Showing 24001 words to 27000 words out of 168608 words

Chapter 9 - Mar'adam's Book 1 Hausa Novel Complete

sanya jallabiyya fara sol ya kashe tv sannan ya karasa Inda   abun sallarsa yake ya tadda ikama yana sallah qirjinsa na dokawa ...

Ya dade yana nafilfili da rokon Allah ya kawo masa sauki ,bai koma bacci ba sai da yayi sallah asuba har karfe goma  bai tashi ba shigowar hjy zulaiheart uku  duba shi yana bacci na hudu ne ta iskeshi kwance idanunshi biyu amman bai tashi ba
ta k'araso ta zauna a bakin gado tana shafa gefen fuskarshi "lafiyarka adam  baccinka yayi tsawo yau  ko baka jin dadi ne ?motsawa yayi ya  daura kanshi akan cinyar mahaifiyarsa  zuciyarsa cike da rauni yana  fatan haka ya zamo Silar samun sausauci ,  "sweetheart ..."! ya kira sunanta a raunane  "menene adam? " fada min meke damunka ?duk ta rude tana son sani halin da danta yake ciki "zuciya ta na cikin rudani sweetheart soyayya na  kikiniya dani ina son yarinyar Nan  sosai sai dai ban san Ina zan ganta ba , ta shiga zuciyata zata iya sawa ki rasani "naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana riko tafin hannunsa cikin nata ta rike gam "Allah  bazai sa ba sai naga aurenka da ya'yanka  " yaushe zan ganta sweetheart  kullum sai nayi mafarkinta  ?har tsoron runtse idanuna nake saboda dole sai tazo .tausayinsa ya kamata ita dai Allah yasa ba aljana bace ta aure mata da "wata rana zanganta ko Sweetheart ?yayi maganar yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa.

"Adam ba dukkanin mafarki ke zama gaskiya ba "Ina ji ajikina gaskiya ne sweetheart  Kuma lokacin haduwarmu  daita ya kusa tunda har tayi  min magana a daren jiya abinda bata taba min ba ,naji sautin muryarta , tana da sauti mai zaki da rikitarwa "shikenan ya Isa ni mahaifiyarka ce zan tayaka da  addua idan mutun ce Allah ya bayyanata idan aljana ce Allah nesantata da Kai  amman ka kwantar  da hankalinka ka aure maryam zata Saka zuciyarka natsuwa zata mantar da kai komai,zakayi alfahari daita  "ya runtse  idanuwanshi gam yana Jin zafin furucin mahaifiyarsa  "Ina jin kunyar auren maryam sweetheart wallahi bansan dalili ba gani nake kmr  abun kunya ne na aureta "Babu wani abun kunya yarinya ce mai sauki hali "Kuma bazata damu  ko ka  aureta sai ka  qara da  princess dinka ta fad'a tana shafa sumar kanshi   "wannan ai  ya zama dole shiru tayi tana jinjina girman alamarin ta fad'a masa haka ne ba dan ranta yaso ba domin ita dai maryam ce cikar burinta ,kuma koda zai hadata kishi da wata ya zamanto ita ce gaba da kowa  a zuciyarsa naunayen ajiyar zuciya ta sauke muryarta a sanyaye tace "shikenan tashi ka shiga wanka  ga break can na jiranka  Allah  ya jishemu alkhairi "ya mike da kyar rike da kugunsa ya shiga bathroom ita Kuma ta fito zuwa parlour.

Karfe  daya daidai ya shirya sai dai ya kasa fitowa zuwa falon mahaifiyarsa saboda baya son haduwa da maryam  shi Kansa Yana mamakin zazzafan soyayyar da yakewa princess wanda ma'abota so da shauki ne kawai suka San zakinta yana son yarinyar kamar ranshi, soyayyar da yake mata mai tafiyar da ruhi ne Ina ma ya ganta a duniyarsa ta zahiri  da shi kadai yasan irin so da tattali da zai mata."sauke numfashi yayi da karfi "anya kuwa zaka iya ?zaka iya nuna mata soyayya a fili ?ban yarda zaka iya nuna mata tarin qaunar da kake mata ba  saboda kai din mutun ne mai jin kai zuciyarsa ta fad'a masa haka ya furzar da iska mai zafi yana shafa goshinsa yana girgiza kai ." a natse ya mike ya goya hannuwansa duka a bayansa  yana zagaya dakin numfashi kawai yake saukewa ya dan tsotsa keyarsa "Ina da tarin kudi Ina  da tarin yan'uwa Ina da fada aji a kasar nan Amman duk na banza tunda duk sun  kasa samammin   abinda zai bawa zuciyata natsuwa da zaman Lafiya .


karfe daya daidai na washegarin ranar ya bar  lagos zuwa kasar togo sai dai a can din ma kasa tabuka komai yayi   haka ya wuni ya kwana yana tunaninta yana son zuciyarsa ta bar tunaninta amman abun ya cutura  duk saukar numfashinsa  tafe yake da tunaninta yana son  ya samawar kanshi natsuwa amman hakan yaki samuwa yayi shiru kawai yana kallon saman dakin da yake kwance yana tunanin abinda ya kamata yayi  babu abinda ya zoma zuciyarsa a wannnan lokacin kamar kwadayin sigari abinda ya dade bai sha ba hassalima baya sha sai yana cikin damuwa irin wannan shiyasa bazaka ta'ba cewa yana sha ba dan bai nuna a skin dinsa ba ."
"a hankali ya qarasa inda  akwatin kayansa yake  har zai bude ya tuna baya yawo dashi  dan haka yaja dogon tsaki yana mai dafe goshinsa  ya koma da baya da baya ya zauna akan kujera jagwba yana murza goshinsa wayarsa dake gefensa ya soma ringing ya kai hannunsa ya lalubo ya dauka ya d'an bude idanunshi kadan ya duba trucaller ne yasa ya gane ko wacce ke kira direct call ya dan ja saki  yaki dauka munubiya ce diyar alhaji  madu tsohon shugabansa nigeria school  mate dinsa ce tare sukayi karatu a chaina ."  ta dade tana son shi Amman shi Sam baya tata gbdy duk hanyar da zata hadasu ya kulleta yanzu ma bai San Ina ta samu wanna number nashi ba ."
Byn second biyar wani Kiran  ya shigo ganin me Kiran  ya dauka yayi shiru har sai da yaji yace  " hello sir ! sannan yace "Ahmed ykk ?  ya  fada a kasalance "okay shikenan zan turo maka  zuwa anjima  Jin yanayinsa ahmed ya fahimci yana cikin damuwa  dan haka  ya dinga  jansa da hira ,Ahmed yana cikin wad'an da Mr ATA  ya taimaki rayuwarsu  ya hadu dashi a bakin titi  Antoni  mota ta bugeshi Mai motar ya gudu ya barshi shine ya  taimaki rayuwarsa daga rana ya Maida shi tamkar danuwansa har ya samammansa aiki akarkashinsa saboda ya gama karatu aiki ne ya zama matsala  Kuma shine babban a d'akinsu ga  kannen da iyaye , agarin  nema  aikin ya hadu da wannan accident din Mr ATA  na qaunar ahmed sosai babu abinda baxai iya masa ba dan jinsa yake  tamkar ciki daya suka fito  zuciyarsa a  cunkushe yake da damuwa  amman sai da Ahmed yayi sanadiyyar dawo dashi daidai dan shi mutun ne me abun dariya da barkwanci  haka nan ya tsinci Kansa da Jin dadi Kuma yasan Hakan nada nasaba da wayarsa da ahmed   ya  sauke wayar yana  farinciki ."


******
Tun  daga  ranar  da'aka tsare hadiza  police basu  sake tuntubarta akan komai ba, illa bincike da jami'an  tsaro suke babu dare babu rana har suka samo wani abu daya  dan  danganci fadan  hadiza da sadear ,macen police ce ta taso hadiza gaba zuwa d'akin bincike ta zauna cike da tsoro "inspector  abbas  kunna mata  voice  dinta taji da kunnenta  nan take aka kunna "shegiya karuwa muguwa mai fitsarin kwance Ina dalili da duk saurayin da zanyi sai ya dawo yana sonki da zarar Kinga nayi saurayi shige da fecenki bai karewa har sai kin d'auke masa hankali, abinda zan bari ki gani da idanunki sai kinyi mamaki , wallahi wannan  yayan naki sai ya tausaya miki sai yace bai sanki ba, ke kadai kike da kan maza wallahi idan baki shiga hankalinki  akan  Umar  ba zan siyawa yan iskan unguwar  nan kayan maye su cire miki abinda yake ciki idanunki , ke wannan yarinyar  anyi tsinanniyar me nayi miki  ? shegiya mai ruwan Ido muje neman aiki  tare  dake  ke aka d'auka  yanzu kuma  Umar dake sona kin shiga kin fita kin d'auke masa hankali sadear ki shiga hankalinki dani dan  wallahi zan iya kasheki zan kasheki  na kashe banza  danuwanki  zayi  kukan rashinki ki shiga hankalinki bani fada kune kuke son maidani mahaukaciya Kinga wannan Umar wallahi muddin kika ce zaki kwace sai dai kije lahira idan baki tsaya matsayaki ba zan kasheki , idan ban kasheki ba kuwa abinda zan miki zaki sha  mamaki , idan zakiyi bacci karki saki jiki dan zan iya zuwa na  tsoka miki wuka tunda voice ya  fara babu  sautin  muryar sadear   yansanda suka zuba  mata Ido a zaune dake  tana kuka tare da danasani "ko  akwai abinda zaki kare kanki dashi ?tabbas muryarta ce Kuma munyi haka daita amman har ga Allah bani na kasheta ba kawai dai na fada mata haka ne dan na bata tsoro "daya daga cikin police yace "a'a hadiza daman haka halinki yake kowa Kuma ya sheidake da son fada , ko kinsan wannan wukar da kika yi kisan daita an ta'ba kashe wata yarinya dashi a gra diyar alhaji jamilu ?nan hadiza ta sake rikicewa ta gigice hawaye na zubo mata , "wallahi ban san komai ba gara ma ki fada gsky dan bawa hukuma saukin bincike abu na karshe ki shirya daukar lawyer da zai kareki nan aka sake tasa keyarta zuwa cikin cell ..yadda take kuka sai ta baka tausayi ."

da  yammacin ranar asabar   zaune  maryam take a kusa da aunty shahida da aunty   khadeja   tana sauraronta  aunty  shahida ta kalleta  a natse tayi  murmushi  ya naga duk kin firgice ki natsu   please  "kinsan abinda  yasa nake ta son muyi  magana dake tun last week ?maryam ta girgiza  mata Kai kawai tana tattara dukkanin natsuwarta  da hankalinta gareta "mun yanke shawarar  za'a had'a  aurenku da Adam "take gaban maryam yayi wani  irin dokawa ya fad'i ta waro idanunta sosai zuciyarta na tsinkewa  cike da  matsanacin tsoro take duban  duban aunty shahida  da aunty khadeja  tana jin kamar ba abinda ya fito  daga bakinta ba kenan  ,maimaitawar da aunty khadeja  tayi ya tabbatar mata da lallai gsky taji  "wani Adam din Kuma aunty khadeja ? tayi tambayar jikinta na rawa hantar cikinta na kadawa "a'a Adam dai na gidan nan  da kika sani dashi za'a had'aku aure tunda yaki fito da mata mu Kuma mun gaji da zamansa haka  " aunty shahida aunty  khadeja  kuyi hakuri ni gaskiya bana sonsa da aure ........"


Mmm sudais
💗💗💗💗💗💗
   MAR'ADAMS
    💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Book one
Free page


*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page7

........" Cikin mugun firgici da tashin hankali aunty khadeja da aunty shahida suka yi shiru gabad'aya suna kallonta cike da sansar fargaba da tashin hankali "me zasu fad'awa mami data d'auki soyayyar duniya ta d'aurawa aurensu ? " ita kam Maryam kasa kallon cikin kwayar Idanunsu tayi ta takure jikinta guri daya tayi kasa da kanta idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye gbdy ta kasa kwakwaran motsi a zaunen da take , wani iri take ji a gabadaya ilahirin jikinta ,sai lokacin taji wani irin kunyarsu tayi mata diran makiya .

ji tayi kamar ta tashi ta bar gurin sai Kuma taga hakan ba daidai bane ,basu cancanci haka daga gareta ba ,zasu d'auka raini ne dan haka ta cigaba da zama zuciyarta na tsalle da bugawa wasu hawaye masu zafi suka samu nasarar zubowa akan kuncinta tasa hannu ta goge wasu na sake zubawa ."
Sanyayyaye numfashi aunty shahida ta sauke tana gyara zamanta tare da janyo maryam zuwa jikinta tasa tafin hannunta tana share mata hawaye "kukan ya isa haka tunda baki son shi shikenan zamu san yadda zamu fahimtar da mani amman da zakiyi hakuri kiso AD hakika maryam da kin san kin dace miji na gani na fad'a ba dan AD ya kasance dan'uwana ba ,duk mace zata yi alfahari ya kasance miji agareta kuma uban ya'yanta ki tsaya kiyi tunani maryam karki yanke hukunci cikin tsoro da tashin hankali ".


Cikin tsananin kuka da tashin hankali maryam tace "a'a aunty shahida babu wani tunani da zanyi akan ya Adam dan yafi qarfina ta kowani bangare ban Isa na tsaya Inda yake ba bare na kasance mata agaresa ta Ina zan soma rayuwar aure dashi aunty shahida ? "Ta Ina zan fuskanci mutumin da bai qaunar ya bud'e idanunshi ya gani ? "duk duniya idan akwai macen da ya Adam ya tsana to nice "Ina zan kai tsoron da nake masa har nayi rayuwar aure dashi ? uwa uba baya Sona ta yaya kuke tunanin nima zan soshi har naso zaman aure dashi ?" wallahi aunty shahida ni tsoro ma yake bani ban ma san ta ya zan fara rayuwar aure dashi ba , da zarar nagansa bana samun natsuwar zuciya har sai na nisanta kaina dashi to ta yaya kuke tunanin zan iya zaman aure dashi Koda Ina son shi bare bana masa soyayya irin ta aure sai ta yan'uwantaka ?"


" ni yanzu tashin hankalina mami wallahi bazan so taji wa......."kuka yaci karfinta ta kasa qarasa maganarta "dan wannan karki damu Ina da tabbacin da zarar kunyi aure shikenan maryam ,bazai nuna miki komai ba sannan zaki daina jin tsoronsa inshallahu zakiyi farinciki a gidansa. "maryam ta zumburo baki "Allah aunty shahida bazan iya ba shine miskilanci shine girman kai , uwa Uba zuciya idan na auri ya Adam bazai barni na rabi Inda yake ba kullum zan tabbata cikin gallazawarsa wa zai ceceni a hannunsa ? ta Kalli aunty khadeja hawaye na gangarowa akan quncinta "yan'uwana ku taimakeni karku bari a had'a auren nan , ban rainaku ba sannan ban ki shawararku ba amman abar wannan maganar yanzu baku ji yadda nake jin zuciyata ba ,ji nake kamar zata fashe tsabar tashin hankalin jin maganarku , Kalli yadda jikina ke rawa aunty khadeja Allah bazan iya ba ta k'arasa maganar tana sake rushewa da wani sabon kuka."

Aunty khadeja wacce tayi shiru tana sauraronsu tace " duk na fahimceki Maryam amman yana da kyau mutun yayi dogon nazari akan duk abinda ya kunno kai cikin rayuwarsa zamu baki lokaci kiyi tunani sannan kiyi istahara ..?maganganu masu sanyi da kwantar da hankali aunty khadeja tayi amfani dasu gurin son janyo hankalin maryam duk da a rikice take amman tana fahimtar komai dake fita daga bakinta ,naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana mai kallon aunty khadeja sannan taja gindi zuwa Inda take ta riko hannunta d'aya cikin nata ta damke gam jikinta na sake d'aukar kyarma muryarta a raunane tace "aunty khadeja bazan iya aurensa ba bari ma na fada muku gaskiya akwai wadan da suke  sona sosai ku bari ya nemo matarsa a waje zai fi zame mana alkairi ......"

duk yadda sukayi daita ta fahimcesu taki sai faman kuka take tana basu hakuri ganin yadda ta rikice sai kuka take tana rokonsu tana juya Kai yasa suka hakura da batun tare da sallamarta da kyar ta mike tsaye tana layi saboda juwar dake dibarta ta bar parlour, a tare aunty shahida da aunty khadeja suka Kalli juna suna sauke ajiyar zuciya " ban ta'ba tunanin maryam zataki amincewa da wannan had'in ba ,na d'auka zata fi kowa farinciki da murna zata kasance matar AD duba ga yadda naga 'yammata na maseefar son shi da son aurensa inji cewar aunty shahida "ai abun ba daga nan take ba aunty abincin wani gubar wani kuma ma ni banga laifinta ba shi kasan AD matsala ne bare a kai ga halin miskilancinsa aunty khadeja ta fad'a tana jan tsaki " bayan wannan miskilanci nashi bashi da wani aibun da zaa ki aurensa gaskiya kawai dan bata son shi ne abar zance zuwa wani lokaci sai mu fahimtar da mami .

"Haka ne amman  ya kamata ki kirasa ki fad'a masa ba'a son shi ko ya dan rage jijji da kai da mislinci da nuna fad'i da Isan da yake  "yanzu kuwa zan sheida masa aunty shahida ta fad'a tana ciro wayarta daga cikin handbag dinta kira d'aya ya katse ya biyo byn Kiranta "kazo yanzu muna parlour'n mami  na uku , tana gama fad'ar haka ta katse Kiran tana jan tsaki dan tasan bancin halaiyan da yake nunawa maryam da babu yadda za'a yi takisa ".

maryam kuwa tana fita d'akinsu ta shiga ta zube kan gado tana kuka sosai har da shesheka tana jin rashin dadin kin amincewa yan'uwanta da tayi , ko babu komai yaci darajansu agurinta ta amincewa aurensa "mai yasa na ma su aunty shahida haka ?mai yasa bazan so zabin su ba kuma jininsu da suka fi qauna akan komai ?" hakika ban kyauta ba na yiwa yayar mahaifina butulci da yan'uwana sam basu canci haka daga gareni ba "why why maryam why do  you do this to them ?tana cikin wannan halin nana hauwa'u ta fito da sauri daga bayi dan sheshekar kukanta ne ya hankaltar daita ganin yadda take kuka kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa yasa  ta k'araso da sauri ta hau sama gadon tana mata magana cikin tsananin tashin hankali "menene  marsi ? dan wani loakcin da haka take kiranta mrym ta sake fashewa da wani sabon  kuka zuciyarta na zafi da qunci banci tsakaninta da nana hauwa'u basa boyewa juna komai tabbas da bazata fad'a mata  ba zata boye wannan maganar ta barwa kanta ita kad'ai tunda tasan su aunty shahida ma bazasu  fito da maganar ba .

sheshekar kukanta ya qara dagawa nana hauwa'u hankali jiki a mace ta kamota ta rungumeta tsam  ajikinta itama ta fara hawayen tausayin yar'uwata duk da bata san dalilin kukanta ba a hankali ta soma jin sautin muryarta cikin kuka "na shiga uku nana hauwa'u na kasa yiwa yan'uwana abinda ya kamata na kasa bin umarninsu nasan zasu ji babu dadi a ransu tayi mgnr hawaye na gangaro mata ...."
"menene abinda kika kasa sannan su wani yan'uwa kenan ? ta fad'a tana sake rungumota jikinata' kiyi hakuri ki natsu marsi ki fahimtar dani abinda ke faruwa "naunayen ajiyar zuciya ta sauke sannan tayi mata bayani komai cikin muryar kuka  tana mai zare jikinta daga nata ta cusa cikin tsakankanin qa'fafunta tana sheshekar kuka tare da kamkame jikinta .


Shiru nana hauwa'u tayi  a matukar tsorace tana kallonta tana maimaita maganarta  kafin daga bisani ta motsa bakinta ta soma magana a zafafe "hakika babu aibu a maganarki sister tunda  shima bai sonki kema bai dace ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login