Showing 9001 words to 12000 words out of 168608 words

Chapter 4 - Mar'adam's Book 1 Hausa Novel Complete

ta sake yunkurin sake yi masa magana ganin bakinsa bai motsi " uhm daman zan wuce ne ma nace mu gai..." bata kai ga qarasa abinda zata fad'a ba cak taga ya dauki yesmin ya sabata a kafad'arsa ya haura samansa a hankali ta juyo tana duban bayansa Yadda yake tafiya ma kawai duniya ne gabadayansa shi din mafarkin kowace mace dake numfashi a duniya ne shiyasa duk runtsi duk wuya sai burinsu ya cika akansa ."

Yesmin ta sakar wa mamanta murmushi tare dago mata hannu tana mata bye bye "abida Kiyi hakuri dan allah nasan Kinsan halin danuwanki ba tun yau ba "no mami ki daina bani hakuri ai idan da sabo na saba da halinsa ya zanyi  da  halin danuwana ?ni gabadaya abubuwansa basa damuna burgeni ma yake ."Masha allah haka ake so duk wani mutumin kirki ya kasance allah ya qara mana hakuri da zaman lafiya da junanmu "Ameen ta amsa ta juya ta fice daga part din hjy zulai ."


"Adam na bani matukar kunya mami ta fad'a a matukar fusace adaidai lokacin da mrym da nana hauwa'u suka dawo parlour'n sosai suna tmbyr ta "kunya kuma mami ?eh mana ku duba kuga yadda abida ta damu da shi amman shi bashi da abun wulakantawa kamarta ,ni na lura ma duk yafi tsanar ta akan kowa acikin family's din nan amman dan iskanci ya iya dauke mata diya ya wuce daita sama ." ta fad'a cike da takaici.
"ta nan bangaren ya Adam fa yana da gaskiya itama banda abunta taya tana matar aure zata dinga wani shishige masa ".?"Uhm auta ai ita ba da wata manufa take yin haka ba tana yi saboda yanuwantaka ne "kai mami kefa bakya fahimta ,wallahi munafuci ce da bakinciki ne taf acikin zuciyar wannan matar da kike kallo amman kin kasa ganewa yanzu da kin qare mata kallo murmushin yake tayi, waya san abinda ke zuciyarta "babu komai sai alkhairi ku dinga yiwa mutane fatan alkhairi ".

*******
Bayan kamar awa biyu da wasu mintuna ya fito sanye cikin wasu kananan kaya riga Orenge da white jeans kana ganin shigar kasan fita zai yi ,lokacin parlour'n Hjy Zulai ya soma cika da kawayen su maryam da yan'uwa sai dai parlour'n babu wani hayaniya a hankali suke komai sanin boss na gida da zarar zasu daga murya, sai maryam ta tsaidasu suna ganinsa kowannensu ya shiga hankalinsa tamkar basa da numfashi ."
yaja tsaki yana janye jikinsa dan kar jikinsa ya ta'ba na wata acikinsu ,ya nufi kofar fita nana hauwa'u da mrym suka hada ido tare da dagawa juna gira alamun jin dadi "nuzla tayi tsalle" yeeee ya Adam ya fita zamu sakata mu wala "tayi mgnr tmkr wata qaramar yarinya "ke dai bari nuzla wallahi tun dazu a firgice muke nida maryam ,wallahi gbdy bama cikin natsuwar mu tun dazu addua nake acikin zuciyata allah ya kawo dalilin da zaisa ya fita ya bar gidan gbdy ko ma sakata mu wala sai gashi allah ya amsa adduata, gashi ma ya fito ya ganmu dayawa bai ce komai ba wallahi baqaramin dadi naji ba inji cewar nana hauwa'u ."


Maryam tai juyi cikin doguwar rigar dake sanye ajikinta sannan ta tsaida kananun danunta akan nana hauwa'u "sister wannan yayan naki mai sufar zaki akwai shi da mugun iyayin tsiya sai dai fa yayi kyau sosai exactly irin mijin da nake muradin aure kenan amman samun irinsu da matukar wahala ,
Ina ma zan samu yadda yayi kyau din nan ace Ana's ne da yau mu dauki hotuna masu yawa mu daura a social media nasan da ba qaramin comments da like's zan samu ba." tunda ta fara magana ya dawo bata sani ba yana tsaye a bakin kofa sai faman zuba take "burin kowace mace a duniya ta samu miji kamarsa amman samun irinsu da wahala amman babu komai mayi hidima wa Allah mu samu a aljanna idan muna da rabo "
"Kun san wani abu dake bani driya dashi ? duk sukai shiru babu wacce tayi tari "abu kadan zai hade fuska ya kalli mutun ya disga mutun da kalmar nonsense , crazy girl " ta fad'a tana karairaya cak ta tsaya tana duban wadan da ke tsaye a gabanta ga mamakinta taga dukkaninsu babu wanda yayi dry Kmr yadda suka saba a duk sanda wani yayi irin maganarsa ."


a hankali ta juya bayanta cike da tsananin faduwar gaba aiko idanunta suka sauka akanshi yana mata wani irin kallo mai dauke da yawon tsanar da yayi mata ,da sauri ta zaro idanuwa waje tana kallonsa kmr a mafarki, ta lumshe idanunta na second daya ta bude taga dai tabbas shi din ne tsaye agabanta ,ta dan juya bayanta tana kallonsu Kmr zatai kuka."
Gbdy jikinta ya kama rawa a hankali ta sakê juyowa ta fuskancesa ta hade hannuwanta duka wuri daya tare da yin kasa har ta kai kasa muryarta na rawa "am very very so.." sorry " .
shiru yayi yana qare mata kallo tsab sanye take ckin doguwar rigar wanda hannunta daya long sleeve ne dayan kuma hamless gabday an canza mata kamani ta hanyar yi mata make up ga gashin kai tayi fix ya sauko har gadon bayanta abinda yafi tsana kenan daga mace too much of kwaliya da qarin gashi da farce ita kuma duk ta kware wurin yinsu "ita fa a ganinta tayi kyau da wannan shigar da kwaliyar da tai ?ya tmbayi kansa yana jan tsaki dan a idanunshi muni tayi masa barin ma rashin tsawon da Allah yayi mata ,shi kam yayi imani banci farin fatan da allah yayi mata da babu shegen nmj da zata dauki hankalinsa har ma ya tsaya bata lokacinsa wajen haukan shirme akanta ".


"kusan second goma ya dauka yana kallonta yana hukuntata da idanunshi kafin daga baya ya bude bakinsa Kmr baya son yin mgn " maid your business duk abinda zaki yi karki sake kuskure ambaton sunana cikin shirmenki me nace ? ya fad'a yana zaro mata ido "Kar...kar !! na sake ambaton sunanka kayi hakuri wannan ma kusku.....you're very stupid dake da kuskuren , daman kin saba this is not your first time koni sa,an wasanki ne ? da sauri ta girgiza masa kai ya gyara tsayuwarsa " ki dinga abu kamar wata mental sam sam baki da natsuwa crazy girl kawai ki godewa allah akwai abinda zanyi mai mahimanci dana tsaya naci ubanki guntuwar banza kawai ." ya fad'a yana sa kai ya hau sama ta sauke wani naunayen ajiyar zuciya aranta tace "oh my god you save me for the first time ,byn kmr second biyar ya sauko ya fice gbdy daga gidan .

Bayan fitarsa cikin bacin rai tace "ko kun tayani jin abinda ya fad'a? suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya "wai kece mental crazy girl mara natsuwa a karshe wai guntuwar banza wallahi ni duk shi yafi bani dariya wai guntuwar banza cewar nuzla ta fad'a tana tafa hannu tana dariya "see me see trouble shi fa idan ba zagi ba babu abinda ya iya arayuwarsa dan wulakanci ma har da zagin halittar Allah cewar diyana "kunga karku qara mata bakinciki byn kunsan yau ranar farinciki ne gareta nana hauwa'u tayi mgnr tana mikar da maryam tsaye dan tunda ta durkushe kasa bata iya ta mike ba tsabar tsoro ."
Byn ta mike tsaye bisa kafafunta ta kallesu daya byn daya tana maka masu harara mai kunshe da bakinciki "gsky gbdy baku kyauta min ba, kuka barni ina ta faman zuba aka rasa wanda zai min alamar nayi shiru acikinku daman burinku yaci min mutunci kuyi dariya ko? Kema idan zakiyi magana next time ki dinga kallon kofar shigowa ba baya zaki bawa kofa ba in case inji cewar nuzla ,asra tace "au ke nan yanzu haushi kika ji da ba ki godewa allah ba kamar yadda yace dan da yanzu ba wannan labarin kike ba "na so oooo I thank god for saving me."

Bayan wani lokaci gidan mami ya cika da ya'yanta da jikokinta da wasu daga cikin jama'ar estate din parlour'n ya hargitse da hayaniyar mutane anci an sha anyi rawa hanan ta yanka cake haka ma maryam tare da daukar hotuna da vedios mutun biyu ne kawai acikin yammatan family's da basa cikin hotunan marigayiya mubina da sultana wacce Ke matakin karshe a jamiar cairo ."

su maryam abun nema ya samu domin kuwa duk hotuna da sukai babu bata lokaci take daurawa a social media "nuzla ta samu wuri ta zauna shiru idanunta na cikowa da ruwan hawaye sakamakon tuno marigayiya mubina ,maryam ce ta lura da yanayinta ya sauya dan haka ta qaraso gareta ta zauna akan hannun kujerar da take zaune tana tmbyrta "Lafiya nuzla kika zauna shiru haka ?numfashi ta sauke tana  furta sunan "mubina...!" tun kafin ta rufe baki sai hawaye sharrr sharr!! sun zubo Kan kuncinta dan haka ta kasa qarasa maganarta , maryam ta tsuke baki tana riko hannunta cikin nata " nuzla ki daina kuka haka addua ya kamata kiyi mata alokacin da kika tunota ,wallahi koni sai data fado min arai kuma nasan gabadayanmu babu wanda bai tunata ba domin mubina ta shiga ranmu fiyye da komai ta fad'a tana goge mata hawaye "ki bar kuka haka kada sauran su fahimta kisa hankalinsu ya tashi ,wanda ya mutu babu abinda yafi bukata kamar addua kuma muna mata babu ranar da zatazo ta wuce banyiwa mubina addua ba allah ya jaddada rahma gareta ta fad'a tana mikar da nuzla tsaye suka shigo cikin sauran yan'uwa nuzla kam baa qarasa gudanar da birthday party daita ba ta wuce ."


******
Byn wata shida

Sanye yake cikin kananun kaya jeans da riga t shirt tsadaddu product din American yana tsaye a haraban katanfarin estate dinsu tare da hisham hannuwansa duka zube cikin aljihun wandonsa , kallo daya zaka masa ka fahimci ransa a 'bace yake dan fuskar nan tashi babu alamun rahma sakamakon abinda ke dawainiyya da rayuwarsa , uwa Uba sweetheart dinsa dake sake hargitsa masa lissafi da batun auren data bijiro masa da yarinyar daya tsani gani a rayuwarsa dan idan yana qaunar mutuwarsa to yana qaunar yarinyar ."Suna nan tsaye hisham nayi masa magana akan sakonnin daya samu akan kasuwancinsu amman shi sam hankalinsa da natsuwar basa garesa , yana nazarin yadda rayuwa ke tangaliliya dashi da Inda zai ajiye akalar rayuwarsa, da rayuwar da mahaifiyarsa da yan'uwansa suke son yayi a yanzu ."
a hankali hisham ya matsa kadan daga gefensa domin amsa kira dan yasan halinsa baya son qarar waya , ringing din wayar hisham daya fara ne ya dawo dashi haiyacinsa ya fesar da iska mai zafi daga bakinsa tare da kai Kyawawan idanunshi saitin gidansu ,maryam da muhd bello babban amininsa ya gani suna 'kokarin fitowa daga cikin gidansu wani irin mugun haushi ya kamashi zuciyarsa ta dinga zafi da tuttukin bakinciki bangaren maryam ganin in da yake tsaye suka nufa yasa bugawar da qirjinta yake ya qaru fiyye da kaida ."


Mmm sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page

*AYSHA A BAGUDO*
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page3

......da wani irin sauri mr ATA yayi saurin d'auke kwayar idanunshi akansu yana juya baya tare da jin wani zafi mai tattare da bakin ciki, gabadaya ya rasa me Ke masa dadi arayuwarsa a halin yanzu babu fuskar daya tsani gani kamar fuskarta ."daga Inda maryam take bata sake yunkurin qara taku daya ba ta cigaba da tsayuwa a waje daya qirjinta na bugawa da matsanancin karfin gaske sbd tsananin tsoronsa ."wannan dalili yasa dole shima muhd bello ya tsaya anan suka qarasa maganarsu ta juya da sauri ta koma ciki ranta duk babu dadi kallonta nana hauwa'u tayi tace " ba dai har kin dawo ba ? ta fad'a haka ne sanin da tayi duk lokacin da suka ke'be da ya muhd bello suna daukar lokaci suna tautaunawa dan jininsu ya had'u sosai dashi ."


maryam bata ce mata uffan ba tsabar bakinciki dake kunshe acikin zuciyarta nana hauwa'u ta cigaba da magana tana dubanta a tsanake "halan ya adam na waje ne naga kin shigo fuskarki wani iri ? ta'be lip's dinta tayi tana cewa " ai kema kinsani idan ba ganinsa ba me zai sa fuskata tayi haka ta sauke naunayen ajiyar zuciya " sister na rasa dalilin wannan tsana da ya adam yayi min ,wannan abu na matukar ci min rai ina jin kamar na tattara na bar gidan nan na huta da ganin irin kallon tsanar da yake min kamar ni kadai ce acikin gidan nan ? " tsana kamar ya kashe ni."


"haba haba !! sister dan me zaki fadi haka?" ai ba ke kadai yakewa haka ba , ki daukeni misali ma kawai ya isa ki kwantar da hankalinki , ba ke kadai ya adam yakewa haka ba shifa tsanarsa kowa yake wa "maryam ta sake tabe lip's dinta "kowa yake wa amman wallahi nawa yafi na kowa nifa ko kallona baya qaunar yayi na rasa me na tsare masa arayuwa kamar fa ya kasheni haka nake gani acikin kwayar idanunshi nana hauwa'u tai murmushi kawai "kisan ma abinda ya qara kona min rai ne ?nana hauwa ta girgiza mata kai "alamun a'a " wai yana hangomu nida ya muhd bello mutumin nan ya juya mana baya da sauri kamar yaga wani mugun abu ,wallahi bakiji yadda na muzanta ba gabadaya kasa cigaba da tafiya nayi " nana hauwa'u ta kamota zuwa Kan kujerar da take zaune ta zaunar daita tana murmushi a hankali ta shiga kwantar mata da hankali tana kawo mata misalai iri iri dan bata son abinda zai sa maryam ta bar gidan dan ko babu komai abubuwanta na social media na sakata nishadi shiru kawai maryam tayi tana sauraronta ."


muhd bello ya k'araso Inda Mr ATA yake tsaye ya Kai hannunsa d'aya ya dafa kafad'arsa ya juyo dashi a hankali ya tsura masa idanunshi fuskarsa kwance da murnushi yace "why ATA ? "me yasa kake quntatawa rayuwarka ?"me maryam ta rasa ? "me yasa bazaka bi zabin mahaifiyarka da yan'uwanka ba ? ya lumshe lumtsatsun idanunshi yana furzar da iska me zafi daga bakinsa "kasan komai akaina m.b tun daga farkon rayuwata har zuwa yanzu da nake tsaye a gabanka babu abinda baka sani ba ..."
Na sani ATA ! ya fad'a yana sake matsoshi sosai " Amman at least ka duba lamarin mahaifiyarka da yan'uwanka sun dauki tsawon lokaci da baka dama amman shiru babu wani bayani amman yanzu tunda suna sonka da maryam ka amince masu ka sota ."

shiru mr ATA yayi yana masa wani irin kallon up and down "ka amince masu ka sota " kwalkwa
luwarsa ta maimaita masa abinda ya fad'a yanzu kafin a hankali ya kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa da yaji bugawarsa yana qaruwa sakamakon furucin muhd bello ,bai an kara ba yaji sautin muryar muhd bello ya cigaba da magana " itama maryam din bata san da maganar ba a yanayin yadda mami ke maganar zaka fahimci hukuncinta ne ta yanke akanka kuma ina da tabbacin ko tasani bazata ki ba, biyyawa kawai zatayi ta aureka koda ranta bai so "shawarata ka amince da aurenta yarinyar nan tana da natsuwa da hankali sosai bazata baka matsala ba ,sannan tana da ilimi tana da kirki daidai nata uwa Uba jininku daya daita abinda yayi ka shi yayita, shi abinda kake gani acikin rayuwarka ba lallai ya zamo gaskiya ba dan ba kowani mafar......"

"Stop!
"Mb don't don't !! talk anything rubbish okay ya fada a fusace yana sake fuskantarshi sosai ya rungume duka hannuwansa a faffadan qirjinsa ido cikin Ido suke kallon juna tmkr ranar suka fara ganin juna zuciyar mr ATA na wani irin tuttukin bakinciki da zafi muryarsa a zafafe ya cigaba da magana "ko kai ne Allah da zaka fad'a min haka ?" well I don't care about all what you said dan nasan da Allah na dogara ba da kai ba kuma nayi Imani bazai wuftar da lamarina ba zai cika min burina."

"Na sani Allah ba zai wuftar da lamarinka ba amman dole sai kabi umarnin mahaifiyarka tukun allah zai duba lamarinka domin Allah ( swa) yace waqada rabuka alla tahbudu ila iyahu wabil walidaini ihsan sannan manzon allah (saw )sai daya ambaci abi uwa har sau uku kafin uba kaga tunda har kasan allah keyin komai to ya kamata kasa aranka kamar anyi wannan auren an gama da izinin Allah har ma na fara tsinkayo sautin muryoyinku cikin farinciki kai har ma ka durka mata ciki yan shida tana takawa da kyar kana rike da jakarta kana mata sannu ya karasa maganar cike da zolaya yana murnushin mugunta tare da dukan kafad'arsa wanda hakan yasa mr ATA sake d'aure fuskarsa sosai yana zabga masa katuwar harara ."

suna cikin wannan halin hisham dake tsaye gefensu yana waya ya gama ya tura wayarsa cikin aljihunsa ya qaraso yana mikawa muhd bello hannu shima ya mika masa nasa hannun yana cewa tun dazu nake allah allah ka gama wayar kazo mu taru mu taya mami yakin karshe "akan wa kenan ?"akan wannan stupid din d'an nata mana mai shegen taurin kai kamar dutse "nan ya shiga zayyane masa halin da'ake ciki hisham ya gyada kai yana cewa "gsky mami ta yanke hukunci mai kyau sai dai muce allah ya tayaka rikon amanar maryam , dan allah friend ka amince karka zubawa mami kasa a idanunta bugu da kari aure shine cikar kimar mutun duk inda zaka shiga matsawar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login