Showing 96001 words to 99000 words out of 168608 words
sake durkusawa a wajen batare da tasan abinda zata fada ba, tana mai bakincikin irin kalar rayuwar da mahaifinta yayi a sanda yake raye, gashi ya bar duniyar amma basu huta ba , wannan wace irin rayuwa ce ? me yasa wasu yanuwa suke yin haka ? "tasani da ubansu mai arziki ne da duk abinda yayi babu mai tuna masu bare har a zagesu dashi ."
tsaki baba gali yaja yana cewa " Munafukar banxa sai anyi magana kisa mutane a gaba kina kuka, da ubannaku bai shaye shaye ba zaa fada? daya zauna da mutane lpy zaa ki fada ?kullum yana cikin d'auko mana magana gashi ya mutu ya bar iri an iya tujara iya tujara sauran shaye shaye .."
"Allah bazai sa ba ,baba ka daina masa mugun fata "me ya saura yaro ya zama dan daba ai sauran shaye shaye, habib zai yi magana maryama tayi saurin dakatar dashi tana cewa "walalhi karka sake cewa komai ai ga irin abinda ka haifar ko ?"ni dai na fada maku maza ku san ynd zaku yi ku bar mana gidanmu tunda gdn bana ubanku bane,"
maryama da tarin qunar zuciya da qunar rai take zubar da hawaye tafi karfin minti goma a durkushe sai daga baya ta koma inda tabar aunty ta durkusa kusa daita hawaye na zuba a idanunta Itama aunty hawayene take zubarwa a nata idanun tana jin ciwon abinda habib yake duk da tasan gsky yake fad'a masu amman bata só yana fadar duk abinda yazo bakinsu dan kome zai faru bazasu ta'ba sonta ba har yau tarasa me tayi masu mai zafi a duniya da suka kasa yafe mata sannan suka kasa danne tsanarsu akanta da yaranta ."
Habib ya kalli aunty ya kalli maryama itama duk kuka suke maryama kam har da shesheka tana rarrashin aunty " ku sani ku daina wulakantamu na kyale , kusani nadamarku ta kusan zuwa a nan kusa kuma munafurcinku ya kusan qarewa domin bazan sake yarda da iskancinku dan kuwa kun bari d'an zaki ya girma yayi girman da zai iya kasheku d'aya byn d'aya ,gidan nan kuma babu mai korarmu acikinsa sai dai a d'aga sa d'ungurungun dinsa a sakashi a kasuwa a siyar a bawa kowa hakinsa kowa ya kama gabansa"
"Ai kuwa baka isa ba wannan gidan ubanmu ne kai har ubanka ya gama iskancinsa ya koma ga Allah cima kwance ne bai da gidan da zaka yi wannan taqamar da kake yi "kai da ba cima kwance bane sannan bakayi iskancin ba ina naka gidan daka gida yake ? "sannan .."
"habib dan girman Allah .." saurin d'aga wa maryama hannu yayi ta hanyar dakatar daita " ki barni dasu heartbeat wallahi kowa sai na bashi size dinsa yau idan sunce basu da mutunci zan nuna masu ni d'an zamani ne , ya d'an tsaya yana kallonsu d'aya byn d'aya ,nan take ya hango tsananin tsoronsa da shakkarsa acikin kwayar idanunsu "oya kuna iya wucewa ku bar mu cigaba da rayuwarmu ko sai na fitar daku d'aya byn d'aya?".
A yadda suke kallonsa sun fahimci zai iya jansu ya fitar dasu kmr yadda ya fad'a dan haka aunty hassana ta kalli aunty "sai ki daina kukan munafurci tunda burinki ya cika kin haifa mana maseefa amman in sha allahu maseefar akanki zai qare tunda ya fara zama d'an daba tana gama fadar haka ta fice daga d'akin tana zage zage
aunty tayi saurin runtse idanunta tana jin zafin kalmar data danganta mata d'a dashi , itama aunty salma tace "shegu a haka zaku qare jiya iya yau babu cigaba ta nufi hanyar fita " da sauri habib yace "Ke ina naki cigaban da kika samu yake ? "Ke da ko sallah bakya yi , qazama mara sallah mai dotti kawai kije ki gyara tsakaninki da ubangijinki zai fiyye miki sauki akan shiga rayuwar wasu ."
shi kam baba gali cewa yayi "bilkisu Ina tarbiyar taki ?yau a gaban idanunki d'anki yake nuna min iyakata "to sai me dan na nuna maka iyakarka a gaban idanunta ? "kai da bakaji tsoron gaban idanunmu kake nuna rashin qaunar mahaifiyarta ba kiri kiri kake zaginta agaban idanunmu akwai abinda yafi wannan ciwo ? wallahi idan bakasani ba kasani yanzu abinda kukayi mata a da tayi hakuri ta shanye yanzu ta haifi d'an da zai kwatar mata 'yanci zan goge wannan tarihin idan ka cigaba da tsayuwa zafin jinina zai iya sa na d'auki takobin can na file maka kai dashi ko na raba katon kan nan naka gida hud'u idan yaso nima akasheni salin alin baba gali ya fice batare da ya sake cewa uffan ba."
Yana fita habib ya qaraso inda aunty da maryama suke durkushe suna kuka "cike da girmamawa yace "ku daina kuka in sha allahu ku daina kuka acikin gidan nan , kun daina damuwa matsawar ina raye zan tsaya maku , zan kula daku da zarar na gama karatu zan ...."bana son jin komai daga bakinka habib na fahimci kana bukatar na bar muku gidan nan shiyasa ka kirkiro abinda za'a koreni daga cikinsa tana gama fad'ar haka bata tsaya jin abinda zai ce ba ta mike ta shiga d'akinta ta d'auko mayafinta kawai ta fito zata fice ta bar masu gidan ."
Atare maryamah da habib suka sha gabanta cikin tsananin tashin hankali "haba aunty ya zaki mana haka ?kiyi hakuri aunty hakika habib bai kyauta ba amman karki tafi ki barmu ."maryama dan'uwanki baya bukatata acikin gidan nan yana bukatar na tafi na bar masa filin gidan nan ya cigaba da rayuwa ta qarasa maganar tana zubar da hawaye ta tabi gefen maryama zata raba ta wuce ."
habib ya riko mata hannu "kiyi hakuri aunty ki fad'a min abinda kike bukata nayi miki alkwarin wallahi zanyi kisani idan kika bar gidan nan bashi da wani amfani a wajenmu "yana da amfani mana tunda gashi kayi son ranka kasa an zageni anci mutuncina anci na iyayena ai gara na kama gabana tunda zamana acikinsa babu abinda yake haifa min sai damuwa da bacin rai ".
Kuka ya kufce ma maryama ta d'an rufe fuskarta da tafukan hannuwanta saboda tuttukin da zuciyarta Ke yi "kai ma kasan abinda kayi ba daidai bane har ka iya cire hannu zaka doki baba gali wallahi baka kyauta ba tunda kasan halinsu to meye amfani tsayawa kana fad'a yana fad'a "ki fahimci wani abu heartbeat wad'an nan mutane basa qaunarmu ,babu abinda Ke cikin zukatansu sai tsanar mu " tunda mun san halinsu sai mu kiyaye abinda zai kawo sa'bani dasu shima kukan yake yi "suna nuna mana bambamci akan ya'yansu ,suna quntata mana suna da fuskar gazawa garemu musaman akan ya'yansu yanzu laifin me kikayi ma aunty salma ta shigo tana zaginki ?"maryama bata sake cewa komai ba illa ta cigaba da kukanta haka ma aunty batayi magana ba illa qoqarin zare hannunta da take cikin nashi ."
"na tuba aunty bazan sake ba ki fad'a min abinda kike so ,nayi miki alkwarin bazan sake ba ya fad'a yana zubar da hawaye itama ta goge hawayen dake zuba akan kuncinta ta cigaba da mgn "daga yau babu ruwanka da kowa acikin gidan nan duk abinda zasuyi ko zasu fad'a akanmu ka kawo ido kasa masu , kai ba zagi ko dukana zasuyi babu ruwanka a rashin yace ba dai duka ba amman a zahiri yace "to aunty an gama ."wallahi abinda kayi yau din nan ba irin tarbiyar daaka bamu bace "in sha allahu bazan sake ba heartbeat ki bata hakuri bazan sake ba kamo hannun aunty maryama tayi suka koma kan kujera mai zaman mutun uku da duk ashon jiki ya batattake suka zaunar daita tare da sakata a tsakiyarsu suna bata hakuri ."
Kamar yadda mlm yahuza ya sanarwa nafisa byn sallahr ishai zai zo sai ga yaro yana sallama da maryama lokacin suna zaune a falon aunty ta dubeta amman ita ko ajikinta sakon da yaro ya fad'a aunty tace "maryama bakiji bane ?ta d'an dubeta ta share yaron ya tsaya yana jiran abinda zaace "to sai ki tashi kije "ina kenan aunty?"bakaji ana sallama daita bane "gsky babu inda zata ban san dalilin da yasa da mutun yazo nemanta ba sai ki bata damar fita baki san ko waye ba mazan da duk 'yan iska ne da zarar sun fara zuwa kamar abun arziki da zance aure ya shigo sai su gudu su barta ni gsky babu wanda zai sake zuwa ta fita ."
"Maryama tashi Kiyi maza kije ki dawo saboda ki samu ki d'an huta karki dade duk da nasan ba dad'ewar zakiyi ba ,ina dalili da zakace bazata ba kai zaka aureta ?ya marairaice murya "bani zan aureta ba amman at least aunty ki duba lamarin nan kawai suzo suna 'bata mata lokaci da dagula mata lissafi "Babu wani dagula lissafi a haka allah zai kawo mata wanda zai aureta ,ina son kasan wani abu habib duk cikin masu zuwa neman auren maryama babu mijinta acikinsu , duk lokacin da mijin yazo to babu makawa sai anyi domin babu mai aurenta matar wani kai yaro je kace gata nan zuwa yaron ya juya da sauri dan daman amsar da yake jira kenan zata fito ko kuwa bazata fito ba ."
maryama ta tashi ta shiga d'aki dan tasan ko waye yazo ta d'auki hijab dinta ta fito "amman dai ni aunty a wajena ba daidai bane ,ni fa kamar mahaifinta ne a matsayina na namiji acikin gidan nan amman me yasa sai a dinga nuna min iyakata acikin gidan nan , na fiku sanin halin mazan wannan zamani babu komai acikinsu sai tsabar yaudara ".
Aunty ta kallesa saboda yadda yake maganar tamkar wani babban mutun tace "wai har guda nawa kake habib ?" duka shabakwai gare fa kawai dan allah ya baka jikin girma "ni dai gsky ban yarda ta fita koina ba girgiza kai aunty tayi tana kallon yadda yake kamaninsa yake canzawa a kullum yana komawa na mahaifinsa tun ba yau ba kusan kowa yana fad'in kamanin nasu "gaskiya habib kar ka zama mai hana neman auren ."
tsayawa maryama tayi tana kallon fuskar habib daya had'eta tmkr ance masa idan ta fita guduwa zaa yi daita ,ahankali ta kira sunansa "after dad "
"Karki wani kirani da wannan sunan dan dani din ina da wannan matsayin da za'a dinga bin umarnina " ta qaraso ta zauna kusa dashi ta riko tafin hannunsa cikin nata tana kallonsa da idanuwanta da suka canza kalla "after dad me kake so dani ?"ta fad'a tana kallon yadda shima ya zuba mata ido yana kallonta ."
"Abinda nake so duk wanda yazo karki qara fita koina idan abinda ake miki acikin gidan nan baya damunki ni yana damuna ,sau nawa kina yi saurayi agidan nan a karshe ko ya gudu ko a kwace miki shi acikin gidan nan ?to ai duk ba mijinta acikinsu ne ,no no aunty akwai cutarwa aciki "to nufinka yanzu haka zata zauna babu mai zuwa wajenta ?"allah aunty dasu dinga 'bata mata lokaci gara ta zauna haka idan na girma na qare karatuna zan mata komai zan siya miki gida da mota itama heartbeat zan siya mata zan kai ku aikin haji ,kai har sojoji zan daukar maku escort duk inda zaku su dinga rakaku aunty da maryama basu san sanda murmushin jin dadi ya bayyana akan fuskarsu ba "shikenan after dad bazanje koina ba domin kai din tmkr uba ne a gareni "yauwa heartbeat sai yanzu naji hankalina ya kwanta muyi zamanmu ."
aunty ta kallesu ta girgiza kai "wallahi wannan ba rayuwa bace kin wani zauna ya tasaki gaba yana miki zakin baki ,wallahi ki daina biye masa Ke macece dole kina bukatar Kiyi aure shifa nan gaba kad'an zai ce zai yi aurensa dan wannan da son girman tsiya nasan .."no no aunty karki hadamu da heartbeat babu wani aure da zanyi na barta idan dole sai tayi aure ni zan kawo mata miji wanda zai dinga kwantar mata da hankali duk ranar da yayi gangancin ' bata mata rai na zage naci ubansa ".
"Lah lah lallai habib abun naka babba ne "allah aunty sai ma ya cika qaidodina sannnan "wannan ai gara kuje kuyi auren kotu ku huta maryama tai murmushi tana jin dadin yadda dan'uwanta ke tsananin qaunarta "babu kotun da zamu amman dole a kular min da heartbeat ko kuwa a tashi mutun aiki "uhm kaga tashina ta mike tsaye " bari naje na bawa baba gali da hassana hakuri na dawo ."
"haba aunty ai komai ya rigada ya wuce wani hakuri kuma zaki basu salon su samu damar ci miki mutunci "? A'a sai naje zaman lafiya yafi zaman dan sarki ina zan iya dasu gara dai naje ."Yauwa aunty kije ki basu hakuri wannan ai ba komai bane wata rana sai labari kai ma ya kamata ka bita kabasu hakuri wani irin kallo ya watsa mata yana cewa "allah kiyaye ai ni .."sai kuma yayi shiru sakamakon tuna alkwarin da yayiwa mahaifiyarsu ."
"ai babu abinda zai sa naje da habib sai ya qara dagula lissafi sunan wani police a isokoko ni na wuce sai na dawo "to aunty sai kin dawo tasa kai ta fice daga dakin ta barsu suka cigaba da hirarsu mai cike da kulawa da soyayya shi kam mlm yahuza tsawon mintuna nan duk yana tsaye yana jira Fitowar maryama ya duba agogon dake daure da taintsiyar hannunsa yaga lokaci ya tafi daman kuma yaron daya aika ya sheida masa komai dan haka a natse ya juya sai dai ya kudurce aransa zai dawo gobe."
Ahankali aunty take tafiya tana tunane tunane abinda zatace idan ta isa gaban baba gali a natse tayi sallama cikin bangaren nasu basu amsa mata sallamar ta ba dan haka taji gabanta ya shiga faduwa kafin ta kai ga yin wata magana taji aunty salma ta hau surfa mata maseefa kamar kullum "me ya kawo bangarenmu "ba komai bane hakuri nazo baku akan abinda habib yayi ,ya gama ci mana mutunci a gabanki shine dan munafurci kika kwaso jiki bayarwa , shegiyar munafuka kin wani marairaice fuska bayan kin gama zuga d'anki yayi mata walima ta uwa da uba zaki wani kwaso jiki to yanzu hakurin me kika zo bamu ?".
Numfashi aunty ta sauke ta samu waje ta zauna kusa da baba gali da ko kallon inda take bai yi ba a tun sanda ta shigo "kuyi hakuri gabadayanku in sha allahu nayi maku alkawarin wannan shine karo na farko da karshe da hakan zai faru ...."dakata bana son jin komai daga bakinki dan duk abinda zai fito daga cikinsa karya ne ni dai abinda nake buqata "ki dauki yayanki ku bar mana gidanmu tunda ussein yake raye bai tsina mana komai ba sai tujara gashi nan ya barwa dansa tsaraba har kamar ni wannan yaron zai dinga gasawa magana kuma a gabanki kina kallo yaron da ya kamata kiyita dukansa har sai kin kusan auna shi lahira amman kika zauna dan tsabar son ya'ya kina kallonsa yana surfa mana zagi ta uwa da uba ai wallahi bazai yuwu ba ."
Sake durkushewa tayi Kmr zatayi kuka batare da tasan abinda zata sake fad'a ba sai dai ita kanta a halin yanzu tana mai bakincikin hada zuria dasu tsaki aunty salma taja tana cewa "munafukar banza munafukar wofi sai anyi magana ki wani durkushewa mutane "ni dai ba wani tashin hankali nazo dominsa ba nazo ne dan na baku hakuri dan nasan danku bai kyauta ba "ni wannan yaron ba d'a bane domin kuwa d'ana bazai min haka ba hakuri aunty tayita basu da kyar baba gali yace komai ya wuce amman tajawa habib kunne aunty salma dai ce taki hakura ta mike tana masu sallama "sai da safenku allah kuma ya huci zuciyarku babu wanda ya kulata acikinsu har ta fice zaginta aunty salma take cikin tsananin tsana ."
Daga bangaren baba gali na aunty hassana ta shiga itama dai tujara tayi mata ta uwa da uba kaf danginta babu wanda ta bari bare iyayenta zuciyarta tayi nauyi kamar an d'aura mata dotse da kyar ta yunkura ta mike ta fito tana tafiya zuciyarta na kokawa. a inda aunty ta fita ta bar yaranta anan ta dawo ta samesu zaune suna hira "har kin dawo aunty ?suka had'a baki murmushi tayi tare da d'aga mata kai alamar" eh! my princess na dawo ".
"Yaya kuka qare fatan sun hakura "Eh to sun hakura my princess!ta fad'a zuciyarta cike da raunin kuka dan shi take bukatar yi a halin da take ciki shi kam habib bai ce uffan ba illa ya cigaba da sauraronsu"my princess Kinga dare yayi bamu samu girka komai a gidan nan ba ni yanzu ban san me zamu dan girka muci ba "wallahi aunty amman bari naje wajen Ummah watakilla bazamu rasa abinda zamu ci ba maryama ta fad'a idanun habib yana kanta "ko zaka raka ni ne? ta fad'a tare da miqewa..."Muje ! kawai abinda ya fad'a kenan maryama tayi murmushi "makalema kawai "kima ce bita zai zai ki huta gbdy muje suka jera ."
Suna fita suka had'u da yaya sadam ya fito daga side d'in din baba gali zai shiga side din ummah cike da farinciki habib ya qarasa suka gaisa! "A she rabon mu had'u ne yaya yasa heartbeat tace nayi mata rakiya ."ai ko baka fito ba yanzu nake shirin zuwa tambayarka a wajen aunty !Ya mika masa hannu ya kwana biyu ina fata dai komai lafiya? "Lafiya lau habib kawae aiki ne ya boye ni 2days ya karatu ?yace "alhamdulillah.!"
maryama ta bude baki da kyar ta gaishesa ya amsa mata cike da sakin fuska "Lafiya su aunty maryam"ji tayi kunya ya kamata da kirata aunty da yayi ! Ya gida da karatu ?Alhmdllh! ta fad'a cikin jin kunya"kema dazu nake tambayarki wajen Ummah take bani labari mai dadi lallai kin fita zakka acikin matan gidan nan kin tsaya kinyi karatunki yadda ya kamata allah yasa muji sakamakon mai kyau you're the best maryama duk nmj daya sameki a matsayin mata baqaramin dacewa yayi ba Allah yasa sawa karatu albarka dad'i maryama taji sosai dan duk cikin yanuwanta sadam ne kawai sai