Showing 45001 words to 48000 words out of 168608 words
.
damuwarta daman yayi aure tana son taga aurensa taga ya'yansa kamar yadda taga na sauran yaranta amman duk da haka bazata sakar masa fuska ba dan tasan halinsa kamar yunwar cikinta canzawarsa bai da wuya ya d'auki mintuna masu tsawo agabanta bata daga Kai ta kallesa ba sai ma ta mike zata bar masa d'akin , ya mike da sauri jikinsa na kyarma ya tareta dan sosai ya hango damuwa qarara akan fuskarta ya sake kamo hannuwanta duka cikin nashi , ta fizge a fusace tana watsa masa harara "sweetheart kiyi hakuri dan girman Allah wallahi zan aureta trust Adamcy zai aureta tunda yace zaiyi wallahi wallahi zan aureta Koda kuwa zan rasa rayuwata....."
hannunta d'aya tasa ta zare hannunta daga cikin nashi ta tsura masa idanunta "wallahi ban san Inda ka d'auko halinka ba , sam mahaifinka ba haka yake ba mutumin kirki ne, mahaifinka baya uhm baya uhm bare miskilanci , kullum cikin neman yadda zai kyautata mana daku ya'yansa da 'yan'uwansa yake , a kullum mahaifinku so yake ku zama na gari a rayuwa sannan masu jin kan iyaye da tausayi Allah ya duba bayan mahaifinku cikin kaf ya'yan mahaifinka Kai ne kawai ka fita dabam acikinsu da wasu halaiya Kai ma Kuma wannan halin miskilancin da zafin zuciyar ne illarka tun kafin ya rasu ya fad'a yace bashi ka d'auko ba .bari na fad'a maka gsky wannan halin naka sam ba nashi bane Kai ka san Inda ka samo abunka dan shi ba haka yake yi ba, dan ta mahaifinka duniya bazai tashi ba ,ga rikon addinin ga tsananin zumunci da sanyi hali ."
ga lokaci yazo daya kamata ka tattara biyayyar Uba da uwa ka had'a kayi min amman kullum cikin musguna min kake akan zance aure auren da kai ne kaji dadinsa , wallahi duk macen data samu miji irin mai halin mahaifinka ta gama dace a duniya da lahira ni kaina kullum kukan da nake yi kenan mahaifinka ya bauta mana ya sangartani sannan ya bautawa zumunci Allah ya jikansa yasa aljanna ce makomarsa ka canja idan zaka canza tana gama fad'ar haka ta fita ta barshi cike da zafin zuciya."
Jiki a sanyaye ya bar d'akin zuwa nashi yana shiga d'akinsa ya shiga zariya kwalkwaluwarsa ta shiga tunani , sai dai Kansa ya toshe ya cunkushe guri d'aya ya kasa tunanin komai ya zauna a bakin gado ya had'e hannunwansa duka a ha'barsa yana tunanin can byn wasu mintuna ya mike ya koma kan bedside ya zauna yayi shiru yana kallon d'akin ,sake mikewa yayi ya d'aura Kashi akan katifa yana Jin quna a ransa.
zuciyarsa na dokawa da matsanacin karfin gaske ya tashi ya nufi falonsa ya bud'e fridge ya d'auki kwalin stute superior cranberry me sanyi ya d'auki glass cup ya d'aura drink akan center table ya juya jiki a mace ya koma zuwa d'akinsa ya d'auko kwalin sigari rotimax ya dawo ya koma kan kujera ya zauna ya tsiyaya ruwan lemun ya d'aura kafafuwansa akan table tare da hard'esu guri d'aya ya Kai Karan sigari bakinsa ya kunna ya fara zuka a hankali yana fitar da hayaki "yaushe rabonsa da sha ? sam bazai tuna yaushe rabonsa dasha ba cike da izza itama sigarin yake zuka idan ba an fad'a maka ba bazaka ta'ba sanin shi din mashayin shigari bane koda yake baya sha sai idan ya tsinci Kansa cikin ' bacin rai mai tsanani " .
yayi shiru yana zuka sigari yana tunani mahaifinsa yasan da yana raye duk runtsi da hkn bata faru dashi ba , shiyasa yake son mahaifinsa Sosai wasu hawaye masu zafi suka zubo masa wanda rabonsa daya zubar da hawaye har ya manta a tsawon rayuwarsa amman yau ya tuna qalbinsa masoyinsa , ana cewa mutun yafi son mahaifiyarsa akan mahaifinsa shi dai sai dai
sonsu yazo d'aya a ransa , yasan soyayyarsu suyi kanka da juna ,mahaifinsa ya soshi har cikin ransa idan yana cikin damuwa sai ya fishi shiga damuwa , haka idan yana cikin farinciki ,daf da zai rasu da zarar ya kyalesa sai ya fashe da kuka alokacin hjy zulaiheart ke tmbyrsa dalilin kuka sai yace "ba kowa nake wa kuka ba sai Adam ,Ina jin tausayin rayuwar Adam bashi da dan'uwa kamar sauran mutane naso sun kasance su biyu ya samu abokin shawara "a she tabbas shi din abun tausayi ne bai ta'ba sani ba sai a tsakanin wannan lokacin da abubuwa suka kwa'be masa yan'uwansa mata sun had'e kai da mahaifiyarsa yasan da yana da dan'uwa nmj zai iya bin bayansa Koda kuwa zaa fi karfinsa ne hawaye ke gangaro masa kamar karamin yaro yana cigaba da busawa cikinsa hayaki ."
ranar a zaune ya kwana cikin tsananin tashin hankali Kash da Kashi damuwar auren dole da za'a masa da tunanin Nurul qalbinsa dan da zarar ya runtse idanuwanshi dan bacci sai yaga hoton princess dinsa tana gargadinsa akan auren da zai yi tana gudu tana binsa tana furta kar yayi aure ya barta .tsawon sati guda tunda daya amince da batun auren mryam bai sake zuwa Inda mami take ba yana d'akinsa yaki barin ya had'u da kowa dan gbdy fita ya fita ransa gbdy soyayyar princess ya dawo masa sabo fil ganin tunanin bazai bar kanshi ba yasashi mikewa daga kwance da yake tare da zura takalmi silifas ya fito ya shiga d'akin zanensa ya tsaya a gaban hotonta shiru yana kallonta kmr yayi mata mgn ta amsa fuskarta d'auke da murmushin da shine ya zanata ."
Hannu ya kai ya ja hoton a zuciye ya yaga yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa"A ina kike tsawon shekaru ?"a Ina zan ganki ?"kin hanani ganinki,kin hanani sukuni daga yau kin zamo tarihi gareni bazan sake damuwa dake ba ,bazan sake tunaninki ba zan manta dake arayuwata ,zan cire soyayyarki a zuciyata tunda baki da imani baki da tausayi ya fad'a yana wani irin ihu tare da daga hannuwansa duka sama "haaaaaaaa!!!
"Hauka yake sosai yana wargaza komai dake cikin d'akin tare da cigaba da yaga hotunan zanenta yana filinging dasu har da system dinsa da tsarkar wuyansa wanda zanen hotonta ne aciki , gbdy ya hargitsa d'akin yana watsi da komai har sanda mahaifiyarsa ta shigo hannunta rike da cup wanda yake d'auke da ruwan coffee, bedroom dinsa ta shiga bata gansa ba dan ita kanta ta kasa jurewa rashinsa na tsawon kwanaki , ganin baya ciki ta fito har zata fita ta jiyo sautinsa a hargitse dan haka ta shigo d'akin ."
ta tsay a bayansa ta cigaba da kallonsa cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa bai sani ba yayi zurfi cikin tsananin damuwa cikin haka ya sake d'aukar hoton zanen princess yay sama dashi sai akan fuskar hjy zulaiheart ta runtse idanunta da sauri jikinta na rawa kamar ance ya juyo ya ganta tsaye tana kallonsa cikin tsananin tashin hankali sanye da doguwar rigar shadda milk colour mai dogon hannu kyam idanunta a kanshi ta kasa daukewa ."
cikin sauri dunkule hannunsa ya naushi iska tare da durkushewa kasa ya soma tattara kayan daya hargitsa yana cewa "so..sorry sweetheart am really sorry cikin in Ina, numfashi ta sauke da ajiyar zuciya sannan ta zauna a bakin gado batare da ta ajiye cup din hannunta ba sai dai har lokacin idanunta na Kansa tana jin ciwo da zafin halin da yake ciki ,kusan minti biyar tana zaune tana kallonsa yana faman tattara d'akin yana mata sannu sannan ta fara magana a tsanake ." kayi hakuri Adamcy karka damu da wannan"
ya k'arasa kwashe kayan da yayi waste dasu zuciyarsa na zafi da quna "kana jina Adamcy ita rayuwa babu takurawa idan baka sameta anan ba wata Killa zaka sameta a aljanna ,yakamata ka gane hakan , karka shiga rud'ani idan an fad'a maka gasky illa ka dinga yarda dashi , komai na duniya babu sauki kmr yadda ka d'aukeshi sai an jajirce be a man Adamcy karka lalata rayuwarka akan yarinyar mafarkinka ."
"kamar yadda na sha fad'a maka ba kowani mafarki ke zama gaskiya ba , ta mike a hankali ta k'araso gurinsa ta riko hannunsa tayi taku biyu ta zaunar dashi akan kujera kwaya d'aya dake d'akin , madadin ta bashi coffee din hannunta sai ta fita gabanta na dokawa da matsanacin karfi dan nan duniya idan akwai abinda ta tsana to bai wuce damuwar tilon d'anta ba , sam bata son ganinsa cikin damuwa ko wannan auren ma zata yi masa ne dan dole saboda tasan muddin batayi masa ba zai iya kare rayuwarsa haka batare da yayi ba ."
ko cikakken minti biyar batayi ba ta dawo da gorar ruwa mai sanyi ta mika masa , babu mutsu ya kar'ba ya kafa a bakinsa bai cire ba sai daya shanye tasssss sannan ajiye yana sauke numfashi taja hannunsa zuwa bedroom dinsa yana biye daita yana zance zuci .ya yarda tabbas mahaifiyarsa na sonshi kuma gsky take fad'a masa akan yarinyar mafarkinsa sai dai ya rasa dalilin da har wannan lokacin ya kasa yarda iya mafarki ne kawai soyayyarsa zata tsaya ..."
Tana shiga d'akinsa ta zauna akan gado ya kwanta ya d'aura kanshi akan cinyarta yana mai Jin damuwarsa tana raguwa , a hankali ta Kai hannunta saman sumar kanshi ta fara shafawa tana mai sake jin tsananin son d'anta Ina ma zata ga wannan yarinyar a zahiri da babu abinda zai hana bata mallaka masa ita ta kowani hali ba ."
ta dade zaune har bacci yayi awon gaba dashi Sannan ta d'auke kanshi ta maida kan pillow ta lullu'be masa rabin jiki ta sauko ta qara masa karfin ac ta kashe masa wuta ta duka tayi kissing din foring head dinsa tana sake shafa sumarsa sannan ta nufi kofar fita tana rufo masa kofar ."
Koda ta koma d'akinta kasa runtsawa tayi tana tsaye akan ka'fafunta tana Kai wa Allah kukanta akan lamarin tilon d'anta sai da tayi sallah asuba sannan ta d'an kwanta Shima bata wani dade ba ta farka ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta sanya awarwaro da zobin ziniri ta feshe ilahirin jikinta da turaren humura mai sanyi kamshi hjy zulaiheart kenna Allah yayita da son kwaliyya da son kamshi tun tana matashiyarta har zuwa wannan lokacin da tsufa yazo mata ta fito zuwa babban parlour'nta tare da danna bell din bangaren masu aiki kafin kace me gbdy sun hallara sun zube a gabanta suna gaisheta cike da girmamawa. ta dubesu tare da amsawa cikin tsananin farinciki dan tana da sakewa da masu aikinta bata zalintarsu sannan bata son su zalinceta yadda take jin dadin zama dasu haka suma suke yabonta da yi mata fatan alkhairi a rayuwarta .
Fuskarta a sake ta bawa 'yan aikinta umarni abinda take bukata su dafa a ranar wanda zai zamo na sadaka ne kasancewarsa juma'a "yau za'a yi abincin sadakan da aka saba yi amman ina son a qara hannu sannan a had'a da wake da shinkafa Ina son a rabawa yara kanana suka amsa da "to" sannan kowace ta soma k'okarin mikewa "ke tabawa ..." wacce aka kira da tabawa ta tsaya sauran suka kama gabansu dan fara aiwatar da aiki "ki shirya breakfast wa sauran jamar gida idan kin gama ki hanzarta sanar dani ."
"shikenan hajiya itama ta fad'a tare da juyawa da sauri ." Hjy zulaiheart tana zaune mrym da nana hauwa'u suka shigo duk suka zauna suka sanyata a tsakiya kowacce hannunta empty babu Komai kamar Koda yaushe sun baro wayoyinsu na gado a d'akinsu d'aya byn daya suka gaisheta ta amsa cike da sakin fuska a fili tace "yau dai babu danne danne waya ko Kuma an gaji da rike wayar ne ?
sukayi murmushi nana hauwa'u tace " ai tun wuri nayiwa marsi kashedi muddin yaya adam zata aura ta saukakawa kanta akan shiga yanar gizo "wannan haka ne domin zai iya kawo rashin jituwa a tsakaninsu abinda bazan so faruwarsa ba kenan nafi bukatarta zaman lfy atsakaninsu.
ta Kalli bangaren da nana hauwa'u take zaune tace " ya batun shari'a da ake da yarinyar da ake zargi ta kashe mubina ne har yanzu na kasa fahimtar gskyr magana gashi Adamcy nata k'okarin shiga cikin maganar uncle jay ya hana ?"ai gsky gara da uncle jay ya hana wani shari'a za'a yi mami Abar ko waye da Allah kawai mubina dai ta rigada ta mutu bazata dawo ba komai za'ayi ,haka Allah ya qaddaro mata nata mutuwar zata rataya a wuyan wani inshallahu ruhinta na aljanna suka had'a baki gurin cewa" Ameen "
" mrym tashi ki shiga ki d'auko min wayata a daki na kira naji yadda ake ciki ta mike tsam ta shiga cikin bedroom din hajiya zulaiheart ta iske wayar akan katifarta ta d'auka tana duba fuskar wayar nan take gabanta yayi wani mummunar fad'uwa sakamakon idanunta daya sauka akan hoton ATA tayi shiru tana kallonsa cikin suit bakake idanunshi manne da farin glass yayinda fuskarsa ke d'auke da murmushin gefen baki wanda bai gama bayyana ba hakan km qara masa kyau yake , ta lumshe idanunta tana Jin wani iri a gbdy ilahirin jikinta ,ada sam bata jinsa aranta amman tun sanda yasa akayi kiranta akan batun soyayyarsa ta soma Jin wani Abu akansa komai nashi mai kyau tamkar shi ya hallici kansa ."
jiki a sanyaye ta Kai mata wayar ta amsa tana kokarin neman layin uncle jay byn sun gaisa take tmbyrsa halin da'ake ciki "mgn dai daya ce nace abarwa Allah abar ruhin diyata ya samu salama ".
"uncle jay taya zaka fadi haka byn kasan zuciyar sha'awanatu bazataji dadi ba ? "nasani amman yarinyar nan da ake tuhunma ba itace tayi kisan ba , tabbas makashin mutun d'aya ne da wanda ya kashe mubina da wanda ya kashe sadear mutun d'aya ne amman ba wannan yarinyar bace, ita dai ta taka tsawun barawo ne gbdy bincike ya nuna makashin da hannun hagu yayi kisan ita Kuma hadiza hannun dama take amfani dashi sam gbdy babu alamun sheidar hannunta ,yanzu haka an gama duk wani bincike ranar monday kotu zata wanke yarinyar Allah dai ya jikan mubina yasa ta huta "Ameen Hjy zulaiheart ta furta a fili tana mai tausaya masa "ko me suka yiwa wannan makashi da yake musu kisan gilla? "Allah masani "sun dan jima suna waya sannan sukayi sallama .
"Maryam ...!" mami ta kira sunanta gbdy ta tattara duk wani attention dinta zuwa gareta tana kallonta "Ina saka rai zuwa karshen satin nan za'a yi mgnr bikinku da Adamcy " gabanta ne ya sake fad'uwa kmr zai fasa qirjinta yayo waje "ya kamata ki sake kwarewa agurin girki da sauran abubuwan da yake da bukata dan haka daga yau kice zaki cigaba da kulawa da komai na bangaren abincinsa kinji ko ".
ta gyada mata Kai kawai tare da amsawa da "to !" hawaye na ciccikowa acikin kwarnin idanunta tayi saurin dennewa ta rasa dalilin da take tsananin Jin tsoronsa da tsoro aurensa."
" ki samu natsuwar zuciya ki tashi kije yanzu ki tmbayesa abinda yake bukatar ci a hankali ta mike jikinta na rawa kamar mazari ta nufi part dinsa
akan hanyarta ta tsaya tana daidaita natsuwarta sannan ta k'arasa kofar shiga falonsa tayi sallama ba'a amsa ba har ta juya taji sautin muryarsa yana cewa ",waye ne ? ta juyo da sauri "ni ...nice ta fad'a da sauri jikinta da bakinta na rawa "ke wa kenan ? ya sake tmby tayi shiru jikinta na cigaba da rawa hawaye na sake cikowa a idanunta ta rasa dalilin hawayen nata Jin shiru yasa ya taso da kyar yana mika daga shi sai gajeren wando army green iya cinyarsa da farar singlet wanda suka bayyana surar jikinsa a fili ake iya ganin kwantaccen sumar dake kwance a cinyarsa da qirjinsa haka kan nipples dinsa sai farin silifas dake sanye da kafafunsa da farin agogo da alamun aiki yake ."
A tsaye ya ganta a bakin kofar gbdy bata cikin haiyacinta a hankali ta d'ago ta kare masa kallo saboda kusancin da suka samu muryarsa a kasalance yace "ke lafiyarki tsayuwar me kike yi anan ya fad'a fuskarsa a murtuke"kayi hakuri please mami ce tace nazo na tambayeka abinda zaka ci a girka maka " ya tsuru mata Ido a zahiri yake iya hango yadda qirjinta ke bugawa wani dogon tsaki yaja a fili ya juya ya koma ciki ya barta tsaye . juyawa tayi tana daga kafafuwanta da kyar ta dawo parlour'n ta tsaya hjy zulaiheart ta dubeta "yaakayi me yace zai ci ?hannuwanta ta tsarke cikin juna sannan ta bud'e baki da kyar "wai a dafa masa komai."
mami ta fad'ad'a fuskarta da murmushin jin dadi , ita Kuwa nana hauwa'u sarai ta fahimci wani abu a tattare da marsi tasan sarai ba abinda yace mata kenan ba "to shikenan maza ki shiga ki dafa masa abinda yazo cikin tunaninki amman ki natsu sosai kinji. "ta gyada mata tana cewa "sister muje ki tayani "me .....?dan girman Allah ki rufa min asiri na tsira da mutuncina ke dai kije Allah ya bada sa'a kiyi kokari yayi dadi sosai ta k'arasa maganar tana kakkabe hannunta. "haba sister ki taimaka mana kin san fa komai tare mukeyi ,nasani amman ban da wannan wallahi bazan Saka hannu ba abinci yazo bai yi dadi ba ya had'amu yaci ubanmu" hjy zulaiheart tayi murmushi "Kai Adamcy hukuma kowa tsoronsa yake ji amman Kuma fa yana da sauki Kai Kinga mryam yi tafiyarki kinji duk abinda baki gane ba kizo ki tambayeni Simi Simi ta juya ta shiga kitchen kmr ta daura hannunta tayita kuka dan tasan muddin tayi kuskure sai yaci ubanta duk iya k'okarinta na dafa masa rice and stew bai ci ba ya wuce juma'a ."
*****
Da misalin karfe biyu na rana bayan an sauko daga massalaci hajiya zulaiheart da kanta ta fito zuwa haraban gidan ta fara rabawa yaran dake shigowa haraban estate din sadaka wake da shimfa acikin takeaway fari tare naira dari biyar biyar sababbin yayinda ATA ke tsaye daga can nesa kadan da inda take kunnensa manne da waya yana tafiya a hankali irin na jinin saurarata