Showing 132001 words to 135000 words out of 168608 words
akawo maka breakfast ."
Yace " zulai ba sai na zauna ba nazo ne na sheidawa adamu tun jiya baa ga halimatu ba daga zuwa siyaya nan da nan hankali mami ya tashi "baa ganta ba to ina taje ?kuma an kira layinta bata d'auka ba ?wallahi kwana mukayi kiran layukanta guda biyu shiru abinda yafi daga min hankali bata saba irin haka ba ,kuma duk runtsi ka kira wayarta zaka sameta "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun mami ta furta tana cewa "Allah ya cecemu " ATA ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yaga lokaci ya fara tafiya ya bude bakinsa da kyar yace "baba babba muje daga waje yana gama fadar haka ya nufi kofar fita suka bar mami cikin tsananin damuwa ."
tare suka jera har haraban estate din baba babba yana sake masa bayanin tashin hankali da suke ciki "ka kwantar da hankalinka baba nasan inda take "wani irin naunayen ajiyar zuciya baba babba ya sauke yana dubansa a tsanake tare da neman qarin bayani ."wani dan bincike zaayi akanta da zarar an kammala zata dawo gida "shiru baba babba yayi yayinda zuciyar tsohon ya shiga bugawa fiyye da kaida domin kai tsaye kwakwaluwarsa ta hasko masa binciken da zaayi akanta muryar tsohon a sanyaye yace "to allah yasa muji alkhairi" ameen !ATA ya furta atakaice anan suka rabu yayi masa sallama ya nufi inda motacinsa Ke jiransa dan tun fitowarsa aka gyara tsayuwar su , tun kafin ya qaraso escort dinsa dake tsaye tmkr mashi suka yo kanshi cike da girmamawa ya shiga mota suka bar gidan ."
Bangaren nuzla kuwa gaba daya duniyar ce ta cakude mata waje daya bata ta'ba sanin haka tashin hankalin irin wanda take ciki yake da ciwo ba"ta dauka zafi da ciwon rashin son da yaya adam ya nuna mata shine damuwa mafi tsayi arayuwarta a she qaramin abu ne damin kwana daya tal da tayi acikin dakin kurkun da take ciki ya ninkashi sau babu adadi ,tana durkushe bisa gwiwowinta tare da rufe fuskarta da tafukan hannunta taji motsin ana bude qaramin kofa ,bata bude idanunta ba bare taga masu shirin budewa ,wata murya taji ta doki dodon kunnenta cikin tsawa tana bata umarnin ta fito sai lokacin ta bude idanunta da suka kumbura tsabar kukan data kwana tanayi ."
Koda ta motsa qafafuwanta dan mikewa sai taji ta kasa yunkurawa dan sun qara sandarewa kamar dotse ,hannunta ta kai ta rike karfen kofar sannan ta kai dayan hannunta ta riko kafarta daya ta yunkura da kyar ta mike tsaye ,ahankali ta fito wani qaramin daki aka nufa daita, babu laifi yafi wanda ta fito tsafta kujeru biyu tagani sai table dake tsakiyarsu ."tun kafin abata umarnin zama ta zauna dan kafafuwanta bazasu iya cigaba da daukarta ba ,mutumin daya shigo daita ya fita byn second biyar wata police mace ta shigo fuskarta a hade
har tafi na farko ban tsoro da razanarwa duk da bata aikata komai ba amman zuciyarta ta cika da tsoro mai tsanani ."
Idanunta na kan nuzla ta ajiye wukake har guda uku akan table din gabanta sannan ta zauna tana fuskantarta ,nan nuzla ta sake tsurewa hankalinta ya sake tashi wasu hawaye masu zafi suka samu nasarar gangarowa daga kwarnin idanunta ."
Bayan mintuna goma police ta soma da tmbyr sunanta ta dago idanunta dake zubar da hawaye ta bata amsa sannan ta cigaba "yanzu dai sheidar da muka samu daga bakin danuwanki ya kore duk wata hujjar da muke nema akan masu amfani da wannan wukar wajen kisa da fari ko zamu san dakilinki nayi kisan ?
Nuzla tayi shiru dan bata da amsar da zata bata sai dai ta dago ta zuba mata idanunta tana kallonta hawaye na zuba daga kwarnin idanunta ,ganin yadda matar ta soma huci tana fito da jajayen idanunta yasanya hankalin nuzla qara tashi ba shiri ta soma mgn cikin rawar murya "ni ..ni ban kashe kowa da wannan wukar ba, hasalima ni a yanzu na fara ganinta "amman ai kin ta'ba turawa yayanki adam sakon zaki ga bayan matar da zai aura ko me zaki iya cewa akan haka ?babu abinda zan iya cewa akan haka baya ga qaddara , kuma nasan tana iya fadawa akan kowa ,a garin na tsoratar dashi akan tsananin soyayyar da nake masa wannan matsalar ta faru dani ."
"kenan kin tura masa sakon cewar zaki ga bayan matar da zai aura ? ta runtse idanunta wasu ruwan hawaye masu zafi suka zubo mata ta gyada mata kai "Eh! na tura masa amman ban aikata komai ba"karya kike karki wahalar da hukuma domin yin hakan yana qarawa mai laifi laifinsa dan haka ki fad'a mana gsky domin kawowa rayuwarki sauki "
Nuzla ta girgiza mata kai jikinta na rawa "Allah ki yarda dani ban san komai ba "da fari kin kashe mubina wacce ta kasance yar uwa agareki kin kashe sadiya dake aiki tare da yayarki shahida yanzu kuma kinyi yunkurin kashe mrym shiru tayi kawai tana tunani wacece sadiya kuma ?ta dai san mubina da maryam amman sadiya kam bata santa ba ."
"Kin kashe mubina yaruwarki dan ta furta tana son adam haka zalika kun hadu da sadiya a hospital kafin rasuwarta itama ta furta tana son adam kin yunkuro kan mrym ita kuma dan ta amince zata auresa kin kashe mutun biyu din nan adalilin sun furta suna son abinda kike so ko ba haka ba ?
Ji tayi zuciyarta ta tsaya CAk ta daina aiki na wani lokacin kafin daga baya taci gaba da bugawa ji take magaarta ba'a kunneta kadai ya tsaya ba har cikin zuciyar ta take jin komai saboda dacin kalmar ."
"kuka ta saki mai cin rai meke shirin faruwa dani ?ta furta a fili cikin tashin hankali da firgice ,wai ita ake zargi da laifin da ba taji ba bata gani ba kallonta tayi da idanunta da suka koma kmr an diga jini acikinsu , tace "me zakice akan haka ?daga kalmominsa komai ya sauya mata ta gane ita din ba kowa bace sannan ta soma fahimtar bata isa tace zata ma kaddarata wayo ba ,yau din taxo mata da tashin hankalin da rudani ya zatayi da kaddara da ta fada mata " ?duk yadda yarsanda taso ta amsa laifinta amman taki dan haka ta mike ta fice ta bada umarnin a canza mata daki zuwa wani dakin dabam ."
Ai tana shiga dakin hawaye nadamar furucinta ya kufce mata domin har gara dakin farko daaka sakata dan wannan bashi da maraba da kabari yayinda zarninsa da warinsa da duhunsa ya zarta duk wani wari da mutun ya ta'ba ji tana kuka tana istigifari" Allah na tuba Allah ni bawar ka ce ya Allah kasani ban aikata laifi mai muni hk ba amman na kudurta yinsa ka gafartamin ban isa na maka wayo na hana faruwar kadarata ba " Allah ka kawomin sauki cikin wannna tashin hankali".
kuka tayi sosai ,sai dai duk rintse bazata taba karban laifin da bata aikata ba ."Ahankali kwakwaluwarta ke son tuno mata wacce sadiya dake aiki da aunty shahida da tunanin wanda zai iya aikata wannan taadanci acikin danginsu a daura mata , sai dai duk tunaninta kwakwaluwarta ta kasa gano kowacee sadiya da kuma wanda yayi amfani da damarta yayi mata haka ,hakika bata da makiyi kamar shi kuma ya cutar daita ya zalinceta ba kuma zata ta'ba yafe masa ba ,wajen bazai isheta zama ba dan hk ta gwamaci ta kwana acikin zarni da kazantar waje tana kwance taci kuka ta koshi idonta sunyi lulu dasu ."
Qarfe biyu daidai na rana ya fito daga cikin makeken office dinsa kai tsaye hanyar massalacin dake cikin ma'aikatan ya nufa yayi sallar azahar sannan ya bawa direbansa da masu tsaronsa umarnin tafiya police station babu bata lokaci kowannensu ya zama ready yana qarasa isowa aka bude masa mota ya shiga suka dauki hanyar police station yana shiga kai tsaye da cp Amir suka hadu suka tsaya suna magana akan nuzla suna gama magana cp yayi gaba zai masa iso wajen dpo ."tun kafin ya kai ga shiga dpo ya mike ya fito da kanshi cikin girmamawa yau ga matun kamar adam tariq abdullahi acikin station dinsu dan kasuwan daya fi kowani dan kasuwa kudi ya shiga office din suka zauna cp ya basu waje suka gaisa sannan suka soma tattaunawa akan nuzla ".
"ranka ya dade mai zai hana awuce kotu kawai ?ciza lip's ATA yayi yana girgiza kai muryarsa a matukar raunane yace "a'a nan ma ya isa banason aje ga kotu fatana ma ya zamanto babu hannunta ciki ,amman yanzu abi mataki na karshe ayi amfani da sheidar hannunta "muma shine last option dinmu domin shi zai warware komai ya runtse idanunshi hankalinsa na sake tashi babu wanda yake tausayi Kmr mahaifinta da mahaifiyarta yayyenta da kuma masoyinta hisham ya tuna halin daya gansa yau din gbdy baya cikin natsuwarsa haka ma yan'uwanta ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana cewa "ko zan iya ganinta ?why not ranka shi dade "inspector runke !ya kwallawa yarsandar dake kan kanta kira cikin girmamawa ta shigo sai data sara masa sannan ta kame waje daya "jeki fito da yarinyar nan wacce akawo jiya "Okay sir ta fad'a tana juyawa cikin sauri ."
Tana fita ATA ya kalli dpo "amman babu wanda ya ta'ba lafiyar jikinta kawai gsky nike bukata ?"yallabai babu wanda ya ta'bata yarinyar ma bata da rigima tunda aka kawota take kuka, very gud kar wanda ya ta'ba lfyta in sha allahu yadda kace haka zaayi batayi ma rashin kunyar da zaa ta'ba lafiyarta ba kawai dai taki amsa laifinta ne ya qarasa mgnr adaidai lokacin daaka shigo daita kallonta kawai yayi yana mamakin yadda kamaninta ya canza acikin kwana daya da yinin datayi ga dai shi babu alamun duka ajikinta amman cizon tsoro yayi mata yankan qauna ga dotti ya soma zama ajikinta tana ganinsa ta fashe masa da kuka tana cewa "dan girman allah yaya adam ka ceceni kasa a fitar dani daga nan wallahi idan na cigaba da zama anan mutuwa zanyi wallahi ban aikata komai ba ."
ATA dake kallonta ya sake hade fuska babu wata alamun tausayi bata damu da yanayinsa ba dan tasan halin miskilancinsa da zafin zuciyarsa dpo Karan kanshi ya tausaya mata ya nuna mata wajen zama ta zauna ATA ya tsareta da idanunshi yana kallonta yayinda ita km ta cigaba da sheshekar kuka "har yanzu kenan baki shirya fad'ar gsky ba ?ban aikata komai ba me yasa zan amsa laifin da ban aikata ba wallahi kasa a tsananta bincike ni nasan ko waye acikin estate dinmu yake amman ni ban aikata ba ,wani kallo yayi mata sannan ya mike tsaye zaa yi bincike na karshe akanki kiyi adduar babu hannunki dan muddin ya zamoto kece zaki qarasa rayuwarki a inda yafi nan muni yana gama fadar haka ya bada umarnin a fitar daita tana kuka tana kiran sunansa aka fice daita ya kalli dpo yana sake jadda masa kar ta'ba lafiyar jikinta har sai an gama bincike yayi masa kyauta sannan ya wuce ."
*****
bayan tafiyarsu alhj alqasim ummah suna hira da maryama tace da zarar kin qare bautar kasa kema zanyiwa alqasim magana ya nema miki aiki mai kyau ta yadda zaki samu damar taimakawa aunty ,dan Allah ummah kiyi masa maganar idan ya dawo kinga yace qasar ma zasu bari kinga idan yasan da maganar wata killa zai barwa wani sallahu".
" in sha allahu maryama zanyi masa mgn kuma nasan zai min wannan alfarma bare kuma naga alamun kin kwanta masa arai murmushin jin dadi maryama tayi tace "ai duk saboda ke ne ummah darajanku naci banci haka ai bazan taka matsayin ko daura kwayar idanuna akanshi ba ".
hirar sukayi sosai cike da so da kulawa wata ya qare ummah ta saka ran zuwansu alhji alqasim amman shiru har wani wata ya kai goma dan haka ta fidda rai da ganinsa koda ummah tayi hirar da maryama ta rausayar mata da kwayar idanunta domin ita a ganinta haka masu kudi suke da fad'ar abu su fasa mussaman idan bai shefesu ba "ummah karki wani damu da rashin zuwansu tunda daman su suka saka kansu ba wani ne ya sakasu ba ."
Satin da suke ciki ya qare babu dalilinsu sai da aka sake shiga wani sati sai ga wayarsa yana sanar da yaya sadam yana nan zuwa ranar lahadi ranar suna jumaa dawowarta kenan daga wajen aiki ta samu labarin zuwansu daga bakin ummah ai kuwa dadi kmr ya kasheta da murna ta shiga side dinsu tana sanar da aunty cewar ranar lahadi zasu zo dan daman ta fad'a mata taimakon da ummah zatai mata sosai taga farinciki a fuskar aunty daman ita kadai take tausayawa a rayuwarta tana son ta taimakawa mahaifiyarta amman bata da hali ,dan zanen da take ba wani manya kudi yake kawo mata ba sakasancewar sai kayita bin office office na masu kudi dan ba kowa ya gama saninta ba bare su nemeta dan kansu, gashi tana son fitar da mahaifiyarta cikin wahalar da take ciki amman bata da iko sai dai ta mika lamuranta zuwa ga Allah dan ya kawo masu saukin halin da suke ciki.
ranar lahadi aka sake maimata irin hidimar daakayi masu a wancan ranar sai dai kuma wannan zuwan nasu akwai qarin abubuwa masu yawa daakayi karfe goma da yan mintuna motarsu ta tsaya a sabon titi market street wannan zuwa babu driver da babban dansa yusif da kuma kanwarsa Kausar sai dady da yake zaune a bayan mota ranar kamar wacan ranar yaya sadam ne ya tarbosu zuwa cikin gida sai dai shi Yusif bai shigo ba ya tsaya a haraban gidan yana amsa waya ."sakina aunty salma da aunty hassana da yayanta da baba gali duk suka fito tarbonsu ita kuwa maryama sai ta koma dakin ummah duk da tana bukatar farinciki wa rayuwarta amman sai ta boye kanta ."Kausar tafi yusif surutu dan ita take ta haba haba da su sakina da Islam da kaulat har ma da shukura da bata ta'ba ganinsu ba umma ta fito suka gaisa ta tmbyesu hanya ."
Wannan dalilin yasa ta fito daga dakin umma dan karta kwatanta na kwana baya sai dai ta kasa shiga cikinsu ta rabe can nesa dasu byn ta gaishe da dady ta fito ta zauna a tsakar gidansu hannuwan yusif acikin aljihu ya shigo bakinsa dauke da sallama wacce ta makale a fatar bakinsa ganin maryama ya tsayar masa da sallama ya tsura mata ido jikinta ya bata ana kallonta dan haka ta dago a natse domin ganin mai kallonta nan take ta firgita ta qara gyara zamanta da daidaitawar mayafinta." ya tsura mata ido sosai yana kallonta ahankali yace "sannu !"
sautin muryarsa ta doki dodon kunnenta amman ta kasa maida masa da sannun da yayi mata sai sunkuyar da kanta tayi dan bata son yawon kallo shine ma dalilin da yasa take yawo da nikaf duk inda zata dan sai mutane suyita kallonta wai tana da kyau da sauri ta mike ta nufi hanyar side dinsu ya dan lekota adaidai lokacin data waiga suka hada ido jin alamun tafiya yasa ya dawo da natsuwarsa sannan ya shiga cikin parlour'n umma da sallama tana ganin shigarsa ta dawo dan bata son tayi nisa ummah tazo tana nemanta ai kuwa tana zama tajiyo sauti muryar ummah tana kiran sunanta jiki a sanyaye ta shiga parlour'n ta durkusa."
Kausar na ganinta ta fadada murmushinta ta riko hannunta "mamana ta bani labarinki ta fad'a hannunta na cikin nata maryama tayi murmushi wanda Ke bayyana kyawunta tace "da fatan tana lafiya? tana lfy tana can tana kewarki tace kin fini kyau da kunya har ma da qoqarin karatu da fari na karyata amman yanzu na gasgata a ganin da nayi miki a karon farko ,alhj alqasim da ummah sukayi murmushi yayinda yusif sai kallon maryama yake bai ce komai ba Islam kam sai wani yatsina fuska take jin yadda kausar ke yabon maryama ,alhj alqasim yace "ku bamu waje kuje kuyi hira "maryama muje wajen mamanki mu gaisheta lumshe idanunta tayi tare da cewa "to !
Hannun kausar na cikin na maryama suka fice Islam na biye dasu a baya maryama ta lura da irin kallon da yusif yake mata dan haka tasha jinin jikinta ,suka shiga side dinsu kausar tabi falon da kallo sannan ta dawo da kallonta kan maryama "tabbas nayi farinciki da ganinki a matsayin wacce mamana ta yaba da halinta har ma naji qaunar yin kawance dake ."maryama tayi murmushi kawai dan ita bata iya doguwar hira ba sai dai acikin ranta taji dadi ,ko bakya sona da Kawa ?ya zaayi naki sonki da qawa ai daman ke qawata ce kuma yaruwata ,ta rike hannuwan maryama da'ace acikin gari kike da yanzu ana nan ana hada gumi akanki maryama bata fahimci maganarta ba sai dai ta fahimci tana yi ne akan kyawunta murmushi tayi tace "akan me zaa hada gumi akaina ."
Ta gyara zama "kyawunki yafi karfin zama acikin geto area bakowane acikin geto area hk zai iya cewa yana sonki ba saboda sanin kinfi karfinsa ko kina da samari ?"Sosai ta bawa maryama dariya ta kuma girgiza mata kai alamun bata da dan ganinta shi ya fiye mata sauki akan tace sun gudu sun barta ne ko kuma an kwace mata ,ai dole samari suji tsoron zuwa irin wannan kyau Masha allah wallahi ba wasa nike ba tun kafin na ganki momy ta fad'a min tayi min kyakkyawar qawa jinta kawai nayi domin ina jin babu wata macen da zan iya qawance daita anan amman ganinki na sha mamaki banda qawa zaki iya zarce komai agareni maryama tayi murmushi kawai tace "na gode ."
"Kinga yayana yusif?
Ta tambayeta tana kallonta "ko da yake ba sai anji a bakina ba maryama ta tsura mata idanu kawai tana kallon kausar cikin rashin fahimta dan ta fuskanci kausar nada yawon magana sosai ita kadai take kidinta take rawarta,dan ko tmbyr manufar abinda ta fad'a batayi ba ta rabu daita suka cigaba da hirar geto area ."acan kuma parlour'n umma alhj alqasim da baba gali da yusif da yaya sadam suna zaune bayan sunci abinda aka kawo masu saí