoton waye a hannunta take kallo tana kuka wasu mutane tagani guda biyu cikin shiga na alfarma suna cikin koshin lafiya da farinciki ko baa fada mata ba tasan hoton iyayenta take kallo cike da nadama lumshe idanunta tayi "iyaye ba abun wasa bane , aunty iyaye suna da kimar da darajan da bazaa iya mantasu ba ."
ahankali taji sautin muryarta tana fita cikin kuka "nayi kewarka baba , nayi kewarki mamana yanzu ku har yanzu bakuyi kewata ba ?yanzu ku baku yafe min ba ko nemeni ba? wallahi ina sonku nayi kewarku ,nayi kewar kowa da kowa ta fad'a tana mai daura hoto a saman qirjinta tana shafawa tana kuka.."
Ahankali maryama ta juya tana zubar da hawaye masu zafi ta koma falo ta zauna kusa da habib tana sheshekan kuka nan take ya birkice ya soma tambayarta "heartbeat me kuma ya fara ?kukan me kike yi ? Ina aunty ?yayi mata tmbyr ajere cikin tsananin tashin hankali tasa gefen rigarta ta goge hawayen "yau aunty ta tuna da iyayenta tana daki tana kallon hotonsu tana kuka ni nasan zuciyarta na cike da qaunarsu shiyasa kaga ina son ta koma garesu ."
"habib soyayyar iyaye da yanuwa baa wasa dasu wallahi a tsakaninsu soyayya ce mai karfi ka misalta hakan akanmu musan da qaddara amman an cuci aunty an yi sanadiyyar rabata da kowa nata ,ta bar iyayenta akan soyayya gashi ta rasa soyayya taki bin umarnin iyayenta gashi duniyar taki mata dadi maryama tana kuka habib na rarrashinta har kukan nata ya ragu adaidai lokacin da sukaji tahowar aunty tayi saurin share hawayenta tana cewa ".
karka nuna mata komai da sanyi jiki ta qaraso "kun samo abinda zaku dan ci ?eh mun samu har da cinci tô maza kuci ku kwanta tayi maganr cike da rauni aunty kizo muci tare "aa ku dai kuci ku koshi aa wallahi tare zamu ci habib ya mike ya kamo hannunta ya zaunar daita ya bude kula abinci yana cewa kai abincin nan zai yi dadi maryama ta dauko spoon ta dibi abinci zata kai bakin aunty habib yayi sauri ya kwace spoon "bani ni zan bata da kaina suka sa da dariya ya soma bata abinci abaki yana fada mata kalamai masu sanyi ."
"idan nayi kudi bazan yi nesa dake ba zan kasance tare dake ,dan allah aunty ki daina damuwa akan komai kinji ki dinga tunawa cewa kina damu mu din zamu zame miki farinciki a rayuwarki Wallahi sai mun sa kinyi alfahari damu ki cigaba da addau ga heartbeat nan kwanan nan zata fara bautar qasa yanzu ma ina mata processing yadda zaa dawo daita lagos né daga adamawa wannan farinciki ya rage tarin qunar da zuciyar aunty take ciki tace "allah yayi maku albarka yayiwa rayuwarku albarka in sha allahu bazaku dangwama haka ba allah zai saukaka maku rayuwa ,Allah nake roko ya daukaka min ku na yafe maku duk abinda kuka min da wanda nasani da wanda ban sani ba suna cin abinci suna debewa juna kewa ."
******
da misalin karfe 9:00 na washegarin ranar lahadi mr ata ya fito parlour'n mami ,duk jikinsa yayi sanyi har wata katuwar rama yayi daman ya lafiyar kura ?ba wani jikin kirki bane dashi kusantowar aurensa da maryam yasashi jin kmr ana fixgar ransa ,shiru ne ya ziyarci parlour'n yana tunane tunane yana jin kamar idan ya tafi france kar ya dawo domin a lissafinsa sauran kwanaki goma cif a daura masa aure da yarinyar daya tsana fiyye da komai arayuwarsa byn kmr mintina goma mami ta qaraso da kanta ta had'o masa abun kari , chips da soyayyen kwai da ruwan tea mai kauri , ta janyo qaramin table gabansa ta ajiye kana ta zauna kusa dashi ta tsura masa ido tana kallonsa batare datace komai ba ."
ya dauki cup din tea ya kai bakinsa ya kurbi kadan yana mai runtse idanunshi shiru har wasu mintuna suka shude yana zaune itama tana zaune tana kallonsa da kyar ya bude baki "sweetheart! "kaci abinci first before anything adamcy , sannan kar naji kayi magana kaci abinci kawai yaushe rabon ka sanyawa cikinka abinci bare a samu magani yayi aiki ajikinka ? ji yadda ka dawo acikin kwanaki uku kacal ka taimakeni kaci wani abu kanshi kawai ya iya d'aga mata batare da ya kalli inda abinci yake ba, saboda sam baya jin cikinsa zai iya amsar komai shima da zata taimakesa da tasa an fasa auren nan da yarinyar an hadashi da wata zai hakura da princess dinsa ya amshi koma wacece duk da zuciyarsa princess kawai take so da son gani numfashi ya dinga saukewa ."sweetheart dina me yasa kika manna min wannan auren haka?
" sweetheart zaki kasheni da kanki wallahi at least ki sake gara min dama koda na tsawon wata guda ne ."
"to me zan maka adamcy nah daya wuce haka ?
"me kake son nayi idan banyi maka haka ba ?
gani nayi kana neman hargitsa min kwakwaluwa da qarar da rayuwarka a banza "me kake tunani mutane zasu ce idan bakayi aure adaidai wannan lokacin ba ? wallahi zaka shiga zargin mutane ,mutun har mutun kamamme kamar ka ka zauna babu aure ko kana neman mata ne adamcy bansani ba da kake gudun aure ."
wani irin kallo yayi mata mai nuna mata bayayi "to idan bakayi me kake jira ?maryam yaruwarka ce fa "yanzu kai kafi son ka dauko min suruka daga waje alhalin ga wacce tasan darajata take sona nake sonta diyar danuwana yanzu idan an fasa auren nan me kake son na cewa mutane da yan'uwana ,dan Allah dan annabi in banda da rigima irin naka ba me ye laifin maryam ..?
"wani far yayi da idanu zuciyarsa na dokawa da numfashinsa da yayi kokarin d'aukewa yayi saurin dawowa dashi gangar jikinsa sannan yace "sweetheart ni bance tana da laifi ba amman ki duba lamarin da kyau tunda nace bana sonta ai sai a hakura kawai kowa ya kawo zabinsa . "kai rufe min baki ban son shirme banza, ka daina ganin ka had'a komai kana da kudi kayi tunani zaka iya juya ni ."Wannan aure sai anyi shi muddin ina raye ."
ya marairace muryarsa sosai tmkr mai shirin zubar da hawaye sannan yace "wai sweetheart me yasa kike ganin kmr wannan yarinyar ce kawai zata iya kulawa dake ? Allah sweetheart ki daina mata kallon haka saboda irinsu sune masu bawa dangi kunya wallahi duk lokacin da naji kince min itace zata san darajarki bakinciki nake ji kmr na kashe kaina saboda ni duk macen dana kawo miki dolenta ta soki tayi miki biyayya bama Ke ba sweetheart hatta yayyuna biyu din nan dolenta ta bisu lalacewar mace daga miji ne ni kuma bazan ta'ba bada wannan damar ba .. "
"Sauran kwanaki goma a daura maka aure da maryam a lissafina gobe ko jibi jirginka zai cale zuwa qasar france fatana allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya shahida ta gama shirya komai na aure fatan alkhairi da dawo da niyyar angeancewa lafiya and if you do anything stupidty I will del with you kai ma kasani ina sonka fiyye da tunaninka amman hakan baya hana idan kayi ba daidai ba naki hukuntaka tana qoqarin mikewa hisham ya shigo ya gaishe da mami cike da girmamawa sannan ya zauna kusa da ata daya runtse tsumammun idanunsa tun byn da mami ta soma magana "yaakayi mutumina ya karfin jikin hope you are getting better?"numfashi kawai ya sauke wanda Ke nuna masa alamun ya amsa hisham ya cigaba da magana "har yanzu sultan da fahad basu dawo da komai ba fa Kmr ma sun dauki abun matsayin shiririta tsabgogin gabansu kawai suke."
"ina sane da komai kai kasan bana canza maganata ina jiran na dawo daga france ne suna zaune suna hira mb ya shigo haka ma yaya Ibrahim ya shigo duba jikin mr ata tare da aunty abida har da yesmin wacce ta dane jikin mr ata haka ma yammatan gidan
d'aya byn daya suka dinga shigowa suna gaisheshi da kyar yake bude bakinsa yana amsa musu cikin rashin sakin fuska , cikin wasu mintuna aka cika gaban mr ata da kayan motsa baki , amman babu abinda yaci illa coffee daya dinga tsiyaya a cup yana kurba ahankali ahankali shima yana sha ne kawai saboda sabon da yayi dashi ."
Parlour'n ya dan rage mutane ya saura daga hisham sai ata nuzla da diyana har ma da mrym da nana hauwa'u suka shigo parlour'n bakinsu d'auke da sallama hisham na ganin nuzla ya saki fuskar ganin masoyi yarsa gbdy suka hada baki wajen yi ma mr ata ya jiki banda nuzla Kmr koda yaushe da kyar ya amsa masu hisham yana kallon fuskar nuzla yayinda nuzla taja ta tsaya daga gefe can ta jingina bayanta da bango ta rungume hannuwanta duka bisa kirjinta tare da tsura ma mr ata fararen idanunta tana kallonsa cike da matsanancin soyayyarsa yadda ko kallon mrym da zai aura bai yi ba abun yayi mata dadi sosai yadda bai son mrym abun na mata dadi har yana bata kwarin gwiwa dan tun daga ranar daaka saka ranar aurenau take jin haushinta sannan take cikin damuwa mai tsanani ."
ahankali ta bud'e bakinta tace "yaya sannu ya jiki banza yayi mata Kmr bai ji ba nan kuwa yaji sarai hisham yayi qasa da murya yace "ata ana maka sannu da jiki "naji !ya fad'a atakaice dan ya fahimci wani abu a attare daita ba tun yau ba yana hankalce da irin kallon da take masa a duk sanda zasu hadu tun a office din aunty shahida yaso yaci ubanta allah ya taimaketa "take gabanta ya shiga fad'uwa sbd fargaba dan ganin ko kallon inda take tsaye bai ba illa kur'ban ruwan coffee daya cigaba dayi kuma taji amsar daya bawa hisham kuma tasan sauran ma
sunji abinda ya fad'a ."
ahankali ta juya ta nufi kofar fita cikin bacin rai sannan sauran yanuwanta suka biyo bayanta "amman ai ya kamata ka amsawa gimbiyata ya sake yin mgn can qasa"gsky hisham baka da hankali km kana bani kunya yanzu kai da gaske sonta kake "?sosai ma kuwa ina sonta sai dai ita bata sona ..""what ?" Wallahi haka ta fad'a ai naso bikin a hadashi da naka amman ya zanyi tunda tace bata só na hakura amman nasan sonta ne zai kasheni "amman shine ka kyaleta baka ci ubanta ba?
aa babu wannan ai kai ma kasan yadda soyayya take ka duba yadda baka son mrym kake son yarinyar mafarkinka "ka daina kawo wannan misalin ni bana son wannan yarinyar ita ma kuma bata sona kaga akwai matsala wajen namu hadin ko ka fahimceni ."?
"Misali ina sonta to ya zama dole dan ubanta ta soni sannan misali da'ace tana sona nima bazan dinga jin tsanarta haka ba duk da nasan nawa rashin son ne babban matsala dan ita prentending ne kawai nasan babu macen da zata kalleni tace wai bata sona dama ne kawai bata samu ba ,ya fad'a yana jan tsaki ka kira min auta "me zata maka ?Kai dai kira min ita kawai yau yarinyar nan zataci ubanta da me tafika da zata ce bata sonka ?shiru hisham yayi yana kallonsa a she haka ata yake sonshi jiki a sanyaye ya dauki wayarsa ya kira nana hauwa'u cikin kankanin lokaci ta bayyana a falon "yaya gani "je kizo min da nuzla yanzu yanzu kafarta kafarki "okay yaya ta juya da sauri ."su kuma suka cigaba da tautaunawa ."
Bayan mintuna goma sai gasu sun shigo nana hauwa'u ta kama gabanta ta bar nuzla tsaye cike da fargaba ta dan saci kallon hisham dake zaune taga ya sakar mata murmushi ta kalli mr ata taga ya hade rai sai kafarsa daya yake girgizawa har kusan mintuna shabiyar tana tsaye sannan tace "yaya gani wai ..."da sauri ya dakata daita ta hanyar daga mata "waye wannan ?ya nuna mata hisham dake zaune "yaya hisham ".
"Very good meye a tsakaninku ?nothing ta bashi amsa atakaice ba hisham ba hatta mr ata sai daya dago tsumammun idanunshi ya tsura mata yana kallonta "kika ce nothing kenan baki san yana sonki ba ?nasani but na fad'a masa gaskiya ni bana son shi dan ..."enough ! bana bukatar jin maganarki ko wani abu kije ki fara shirin aurensa nan da kwanaki goma ." cikin firgici da tashin hankali ta shiga d'aga kafafunta zuwa inda yake zaune "me yasa yaya ?" dan Allah kayi hakuri karka min haka wallahi ni bana son shi a matukar tsawace yace "nace karki sake fad'ar wata magana anan , karki sake kula kowa acikin masu sonki shima wanda kike so ki kashe soyayyarsa acikin zuciyarki ki so wanda yake sonki .."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 20
jikinta na wani irin rawa ta k'araso ta durkushe a gabansa har bata san sanda ta d'aura hannuwanta duka bisa cinyoyinsa tana kallon cikin kwayar idanunsa da suka rikid'e suka canza kala a wulakance ya zame jikinsa yana mai kawar da fuskarsa gefen hisham dake zaune tmkr mutun mutumi yana kallonsu cike da matsanancin tashin hankali ,shi kuwa mr ata alamun baya son kallon fuskarta ne yasa shi maida idanunshi kan hisham ".
"dan allah dan Allah !! yaya adam kayi hakuri ta kai hanuta tana qoqarin juyo da fuskarsa gareta domin su fuskanci juna , zuciyarta na wani irin bugawa da karfin gaske take kallonsa haka ma hisham zuciyarsa ce take ta bugawa fiyye da kaida ya soma jin wani sauyi na daban a gabadaya ilahirin jikinsa wanda ke gauraye da tsantsar tashin hankali, shi kuwa mr ata mamakinta yasa gbdy ya qasa magana duk da maganar yake son yi .
Kwayar idanunta suka cicciko da ruwan hawaye muryarta a sarke tace "dan Allah yaya kayi hakuri karka bari wannan auren ya kasance domin zuciyata bazata iya d'aukar wannan nauyin ba, wata razananniyar tsawa ya buga mata wanda ya kamata ace ta tsorata ta dawo da hankalinta jikinta amman ina sai ma sake narkewa tayi a wajen zuciyarta babu tsoron komai acikinta , muryarsa a kausashe yace " tashi ki bar nan ki kuma fara shirinki kamar yadda na fad'a miki oya leave ."
"dan Allah ka saurareni yaya "ya girgiza mata kai yana cewa " I don't want to listing anything from you just leave now "dan allah yaya adam kayi hakuri ka saurareni akwai maganar da idan na fad'a maka nasan zaka fahimceni "ata dan Allah ka barta ta fad'i abinda ke zuciyarta Hisham yayi maganar yana qarewa jikin nuzla dake rawa tmkr mazari da kallo , yadda take