Showing 129001 words to 132000 words out of 168608 words
me ? yes of course uncle domin babu shi acikin kundin da dad yake rubuce rubucensa aciki , amman mai yasa tun tuni baka taso da wannan maganar ba sai yanzu ?yanzu né naga ya dace nayi magana tunda naga ita wannan uwartaka batasan abun arziki ba, idan kowa yaja bakinsa yayi shiru saboda jin tsoronta da gudun magana toni bana jin tsoronta kuma bana gudun magana ,zanyi mgn km dole a kasafta abani rabona bazai yuwa kayi mana karfa karfa akan gumin da mahaifinmu yayi wahala ya tara tsawon shekaru ba ."
"babu abinda zan bayar..., ."ya sake maimata mgnr daya fada yana sakin spoon din hannunsa hakan yasa hankalinsu yayi matukar tashi gab gab !! baba qarami yaji gabansa na wani irin faduwa gbdy parlour'n ya dauki shiru tmkr babu wasu hálittu a wurin "koda ma akwai dukiyar babu abinda zan cire na bawa kowa tunda babu shi a rubuce idan kuma kayi trying wani non..."shiiiii mami ta furta tana daura dan yatsanta akan lip's dinsa dan dakatar dashi domin tasan halin kayanta karshe kalmar nonsense ne zata fito daga bakinsa "wai meye haka kake yi adamcy ? baba qaramin sa'anka ne"?
"Karka manta kanin mahaifi ne me yasa ma sai anan zaa yi discution din wannan matsalar dan kawai a daga min hankali ? ta juya inda baba qarami ke zaune "karki fada min hk sannan abu na gaba ki fada wa d'anki yayi bincike mai kyau akan abinda na fada tabbas akwai dukiyarmu acikin dukiyar ubansa wanda byn mutuwar mahaifinmu muka barshi a hannunsa idan kuma ba hk ba komai zai iya faruwa idan wani abu ya faru ki kuka da kanki karki yi kuka da kowa." yana gama fadar haka ya mike cikin tsananin fushi yaransa maza biyu salim da sultan suka mike suna hararar ata kafin daga baya suka marawa mahaifinsu baya .
Hajiya zualai ta mike tsaye cikin tsananin tashin hankali tana binsu da kallo gabanta na faduwa tasan yana son kunno da damuwa ne sbd rashin amincewar auren adamcy da hindu da kuma makudan kudaden da yayansa sukai qoqarin hadamewa adamcy ya hana ,ATA ya kai hannunsa ya riko tsintsiyar hannunta "sweetheart ki zauna "ta zauna cike da sanyin jiki tana duban kyakkyawan tilon dan nata nmj kwaya daya da allah ta mallaka mata "karki damu sweetheart da mgnrsa everything will be fine tunda ni bani da wani business dashi so karki saka wani abu aranki ,ban san meye damuwarsa ba ."?
" ban san me yasa yakewa kudi mugun só haka ba ."? duk ribar dake shigowa ta AGC ina iyakar kokarina ana cirewa kowa hakinsa na bashi kuma sweetheart a qokarina na kar company ya ruguje kullum hannun jari nake qarawa batare dasanin kowa ba kuma su waye ke kokarin karya company ? yaransa né kullum cikin sata suke sannna yanzu yazo da wani batu this time around sweetheart sai dai ki yi hakuri I can take it dan bazan dauka ba wallahi baba qarami na mugun son kudi duk ma yafi sauran karbar kudi a kamfani amman yanzu yazo yace ga zance ga magana agc ne dai yanzu na soma zuwa kula dashi bazan yanke zuwa ba bare su samu damar yin babakeri da dukiyarmu ."
" adamcy ni nasan baba qarami ba kudin yakewa ba, tunda bai taba mgnr wasu kudade ba sai yau na dai lura tunda aka fito da batun mgnr auren da maryam ya canza , amman nasan ba komai yake damunsa ba so yake ka auri diyarsa hindu ."shiru adam yayi yana sauroronta yana tsakurar abincin gabansa batare da ya furta komai ba dan babu ruwansa da mgnr "ko zaka taimaka adam ka had'asu duka biyu ka auresu"?
"What ?"
ya furta da mugun karfi yana sakin spoon din hannunsa "mami ta lumshe masa ido "kayi tunani akai kaji adamcy nah "am done am leaving kiyi min addua fatan alkhairi ya fada yana mikewa da d'an hanzarin ya soma tafiya cike da kuzari hannunsa daya cikin aljihun wondonsa." tabi bayansa da kallo tana kiran sunansa cikin tsananin tashin hankalin "adamcy !adamcy !!! Ka tsaya kaji me zance adamcy ."amman ina bai juyo ba bare ya tsaya yaji mai zatace,itama tasan adaidai wannan yanayin da yake ciki bazai tsaya ya saurareta ba domin maganarta ce tasa zuciyarsa ta yunkuro har ya kasa sauraranta shiru tai tana dafe goshinta cike da takaici da kuma mamakin halin biladam ."mutane sam sam babu tsoron allah aransu "shekara da shekaru baka tashi dauko maseefa ba sai yanzu dakaga yaro zai yi aure kazo da wata magana ."
Tana cikin wannan halin maryam ta qaraso hannunta rike da glass cup da magani ta mika mata "ki cire damuwa aranki mami ki sha magani lokacin shan maganinki yayi mami ta dago kanta ta kalli mrym yana daya daga cikin abinda yasa ta kwadai tawa danta aurenta domin zai samu natsuwa daita muddin tana raye sai ta zama uwar gidansa km uwar yayansa ".na gode maryam da kulawar da kike bani "haba mami kullum sai kinyi min godiya karki manta ni din fa dolenki ce haka kema dolena ce duk abinda nayi miki tmkr nayiwa mahaifiyata ce "haka né maryam amman duk da hk na gode sosai allah yayi albarka kinci abincinki ko kuwa kin tsaya tallatawa duniya "?mrym taí murmushi tace "kai mami naci !"kina ji ko mrym kiyi kokari ki rage son social media din nan idan ba hk ba bazuku shirya da adamcy ba kasancewar shi mutun ne da yake da raayi dan allah ki daina kmr yadda na sha fada miki "in sha allahu mami zan rage tare suka baro parlour'n ."
******
Karfe 11:00 daidai na safiyar laraba nuzla zaune a parlour'nsu ita kad'ai cikin tunani da zullumin abu biyu aurenta da hisham da kuma aikin da ata ya bata wanda ita sam bata jin zata iya aikatawa ita da kyankyaso ma tsoronsa take ji bare akai ga kissan mutun ai tasan duk runtse duk wuya bazata iya ba kullum tana gida bata fita koina duk da tana buqatar fita yin shopping din abubuwan buqatanta amman haka ta hakura ,tun kwanaki uku da suka wuce waadin da ata ya bata suka cika amman shiru babu wani sammacin daga yansanda haka zalika babu wanda yazo mata da magana makamanciyar zarginsa akanta dan haka ta dan samu natsuwar zuciya ta mike tsam ta shiga dakinta ta shirya cikin kananan kaya ta daura abaya a saman kayan tayi roling kanta da mayafin abaya ta dauki turare ta feshe jikinta ta dauki handbag dinta ta rataya ta fito ta shiga dakin hjy salema tana zaune tana lazimi akan dadduma dan ta idar da sallar wallaha kenan ."
"momy zan dan je shooprit na dawo murmushi jin dadi ta sakar mata dan yaushe rabon ta fita kullum tana kunshe a daki cikin damuwa "sai kin dawo nuzla allah ya tsareki ta bata amsa da haka cikin halin farinciki "akwai kudi a hannkin ne ?ta waiwayo tana dubanta "akwai kudin da yaya Ibrahim ya tura min cikin account dina dasu zanyi amfani to shikenan sai kin dawo ta juya ta fita daga dakin tana kiran bolt dan bata jin yin driving ."
a hankali take taka qasa har ta fito bakin get din estate dinsu fuskarta a daure kana ganinta zaka fahimci tana cikin damuwa kadan tayi tafiya tana kiran mai bolt taji a inda yake kawai taga motar yansanda a gabanta nan take taji gabanta yayi wani mummunar bugawa da matsanancin karfin gaske ta sauke wayar kunneta batare data kashe ba ta tabi gefe zata wuce cikin tashin hankali tana adduar allah yasa ba wajenta suka zo ba amman ga mamakinta mutun biyar suka fito suka sha gabanta suka tsaya ta kallesu daya byn daya cikin tashin hankali kafin ta kai ga bude bakinta duk suka fito mata da ID card dinsu daga gaban aljihu suka nuna mata daya daga cikinsu yana cewa "sunana inspector Almustapha hasan umar da fatan kece nuzla ?
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 24
Qoqarin cire tsoro da fargaban dake tattare da jikinta tayi ta aro jarumta ta sanyawa jikinta tace "Eh yes nice nuzla fatan dai lafiya kuka tsayar dani ? "Ki adana tambayarki tukunna muna gayatarki zuwa office dinmu yanzu ."akan wani dalili kenan kuke gayyatata ? idan munje zaki ji komai ,kamar tayi musu taurin kai amman sai taga d'aya daga cikin 'yansanda na qoqarin fito da handcuff daga cikin aljihu yana cewa "zaki wuce muje ta girma da arziki ko kuma sai mu saka miki handcuff mu wuce dake ta karfin tsiya ."
ba tayi mutsu ba dan ta rigada tasan da komai dan tun tuni take jiraye dasu saboda dama tasan hakan na zuwa saboda tun rabuwarsu da yaya adam tasan ya zuba tsaro sosai akanta ta yadda duk wani motsinta arayuwarta yana sane dashi ,haka ma yansanda, dan tayi imani anan din ya bada umarnin aka mata dan da suna son kamata cikin tonon silili da har ciki zasu biyota ,ba tayi ma tunanin zata wuce lokacin daya bata batare da ta shiga hannun hukuma ba." sosai zuciyarta ta shiga rudani taji wani gagarumin bakinciki ya rufe mata kahon zuciya kuma tayi imani matukar tayi gardama dasu haka zasu da'ba mata handcuff su wuce daita , ta ma godewa Allah da ba har cikin estate dinsu suka shigo suka tafi daita ba ai da kuwa ta shiga ukunta ."
Ahankali ta soma daga kafafunta domin isa inda motarsu take jikinta na karkarwa a duniyarta idan akwai abinda ke firgitata shine hukuma tana tsanani tsoron shiga hannun yansanda, duk da tasan ba wani laifi tayi ba ,dan abinda har yasa suka gayyace din akanshi bata aikata ba ."tafiya take tana tunani da mamakin wanda ya aiko su "me ta yiwa yaya adam da zafi har haka daya kasa yafe mata ? shin laifi ne dan tace tana son shi?dan dai tasan hukuncin zafin furta masa kalmar só ne ya janyo mata wannan tashin hankali, tayi masa runtsuwa da Allah bata aikata abinda yake zarginta akanshi ba amman ya kasa yarda daita "shin tayi masa kama da wacce zata iya kisan kai ko yunkurin kisa ne ? zuciyarta ta dinga mata zafi tana mai sake tabbatarwa kanta lallai yaya adam baya sonta, bayan soyayya ta aure har da soyayya ta yanuwantaka ma baya mata gashi ita duk duniya babu wanda take so sai shi ."
"anya bazata rushe wannan wahallalliyar soyayyar ba ta dawo qiyayya da tsana mai tsanani ba "? ji tayi jikinta yayi sanyi matuqa dan bata jin zata iya wannan aika aikan ,jikin nuzla a sanyaye yansanda suka sakata a bayan mota tare da wasu jami'an tsaro mutun biyu inda zuciyarta ke wani irin bugawa da karfin gaske sakamakon bakincikin sakata a tsakiyarsu da sukayi tun anan idanuwanta suka canza kala tana kallon tafkeken get din estate dinsu aka wuce daita ,tafiya kadan sukayi suka iso police station."direban motar yayi parking ya kashe motar sannan suka firfito suka shiga ciki suka karbi duka kayanta sannan aka bude wani daki wanda babu kowa aciki suka sakata ciki suka maida kofar suka rufe kukan bakinciki ne ya kufce mata ,ta soma rera kuka tana jin wani irin zafi acikin ranta saboda ta duba hagu da dama babu inda zata zauna duk inda ta kalla qazanta ne da zarnin fitsari uwa uba duhu ."
Aqalla ta kusan awa biyu tsaye tana jiran azo a fara tuhumarta domin a tunaninta da sunzo zasu fara jeho mata tamabayoyi tana basu amsa idan sun gano bata da laifi su saketa ta kama gabanta batare da sanin kowa ba sai taga sun shareta sun ma shiga wata tsabgar dabam har wata awa daya tazo ta wuce basuyi lokacinta ba ,wanda zuwa wannnan lokacin kafafunwanta sun fara sandarewa da tsayuwa ahankali tayi qasa ta tsuguna a cimintig dakin tana hawaye yayinda bakinta ya soma furta adduar neman dauki ."
Shi kuwa ATA lokacin da sakon samun nasarar kamata ya isar masa yana zaune a parlour'n mami tare daita dan bai jima da shigowa ba lumshe tsumammun idanunshi yayi sannan ya motsa labbansa da kyar "ina fatan babu wanda yaga lokacin da kuka wuce daita ?okay sai nazo ya fad'a tare da jan boyayyan numfashi ya sauke ,okay zaku iya fara aikinku kafin na shigo amman karku ta'ba lafiyar jikinta ,sun dauki Kmr minti goma suna magana yana gama waya ya ajiye wayar a gefensa yana jijjiga kafarsa daya mami wacce kwayar idanunta Ke kanshi a tun sanda ya fara wayar yace ."
"Yaakayi adamcy nah naga kayi wani iri ko akwai damuwa ne ?cikin kwantar da murya yace "no sweetheart yunwa nake ji ,bari nasa aka ..."haba sweetheart karki saka kowa please ni ban san me yasa kike yawon sako wasu cikin lamarina ba" to sarkin korafi ,kai dai da wannan halin naka Allah yasa ka canza ,kullm kai kenan cikin bakin hali naga ranar da zaka canza bazaka barni naji da tsufana ba tun kana yaro nake hidima da kai har gashi ka tsufa ta qarashe mgnr cikin salon tsokona tana hade rai ."
Ya dago a sukwane ya tsura mata idanuwanshi "yanzu ni ne na tsufa sweetheart?sosai kuwa kai yanzu tunaninka baka tsufa ba ?haba haba !!sweetheart allah idan ba fad'a akayi ba babu mai cewa na wuce 40,dan ni wallahi jina ma nake Kmr .." "kai dan Allah kama mana baki shima gyara ne ,da babu gyara da kasan kai ba yaro bane "wel ko babu gyara zan zama Kmr yaro dan gadon jikin mai kyau nayi "
"A wajen kenan ?
Ya sake tsaita idanunshi akanta sosai yace "wajenki mana! shakiyi kawai ya dai kamata ka rage wadan nan abubuwan dan ka kusan zama baba nan da wani lokaci ,nan da nan ya hade rai Kmr wanda aka fadawa sakon mutuwa duk da tsananin son haihuwa da yake amman kwata kwata baya qaunar haihuwa daga mrym ya gwamaci ya qare rayuwarsa babu haihu akan ya haihu daita ".
Ahankali ya bude bakinsa zaiyi magana mami ta katseshi dan tasan ba alkhairi zai fad'a ba "ina son zuwa yanzu ka bawa mrym matsayi mai girma acikin zuciyarka ,ya sake kallonta cikin rashin fahimtarta "Eh !nasan abinda nake yau idan ka runtse idanunka da zumar bacci ka matso daita kusa da zuciyarka zaka ga abubuwa masu yawa akanta" ya dage girarsa daya yana dubanta dan ya fara gano rikicin tsufa ya fara kama mahaifiyarsa idan ba hk ba ina shi ina wani kusantota da zuciyarsa yaji me ?bai gama mgnr zuci ba ya sake jiyo sautin muryarta ".
"tunda ta zama mahadin rayuwarka dole zuciyarka zata dinga bibiyarta " numfashi ya sauke da karfi dan yasan ba abune mai yuwuwa ba shirunsa ne ya bata amsa mgnrta "ta gyara zama kai dai kayi qoqarin yau kawai ka kusantota da zuciyarka idan Allah ya kaimu gobe zan tmb..."sweetheart yunwa !"Okay bari na tashi sarkin korafi "thank you my sweetheart Kiyi sauri please dan yunwa nake ji sosai har cikina ya fara zafi "dariya ma ya bata a duk sanda taji ya fadi haka sai taganshi tmkr yana yaro ,adamcy kenan ko yaushe zai san ya girma ? kullum idan yana gabanta tmkr qaramin yaro yake dawowa ."
Jallof din kuskus wanda yaji hanta da nama da ugu ta kawo masa ta ajiye agabansa tace "bismillah sarkin korafi kallonta kawai yayi yana girgiza kai sannan ya fara ci a natse ta zauna a kujerar dake fuskantarsa tana kallonsa hatta cin abincinsa dabam ne ,yana ci tana yi masa hirar yadda take son bikinsa ya kasance shi dai bai ce uffan ba ya cigaba da kwasar abinsa bayan ya gama cin ya mike ya haura saman d'akinsa wanka yayi ya canza kaya marasa nauyi ya zauna abakin gadonsa ya kunna system ,ahankali sakonnin abokan kasuwancinsa ke shigowa wasu ya amsa wasu kuma ya wuce ."
Washegari yana zaune akan daya daga cikin kujerun dinning sanye da wondo da riga long sleeve sai dai ya dan nade hanuna rigar kadan ta yadda zaa iya ganin hadadden agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ,yayinda mami ke tsaye a gefensa tana qoqarin saving dinsa ,ta kallesa zaune shiru ya hade hannunwansa waje daya tace "jiya da nace ka rufe idanunka tare da kusanto mrym da zuciyarka , fad'a min daka rufe idanunka me ka gani ."Kai sweetheart "nasan mrym ka gani alokacin daka rufe idanunka ko ba haka ba ?" ni ba wata mrym dana gani sai princes dina na gani ."
" kada kayi min karya dan nasan baka iya karya ba "tunda Kinsan bana karya ya kamata ki yarda dani wallahi ni banganta ba Kinsan wani abu a duk sanda na runtse idanuna princess dina nake gani wata rana cikin farinciki wata rana cikin damuwa nifa jikina yana bani yarinyar nan ba karya bace gsky ce km ba aljana bace tana nan acikin duniyarmu sai dai a ina take? " yaushe ne zan ganta ?shine bansani ba amman nasan zamu hadu shiyasa nake jin Kmr a fasa wannan auren "kai sakarai menene ya kawo batun a fasa aure kuma daga magana ?"
Kamar yayi dariya ganin yadda magaarsa ta d'aga mata hankali "wannan auren fa sai an daurashi babu makawa zaku rayu tare har ma wata rana zaka amince daita tare da furta wa mrym kalmar so na tabbatar maka da haka "tunda ya fara cin abinci bai sake cewa uhm ba bare uhm uhm har ya gama ya goge bakinsa da tissue ya mike tsaye yana qoqarin yi mata sallama suka jiyo sallamar baba babba fuska cike da damuwa mami ta bar ATA ta qaraso wajensa a inda yake tsaye dan ko zama bai samu damar yi ba kallo daya mami tayi masa ta fahimci yana cikin damuwa suka gaisa adaidai lokacin da ATA ya qaraso ya gaishesa cike da girmamawa sukai shiru mami ta dubesa tace "baba babba ka zauna mana bari