Showing 123001 words to 126000 words out of 168608 words
masu ."
Washgari baba babba ya tara manya gidan tun daga kan kannensa har zuwa kan yayyansa na sama dasu dana kasa dasu dake esatate din acikin dakin na musamman da suke ganawa a duk sanda abu makamancin hk ya faru ,ya dade yana bayanin abinda ya faru a daren jiya tare da jan kunne da nasiha mai ratsa zuciya a karshe yace zaa yi bincike duk wanda aka samu da sa hannusa zaa mikasa hannun hukuma dan maganar da nake daku yanzu haka nayi report wajen police har na mika masu wukar domin a fara bincike duk hankulansu a tashe mrym kuwa har wanna lokacin kuka take aunty shahida da khadija kaf yayan mami tun safe suka yiwa gidan diran makiya jama'a kuwa sai zuwa jaje suke yi wa mami haka ma iyayen maryam sun kira yafi sau babu adadiΒ wuni ranar haka mrym tayi shi cikin dakin mami cikin tsananin tashin hankaliΒ ."
Bayan kwana biyu da faruwar lamarin da misalin Karfe hud'u sauran wasu mintuna mr ata ya shigo estate dinsu drivenshi na tsayawa batare da bata lokaci ba masu kula da lafiyarsa ta hukumar dss suka fito da sauri kafin ma su bude masa ya bude ya fito yana gyara zaman rigar jikinsa kai tsaye masalacin dake cikin esatate din ya nufa domin gabatar da sallah bayan ya idar da sallah ya nufo gidansu nana hauwa'u da da maryama na zaune idar da sallar su kenan sai ga diyana ta shiga hira suke kadan kadan mrym na bawa diyana labarin abinda ya faru daita "amman Kinsan wani abu diyana duk yadda muke da nuzla bangata ba kuma nasan taji abinda ya faru dani har cikin daki aka biyoni zaa kasheni amman ta kasa zuwa tayi min jaje tunanina ni kuwa laifin me nayi mata? wallahi har da kwalla nayi na rashin zuwanta saboda banyi tunanin hk daga gareta ba ."
"gsky da mamaki kuma kinga ai ba haka take ba tana da kulawa da mutane most especially idan abu ya sameka na farinciki ko akasinsa amman Kiyi mata uzuri wata killa tana nan hanyar zuwa tunda duka yau kwana biyu ne da faruwar abun ,wannan gsky ne nuzla bata da haka amman baku lura a tsakankanin lokacin nan ta dan canza ba ?inji cewar nana hauwa'u"eh ta canza kam sosai ko Kinsan damuwarta ?ko daya ban sani ba wallahi na dai kula ta canza ko a yanayin jikinta zaki fahimci akwai abinda ke damunta mrym tace " to koma meye allah yafi mu sani Allah ya yayewa kowa damuwarsa Suna zaune mr ata ya shigo gbdy suka masa sannu da dawowa ya amsa Kmr yadda ya saba aciki sannan ya kalli auta yana tmbyr mami "ke auta ina sweetheart. ? "tana ciki ta shiga tayi sallah yana gama ji ya haye sama suka cigaba da hirarsu ."
Bai sauko ba sai bayan awa daya sanye da shirt ajikinsa da wondo ficewa yayi bai tsaya akoina ba sai gidansu nuzla ya tmbyi mahaifiyarta ta sheida masa tana dakinta bata jin dadi a natse ya nufi kofar dakinta ya tura kofar ya shiga tare da sallama akan lip's dinsa tana ganinsa ta mike zaune tana ware fararen idanunta akanshi tayi qoqarin ta sakashi cikin nashi idon sanda yake takowa zuwa inda take tana masa duban mamaki dan bata ta'ba expecting zata ganshi har cikin bedroom dinta ba ."
sosai ya dauki hankalinta yayi wani fresh yayi qara kyau kaman zane ta koina ya hadu matsalar dai shi din mugun miskili ne sai dai hakan ma qara masa kyau yake ahankali ya janye idanunshi acikin nata ya maida dakin yana qarewa koina kallo "Lafiya
yaya adam da wannan zuwan naka na bazata ?"
Shiru yayi yana cizan lips dinsa na kasa kafin daga bisani yace "bai kamata kiyi min wannan tmbyr ba domin kuwa Kinsan dalilin zuwana "ya fad'a alokacin daya jingina jikinsa da mirrow dinta yayi crossing leg's dinsa ya rungume hannuwansa duka a saman faffadan qirjinsa yayi da idanunshi ke kallon zara zaran yatsun kafafunsa."
da kyar ta mike daga zaunen da take tana cewa "ni ban san abinda ya kawoka ba idan dai ba kazo da niyyar karbar soyayyata bane amman kafin nan me zan kawo maka ?"yayi mata banza zuciyarsa na zafi jin yayi shiru km ta rigada tasan halinsa tayiΒ tunanin ta kawo masa ko ruwa ne har tayi taku biyu taji ya fixgota da karfi yana watsa mata wani kallo da idanunshi dake cike taf da bacin rai gbdy taji ta fara muzanta daga kallon da yake mata taji gwiwarta tayi sanyi ."Idanushi ya tsareta dashi yana kallonta yayinda gabanta ya fara faduwa tana adduar allah yasa ba wani laifi tayi masa ba ."
Sai daya gama kallonta sannan ya watsata akan katifa ta sauka da karfi sai da hantar cikinta ya kada still bai dauke idanunshi akanta ba ,nan take ta soma sheshekan kuka sannan ta fara mgn "yaya idan wani laifi nayi maka ya dace ka fad'a min amman wannan kallon naka na hargitsa min lissafi .kallonta ya cigaba da yi bai ce uffan ba har sai data gama ,cikin izza ya motsa labbansa "nasan kin san abinda kikayi sannan kuma kinsa shine dalilin zuwana " cikin mamaki da tsoro take kallonsa ya tsareta fes da idanunshi yana mata kallon banza ."
ranshi a bace ya daidaita tsayuwarsa yana cigaba da kallonta kallon dake qara kashe mata jiki da tsoratarwa "hakika kin tabbatar min da abinda kika turo min a kwanaki uku da suka gabata na zakiga byn mrym , kinyi yunkurin kasheta Kmr yadda kika kashe mubina dan tace tana sona ko?"Idanuwa ta zaro gabanta na faduwa a fili tace" na shiga uku tana dafe qirjinta tare da nuna kanta "ni din na kashe mubina sannan nayi yunkurin kashe mrym ?wani kallon banza yake mata yana jin Kmr ta raina masa wayo ne babu abinda yafi tsana sama da karya yafi son duk abinda ya tmbyeka ka fad'a masa gsky ta haka zaka samu sausauci daga garesa "ban kashe mubina ba me yasa zan kasheta ?"wallahi ban aikata komai ba sannan banyi yunkurin kashe mrym ba tabbas na tura maka sakon zanga bayanta amman wallahi ban aikata hakan ba ,amman ina da niyya to waye yasan da wannan shiri nawa da har ya rigani aiwatarwa?
"Lafiyayyen mari ya zuba mata yana cewa "ni kike wa wannan tmby ?nan take ta rude ta dafe kuncinta inda marin ya sauka abinda yafi damuna kashe mubina da kikayi me tayi miki nuzla ?kuka ta saka mashi tare da durkushewa kasa "wallahi sharri ake son min dan ban san komai akai ba .wani kallo ya watsa mata sannan ya juya mata baya "nasan tabbas kece kika kashe mubina dan hatta wukar da kika kasheta kinyi kuskuren barinta a yunkurin kashe mrym ."
"Da mrym kika kashe wallahi bazai ta'ba damuna ba saboda neman kai nake daita ,ni da zaki kashe min ita amatsayinki na yartaada kafin ta zama mallakina lallai ni kuma da nayi akawarin aureki .nuzla ta sake rudewa ta gigice ta soma jan gwiwowinta ta qaraso inda yake tana kuka "na baki kwanaki goma masu zuwa ki kashe min mrym kafin ta zama mallakina batare da an samu wata hujjar cewar kece kika aikata hakan ba , sannan kada asirinki ya tono ni kuma zan aureki idan kuma kika gagara kasheta har lokacin dana baki ya cikaΒ ni kuma nayi miki alkwarin zan damkaki a hannun hukuma a kwatarwa mubina hakinta kin dai sani idan hukuma ta tabbatar da kece kika kasheta karshenki biyu ne, kisa ta hanyar rataya ko kuma zaman gidan yari na har abada muddin rai kenan yana gama fadar haka ya soma qoqarin ficewa daga dakin .."
Mmn sudais
ππππππ
MAR'ADAMS
ππππ
ππππππ
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 23
Ji tayi qasusuwan jikinta suna barazanar kasa riketa , lokaci guda zuciyarta na barazanar tarwatsewa bata san sanda ta kurma ihu da iyakacin karfinta tana d'aura hannuwanta duka bisa kanta mahaifiyarta hajiya salema ta shigo d'akin da sauri tana dubanta cikin tsananin kad'uwa da tashin hankali, zata iya cewa yanayin data ganta ciki bata ta'ba ganinta cikin irin yanayin ba sai yau wanda shine karo na farko da taga wannan yanayin atare daita , yanayi ne mai cike da firgici da tashin hankali."
Rawar da jikin nuzla yake ya qaru hjy salema ta matso kusa daita ta soma girgiza nuzla wacce ta koma tamkar mutun mutumi a wajen "nuzla nuzla!! lafiya what's wrong with you ?!me ke faruwa dake ? me adam yayi miki kike kuka haka ko ince laifin me kikayi masa dan nasan ruwa baya tsami banza tunda naganshi nasan akwai abinda kikayi masa ? ta jera mata tmbyoyin a rud'e tana riko hannunta cikin nata. nuzla tayi shiru tana wani irin kuka mai d'aga hankali "ki min magana mana ko hankalina zai kwanta ? ta mike a matukar firgice tana duban hjy salema sai dai bata iya amsa mata tmbyoyinta ba dan bata da amsar da zata bata a halin da take ciki ,dan haka ta cigaba da kallonta da rinannun idanunta dake cike da ruwan hawaye kafin daga baya ta fara kuka wiwi tana safa da marwa acikin d'akin hajiya salema na biye daita cikin tsananin damuwa ."
" tabbas idan har hasashe da yarda yaya adam akanta ya tabbata a zuciyarsa to fa tabani ta lalace ta shiga ukunta dan wallahi tasan zai iya aikata fiyye da abinda ya fad'a mata .hankalinta ya sake matukar tashi tabbas tayi niyyar aikata hakan amman daga ita sai Allah'n daya halicceta da zuciyarta da kuma yaya adam ne kawai suka sani ,"ba itace tayi kissan ba to waye yayi ?ta furta hkn a qasan ranta tana furta "wayyo allah na shiga uku ni nuzla ta ina zan fara ? waye yake son jifa rayuwata cikin maseefa ? da wani irin sauri ta nufi kofar fita hjy salema ta biyota tana kiran sunanta amman ina bata tsaya ba tunin ta kai kofar fita daga gidan ta biyo bayan ata ."
ya d'an yi nisa amman bai kurewa ganinta ba dan tana hango bayansa daga inda take ta kira sunansa da karfi cikin tsananin tashin hankali , shi kuwa ata yana jinta amman yaki waiwayowa ya cigaba da tafiya kmr baya son taqa qasa ."ta qara sauri sosai kamar zata hantsila , kallo d'aya zaka wa nuzla ka fahimci bata cikin haiyacinta da natsuwarta ."adaidai bakin kofar shiga side din mami ta iske shi tare da shan gabansa gif haka nuzla ta zube qasa bisa gwiwowinta agabansa idanunta na qoqarin sake kawo ruwa cikin wani irin murya mai gauraye da tashin hankali hade da rudani take furta "yaya ka taimakeni ka tsaya ka fahimceni karka yanke wannan hukuncin wallahi ban san komai akan lamarin nan ba."
ya tsura mata tsumammun idanunshi kafin ahankali ya soma magana cikin izza "taya zan iya yarda da hakan bayan kece da bakinki kika furta hakan kuma kika aikata ? "wallahi wallahi !! idan ka yarda da rantsuwata bani bace sam sam ban aikata abinda kake zargina akai ba hasalima ni yau tsawon kwanaki goma sha biyar kenan kafafuwana basu taka haraban gidan nan ba ina kwance bani da lafiya ."yadda take maganar zaka fahimci tana cikin rud'ani da tashin hankali kamo kafafuuwansa tayi cikin kuka tace "please yaya try to understand me bazan ta'ba aikata hakan ba kawai dai na fad'a maka haka ne dan ka tausaya min ka aureni amman ka yarda dani ban san komai akai ba ."
"Bazan ta'ba yarda dake ba domin nasan zaki iya aikata taadanci makamancinsa koma fiyye dashi a halin yanzu ba wannan magiyar bace ta kamaceki ki fara shirin yadda zaki aiwatar da aikin dana baki idan kuma zaki tonawa kanki asiri nΓ© tun yanzu bismillah ." jikinta da muryarta na rawa tace "baxan damu ba koda asiri zai tono dan ban aikata komai ba bare naji tsoron fallasa kuma Allah shine sheidata ban aikata ba amman zaka iya bincike akan wanda ya aikata abinda kake zargina akai amman ni bani bace kuma duk inda zaa kaini zan tsaya ne akan gskyta bazan ta'ba karban laifin da bani na aikata ba ."
a natse ya soma daga kafafunsa dan wucewa ya barta dan ya gaji da jin sautin muryarta da kukanta yana shiga kanshi over ,yaga tana qoqarin jan gwiwowinta domin biyosa ya kalli securities din dake tsaye a wajen "karku sake ku barta ta shigo ciki "okay yallabai an gama ya shege ciki ya barta durkushe tana kallonsa tmkr wani sabuwar halittta a wajenta ."mikewa tayi tare da cure hannayenta waje daya tana bugawa da juna bata ta'ba shiga tashin hankali da nadama irin ta yau ba har ga allah bata san haka abun zai rikice ya dawo kanta ba ta dauka idan ta fad'a masa haka zataci bulus ne ashe masefa zai zame mata ashe bazataci bulus ba wahala zata sha ?"me yasa batayi shiru da bakinta ba ?me yasa ta gaza hakuri har sai data fito ta fad'a masa shirinta gashi ta kai kanta ta baro ? kaicona ni nuzla bakina ya janyo min matsefa na tarowa kaina bala'i da kaina ta sauke ajiyar zuciya tare da furzar da zazzafar iska daga bakinta ."
"Ai kam wallahi sai dai yayi mata duk abinda zai mata idan ta kama ma ya mikata ga hukuma amman bazata ta'ba aikata abinda yake bukata ba sannan bazata ta'ba karban laifinta ba sai dai idan kasheta zaayi akasheta ta yarda amman bazata cika masa burinsa ba, shi idan har da gaske yake baya qaunar maryam din ya aikata lahira da kashi ba sai ya had'a daita ba da sauri ta juya ta soma tafiya kamar zata tuntsura kasa sai kace mahaukaciya ta shigo gidansu inda ta iske mahaifiyar tsaye cikin zullumi ."
Tana ganinta ta qaraso gareta tana tmbyrta nuzla ta zauna akan kujera jagwaba tana fidda numfashi duk tmbyr da mahaifiyarta take mata bata kulata ba illa hawaye dake zubar mata "wani laifi kikayi wa adam ?tayi shiru kawai batare da tace uffan ba hjy salema tace "to da alamun laifin mai girma kikayi masa yasa har ya biyoki "kamar ta bayyanawa mahaifiyarta halin da take ciki kafin ya damkata hannun hukuma a kashe mata ita a banza a wofi amman ta kasa dan gaskiya bazata iya ba domin tasan irin qaunar dake tsakaninsu kasancewarta auta a wajenta ,banda kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun babu abinda take furtawa tare da dafe kanta dake mata wani irin sara Kmr zai rabe gida biyu hjy salema ta barta ta koma dakinta dan ta fahimci laifi tayi masa mai girma wanda yasa ta kasa furta wa ."
Nuzla ta rufe idanunta gam tana jin yadda maganarsa ke tashi acikin kunnuwanta da zuciyarta so take ta sakawa gangar jikinta hakuri da jarumta har zuwa waadin daya dibar mata ya cika amman ta kasa bata jin zata iya, a halin yanzu ma ba mgnr aurensa bace a gabanta illa mafuta lallai tana bukatar mafuta ta mike tsaye tana zariya acikin parlour'n "ko na gudu ne na bar gidan ne ?ta tmbyi kanta ,gudunki bashine mafuta ba nuzla hakan ma qara min laifi zai yi idan kuma maganar ta fito shikenan kin tabbata mai laifi a wajen kowa dakinta ta shiga tayi zaman dirshan tana saqa da warwara ni dai wallahi nasan bani na kashe mubina ba haka zalika banyi yunkurin kashe mrym ba ,"shin ta ina zan fara ?ni kaina ina bukatar gano wanda yayi hakan , ta lumshe idanunta tana tunani dan dole tayi bincike dan gani wacce tayi yunkurin kashe mrym kuma ko wacece acikin estate dinsu take km itama tana son adam ne Kmr yadda take son shi jikinta ya dauki zafi sosai ."
Zaune mr ata yake akan kujera kushin dake d'akinsa yayi zurfi cikin duniyar tunani yayinda hankalinsa gabadaya ke sake tashi a duk sanda ya tuna da maganar aurensa da mrym sai ya dinga jin hankalinsa na sake tashi , yayinda a kullum ya daura kwayar idanunshi akan yarinyar sai ya dinga jin tsananin tsanarta ,shi da kansa ya kasa sanin takamaimain dalilin dayasa yake jin tsananin tsanarta haka dan bazai ce dan rashin tsawonta bane da kuma kasancewar ta fara bane ya janyo haka yanayinta dai ya taimaka wajen tsanarta ne ,duk yadda yake qoqarin yakice tsanarta da sanyata ko kadan acikin ransa zuciyarsa taki amince da zamanta a tsakaninsa tafe tafe har tunaninsa ya kawo kan zanen wukar dake ajiye akan bedside dinsa wanda aka kashe mubina daita kuma ake qoqarin kashe mrym dashi shine ya zana ya ajiye a wajensa kafin a mika wukar ga hukuma ."
ahankali ya sauke naunauyen ajiyar zuciya ya sake gyara zamansa sosai akan kujerar da yake zaune tunanin duniya yayi akan wacce tayi karfin halin shigo masa gida da taadanci , baya da tabbacin ko nuzla ce domin kuwa har ya gama kallon mai shi ta camerar d'akinsa bai iya gane ko wacece ba zargin nuzla kawai yake bisa yanayin jikin wacce ta shigo da kuma furucin bakinta amman bashi da tabbas akanta bincike ne kawai zai tabbatar masa daita ce ko kuwa wata ce dabam ta kashe mubina km tayi yunkurin kashe mrym "idan wata ce dabam meye dalilinta ?meye hujjarta ? me yasa take yunkurin aikata hakan ?iya tunaninsa yanzu ya fara gane