Showing 6001 words to 9000 words out of 168608 words
mamartaka da shekarunta yaja ? "
"Adam at any time zan iya amsa kiran allah ko sai bayan mutuwata zakayi aure ? tayi mgnr tamkar zatai kuka nan fa hankalinsa yayi mugun tashi ya mike zaune tare da riko hannuwanta gabadaya cikin nashi yana kallonta cike da matsanancin soyayyarta gbdy yanayinsa ya sauya kamar zai yi kuka dan baya qaunar abinda zai nisan tashi da mahaifiyarsa bare rabuwa ta har abada ,muryarsa a kasalance ya soma mgn "haba sweetheart me yasa zaki fadi haka ?"
Me yasa bazan fadi haka ba ?ai gaskiya na fad'a kaki kayi aure kai dai kullum aiki kawai kasa gaba baka ma duba lamarina bare ka tausaya min Adam , bana son na koma ga allah banga aurenka da ya'yan ka ba ta qarasa mgnr cikin raunanniyar murya wannan karon kam hawaye ne taf acikin kwayar idanunta "karki min hk sweetheart Kinsan illar zubar da hawayenki akaina, kuma Kinsan babu abinda na tsana kamar na ganki cikin damuwa "idan har da gaske baka son ganina cikin damuwa to ka dan duba ko a cikin yammatan estate din nan ai bazaka rasa masu sonka da aure ba sai ka zabi biyu ko daya acikinsu ".
Ya ware mata lumtsatsun idanuwanshi sosai yana mamakin jin abinda tace "har mata biyu sweetheart ina zan kai su ? "bansani ba ta fad'a tana zabga masa harara sannan ta cigaba da mgn "wallahi shine burina ka auri mata biyu kuma duk arana daya saboda kasancewarka namiji kwaya daya tilo da allah ya mallamin "girgiza kai kawai yayi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa batare da yayi yunkurin sake cewa wani abu ba ya sake jin sautin muryarta "zakayi abinda nace ko nasa araina sai bayan na mutu zakayi aure ?" ya shafa goshinsa yana cewa "okay zanyi kokarin yin haka sweetheart." Ya fadi hk ne dan ya kawo karshen mgnrsu ."ko kai fa yaron albarka allah ya zaba maka mata na gari , runtse idanuwanshi yayi sosai tare da yin shiru yaki cewa komai dan har kanshi ya fara ciwo ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page2
....Da misalin karfe goma na safiyar ranar asabar mr ATA ya sauko daga saman dakinsa jikinsa sanye da bakin riga da wondo baki yayinda kafafunsa ke sanye cikin wasu hadaddun silifas masu matukar kyau suma black kana gani kasan masu tsada ne haka idanunshi suna makale da farin glass wanda ya zame masa tamkar na gado, ko bacci wani lokacin dashi yake sai idan Mahaifiyarsa ta shigo ta gansa dashi ta cire masa ,yayi kyau sosai acikin shigar kasancewarsa fari ."ya qaraso ya dauki jarida daily trust da'aka ajiye masa ya samu wuri ya zauna akan doguwar kujera mai zaman mutun uku ya daura kafarsa daya a kan daya ya shiga duba jarida "
yana zaune nana da maryam suka fito suna magana akan inda mai decoration zatai decorate din birthday din maryam dana hanan diyar Aunty zabiba kanwar mr ATA da zaa gabatar a ranar ." suna gama qarasowa parlour'n suka gansa zaune Kmr an dasashi a gurin ."suka bishi da kallo suna jin faduwar gaba babu yadda zaka ga mr ATA gabanka bai fadi ba ko kai waye kuwa saboda tsananin tsare gida , ya gansu amman yayi tamkar bai san da wasu halitta tsaye a wurin ba ,nan take kowacce ta shiga taitayinta jiki a sanyaye suka hada baki wurin gaishesa "good morning ya adam" ? sai daya dauki second goma batare daya amsa ba har sun cire rai da zai amsa suka jiyo sautin muryarsa daga can kasan makoshi "morning ! ya amsa batare daya dago ya dubesu ba ."
Naunayen ajiyar zuciya maryam ta sauke dan tasan darajar sister taci yasa har ya amsa gaisuwar dan da ita kadai ta gaisheshi bazai ta'ba amsawa ba Kai tsaye hanyar kitchen suka nufa domin bawa masu aiki umarnin abinda zasuyi na birthday duk da sauran abubuwa masu wuya tun jiya a kammala ,duk abinda suke hankalin maryam na kan mr ATA bini bini ta kallesa taja tsaki acikin ranta dan hakan nan kwanaki take jin matsanancin tsanarsa a ranta dan tasha alwashin tunda bai qaunarta itama bazata qaunacesa ba mai qaunarsa ma baso ."
Sai dai duk da wannan tsanar da tayi masa ta kasa dauke kwayar danunta akanshi har sanda ya mike ya isa dining table ya dauki cup din coffee dinsa baki mai shegen kyau da gani daga wata kasar yazo dashi , a natse ya sake dawowa mazauninsa ya zauna fuskar nan tashi a hade tamkar wanda ake masa wahayi da bacin rai."
"tunda aka haifeta ta bude idanunta akansa bata ta'ba ganin dariyarsa ba ,kuma haka kowa yake fad'a acikin family's ,komai zaayi na dariya sai dai ya bata rai yaja tsaki tare da cewa nonsense ko rubbish ga shegen miskilanci wani lokaci halinsa na dan burgeta Irin mijin da take so kenan mai matukar kamewa da sanin ciwon kai, dan gsky ita dai nmj mai yawon surutu ko shiga abinda bai shafesa ba yawon fara'a matsala ne agurinta bata so sai dai nashi yayi yawa ko dan murmushin nan ba yayi matukar kaga fuskarsa a d'an sake to yana tare da mami ne shima wani lokacin bata gane kansa kome zatayi bazai sakar mata fuska ba ."
byn ya sha kad'an ya ajiye cup ya cigaba da abinda yake har sanda hjy Zulaihat ta fito itama ta shiga kitchen yana nan zaune ya tsurawa jarida idanunshi , al'ameen daya daga cikin securities na bakin get
ya shigo bakinsa dauke da sallama sannan cike da girmamawa hannunsa rike da white lailon da box blue and white ,mr ATA ya amsa sallamar aciki yana mai d'ago kansa ahankali ya zubawa al'ameen lumtsatsun idanunshi "Alameen ya qaraso gabansa kad'an ya rusuna "barka da safiya yalla'bai "mr ATA ya gyada masa kai kawai batare daya amsa ba .
" amm ga sako wai inji Ana's" mr ATA ya d'an kankace lumtsatsun idanushi yana bukatar qarin bayani daga bakin al'ameen,alameen yayi sauri yace "sakon hjy maryam ne ita yace abawa "shiru mr ATA yayi yana kallonsa da sakon hannunsa kamar bazai ce komai ba sai kuma ya nuna masa kan table din dake gabansa yana jan tsaki a fili al'ameen ya ajiye ya juya ya fice da sauri ya kama gabansa."
Maryam dake kitchen wacce daman idanunta da hankalinta yana parlour ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, da sauri ta qarasa inda nana take tsaye "sister na shiga uku nah" ta fada tana riko hannun nana cikin nata "me kuma ya faru allah ya rabamu da shiga uku sister ?"kalli can ki gani sister ta nuna mata parlour'n "me ya faru ? "sakon Ana's ne daman ya turo min text message zai zo ya kawo min gift gsky al'ameen bai kyauta min ba maimakon ya kirani ya bani a hannuna tana magana idanunta na cikowa da ruwan hawaye hjy zulaiheart ta juyo a natse ta dubesu "ku kuma lafiya kuka tsaya kuka hade kai wa ya mutu ? a matukar firgice suka juyo suna dubanta maryam na 'kokarin dauke hawayenta a d'an rikice suka girgiza mata kai alamun "babu kowa " to meke faruwa daku ?babu komai suka sake hada baki "to allah yasa babu komai din amman ni dai na fahimce da komai tsayawa sukai suka qasa cigaba da aiki ."
shi kuwa Mr ATA naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske yana shan yaji kamar yadda ya saba sosai ya tsurawa box din dake dauke da sunan maryam da kallamar happy birthday yana lissafa abubuwa dayawa acikin ransa "wai gashi inji Ana's sakon hjy maryam "ya maimaita abinda al'ameen ya fad'a , kafin daga baya ya kwabe baki tare da kai hannu ya bude box din ,da wani hadadden freme idanunshi ya soma cin karo mai matukar kyau da d'aukar hankali an rubuta sunanta da larabci da kuma hausa ."
"shiru yayi yana jin wani iri a gabadaya ilahirin jikinsa na tsantsar bakinciki ,a hankali ya dinga kallon abubuwan dake cikin box din mug, pray mate ,Casbaha alqurani da wani qaramin greating card na sokon taya murnar birthday sai kuma qaramin yellow takarda mai dauke da kalaman soyayya "ya dauka yana tabe baki kamar yaga wani mugun abu ya soma karantawa ."
hjy Zulaihat ta fito daga kitchen tare da masu aiki mutun biyu zuwa dining maryam da auta suka biyo bayanta jikinsu duk a sanyaye dan basu san abinda zai faru ba "na shiga ukuna sister ki taimakeni karanta sakon fa yake " maryam ta sake fadan hk cikin tsananin tsoro "to sai me idan ya karanta ? " wallahi kin cika abun ban haushi kamarki dan an aiko miki da sako zai zama abun tashin hankali? Ke yarinya ce karki manta master's gareki kuma dole zakiyi aure "ni sister rabani da wani master's na yarda kowa ya karanta sakon amman ban dashi "bangane banda shi ba ? shi waye naki da zakice ban dashi ? tayi mata tmbyr tana kallonta "haba sister ya kike yi kamar baki san abinda nake nufi ba kema kinsan ba haka nake ba ni ba matsoraciya bace amman wallahi shi mugun tsoronsa nake ji ,sannan kinsan halinsa da disgi ."
"Dana san halinsa fa ? shi zai auremu?Ko kuwa munyita zama haka kenan bazamuyi aure ba ?"Kinga idan zaki cire tsoro ki cire dan ni wallahi ina samun miji aurena zanyi na barki bazan zauna ba aiki ba aure ba dole zanyi daya ta qarasa mgnr tana jan tsaki maryam tace "banza kamar kema ba tsoronsa kike ba "ina jin tsoronsa amman ban kai ki ba dan dani anas da abbas suke mutuwar só da son aure da tunin ina gidan daya daga cikinsu "ta fad'a tare da qarasawa wurin Hjy Zulai ta rabe a gefenta."
daga can inda hjy zulai take tsaye ta hangosa ya baje kayan sannan yayi zurfin cikin karata yellow takarda "Lafiya adam !? ta furta tana cigaba da dubansa ,a tsanake ya mike tsaye fuskarsa a yatsine ya nufo wurinta yana cewa "wani haukan shirme nake karantawa ".maryam tayi wuf ta koma kitchen da sauri tana daura hannuwnta duka bisa kanta itama auta tayi nesa da hjy zulaihat "haukan shirme kuma adam ? hjy Zulaihat ta maimaita abinda ya fad'a "yes sweetheart wannan bashi da maraba da haukan shirme ,wai nmj né zai zauna yana wannan haukan abun kunya kawai "yayi maganar yana yatsuna face dinsa kamar yaga wani mummunar abu "wannan ai iskanci ne ba soyayya ba ya sake mgn yana jan dogon tsaki ."
hjy Zulaihat tayi shiru tana duban mr ATA cikin tsananin tausayawa kanta dashi kanshi ,"bata san ranar da zai canza wannan mummunar halin nasa ba ,bata san ranar da zai bude baki yace ga matar da yake so ya aura ba ko fad'awa soyayya "duba ki gani sweetheart ya mika mata letter yana sake jan tsaki kamar wanda akayiwa dole sai ya karanta."
Jiki a matukar sanyaye mami ta karbi letter daga hannunsa tana dubawa gabadaya bata ga inda zantuttukan dake rubuce sukai kama da haukan soyayya ba ,illa ma maganar soyayyar mai sanyaya zuciya da kwantar da hankalin abokin rayuwa , byn ta gama karantawa ta kalli nana hauwa'u fuskarta dauke da tmby, kai ta gyada mata "mami sakon maryam ne "wani mugun kallo ya wurga mata wanda ya hargitsa hantar cikinta da mugun sauri ta bace masa da gani ."
sai lokacin Hjy Zulaiheart ta fahimce abinda yasa taga hankalinsu a tashe a kitchen ,numfashi ta fesar tana kallon bayansa dan tuni ya juya ya koma inda kayan suke tare da rike kugunsa ,qarara ake iya ganin bacin ransa bancin alqur'ani dake cikin kayan daya banka masu wuta gabadaya ya kona dan takaici ." wannan shine soyayya ta gsky da gsky yaji sautin muryar mahaifiyarsa tana magana tana tahowa zuwa in da yake "duk abinda ka gani anan kyautatawa ce ta soyayya tare da nuna kulawa "okay yanzu ta haka ne zai nuna emotiona dinsa ?kai gsky dai wasu mazan jakai ne, ya fad'a yana jan tsaki tare da nufar hanyar step har yayi taku biyu yaji mahaifiyarsa ta kira sunansa "adam !."
cak ya tsaya tare da juyowa ya tsura mata kwayar idanunshi da suke cike da bakinciki" zaka iya kin yarda da wannan kalaman amman at least kayi respect din emotion din wani ,karka wulakanta soyayyar wani domin bakasan yadda taka soyayyar zata kasance ba ,idan kai baka raayin soyayya karka ji haushin masuyin soyayya domin soyayya maganar Allah ce ."shiru yayi lokaci daya emotion din mafarkinsa ya shiga kai kawo a gabadaya ilahirin jikinsa ,mafarkin ma ya daukesa da mahimanci fiyye da komai arayuwarsa wannan tunanin yasa ya bude bakinsa da kyar "alright sweetheart amman yana da kyau idan har soyayyar gskiya ce ya turo magabatansa "ya fadi haka ne saboda ya gaji da ganin fuskar maryam din acikin gidan dan bai san dalilin dayasa ta tare masu a gida ba ,a natse ya juya ya cigaba da taka step fuskar yarinyar mafarkinsa na yawo acikin kwayar idanunshi yayinda mami tabi shi da kallon tausayi tana girgiza kai ."
Sallamar abida né yasa mami ta dauke idanunta daga kallon hanyar da mr ATA ya bi ta maida bakin kofa tsaye take hannunta rike da hannun yesmin sanye cikin doguwar riga yar saudiya mai tsansi sosai cike da sakin fuska mami ta amsa sallamarta tana mata sannu da zuwa "yauwa mami fatan kin tashi lfy ?" ta fada tana zama cikin daya daga cikin kujerun falon .mami ta qaraso ta zauna kusa daita tana kamo hannun yesmin a lokacin mrym da nana hauwa'u sun gama tattara kayan ."
a mutunce suka gaishe da aunty abida sannan suka bar wurin zuwa dakinsu nana hauwa'u na cewa "ai kin dai ji abinda ya Adam yace ?me yace sister ? ban gane me yace ba yanzu ke bakiji yace idan soyayyar gaskiya anas yake miki ba ya turo magabantasa ba ?"oh ! abinda ya fad'a kenan ai gabadaya rudewar da nayi bai sa naji komai ba?ta numfasa sannan ta cigaba da magana "wannan ai ba matsalarsa bace idan naga dama na zauna har karshen rayuwata babu aure bai shafesa ba ,yadda bai son ana shiga lamarin rayuwarsa bai dace shima yana shiga rayuwar mutun ba ".
oh! ai bansan wuyanki ya isa yanka haka ba amman zo muje ki fad'a masa kar ya sake shiga rayuwarki"
nana hauwa'u ta riko tsintsiyar hannunta ta nufi step din da zai kai mutun samansa ,nan take maryam ta zaro idanuwa waje "haba sister kar muyi haka dake mana wannan ai maganarmu ce " a'a babu wani maganarmu ce Ke dai muje kinga daga yau zai kiyaye ,maryam ta fixge hannunta da karfi sauran kadan kwalin hannunta ya subuce "haba sister ! haba sister Ko gskiya? shegiyar masoraciya kawai iskancinki baya qarewa akan kowa sai akanmu yake qarewa dasu anas."maryam ta kwashe da dariya "ai kema Kinsan oga nada ogansa, ina ni ina tarar aradu da fad'in kai ai sai ya tarwatsani , barni na tsira da raina da lafiyata kar ya rage min sadaki suna tafiya suna magana kuma duk akan mr ATA ne ."
shiru aunty abida tana zaune har kusan mintuna shabiyar sannan ta dubi mami da kyau "wai ina ATA ne nasan yau asabar yana gida dan duk kwanakin nan bana ganin shigarsa da fitarsa ?"kullum sai yesmin ta tmbyeni shi shiyasa ma yau nace bari na kawota ta gaishesa tunda weekend ce ta fad'a tana murmushi ,mami ta gyara zamanta tana kallon fuskar yesmin "Adam yana nan galau yanzu nan ma ya hau sama ,kwana biyu da bakya ganin shigarsa da fitarsa yanayin aiki ne kwanakin nan duk bai dawo wa gida da wuri haka zalika da wuri yake fita amman yau kam yana gida bana tunanin ma zai fita dan ma ya dauko rigima ai da kin samesa a kasa .
"Rigima kuma mami kamar wani qaramin yaro ?ta fad'a tana murmushin farinciki".
"wallahi fa nan mami ta zayyane mata abinda ya faru, dariya aunty abida tayi sosai "lallai kam rigima amman ai wani lokacin akan gsky yake abubuwansa ni wallahi yana matukar burgeni yadda yake gudanar da rayuwarsa babu ruwansa da kowa sannan baya daukar raini kamar su abban yesmin koda yaushe hakoransu a bude Kmr masu tallar close up ."
"ikon allah banda abunki abida me zaayi da miskilili? ai gara masu farar nan akan masu nunkufurci da miskilanci sun dan jima suna hira sannan ta mike "to mami ni zan wuce daman abinda ya shigo dani kenan sai anjima . "shikenan abida
na gode sosai da kulawa amman ki bar yesmin ki aiko mata da sabbin kayanta zuwa anjima zaa kawo hanan domin gabatar da birthday dinta "aunty abida tai murmushi "to ai shikenan mami zan aiko mata da...." shiru tayi sakamakon jiyo sautin muryarsa yana saukowa daga matattakala cike da izza da shan kamshi hannunwansa duka zube cikin aljihunsa wandonsa, yayinda iPod Ke manne da kunnensa yana amsa waya yesmin na ganinsa ta kwasa da gudu tana kiran sunansa "uncle AD! Hannunwansa duka yayi saurin zare wa daga cikin aljihun wondonsa ya dauketa yayi sama daita na second biyu sannan ya riketa a gefen jikinsa yana shafa fuskarta sai dai ko kadan babu alamun annuri akan a fuskarsa."
qarasa saukowa yayi ya wuce aunty abida da mami ya daurata akan wani dogon stood mai tsawo yana cigaba da wayarsa murmushi abida tayi najin dadi domin duk cikin jikiokin gidan baya daukar kowa sai yesmin kuma ta fahimci yana matukar qaunar yarinyar sosai hakan yasa itama take mugun qaunarsa fiyye da qaunar burinsu akansa."
a hankali ta qarasa inda yake tsaye "AD ..! ta kira sunansa " baki ga abinda nake yi bane ?ya fad'a a matukar hassale yana wasa da gashin yesmin."Taja bakinta tai shiru na second biyu sannan