Showing 168001 words to 168608 words out of 168608 words

Chapter 57 - Mar'adam's Book 1 Hausa Novel Complete

ta sunkuyar da kanta kawai tana jinsa tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ita yanzu bata jin mlm yahuza acikin ranta tunda tagansa da shukura har abada babu ita babu shi ko mutuwa zaiyi akanta wallahi bazata auresa ba sannan wannan magana ce kawai baba gali yake batun soyayya tsakanin mlm yahuza da shukura sunyi kawai dai anje an warware aiki ne komai dake faruwa da sanin aunty salma ita Ke shirya komai ."

Sarai baba gali ya karanceta dan hk muryar a fusace ya cigaba da mgn "tunda naga kamar kin kamu da soyayyar yusin din allah ya baku zaman lafiya da yusif ita kuma shukura ko sakina allah ya kawo masu nasu rabon "uhm kawai ta furta dan tasan ya fad'a haka ne ba har acikin ranshi ba ,ta dago ta girgiza kai cikin takaici irin rayuwarsu "ni baba bana ja da maganarka a yau ida ka shirya aura da kowacce daga cikinsu ga yusif kayi ." ya sauke ajiyar zuciya yana cewa tô shikenan na gode na tabbatar daman bazaki aikata abinda zai jawo min zagi ba su yusif din zasu zo karshen satin nan dan mun gama magana da mahaifinsa cewar shukura zai aura shima yusif din ya amince da hakan dan haka ko yau mlm yahuza ya kiraki ki amshesa kije ."


Nan taji gabanta ya fadi jin wai abba ya amince da kuma amincewar yusif daman yusif ba soyayyar gsky yake mata ba tabbas duk maza mayaudara ne babu nmj dan goyo kalamansu daya haka salon yausararsu daya haka ta mike tsaye jiki babu kwari ga lokacinta daya bata mata ga bakinciki daya kunsa mata abun yayi mata yawa ,bakinta na rawa tace "baba Allah ya tabbatar da alkhairi sai dai ka fadawa mlm yahuza ya nemi matarsa a gaba dan ni a halin yanzu gbdy babu mgnr aure a gabana bazan yi aure ba har karshen rayuwata tana gama fadar haka ta soma daga kafafunta bayanta yabi da kallo yana kwabe baki alamun matsalarta."

Yau sunyi very busy a wajen aiki dan daga maakatarsu kwasasur akayi zuwa ma'aikatan man petir  dake apapa saboda kwarewar wasu daga cikinsu ranar haka tayi aiki cikin sanyin jiki da wahala ita ba soyayyar yusif bace damuwarta tunda daman bata fara son shi ba mamakin baba gali ne ya addabeta tmbyr duniya subai'a tayi mata tace babu komai ."bayan an tashi daga aiki ta fito bakin get ta tsaya tana jiran fitowar subai'a su wuce gida ,ta tura hannunta cikin jakarta zata ciro nikaf dinta adaidai lokacin wata mota reven rover ta sanyo kai zata shiga cikin ma'aikatan ,gani tayi motar taja ta tsaya motar bata shiga ciki ba haka zalika bata juya ba mutumin dake zaune a bayan motar taga ya fito jikinsa sanye da suit bakake."


da wani irin sauri ta dan matsa gefe ,shi kuwa fuskarta yake kallo daga inda yake tsaye cike da faduwar gaba tabbas wannan fuskar idan ba mafarki yake ba fuskar da mai gidansa yake gani ce acikin duniyar mafarkinsa ."duk da fuskar zane ce  ,amman ya rantse da wanda ke busa masa numfashi itace wace zuciyar mai gidansa take muradi kasancewa tare daita, gbdy idanunwansa sun rufe akanta baya ganin tarin jama'ar dake gurin burinsa ya isa gareta tana qoqarin sanya nikaf taji ya rike mata hannu jikinsa na wani irin kirrrma kafin tayi wani abu taga ya janyo hannunta da sauri zuwa cikin ma'aikatan qoqarin fixge hannunta take cikin tsananin tashin hankali amman yaki sakar mata hannu ."

Ana zan dataka sai a book 2 in sha allahu wadan da suke bibiyarmu a arewabooks inshaallahu zasu cigaba da ganin update dinmu kmar yadd muka saba ."
Alhamdulillah


Mmn sudais

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login