Showing 72001 words to 75000 words out of 168608 words
masa a saman goshinsa yayi baki tmkr tawadar Allah ."
ahankali zuciyar mr ata ta soma bugawa da karfin gaske yana jin tmkr ta kunno masa emotion's din da yake ta qoqarin dannewa acikin zuciyarsa nan da nan idanunshi suka canza kala cikin tunanin da maryam take taji yana cewa "yarinyar mafarkina ce dana zanata da hannuna, itace cikar burina ce farincikina ina matukar sonta itace mace ta farko da zuciyata take so .." jin haka yasa gaban maryam yayi wani mummunar faduwa sakamakon jin abinda ya fad'a ta juyo ahankali ta tsura masa idanunta duk da ba karon farko kenan ya ta'ba fadar haka agabanta ba amman na yau din yasa taji wani iri a gbdy ilahirin jikinta ta lura baya iya boye fellings dinsa akan zanen ."
ina ma zata ga fuskar yarinyar taga dame tafita da har zuciyarsa ta zabeta alhalin ita din ba gsky bace ?tuna zane ce yasa ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya mai had'e da zallar kishi "ina matukar sonta auta amamn na rasata a yanzu haka ina son raba rayuwata da tunaninta da duk abinda ya shafeta yana magana yana kallon screen din wayarsa wanda Ke dauke fuskarta "mun dace da juna ko ?ya tambayi nana hauwa'u yana lumshe tsumammun idanuwanshi dake cike da azaban ciwo ."
Nana hauwa'u bata bashi amsa tmyr da yayi mata ba ta kalli maryam dake tsaye tana dubansu idanuwanta cike da kishi ajiyar zuciya ta sauke tace "yaya zamu ce allah ya baka lafiya "na tambayeki baki bani amsa ba ya fad'a a mutukar fusace yana watsa mata harara "me kace ?" shiru kawai yayi tare da tsura mata idanuwanshi itama kallonsa take tasan abinda ya tsana kenan dan hk muryarta na rawa tace "kun..." kun dace sosai kawai dai matsalar ita din ba genuine bace wani dogon tsaki yaja yana cewa "nonsense !"you and this stupid girl should leave this room right now "ya fad'a yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa da sauri ta kamo hannun maryama suka fice daga d'akin ."
Bayan fitarsu kwanciya yayi yana cigaba da kallon hoton screen din wayarsa dayawa daga cikin hotunta ya konasu hatta tsarka zanenta dake wuyansa always yayi flushing dinsa ,kadan ne daga cikin zanenta suke cikin d'akinsa sai na kan screen din wayarsa suma nan kusa yana sa rai zai rabu dasu ya huta da tunaninta sosai yake kallonta "muguwa "ya furta a wahalacce "kin addabi rayuwata kin hanani zaman lafiya ke wace irin muguwa ce da zaki damun rayuwata ?ya tambayi kanshi yana mai kawar da kansa daga kallonta yana tunani "anya bazan dinga zagawa cikin anguwane anguwani ba ko allah zai sa na ganta "? wannan ai hauka ne mr ata kake shirin yi ,me yasa bazaka yarda cewar yarinyar nan ba gsky bace Kmr yadda aka Ke fad'a maka ?
shiru yayi yana jin wani irin buguwa da zuciyarsa ke yi akanta sosai yake son raba kanshi da tunaninta ."
Bangaren maryam kuwa suna taka step tana maseefa "nifa shiyasa bana son zuwa inda yake bashi da aiki sai maseefa da disga mutun sannan wulakancinsa baya qarewa akan kowa sai akaina ko ban shiga tsabgarsa ba sai ya hada dani ni wallahi bana son auren zan dai yi ne kawai dan kun dameni , dan allah ku raba ni da aurensa na huta tunda ba'ayin aure mutun daya ." murmushi nana hauwa'u tayi "na lura kishi kike da zane fa "babu wani kishi sister amman ka auri mutun zuciyarsa na mafarkin wata aljana can wannan ai sai su shafi mutun azo arasa meke damuna "hhhhhhh nana hauwa tayi dariya "yarinya kina da aiki kam dan fasa wannan auren sai dai idan daya daga cikinku ne ya mutu maryam taja tsaki ta d'auki hanyar da zata kai ta d'aki ta shige tayi kwanciyarta dan kar mami tayi amfani da zamanta a parlour tayita aikenta d'akinsa shi kuma ya samun damar ci mata mutunci ."
Mr ata na kwance akai knocking kofar falon yana daga kwance ya bawa mai yi knocking din izinin shigowa hisam ne ya shigo cike da kulawa ya qaraso ya zauan yana cewa "a she bakaji dadi ba ? ya amsa da kai kawai "oh my god amman dai ba matsalar nan bace ? "no ! wannan muguwar yarinyar ce "
maganar ta daki kunnuwan hisham ya dan tsaya yana kallonsa yana nazarin maganarsa "yes muguwa ce taki barin na ganta a zahiri taki barin zuciyata ta zauna yanzu ko mafarkinta nayi bata min magana , bata min murmushi this love is so hurt wallahi muguwa ce amman har yanzu ina jin sonta hisham na qasa cireta araina ."
ya sake kallonsa ya girgiza kai cike da tausaya masa ya mike da kyar ya shiga bayin dake ciki ya zubar da yawu ya dawo ya zauna ya sake kallon hisham yaga shi yake kallo fuskarsa da mamaki ya sake girgiza kai dan gbdy ya fahimci wa yake nufi "gsky wannan yarinyar tana baka wahala " ya langwabar da kanshi gbdy ya koma kalar tausayi "wallahi yau shekara nawa ina faman da soyayyarta amman sam sam yarinyar nan bata tausayina yayi mgnr duk jikinsa ya sake kana kallonsa kasan bashi da lafiya ."
"da ba dan baka da lafiya ba ai da mun dan dinga zagawaya cikin unguwani ko zamu ganta ko wanda yasanya nima nayi wannan tunanina hisham amman bazan iya ba ya fad'a yana lumshe ido yana jin wani d'aci a bakinsa wanda ya rasa na meye ,"karka ce haka ata ka bari idan ka samu sauki kaje france ka dawo lafiya sai mu fara nemanta " nace bazan iya ba wannan muguwar yarinyar kona ganta damuwa zata zame min
a zuciyata ."
Zuciyarsa na zafi yace tashi muje ka d'a zaga gari ko jikinta zai rage nauyin da yake "ya fad'a yana jin tsantsar soayyarta na ratsashi koina ajikinsa ya mike da kyar "ata kayi zauna gida wallahi jikinka babu kwari "karka damu muje kawai tunda kana tare dani bani da wata matsala ahankali suka sauko falon qasa babu kowa a falonta farko da alamun mami tana falonta na uku yaso sheidawa mami amman yasan zata hanashi fita koina dan haka ta kofar baya suka fice dan baya son escourt dinsa su bishi ya zauna shiru a gefen hisham dake tuki yana ciza lip's dinsa "ina muka dosa "?cewar hisham ".
muje gra dan ina ji ajikina a irin wuraren nan zamu samu muguwar yarinyar nan "hisham ya kwashe da dariya har da dukan stearing mota shi kuwa gogan ya hade rai a she a fili yayi mgn ba "wai muguwar yarinyar nan wallahi ata baka da dama
,yanzu dai wani gra ne a kusa damu ?mr ata yayi masa banza ya maida kallonsa gefen titi yana kallon mutane da motocin dake kai kawo "duk da kaki kayi mgn bari muje ikeja gra nan ma shiru yayi yaki cewa komai "gskiy ata ka iya bada suna pricess ta tashi da sarauniya ta dawo muguwa"dan allah malam ban son isknaci ka maida hankalinka ga tuki " ya fad'a yana nuna masa gaban mota da hannunsa "naji amman yanzu ace taki sa'a ka ganta a zahiri zaka ganeta "wallahi zan ganeta ". daga haka bai sake yin magana ba shiru motar tayi babu wanda ya sake cewa komai har suka d'auki titin ikeja ."
Ahankali Ummah da aunty da maryama suke tafiya a hanyar fitowarsu titin unguwarsu domin su dauki hanya zuwa marcaz duba jikin hafsat diyar aunty fati , maryamah ta hango mlm yahuza ya nufo hnayar da suke da littafi a hannunsa da alamar islamiyya zashi tun daga nesa ya fara raragefen alamun Kamala ya durkusa har kasa ya gaishe da aunty da Ummah tare da cewa "unguwa zaku né ? maryama ta d'an kallesa ta d'an basar dan kar aunty da umma su fahimci akwai wani abu atsakaninsu tace" rakiya zanyiwa aunty tare da umma zuwa bakin titi ."
" allah sarki ya sake durkusawa har kasa ya gaidai umma da aunty duk da yasan tahirin rayuwarta amamn bai ta'ba sanya mahaifiyarta acikin kwayar idanunshi ba amman ya gane aunty ce mahaifiyarta dan ko dan yanayin tsawonsu iri daya ne , mlm yahuza yayi murmushi yace "dan allah ku dan jirani minti uku kafin ku isa titi ma na dawo amman dan allah karku tafi a kafa Ummah ta d'an yi murmushi tace "kada ka damu dan allah , kada ka wahalar da kanka ba wani nisa da inda zamu ba mu gode Kwarai da gaske ."
" a dai min Afuwa ina zuwa yanzu Ummah tace tô shikenan mlm yahuza yayi murmushi ita dai maryama ta bisa da kallon mamaki dan bata san me yake nufi da kafin suje titi ya qaraso ba ummah ta dubeta cikin mamaki "wannan kuma wanene ? wallahi malamin mu né na makaranta islamiyya ummah tayi shiru domin ta danyi zargin son maryama din yake itama dai marayam taso ta fada mata kasancewar bata boye mata komai amman ganin fadar bashi da wani amfani tunda da zarar ta amincewa mutun ya fara zuwa kwana biyu sai ya gudu batare da laifin komai ba ."
suna tafiya suna hira har suka karaso bakin titin gwagulori wanda ya dawo sabon titi a yanzu sakamakon gyaran daaka masa suna tsaye kawai sai ga mota ta nufo inda suke maryama tasha jinin jikinta domin dai tasan bashi da mota amman babu mamaki ko ta abokinsa ce yayi burki agabansu ya fito daga cikin motar "umma ku shigo na kaiku har inda zaku "maryama shiru tayi mamaki ne ya damu zuciyarta tunda take bata ta'ba jin mlm yahuza ya dan burgeta ba sai yau sosai tayi farinciki da abinda yayiwa mahaifiyarta da ummanta ido kawai ta tsura masa ta cikin nikaf dinta tana kallonsa cikin farinciki shi kanshi ya fuskanci hakan ."
ya zagaya ya bude masu mota suka shiga kafin ya zagaya bangaren direba ya jefa mata wani kallo mai nuna tsantsar so kawai itama ta tsinci kanta da mayar masa da murmushi suka wuce ita kuma ta koma gida duk da abinda yayi mahaifiyata da ummah a yanzu bata ji ta fara jin mlm yahuza acikin zuciyarta ba amman ta kudirce zata danne zuciyarta ta fara sauraronsa ."
Hud'u daidai ta shirya zuwa islamiyya bata tsaya jiran sakina ba ta kama gabanta acikin aji sune na farkon zuwa ita da kawarta subai'a wacce suka qare karatu tare ahankali suke hira fitowar result dinsu kafin malamin da zai daukesu darasin qurani ya shigo sosai taso tayi mata hirar mlm yahuza amman ta kasa har aka cika a ajin mlm abbas ne ya shigo nan da nan suka fara karatu ita dai karatun yau dai tazo makaranta tayisa amman zuciyarta fal da walwala da irin farantawar da mlm yahuza yayi mata dan tana matukar qaunar mahaifiyarta da umma duk wanda yaga girmansu kuma ya mutunta matasu tô lallai zai samu wani babban matsayi acikin zuciyarta most especially mahaifiyarta tana tausayin halin data tsinci kanta ciki yana daya daga cikin abinda yasa ta d'auki komai nata da mahimmanci ."
"ta godewa allah ta kuma ta godewa mahaifiyarta da umman tare da abban sadam domin sun tsaya akan ganin sun ingata rayuwarta da karatun boko da Arabic tun alokacin da take secondary babu wanda yasa rai zata cigaba da karatunta zuwa jamia sai gashi kwatsam allah ya taimakesu ita da subai'a sun samu scholarship daf da zaa tashi ta shigowar mlm yahuza makaranta ,taso Kwarai ta gansa tayi masa Godiya ta fito tana duddubawa ko zata gansa amman bata ganshi ba zuciyarta taso ta gansa farincikin da yasa iyayenta take son tayi masa godiya dan tasan dole zai ji dadi acikin ranshi ."
Bayan an tashi daga makaranta bai biyota ba kamar yadda ya saba sai dai kafin ta isa gida kanwarsa nafisa tayi saurin isa inda take daman kuma tasanta sai dai ba aji daya suke ba tana gaba daita sosai suka gaisa tare daita suka cikin gidansu inda suka iske aunty salma a tsakar gida tana zaune tana waya ganinta tare da nafisa yasa aunty salma kashe wayar suka gaisheta suka wuceta suka shiga bangarensu maryama." suna shiga ta nuna mata wajen zama "nafisa ki zauna ga waje tayi murmushi ta zauna akan kujera ita kuma ta shiga dakin aunty ta duba inda aunty tasaba ajiyar kudi taci saa ta samu naira dari ta dauka ta fito tana cewa nafisa "ina zuwa ."
"nafisa ta mike ta biyota ina zaki bari muje tare maryama tayi dan Jim dan taso ta zauna taje ta siyo mata lamurje ta kawo mata amman bata da choice dole ta barta suka sake fitowa tare kai tsaye bangaren aunty hassana suka shiga tayi sallama ta isketa zaune tare da yaranta babu wanda ya amsa sallamarta bare ya kalli inda take bata damu ba dan ta saba "aunty hassana ina yini akwai lamurje?
"Akwai na nawa zaki tsiya "?amm.. na naira dari ne wani dogon tsaki taja "ai nasan bazaki canza zani ba daga na naira darin babu qari kullum ana waje daya baa cigaba ni bani kudin ki shiga ki dauka ki bace min da gani ."
Zuciyar nafisa ta cika da mamakin aunty hassana maryama ta mika mata kudin ta shiga ciki ta dauka suka fito ta mikawa nafisa gashi nafisa babu yawa "kai haba ai babu komai ai danasan ma kashe kudinki zakiyi da tun farko na hanaki " karki damu ai ba wani abu bane maryama ta fada tare suka shiga bangaren Ummah duk inda maryama tasa kafarta nan nafisa take ajiyewa ta share wa umma gida ta gyara mata koina tare da nafisa suka fito zasu wuce aunty salma ta kirata cike da isa ta isa inda take "kije kiyi min shara "
"Shara !"
Maryama ta furta a hankali?eh ko bazakiyi bane kika tsaya kina maimata min abinda na fada ?zanyi ta fada a taikaice tare suka shiga bangaren aunty salma ta fara shara "aunty maryama kawo na share miki da sauri dan akwai abinda ya kawoni "? itama tashi jinin jikinta dan tunda suke da nafisa bata taba zuwa inda take ba sai yau "no ki barni na share nima yanzu zan gama ta zauna akan kujera sakina da shukura suka shigo shukura na ganinta ta washe mata hakora "nafisa yau kece agidanmu ?ta tambayeta murmushi ya sake bayyana akan fuskarta "eh nazo wajen aunty maryama ne "aunty kuma ?ta fada a rude "eh mana aunty ce ai maryama tunda zuciyar babban yayanmu ta kamu da matsanancin sonta dan har wani kirki ya kirkirawa kanshi dan kawai ya aikoni wajenta ta fada batare da wani shakka ba ."
shukura batace komai ba ta zauna kusa da nafisa " inata son nazo gidanku amman ban samu damar zuwa ba saboda makaranta nafisa tayi murmushi "ai kuwa sai ki arawa kanki lokacin ki dinga zuwa gidanmu tunda yayana ya kamu da soyayyar maryama nasan naki matsayin sai yafi nawa zance bai yiwa shukura dadi ba dan haka kawai taji bata son wata halaka a tsakanin maryama da mlm yahuza haka kawai take jin rashin jin dadi aranta ."
Maryama tana gama shara ta fara kokarin wucewa yayinda nafisa take qoqarin mikewa shukura kuma tana janta da hira "kinga bari na isar da sakon da aka aikoni gobe ma hadu a islamiyya ta tashi tabi bayansa maryama suka jera har cikin falonsu atare suka zauna akan kujera nafisa na cewa "aunty nah "maryama tayi murmushi "kai nafisa da ki daina ce min aunty kullum fa da sunana kike kirana "ai yanzu komai ya canza baki ji yan karin magana ba sunce idan kidi Ya canza dole ma rawa ta canza nafisa ta fada tana dariya "ya karatu yanzu uzukin nawa ?maryama ta sauya magana dan bata son wata maganar soyayya mlm yahuza yayi mata mutunci Kwarai kuma ta yaba masa amman batu na soyayya bata jin zata iya
yayana ne yace na fad'a miki zai zo zuwa anjima maryama tayi murmushi amman shine tun dazu baki fad'a ba kika zaunar da kanki "ai ina sane na zauna ina qarewa zabin yayana kallo naga shin haukan da yake akanta ya dace abun mamakin sai naga tafi gaban tunanina ashe da kawai kallonki nake ta fad'a tana dariya "kai nafisa a she haka kike kema?maryama ta fad'a tana murmushi santi nake yi yayana ya iya zabe wallahi maryama nayi matukar farinciki da yaya ya sanar dani Ke yake so kuma har kin amince nan fa yanayin maryama ya sauya daga murmushi da take zuwa mamaki "ita a ina ta amince masa da zai qarar .?
"kun dace da yayana sosai ni daman ina tunani wa yahuza zai dauko mana acikin yammatan dake mutuwar sonshi saboda tsananin kyawunsa da kyawun halinsa uwa uba ilimi kema kuma munyi saa a komai kina dashi taso kwarai ta tsaida nafisa akan yayanta amman kuma sai ta kasa har zuwa lokacin data ciro wata karamar takarda ta bata tace gashi inji yaya in baki hanuna da naki ta fad'a tana shirin tashi daga kan kujerar da take zaune itama maryama ta tashi ganin tana alamar fita domin rakiyarta da hannunta ta dakatar da maryama "zauna abunki ba sai na wahalar dake ba ki zauna ki karanta sakon yayana cikin tsigar wasa maryama tace "ban son iskanci nafisa naga alamun raini ya fara shiga tsakaninmu ta bude baki "ni kuma asuwa na raina aunty amman dai Kiyi zamanki wallahi na gode ?"
Ta koma ta zauna ganin idan ta biye mata sai su kai dare bata gama iskancin ba ta fice ita kuma ta samu waje ta zauna ta bude takarda da nafisa ta bata ."
_Ina son ki takaita kanki da abinda kikasan zai war gaza farinciki dana gani akan fuskarki ina bukatar ganinki cikin farincikin dana ganinki dashi yau my maryama ina son jin muryarki cikin kunnuwana ina son jin hirarki zanzo yau byn sallah ishai_
Ta sake karantawa ta sauke naunayen ajiyar zuciya ita sam bata jin wata soyayyarsa wata killa da a shekaru biyu da suka gabata yazo lokacin tana shekara shatakwas kuma alokacin maza basu zama abun tsoro a wajenta ba da babu mamaki taji tana sonshi har ma ta iya aurensa amman zatayi kokari ko yaya ta fahimtar dashi illa soyayya gareta ."
ahankali ta jingina