Showing 18001 words to 21000 words out of 168608 words
asiri duk wanda keda sa hannu a kisan sadear ya sake amsawa da" amen
na gode Kwarai da gaske yana kukan an cucesa an rabashi da yar'uwarsa tilo , a lisafinsa yanzu tayi awa hud'u a kabarinta shiru yayi yana juya girman alamrin zuciyarsa na zafin da bai san ranar dainawa ba ."
"Nan su aunty shahida suka barsu tsaye suka shiga cikin gidan suka nufi bangaren yayan sadear Inda suka tadda tsirarun mutane zaune
a cikin d'akin ana karba gaisuwa ,a natse suka gaisa da mutane tare da yi musu gaisuwa suka zauna Inda ake ta jimamin mutuwar kowa na fad'ar albarkacin bakinsa ,wasu na cewa ai hadiza ce ta kasheta tunda daman ta furta cewar itace zataga bayanta a bayyanan nasi ,yayinda wasu na cewa ba lallai bane ya kasance itace ta kasheta ."
Suna zaune police officers suka shigo tare da
aminu da yaronsa sadi dan kimani shekaru goma shabiyu yana musu bayanin wacce ya gani ."
'yansanda na sauraron yaron daki daki gefe guda kuma suna dudduba gidan a karshe suka tsaya a kofar d'akinsu hadiza tare da tambayar wacce ake zargi da aikata kisan ."
batare da 'bata lokaci ba akayi sallama a bakin kofar d'akinsu, hadiza kam tunda taji sallama police cikinta ya duri ruwa ta soma juya Kai zuciyarta na tsinkewa dan tunda akayi mutuwar take cikin tsoro da matsanacin firgici mara iyaka gabadaya komai nata ya tsaya cak ."mahaifiyarta ce ta amsa sallamar tana fitowa daga cikin d'akin "muna son ganin hadiza ko tana ciki ?"."eh ! tana ciki ta fad'a muryarta na d'an rawa "hadiza ki fito ana son ganinki da kyar hadiza ta fito kamar wacce kwai ya fashewa aciki ta tsaya a bakin kofar d'akinsu , kana kallonta zaka fahimci a tsorace take , sai da suka mata duban tsanake sannan daya daga cikin police din yace "kece hadiza ko ? ta gyada masa Kai alamun "eh! gabanta na faduwa da sauri da sauri suka ce "muje akwai wasu tambayoyi da zamu miki a office dinmu ."
"akan wani laifi kenan? mahaifiyarta tayi
karfin halin tambayarsu". idan muje office
dinmu kwaji akan wani laifi ne " suka tasa keyarta gaba mahaifiyarta ta biyosu da sauri
tana cewa "bazan bari ku tafi min da yarinya ba ku zubar mata da mutunci ba ." jin maganar mahaifiyarta yasa hadiza ta tsaya cak taki cigaba da tafiya police suka ce "muje ko!" "shiru tayi jikinta na rawa taki motsawa daga Inda take aiko daya daga cikin yar sanda mace ta rike tsintsiyar hannunta "zaki da girma da arziki ko kuwa mu tafi dake ta karfin tsiya ? "cike da tashin hankali hadiza ta fixge hannunta daga hannun yarsanda tare da marairaice fuska kamar zatayi kuka "ni bazani koina ba har sai na san dalilin da yasa zaku tafi dani office dinku ". zata sake magana suka daura bakin bindiga keyarta "idan kika sake furta wata Kalma zamu sakar miki wuta mu tasheki aiki," oya muje "tsimi tsimi hadiza ta soma tafiya mutane gidan na kallonta cikin tsananin farinciki dan daman taadabi kowa acikin gidan kowa tsoronta yake ."
"wani mummunar tashin hankali ya shigi mahaifiyar hadiza da hadizan karon kanta, ana k'okarin turata cikin motar 'yansanda su aunty shahida suka fito suka kama gabansu zuciyoyinsu cike da tsoro da fargaba ,direban aunty shahida ya sauketa a kofar gidansu sannan ta bashi umarnin ya kai doctor sa'a da zinnira ya dawo, suka yi sallama da abokan aikinta da zumar sai sun had'u gobe , Jiki a sanyaye aunty shahida ta shiga cikin tangamemen falon mahaifiyarta parlour'n shiru babu alamun akwai wani bil adama acikinsa hatta 'yan aikin gidan bata ji motsinsu ba ."
Ta samu guri ta zauna jagwab akan d'aya daga cikin kujerun Parlour'n tana sauke ajiyar zuciya har lokacin wani iri take ji ajikinta , shiru parlour'n baka Jin motsin komai sai na AC dake aiki a falon .
ko cikakken minti biyar batayi ba ta fara Jin motsin mutane , ta d'ago a hankali masu aiki ta gani cikin shigarsu ta kullum dukkaninsu rike da farantin silver suka rusuna tare da had'a baki "barka da zuwa hajiya "barka sannuku ya aiki ?"
"alhamdulillah ! suka amsa tare da ajiye tire suna tambayar abinda za'a kawo mata " me za'a kawo miki hjy akwai rice and stew akwai tuwon shekafa akwai dabmu shimkafa akwai ......? "duk babu wanda zanci aciki ta fada tana runtse idanunta dan kanta wani irin sarawa yake kmr ana buga mata guduma ,tana nan zaune hajiya zulaiheart ta shigo cikin shigar alfarma doguwar rigar lace har kasa wanda kimanin kudinsa ya Kai 500k ta zauna akan kujera mai zaman mutun d'aya tayi shiru tana duban fuskar babbar diyarta "lafiya shahida duk na ganki haka ?a hankali ta bud'e idanunta ta saukesu akan hajiya zulaiheart "wallahi mami wata mutuwa akayi mana agurin aiki mai shiga jiki ko ince an kashe yarinyar ......"
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun oh ni zulai me mutane suka d'auki rayukan mutane ne yanzu
kashe mutun bai musu wahala ?"wallahi mami sai ma Kinga yayan yarinyar abun tausayi marayu ne babu uwa babu uba sai Allah abun daya fi d'aga min hankali yankar rago akawa yarinyar abun tausayi sam babu Imani a zukatan wasu mutane taya zan iya kashe mutun da hannuna ?ta karasa maganar hawaye na zubo mata."uhm duniya kenan Allah dai ya tona asiri ko suwaye suke bin ya'yan mutane har gida suna kashesu to Kalli mutuwar mubina kigani abu kamar wasa har an kusan shekara biyu amman har yanzu babu labarin wanda yayi kisan."
Allah dai ya kyauta sam kasar nan babu tsaro shiyasa nasa aka qara tsaro mai karfi a gidan nan."
"hajiya ai ita sadear ana zargin makwafciyarsu ce tabi dare ta kasheta yanzu haka maganar da nake miki tana hannu jami'an tsaro zasu fara bincike akanta "alhamdulillah ai gara kam ita kuwa me yayi zafi haka ko akan me zata kasheta ?mutumin duniya hjy ai ba'a iya mutumin duniya sai Allah daya haliccesa, Allah dai ya sawaka kawai zamuce ."
"Ameen inji cewar hjy "wai Ina maryam da auta suka shige ne ? sunje gidan zabiba amman dai
nasan zuwa la'asar idan anci sa'a babu traffic zaki gansu sun dawo " Anya kuwa zan jira har wannan lokacin ? bari kawai nazo na wuce gida ."
"kin kuwa fada ma maryam batun wannan sarkin zuciya ?"wallahi a'a jiya dai nayi kokarin had'asu gbdy a office dina sai Kuma hakan bai yiwu ba ga yau ma ,Ina ganin sai dai weekend zanzo dan gbdy jina nake wani iri, wallahi mutuwar nan ta shigeni yarinya mai kirki da biyyaya da sanin ya kamata sam sadear bata da matsala a rayuwarta sannan bata da abokin fada kowa nata ne agurin aiki ga wasa da dariya ga ..."kira ne ya shigo wayar aunty shahida wanda yayi sanadiyyar katse mata magana ta d'auka tana duba screen din wayar direbanta ne mlm garba dan haka ta mike ta d'auki jakarta tayi wa hjy zulaiheart sallama ko a gidanta ma kasa tabuka komai tayi babbar yarinyarta madina duk ta damu sai faman tambayarta take ta fada abinda ke damunta bata ,boye mata komai ba ta fada mata mutuwar , mutuwar tsaye madina tayi dafe da qirji dan tasan sadear sosai tana janta ajiki idan taje gurin mamanta ,addua tayi mata hawaye na zubawa aunty shahida lokacin da take tuna moment dinsu da yarinya babu abinda yafi daga mata hankali kamar maganar da tace zasuyi a yau din gashi ta mutu batare da san ko akan me zata mata magana ba kwarai taso tasan ko akan meye , Allah sarki rayuwa kenan ta dade zaune tana jimamin mutuwar sadear kafin daga baya ta mike ta shiga dakinta ta kwanta zuciya da gangar jikinta na mata ciwo .."
Har yansanda suka karasa office dinsu kuka hadiza take , aka nufi d'akin bincike daita aka nuna mata gurin zama sannan bayan kamar awa daya wasu qararrun 'yan sanda suka shigo nan suka fara Aiko mata da tambayoyi d'aya daga cikinsu tace "ko zamu iya sanin dalilin da yasa kika kashe makwafciyarki sadear ? hadiza taji tambayar tamkar saukar aradu
take idanun sukayo waje tare da dafe qirjinta "wallahi bani na kasheta ba nima tashi nayi naji labarin mutuwarta ,"karki wahalar da hukuma zai fiyye miki sauki ki fito ki fada mana gskiya kunyi fad'a da sadear ko ba haka ? cikin tsananin firgici da tsinkewar zuciya tattare da tsoro ta gyada Kai alamun "Eh!"can km ta girgiza musu Kai alamun "a'a! police ta gyada Kai sannan ta cigaba "kenan kina nufin babu wata matsala ko fada wacce tasa kukayi sa'insa daita ? nan ma ta gyada Kai alamun babu cikin kankanin lokaci ta fita haiyacinta saboda tambayoyin da suka dinga mata tana kare kanta a karshe daya daga cikin police mace tace ' kinyi furucin zaki kasheta Kuma kinyi nasara ko ba haka ba ?ta girgiza kanta alamun a'a juyin duniya akayi da hadiza amman ta tsaya akan ba itace ta kashe sadear ba suka barta tare da turata wani d'aki tana shiga taji an rufeta da duka cikin kankanin lokaci kamanin hadiza ya sauya tayi laushi sosai tana ihu tana Komai aka shiga daita wani daki aka garkame . tayi kuka sosai idan ka ganta sai ta baka tausayi gabadaya ta tabbatarwa kanta tata takare Ina ma batayi fad'a da sadear ba ,a she da me kararen kwana tayi fada ? wayyo Allah ni hadiza kaicona me ya kaini fada da gawa ....?yau dai ga Inda karshen wahalana ya kawoni ni hadiza nayi nadama ,nayi danasani ban bar yara ba ,ban bar manya ba ,ban bar matan aure ba, ban bar tsofafi ba , ga dai karshena ban san me gobe zata haifar ba ta karasa maganar tana matso ruwan hawaye mai zafi daga idanunta ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
Arewabooks username
Ayshabagudo
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page5
" da misalin karfe tara na daren ranar Juma'a mr ATA ya fito daga bathroom jikinsa sanye da rigar wanka iya gwiwarsa yayinda hannunsa d'aya ke rike da white towel yana goge kanshi zuwa wuyansa ,ahankali ya qarasa gaban mirrow ya tsaya yana kallon kyakkyawar fuskarsa yana qoqarin zare rigar jikinsa ."shiru yayi yana kallon faffad'an qirjinsa dake kwance da laulausan suma tamkar na jariri sabuwar haihuwa ga Kan nipple's dinsa a tsaye makale da qirjinsa sai sheki suke, babu lafiyayyar macen da zata gansa a haka bataji sha'awarta ta motsa ba saboda kyawun cikar halittar da allah yayi masa ."
kusan minti goma ya dauka tsaye yana qarewa kansa kallo kafin daga bisani ya juya a natse ya koma bathroom ." ko cikakken second uku bai yi ba ya fito ya d'auki kwalbar bodyspry ya feshe ilahirin jikinsa ya saka white singlet boxer's sannan ya shirya cikin wasu hadaddun kananan kaya t shirt fari sol da dogon wando baki , ya kai hannu inda tsadadden Turarensa (Reed ) yake ya d'auka ya feshe kayan jikinsa , ta koina a sansar jikinsa kamshi yake tashi mai sanyi da tada tsumin shaawa." ya ajiye kwalbar turaren a mazauninsa yasa hannun ya kwashe wayoyin business dinsa guda biyu ya juya ya fito daga cikin dakin tare da janyo kofa ."
a natse yake saukowa daga Kan matattakala bene hannunsa daya soke cikin aljihun wondonsa kai tsaye yana gama saukowa ya qarasa dining area ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun dining yana sauke numfashi kana ya ajiye wayoyinsa akan table ."ahankali sanyin ac dake aiki a parlour'n ya dinga ratsa sansar jikinsa ,lumshe lumtsatsun idanunshi yayi yana ciza gefen lip's dinsa , cikin haka mami ta fito daga kitchen ta soma hidimar zuba masa abinci ,dan shi baya son masu aiki na shiga huruminsa saboda Allah yayi shi mai tsananin tsabta da kyakyami , shiyasa ba koina yake cin abinci ba, ko fuskar abinci ya kalla yaga yayi wani iri to komai za'a yi bazai ci ba shiyasa duk sanda zai ci wani abu mahaifiyarsa ce kadai ke masa hidima abinci wannan halin kuwa ya samo ne daga gurin kankansa alhaji abdallah dan shima ba abincin kowa yake ci ba sai wanda yayi masa ."
bayan ta zuba masa jollof din shikafa yar waje wacce taji pepper chicken ta hada masa coffee dinsa na gado ta ajiye masa a gabansa sannan ta koma ta zauna a kujerar dake fuskantarsa tana dubansa a tsanake tace "kasan wani abu my love ? ta tambayesa idanunta na kanshi ya d'an girgiza mata kansa batare da yace komai ba sai ma lumshe lumtsatsun idanunshi da yayi yana jiran yaji me zatace .Allah Allah !!nake kayi aure na huta da yi maka hidima "shiru yayi bai yi magana ba yana jiran yaji spoon din abinci bakinsa amman yaji shiru har tsawon second goma sai ma maganar aure da yaji ta cigaba dayi masa wanda hakan Ke mugun bata masa rai tare da dagula masa lissafi dan a halin yanzu idan akwai abinda yafi tsana bai wuce maganar auren da take bukatar yayi ba gashi burinta ba abu bane dake cikin lissafinsa ."
shiru yay har wata second biyar tazo ta wuce bai ga alamun tana da niyyar bashi abinci ba dan haka ya bud'e lumtsatsun idanuwanshi a hankali ya tsura mata yana kallonta fuskarsa a shagwabe kamar koda yaushe idan yana gabanta "kana wani kallona da wad'an nan idanuwan naka masu firgita mutane ai gsky na fad'a ina bukatar na huta da maka hidima ." muryarsa a kasalance ta fito tamkar mai koyon magana "haba my sweetheart ki daina fadar haka mana yanzu baki jin tsoron wani yaji kina cewa kin gaji dani ?ni bance na gaji da kai ba karka canza min magana hidima nace ta fad'a tana hararasa wanda da gani na soyayya ce." ya sauke naunayen ajiyar zuciya still kwayar idanunshi na kanta sai daya numfasa sannan ya sake motsa lip's dinsa "sweetheart ! ya kira sunanta a shagwabe ta kalleshi kawai tana jiran taji abinda zai ce " ai ko na yi aure bazan daina cin abinci daga hannunki ba domin dashi na saba ."
"Ina bazan yarda da wannan tsarin ba dan bazan shiga hurumi da ba nawa ba ,wannan hurumin matarka ce yana da kyau idan mutun yayi aure ya samarwa matarsa farinciki , hurumin mahaifiya dabam haka zalika na mata da dabam , dan haka kasa wannan a ranka da zarar kayi aure babu Kai babu cin abinci daga hannuna ." ta karasa maganar tana murmushin jin dadi jin bai ki maganar data fad'a ba ga dukkanin alamun dai yayi amanna da zabinta dan haka ta dauki spoon ta soma bashi abinci a baki tana kallonsa cike da tsantsar kulawa "kinsan wani abu sweetheart ? ta tsura masa Ido kawai batare data ce Komai ba dan ta lura yana cikin farinciki shima ita yake kallo cike da matsanacin soyayyarta , anan duniya bashi da kamarta ita kadai yake kallo yaji duk tarin damuwarsa ta Kau."
"wallahi idan Ina cin abinda kika sarrafa wani farinciki nake tsintar kaina ciki , nifa ganin nake ko Allah ya qaddaro nayi aure to kece zaki dinga girka min abinci , dan abincin my sweetheart babu sauki akwai dadin dandano dan zai iya sa mutun ya cire kansa ya bayar kyauta ."ta sake yin murnushin jin dadi tana zabga masa harara "Kai ko Allah naki wayon." ahankali yake cin abinci suna hira cike da so da qauna dake tsakanin uwa da d'a suna cikin haka auta ta shigo bakinta d'auke da sallama ta zauna a kusa da mami tana Kiran "washhhhhh Allah nah na gaji sannan ta maida hankalinta gurin mr ATA "Ina yini yaya ? "Lafiya ! ya fad'a atakaice yana sake tamke fuska sosai , ta maida hankalinta kan wayarta tana chart "wai ke auta idan kina gida baki da wani aiki ne sai rike waya baki istergram baki facebook baki what's app ? Ko karfe daya na dare na hau online sai na ganki ."yayi maganar a can kasan makoshi sam bazakace shi yay maganar ba tsabar miskilanci ."
"wallahi kamar kasani son ita da maryam sam basa gajiya da rike waya da daukar hotuna kamar masu aljanu , wad'an nan duk randa aka daina amfani da waya a kasar nan ban san yadda zasu dawo ba " wallahi kuwa mami akwai matsala nana hauwa'u ta fada tana cewa "shekaranjiya fa muna zaune wayar maryam ta d'auke wuta kamar almara kinsan a daren sai da taje aka gyara mata, ai wallahi garani sau dubu akan maryam tunda ta sako sunan maryam ya d'auke wuta dip kamar anyi ruwa an dauke ya maida hankalinsa kacokan a kan wayarsa dake qara ya d'auka ya manna a kunne yana maganar million kudade da zasu fita da wadan da zasu shigo ."
"babu gara auta dake daita duk d'aya ne ,ku dai rage son duniya dan gidan wasu zaku ba kowani namiji ke son irin wannan rayuwar ba , sannan lokacinku kuke ci bamu San sanda mutuwa zata zo ba , suna cikin mgn maryam ta shigo da sallama sanye da riga da wando na bacci ash colour masu yanayi dana sanye sai dai su anyisu ne dan