Showing 36001 words to 39000 words out of 168608 words

Chapter 13 - Mar'adam's Book 1 Hausa Novel Complete

duniya yace babu komai ya boye mata saboda muddin taji abinda ke damunsa sai ta fishi shiga damuwa yau kwana biyu kenan bai sake d'aura  maryam a cikin kwayar Idanunsa ba bai damu ba dan damuwarsa tafi rashin qaunar data nunawa yan'uwansa tana yi masa  ."

yana zaune a part dinsa yayi shiru yayinda
MB ke zaune a gefensa "ka daina damun kanka da tunani kada wani ciwo ya kamaka kasa mu shiga uku meye ma matsalarka?sai daya furzar da iska yace  "ka kasa fahimtata ne kawai  amman matsaloli gasu nan takoina kuma ace mutun bazai ji babu dadi ba.
"friend abinda zaka dinga dubawa Allah ya baka Lafiya ya baka tarin dukiya bila'adadin wanda Kai kanka baka san adadin kudadenka da gadarorinka ba ,Allah ya baka komai da komai me yakamata kayi sai ka gode masa  ?komai mai wucewa ne inji cewar MB  "to alhamdulillah na gode masa amman bangaren damuwata ba mai karewa bace.
"kaga duk wannan mai sauki ne ni sai nake ganin kamar har da rashin amincewa da aurenka da mrym yasa damuwar tayi maka yawa koma nace   yana cikin abinda ke damunka karka ji komai zanji dashi.


"Me zai sa damun tunda ba sonta nake yi ba kawai zan auri maryam ne saboda darajan mahaifiyata kuma zata kare rayuwarta a gidana sbd darajanta "Kai yanzu kana ganin zaka aureta?" zan aureta saboda sweetheart "angama zan san abun yi sun dade suna tautaunawa kafin daga baya ya mike ya fito a parlour ya iskesu har hjy zulaiheart yayi mata sallama "har zaka wuce muhammadu bello bazaka tsaya Kaci abinci ba ? a'a mami a koshe nake da zai fice daga falon yace "Maryam muje na dan ganki tace "to ! tare da d'aukar mayafinta ta yafa ta fito a haraban gidan suka tsaya ."

"wato maryam kinsan abinda yasa na kiraki ?ta girgiza masa Kai "ba'a kan komai bane sai akan maganarki da ATA me yasa bazaki amince da aurensa ba ?"banason ki rufe min komai idan kin boyewa su aunty nasan ni zaki fada min gasky menene dalili ? Numfashi ta sauke tana lumshe ido"ina jinki ? a natse ta fara mgn cikin raunanniyar murya "abu na farko ya Adam bai sona sannan abinda na fahimta kamar dole akayi masa ya aureni , ni km bazan iya auren mijin da baya sona ba gsky .

"da zai fada miki da kanshi zaki yarda ki auresa ?"a'a bazan auresa ba saboda bana son shi shima km baya sona "shiru yayi yana kallonta "ki dai yi tunani ba yabon Kai ba abokina yana da nagarta da za'a auresa ke ya'yan manyan kasar nan fa binsa suke suna rokonsa ya auresu babu wacce ya amincewa zai aura sai ke "gsky sunyi kokari da son aurensa   ni Kuma kaga banason shi zaka iya fada masa gara ya zabi daya acikinsu ya aura "bazaki duba darajan mami ba dan itace me son had'in ko shi baya so sbd mami ne ?ya fada cike da Jin haushin furcinta ."gaskiya da wahala duk ta Inda
MB ya bullo mata sai ta kawo masa hujja haka ya gaji yayi mata sallama sai dai yasan ko giyar wake ya sha bai Isa ya fadawa ATA cewar mrym bata bashi had'in Kai ba ."

washegari ranar mr ATA yayi tafiya zuwa hollond Kan harkokin kasuwancinsa gbdy   ya manta wata aba maryam a rayuwarsa harkokin gabansa kawai yake da tunanin princess dinsa ."Kwana biyu da tafiyar ATA maryam ta soma hada kayanta da abubuwa amfaninta ta fad'awa hjy zulaiheart da nana hauwa'u cewar ranar juma'a inda Allah ya kaimu zata Abuja zatayi sati biyu ta dawo "Kinsan sati biyu zakiyi shine baki bari mun tafi tare ba ?inji cewar nana "kiyi hakuri sister nayi kuskure nest time inshallahu iya haka kawai ta fad'a saboda taikaita maganar .

Ranar juma'a jirgin karfe goma tabi zuwa Abuja tana sauka ta tarar da kannenta da mahaifiyarta sunzo tarbarta dake sun san da zuwanta daya byn daya ta rungumesu ajikinta suna murnar ganin juna "nayi kewarku sosai "muma mun yi kewarki inji cewar izza ta k'arasa ta rungume mumynta dake tsaye tana sakar mata murmushi "mumy na sa
meku lafiya ? Lafiya qalau maryam ya mutanen lagos ?tayi mata tambayar tana shafa bayanta da gani kasan akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu,
Ta zareta ajikinta ta rike hannunta suka d'auki hanyar gida tun akan hanya mumy ta fara mata magana akan ATA tayi matukar mamaki da Jin tasan komai "eh haka naji sai dai gaskiya ni bana son shi dan bazai yi caring din mace ba shi kenan kullum cikin dacin rai no yayi gaba ya nemi mata nima Allah zai bani nawa mijin ."

"karki soma wannan maganar ke Ina ruwanki da dacin ransa tunda yana da kudinsa ,shi fa mai kudi sai a hankali har suka karasa gida mgn daya suke yi Koda mahaifinta ya dawo yayi murna da ganinta nan ya shiga zolayarta "Hjy mrym ko ace maryamu damtso ko amaidashi irin na turawan nan ace mary
duk ke kadai gilashina a she babban kamu kikayi alagos ? Kin tashi daga diyata kin zamo surukata matar d'ana da nake ji dashi gskiya naji dadin wannan had'in, kwarya tabi kwayar kenan kinyi sa'a da dace miji na gari .mrym ta zumburo masa baki "Allah dady ka daina cewa hk ni yarkace ba wata suruka ba km ni babu wani dacen miji danayi tsokanarta sukayita yi har dasu izza..."

"zamanta a Abuja taji dadinsa tana zaune cikin yan'uwanta cikin kwanciyar hankali da annasuwa babu tsana babu tsamgwama Kuma kullum suna waya da nana hauwa'u da hjy zulaiheart sati daya sati biyu mrym shiru taki komawa lagos tun abun bai damun hjy zulaiheart har ya fara damunta wani tunani tayi tasan halin d'anta Allah yasa ba wani abun yayiwa maryam ba kafin ya tafi hollond yasa tayi musu wayo ta koma gurin iyayenta ".

da yammacin ranar asabar hjy zulaiheart ta kirasa yana dauka tasa masa kuka "wallahi muddin baka auri mrym ba babu ni babu Kai Adamcy "subhanallah sweetheart ki kwantar da hankalinki menene ya faru kike kuka da fad'ar haka ? ni dai ka auri maryam shine kawai abinda nake bukata ,Idan km kana son kwancinyar hankalina Kuma tabbas ni ce rayuwa agareka kmr yadda kake fada lallai kayi wani Abu mrym ta dawo gidan nan sannan ka hanzarta aurenta acikin kankanin lokaci na ganta acikin gidan a matsayin surukata ". Sai daya sauke numfashi sannan yace "shikenan naji ki daina kuka zanyi yadda kike so nayi miki wannan alkwari zan aureta sai da yayita rarrrashita sannan ta sake , suna gama waya Kiran MB ya shigo wayarsa byn sun gaisa mgnr minti biyar sukayi sukayi sallama .

kullum abu daya ke damunta har yasa gidan ya fita ran mrym kullum sai mahaifiyarta ta dameta da batun ATA cikin zafin rai tace "mumy nifa inada Wanda nake so jira lokacin nake zan bashi dama ya turo" ke ban son zance banza da wofi ni na haifeki ko yar riko ce ke arzikin rikon danayi miki nace ki auri Adam zaki min alfarma ballanata ni na haifeki acikin cikina har nace ga abinda nake so kiyi min gardama to ki d'auke soyayyar wancan ki maye na adam agurin dan dashi za'a yi babu fashi munafukar Allah butulu kawai , shiyasa kika wani tattaro kika dawo nan? " to dan ubanki sai kin koma tana gama fad'ar haka taja tsaki tana zuba fada ."

mrym ta fashe da kuka mai tsananin har ana iya jiyo kukanta "zance banza zance wofi ba kuka ba idan idanunki zai fado tsakiyar d'akin nan aure babu fashi sai anyisa saboda haka garama ki daina kuka karki je kisawa kanki bacin rai hawan jini ya kamaki dan ko hawan jini zai kamaki sai na zama surukar adam, wannan aure babu fashi tana magana mrym na sharba kuka kmr wacce aka aikowa da sakon mutuwa ".Iskanci banza har da cewa Ina da Wanda nake so to ni wannnan nake so Kuma shi zaki so wancan kisa masa kiyayya daga yau na gaya miki ki dauko soyayyar wancan ki d'aurawa Adam ki dauko kiyayyar Adam ki d'aurawa wancan shashar banza shashar wofi munafuka kawai mai yiwa kanta bakinciki ta k'arasa maganar tana sake jan tsaki ,
Yayan zamani Allah ya shirya wannan maganar fa tun asalin iyaye da kankani uwa ko Uba suna da iKon da zai d'auki duk wanda yake so ya bawa yarsa batare da yar taí yi gardama ba dan yanzu zamani ya rigada ya canza nan ta mike ta barta tana surutai da zaginta ."

Tana kwance a d'akinta tana kuka faiza ta turo kofar dakin ta shigo ta hau har kan gadon ta rungumeta tana rarrashinta nan kukanta ya qaru "aunty mrym ki daina kuka dan Allah sheshekar kawai take "wai me yake faruwa ne kike kuka haka?, Kin cewa komai tayi tana cigaba da kukanta nan Faiza ta fashe da kuka tana cewa "Dan Allah ki fad'a min ki Daina kuka cikin muryar kuka tace "wallahi bazan auri ya Adam ba sbd banason shi "Amman aunty mrym yakamata ki duba daranja mami tunda tana sonki sosai "wallahi bazan iya ba bazan iya ba tunda ba da ita zanyi rayuwa aure ba ta k'arasa maganar tana sake rushewa da wani sabon kuka ...."

Da daddare ta iske mahaifinta akan batun auren "mrym naji duk bayaninki sai dai banji dadi ba Amman Ina son ki rike abinda zan fada miki mrym karkice zaki yiwa yar'uwata haka karki bari wannan abu yayi silar rugujewar zumuncinmu mrym , idan har kika ki wannan auren zakiyi danasanin a rayuwarki dan bazan yafe miki ba a matsayina na mahaufinki bazan so kiyi nadama a rayuwarki ba, duk d'a na halak so yake ya rabu da iyayensa lfiya ki d'aure kiyi ta addua da sannu soyayyarsa zai shiga zuciyarki idan wannan auren alkhairi ne arayuwarki allah ya tabbatar dashi idan ba alkhairi bane mrym Allah ya canza miki da wanda yafi shi zama alkhairi bare Ina ji ajikina wannan auren alkhairi ne ni kaina bazan so Adam yaje ya auri wata ya barki ba, ni kaina na dade Ina wannan mafarkin duk da na gari zai so ya rabu da iyayensa lfiya Ina sonki mrym hk zalika Ina son aurenki da Adam kuka take a tun sanda ya fara magana har ya dasa Aya yana gamawa ya mike ya shige bedroom dinsa ya barta tana kuka ..."

*******
Barrister hayat ne zaune a gaban hadiza lawyer da suka dauka domin kareta "Ina son ki fad'a min gaskiya menene gaskiyar abinda case din yake ciki domin mu san yadda zamu kareki "menene gaskiyar halakarki da wadan wukaken da ake tuhumarki da kisan Kai dasu karki boye min komai yadda zan fuskanci shara'a na kareki "barrister zan fada maka gaskiya yadda alamarin nan yake bazan boye maka ba saboda Ina bukatar na fita acikin wannan matsalar tayi shiru tana numfasawa tare da fargaba fadar abinda ke zuciyarta ...."

Bayan wasu mintuna ta cigaba da magana
"Wallahi  barister  bani  da  halaka da  wad'an  nan  wukaken  ban san  komai   akansu ba , yadda ka gansu  haka  nima na  gansu  kawai dai  na shiga  track ne  a sanadiyyar furucina.   shiru  barister hayat   yayi  yana  kallonta   tare da nazarinta  "ka yarda  barister  bani  na kashesu  ba  ta sake  fad'a   tana  rushewa da wani  kuka  mai  ta'ba zuciya  "mai   zai sa na kashesu  bani da wani halaka da kisansu   gara ma  ita sadear  mun samu  matsalata daita  har  nayi furucin zan  kasheta  amman ita wannan  yarinyar da naji ana  fad'ar  sunanta  sam  ban santa  ba   hasalima ban  ta'ba  ganinta a rayuwata  ba   tayi maganar  tana  sheshekar  kuka.

Ganin yadda barister hayat ke  kallonta  yasa ta  shiga  furta kalmar    "na shiga ukuna ni hadiza  na jawowa  kaina  rashin kwanciyar hankali, ni kaina a daren ranar da sadear   zata   mutu  naga shigowar  mutun cikin bakaken  kaya  an shiga d'akinsu  amman sam ban  kawowa zuciyata cewar  kashe sadear za'ayi  ba ,  Ina da  tabbacin  da  police  zasuyi  aikinsu  yadda ya kamata  zasu  gano ko waye  yake  da saka hannu  cikin mutuwar wad'an nan  mutane guda  biyu  da'ake tuhumata  akansu ta k'arasa maganar cikin tsananin tashin hankali ."

      kuka  take sosai  kamar  ranta  zai  fita  "naunayen  ajiyar  zuciya  barister  hayat  ya sauke "tabbas  na   yarda dake  Kuma  inshallahu  zanyi iya  qoqarina  naga kinsamu   ku'buta  duk da mahaifiyar  mubina ta tubure  lallai sai an kar'bawar  diyarta hakinta    shi  dai mahaifinta  alhj   jamilu   ne yace  ya  barwa allah amman   kiyi addua sosai    dan  idan mahaifiyar   yarinyar  ta rinjayi  mahaifinta gsky   sai  dai wata bake ba , bangaren  su  sadear   wannan  mai   sauki  ne   da kansu zasu gaji da zuwa kotu  kar'ban  kwana  wata su hakura , amman su  alhj jamilu suna da baki a kasar nan suna da fad'a aji akoina  dan haka  ki dage  da   addua  sosai  .  "na  gode  sosai barister da  k'okarin, "karki damu  Allah  ya bamu sa'a inji cewar  barister hayat   "Ameen   ta  furta tana kuka   sukayi  sallama da zumar  zai sake waiwayota  kafin a zauna kotu ."

******
Zaune   mahaifiyar  mubina   hajiya  sha'awanatu   take a had'ad'd'en kujera  a parlour'nta kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana cikin tsananin damuwa domin kuwa idanunta sun kod'e  saboda  kuka dan tunda jami'an tsaro suka zo musu da bayanin anyi kisan Kai da irin wukar da aka kashe mubina har anyi nasarar   kama mashekiyar  take cikin damuwa  da kuka , duk yadda    mijinta alhj jamilu ke  k'okarin shawo kanta taki  yarda burinta  bai  wuce a gurfanar  daita a yanke  mata hukunci  daidai da abinda ta aikata ba .a yanzu ma zaune yake   a gabanta yana  fuskantarta domin son kawowa zuciyata natsuwa "dan  Allah ki bar maganar  kisan  mubina  da ma duk wanda yake da saka hannu cikin kasheta mubarwa  Allah ,haka Allah yaso bazamuyi rayuwa mai tsawo tare daita ba , yanzu  karshe  wad'an  da basu ji ba basu gani ba sune  zasu zo suna cin wahala  bana jin wannan yarinyar zata iya shigowa har cikin gidan zainab ta kashe  mubina , dan haka ki natsu dan Allah ki samawa zuciyarki salama da hakuri  ".

"uncle jay ........."  da  yake haka itama take  kiransa  kamar yadda ATA ke kiransa " kace na hakura na bar maganar alhalin an kama wacce tayi kisan  ?ya gyada mata Kai  al'amun haka  yake  nufi"  nifa  say  Inda karfina  ya  tsaya, wallalhi  sai nayi shari'a  daita  Koda duk zan qarar da abinda na mallaka  ,
Kai  bari  ma na takaice maka sai na rakata har  zuwa gidan yari  sannan ruhina zai samu salama , ai tunda asirinta ya tono bazan yarda ba sai itama an sha jininta  kamar yadda tasha jinin di........."
Nace   kiyi  hakuri mu barwa Allah ya katse mata numfashi ta hanyar fad'ar haka " duk  wani  matakin da zaki d'auka bafa zai dawo mana da diyarmu da muka rasa  ba ,ta kwa'be.  masa  baki  da fuska  dan sam maganarsa  basa  shigarta   ya mike tsaye yana  dubanta "muddin Ina da iko akanki  ki  bar maganar  nan  mubarwa  Allah  Komai  yana  gama fad'ar   haka ya shige bedroom  dinsa ya barta tana  girgiza Kai  hawayen bakinciki rasa tilon diyarta na zubowa akan kuncinta bata Jin zata iya yafewa wannan yarinyar ."

********
"Adam  zaune  a makaken  office   dinsa  dake  cikin kasar hollond   zagaye da  makeken  table  wanda ke d'auke da file  files  dabam  dabam  sai qaramin  frem din  hoton  mahaifiyarsa da mahaifinsa  , sanye   yake   cikin  riga fara  sol da  wondo  baki  sai  yar  saman suit  dake  sanye a saman farar rigar  .  ya  d'auki  wayarsa  dake  qara tun mintuna   ashirin da suka gaba  har zuwa  lokacin daya d'auka  yana dubawa  miss call's ne rututu  bama zai iya  kirgawa ba , wasu yasan number's  wasu  kuma bai sani ba .
ya sauke numfashi   sannan ya fara  da  kiran  MB  kasancewar shine wanda  ya kirasa karshe MB  ya  d'auka  yana  cewa " hello  friend  ykk ?  Lafiya  alhamdulillah  okay  ai Ina ganin  zan  shigo  cikin  satin nan   dan  sweetheart  ta matsa lallai nazo ayi  mgnr  aurena  da wannan yarinya gashi  ni wallahi har yanzu  bana Jin son yarinyar  Ina  jin qinta sosai  abinda  ke Kona min rai yadda sweetheart  ta nace  akan  lallai sai anyi auren nan kusa .  
"kasan har cewa tayi  bata yafe ba muddin ban aureta ba ."Kai  gskiya Ina ganin ya kamata  kayi wani Abu tunda kaji abinda tace maganar MB  ta  doki  kunnensa   ",amman ni  aganina da an  bari zuwa wani lokaci sai ayi auren tunda ba neman kai akayi dani ba  " waya fada maka ?ai kuwa muna neman kai da kai mun gaji da ganinka haka dan haka   karka fara  cewar ba yanzu ba domin kuwa zaka samu matsala da mami   kawai  kabi umarni ka  tunkari yarinyar  da kanka."nace mata me MB   ? yayi masa tambayar yana ciza lips dinsa na kasa , shiru shima MB yayi yana sauke numfashi "ya  kake wata mgn haka ?ya sake tambayarsa a kufule  "darajan  da tsinuwar mami shine  abun lura
shiru ATA   yayi  can  yace "Anya kuwa zan iya MB  gara  kawai a d'aura  auren zai fiyye min sauki akan na tunkareta  da batu na soyayya dan har abada bazan iya ba ."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Last free page

*AYSHA A BAGUDO*
AREWABOOKS
AYSHAABAGUDO
WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 10

"ai Kuma shine babban matsalar abokina domin yarinyar  itama ta kafe akan bata sonka amman nasan da zaka mata magana  da kanka zata iya amincewa kayi k'okarin  ka shawo kanta da kanka dan Allah ,ka kwantar da kai  ka shawo kanta  yarinya nan yar'uwarka ce jininka ce  sannan ita din mace  ce ,mace Kuma 'yar rarra..."
"ban son iskanci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login