Showing 27001 words to 30000 words out of 135096 words
cikin gidan, babu wanda yake da wannan damar ta shiga cikin gidan kai tsaye, ko ba Aiken sa akayi ba se Yusuf, shi Yusuf be san da wannan dokar ba ma sam, kai tsaye ya shiga Babban falon da yake shine mahaɗar iyalan gidan.
Ya shiga da sallama a bakin sa, ya tarar da Amal a zaune tana kallon zee world, tana ganin sa tayi murmushi tace
"Sannu da zuwa, yau ka makara fa"
Murmushi yayi yace "Allah ya bada haƙuri, Madam ta tashi ne?"
Amal ta kwaɓe baki tace "waya san mata, ka zauna mana ka tsaya a tsaye"
"karki damu nidai ace mata nazo"
"Ni ban zanjeba seka zauna"
Yusuf ya zauna a ƙasan carfet, Amal ta ɓata fuska tace "ya zaka zauna a ƙasa kuma, haba Yusuf dan Allah ka zauna"
Haka Amal ta uzzura masa seda ya zauna akan kujera, ta miƙe tsaye tace
"bari in kawo maka ruwa, kafin ta fito bana so inje ta Wulaƙanta ni, idan ta ga dama zata fito da kanta" tana gama faɗin haka ta miƙe ta shiga wani ɓangaren.
Yusuf na nan zaune, ya ɗakko wayarsa yana ɗan daddanawa, sega Nura direba ya shigo da wata babbar jaka a hannun sa, da alama Aiken sa akayi yana ganin Yusuf a zaune akan kujera yayi turus yana kallon Yusuf.
Yusuf ya ɗaga kai ya dube shi yace
"ya dai Nura? Naga ka tsaya kana kallo na kamar baka sanni ba"
Kafin Nura yayi magana, sega Ramla da mahaifiyar ta sun fito, idon Ramla ya sauka akan Yusuf dake zaune akan kujera, buɗe baki tayi tace
"iyeee samun guri, ɗan kuturu da gaɗa cikin Rama, wato isarka da ƙasaitar taka harta kai ka dinga zama akan kujera sannu fa"
Rai a ɓace Mummy tace
"Kai ubanwa ya baka izinin shigowa falon nan harka zauna akan kujera, gidan ubanka ne kona uwarka da zaka shigo min falo ka zauna akan kujera, kai na fuskanci kanka na rawa fa"
Amal ce ta fito da ruwa da cup a hannun ta, ta ƙaraso falon tace
"Haba Mummy dan Allah kiyi haƙuri, wallahi ni nace ya zauna"
Yusuf kam shiru yayi bece komai ba, zama akaan kujera kawai yaja masa zagi da cin mutunci.
"dalla rufe min baki, se nayi maganin yaron nan, saboda jin kansa yake kamar ɗan uban wani, matsiyacin banza ɗan talaka, dama haka kuke baku iya samun guri ba, kana wani sumi sumi da kai mara mutunci, dama gaba ɗaya siffofifinka na munafukai ne bari Alhajin ya dawo, sena sa anyi maganin ka, bazaka tashi ba kana jina ina magana "
Gaba ɗaya ran Yusuf ya gama ɓaci, kujera kawai wannan akanta ake masa wannan cin zarafin.
A hankali ya yunƙura ze tashi rai a ɓace, cikin tsawa da rashin mutunci Ramla tace
"ba magana ake maka ba ba zaka tashi ba, banza kawai ɗan talakawa, an kusa korarka kowama ya huta, dalla tashi sakarai"
"baze tashi ba, Kujerar ba wani ya kawo ta ya ajiye ba se mamallakin gidan, dan haka babu wanda yake da ikon cin zarafi ko korara wanda ni yakewa aiki a gidan nan, baku kuka ɗauke shi aiki ba, Kuma duk wanda yake tunanin ze kori wanda na ɗauka aiki sedai ya bar gidan nan tunda mutum ba gidan nasa uban bane"
Widad ce tsaye sanye da gajeren wando, da vest a jikin ta gashin kanta a kwance a kafaɗarta kamar yadda ta saba shigar ta, cike da isa da nuna tsantsar iko tayi maganar.
Ramla ta harzuƙa za tayiwa Widad rashin mutunci Amma Mummy ta hana ta.
Widad tace "ki ƙyaleta ta faɗi abunda take so mana, keda ita kun sani banbancin ku da masu gadi da direbobin nan kaɗan ne ai, dan haka ku tsaya iya matsayin ku, kar wanda ya ƙara shiga hurumi na da wanda yakemin aiki, wannan ya zama kashe dina da gargaɗi na na ƙarshe a gareku, babu ruwan ku da ma'aikata na, wallahi duk wanda ya kuma karyamin doka zanyi ba dai dai ba, na gaya muku"
Wani ƙululun baƙin cikine ya ƙule zukatan su, a gaban masu aiki tayi musu wannan cin zarafin da wulaƙanci, saboda wannan sakaran talakan.
Widad ta ɗago idanunta cike da rashin mutunci da tsantsar izza ta kalli Yusuf tace "kai kuma biyo ni"
Jiki a matuƙar sanyaye Yusuf ya miƙe yabi bayan ta, kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, dan yasan tistiye shi zata yi da tambayoyi.
Share please
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Special thanks to all members of my Association
Perfect writers Association may Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will bring positive changes to our Community.
PART1
Page 8
Jinjina kai Mummy tayi ta juya ta nufi part ɗinta, jiki a saɓule yaranta na suka bi bayanta.
Koda taje ɗakin ta safa da marwa ta shiga yi tana sauke wata nannuyar Ajiyar zuciya me bayyanar da tsantsar baƙin ciki da takaici.
Ramla ta numfasa tace "Mummy akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa akan wannan ɗan iskan mutumin, na rasa Wani asiri yayi wa wannan daƙiƙiyar da take tozarta ki akansa, kawai kisa a kawar da shi daga hanyar ki mana"
A gigice Amal tace "A'a Ramla, meye laifin sa? Laifin sa fa kawai ya hau kan kujera, shikenan Amma Widad ce tayi laifi anan bashi ba, kiyi tunani mana"
Ramla ta daka mata tsawa ta hanyar cewa "dalla rufe mana baki, dalilin wa akayi mana haka, a gaban masu aiki aka Wulaƙanta mu? saboda wanna ɗan matsiyatan ne me kama da mataccen silifas, wallahi Mummy ko baki ɗau mataki akan sa ba ni zan ɗauka, zan ɗau matakin da ya dace da shi da gaggawa"
Cikin hanzari Mummy tace "A'a Ramla da alama akwai Amfanin daze iya yi mana a nan gaba, nasa Isa mai gadi ya binciko min ɗan wace unguwa ne"
Ramala tace "Mama Isa megadin me? Me ze iya tsinanawa, kawai Kisa abi bayan sa kawai a gano inda yake, kuma ɗan uban waye shi"
Amal cikin sanyin jiki tace "dan Allah Mummy karkisa a masa wani abu dan Allah, abi komai a hankali"
Mummy tace "dalla rufemin baki sakarya!"
Ramla tace "Mummy ƙyaleta dan Allah, me abun haushi kawai, Amma Mummy ta yaya ze iya mana amfani a nan gaba?"
Murmushi Mummy tayi tace "zan miki bayani Ramla, ba zanyi a gaban wannan shashashar ba, dan yanzu na kasa gane inda tasa gaba"
Widad kam, suna zuwa falonta ta tsaya ta juyo ta kalli Yusuf, ta ƙure shi da ido tun daga sama har ƙasa, yayin da shi kuma ya ƙi yadda ya ɗago ido ya kalle ta, ta daɗe tana kallon sa tana nazarinsa.
"Look up" ta faɗa a taƙaice, ɗan ɗagowa yayi ya kalleta ya maida kansa ƙasa.
"Ya aka yi na dawo gidan nan jiya? Meyafaru dani a gurin party jiya?"
Dama Yusuf yasan a rina, dan haka a dake yace
"Eh kin faɗi ne akan stage, shine muka taho gida"
"Malam ƙarya kake, ka gayamin meyafaru? Ko kaima kazo ne dan a haɗa kai da kai a cutar dani?"
Yusuf ya girgiza kai yace "Me yasa kike tunanin za'a haɗa kai dani a cutar dake? Meye riba ta in an haɗa kai dani an cutar dake?"
"Saboda talaka ba abunda baze iyayi akan kuɗi ba, An haɗa kai da kai an turo ka ka cutar dani, in ba hakaba meyasa lokacin da nace kasa hannu a death contract ka yadda ba tare da ko ɗar ba ka cigaba da aiki dani? Wannan shi ne karo na biyu kana min ƙarya, meyasa? Ta yaya zan faɗi haka kurum bani da wani special case, se taɓin hankali, shima kuma ƙaƙabamin shi akayi, ta yaya haka zata faru? Bana tunanin na samu mental attack ne haka kurum a gurin nan, Ka gayamin gaskiya you are here to kill me, you were sent by someone to kill me " cikin ɗaga murya, tare da tsantsar rashin yadda take maganar.
Gaba ɗaya ta birkice, Yusuf yai shiru ya ƙura mata ido yaƙi cewa komai.
A fusace tace "talk to me!!"
"Am not here to kill you, na karɓi aikin nan ne saboda shine last option ɗina, idan banyi aikin nan ba babu wata hanya da zan samu abunda zan kula da kaina da mahaifiya ta, talaka ze iya komai akan kuɗi, Amma be kai yadda me kuɗi zeyi ba, me kuɗi yafi talaka son kuɗi da aikata komai dan ya mallake su, da zan cutar dake da tuni nayi tunda kika amince kije ko ina tare dani, someone attempts to kidnap you yesterday night, that's all I know"
Dafe kai Widad tayi ta shiga sintiri a gurin, gaba ɗaya idonta yayi Ja se gumi take, a hankali ta furta
"Jeka falo ka jirani, zamuje gidan Bulama yanzu"
Yusuf ya jinjina kai ya koma babban falon.
Kusan mintuna sha biyar yana jiran ta sannan ta fito, yauma dai babu batun mayafi balle hijjabi a jikin ta, haka suka fita.
Alhaji Haruna ne mahaifin Nurat ɗauke da waya a kunnen sa yana waya, yana yi yana sharce gumi duk da sanyin Na'urar sanyaya ɗaki dake ɗakin amma gumi yake yakicewa, cikin inda inda yake cewa
"wallahi ranka ya daɗe seda aka shirya komai, dan yarinya ta Nurat ta tabbatar min da taje gurin party, taje gidana, dan an gama komai an sumar da ita, ana jiran sahu ya ɗauke azo a ɗauke ta, wani matashi yayiwa Yarinya ta barazana ya ɗauke ta ya tafi da ita, kuma ni a iya sanina ko su Alhaji Musa da muke komai tare dasu muke neman abu ɗaya basu san mun ƙulla alaƙa da kaiba balle ince haɗin baki ne"
Ɗaya ɓangaren yace "Shikenan zanyi wani shirin na mussman, Amma idan ka bari muka kuma rasa damar mu a karo na biyu zan ajiye ka a gefe in nemo wani"
"Insha Allah baza'a sake samun matsala ba Alhaji Bukar"
Alhaji Bukar yace "Allah yasa, sannan batun wannan matashin kabar komai a hannu na, nasan abunda zanyi"
"Shikenan godiya nake ranka ya daɗe " daga nan suka yi sallama.
************************
Bayan fitar su Widad, Mummy tasa aka kira mata Isa mai gadi.
Isa yaje ya same ta a falo, cikin rawar jiki ya gaida ita ta amsa masa a wulaƙance ta kalle shi tace
"Kai na baka aiki amma har yanzu nani shiru ko bazaka iya bane?"
"A'a ranki ya daɗe, yaron ne gaba ɗaya baya sakin jiki damu yanzu, wani mugun jin kansa yake kamar wani basarake"
Ta jinjina kai tace "tabbas nima naga hakan, kuma da sannu zan kawo ƙarshen wannan izzar da yake ji da ita, talakan banza asararre, kaje kayi abunda na saka, bana so yasan nasa a bibiye shi ne, ka nemo min inda yake zaune, zan sa ayi maganin sa, tashi ka koma bakin aikin ka"
Ya tashi sumi sumi ya fice.
***********************
Yusuf suna zuwa gidan Bulama suka yi sa'a yana nan, a harabar gidan suka ganshi yana shan lemo, hannun sa ɗauke da Jarida.
Ɗago idon da yayi ya sauke akan Widad yasa shi sakin murmushi, itakam fuskar nan a murtuke ba annuri.
Alhaji Bulama yace "barka da zuwa lovely daughter"
A ɗan ciki tace "barka da hutawa Daddy"
"Yawwa barka lovely daughter, ya akayi ne na ganki a haka? Meke faruwane? Ko ciki zamu shiga?"
Yusuf a ransa yace "wata sabuwa, yau kuma Alhaji Bulama take kira da Daddy, idan taga dama kai tsaye take kiran sa da Bulama, wannan yarinya akwai ta da rikici, bata da Alƙibila sam"
Ta yamutsa Fuska tace
"A'a nan ma ya isa, Amma Daddy akwai matsala fa"
Ya tattaro hankalin sa kanta yace "matsalar me daughter"
"Ana farautar rayuwa ta har yanzu, daga fita jiya aka kusa saceni, nidai tunda Daddy baya nan kamin visa zan bar ƙasar nan, gara in ƙarasa Rayuwa ta a can ƙasashen wajen"
Alhaji Bulama yace "waye yayi attemptin ɗin sace ki, kuma a ina? Shiyasa tuntuni nace a samo masu tsaron lafiyar ki"
"Bashi da mahimmanci kasan inda naje, da wanda yai yunƙurin saceni, duba da tsawon shekaru kun gaza maida hankali ku gano hakan, kuna ɗaukar wasu maganganun nawa a matsayin maganganub hauka, kawai ka nema min visa zan bar ƙasar nan"
"Haba lovely, saboda me zaki bar ƙasar ki ta haihuwa? kije ki cigaba da rayuwa ke kaɗai a wata uwa duniya? Nace a ɗaukar miki masu tsaron lafiyar ki da zasu dinga miki rakiya kinƙi, kin ɗakko wannan dogarin duk inda zaki yana biye dake kamar inuwa, shiba soja ba, shiba wata tsiya ba ta ina ze iya tsare lafiyar ki?" yai maganar yana nuna Yusuf
Widad ta haɗe fuska tace "kaikam wani lokacin se in rasa meke damun ka, aini babu me tsaron lafiya ta se Allah, Akan me zan ɗau masu tsaron lafiya ta, haka kurum a haɗa kai da masu tsaron nawa a cutar dani? I don't trust anyone"
Alhaji Bulama yace "shi wannan ɗin kina da tabbacin baza'a haɗa kai dashi a cuce ki ba?"
Ta juya ta kalli Yusuf dake tsaye, sannan ta kalli Bulama tace "Ba'a kansa muke magana ba yanzu , babu ruwanka kasancewarsa tare dani, muna magana akan Visa zakamin in bar ƙasar nan kawai"
"wai tayaya zan miki visa ki bar ƙasar nan? Keda muke saka ran Dawowar Fahad in next couple of weeks a fara zancen Auren ku, meya.......
"shut up please! " ta faɗa a hasale tana ɗaga masa hannu sannan ta ɗora da cewar
" wai har yanzu baka janye wannan banzan ƙudurin naka ba ko? Kana tunanin abunda na gaya maka ƙarya nake, let me repeat myself, bazan yi Aure ba, babu namijin daya dace dani, ni ba zanyi Aure in zauna a ƙarƙashin wani ba, Allah ya bani dukiya wadda ta isheni rayuwa, bana buƙatar wani Aure, hankalina na kan son ganin bayan maƙiya na, koni ko su, ko kuma muyi mutuwar kasko"
"Widad, dukiya shirme ce idan babu Soyayya da kulawa, ban hanaki gano wanda suka rusa farincikin rayuwar ki ba, Amma aure yana da mahimmanci a rayuwar ki, bakya son ganin 'ya' yan ki a duniya? Aure garkuwa ne Widad"
"Soyayyar banza, is just stupidity and form of mental disorder, an imagination and bunch of problems, bana buƙatar soyayyar kowa, nikaɗai zan gudanar da rayuwa ta, na ishi kaina rayuwa bana buƙatar kowa yayi min garkuwa"
Zuwa yanzu Yusuf ya saba jin ire iren wannan maganganun na Widad, Amma yana kallon ta a wani iri idan yaji tana faɗin wannan kalaman, ta yaya mutum zece ze rayu shi kaɗai, ba abokin rayuwa ba 'yan uwa ba Abokan Arziki? Kafin ya bawa kansa amsar tambayoyin ya tsinkayi murayarta tana cewa
"Wallahi ko kana so ko baka so, ba zan cigaba da zama a ƙasar nan ana farautar rayuwa ta ba, kuma ba zanyi Aure ba babu shi a tsarina"
Bukama yace "Aini bance dama ki zauna a ƙasar nan dole ba, da zarar an ɗaura miki Aure ƙasar nan zaku bari gaba ɗaya keda mijinki, kinga kin tsallake tarkon maƙiyanki"
Cikin izza me bayyanar da tsantsar ikon da take dashi tace
"Wani tabbaci kake da shi shi ɗan naka baza'a haɗa kai dashi a cutar dani ba?"
"Idan har ɗan dana haifa ze cutar dake, da nine mutum na farko da ze cutar dake da mahaifinki, dan a yanzu mahaifinki bashi da ka mata"
Widad ta miƙe tsaye ta dafa teburin ta kalli idon Bulama tace
"Zan bar ƙasar nan ko kana so ko baka so, kuma bazan Auri ɗanka ba, babu Aure a tsari na, ina fatan wannan ya zama karo na ƙarshe da zan gaya maka babu Aure a tsarin Rayuwa ta, Ganin bayan maƙiya na shine a gaba na"
Ta juya ta nufi inda Yusuf yayi parking ɗin mota, da sauri Yusuf ya riga ta ƙarasawa ya buɗe mata gaban mota, dan bata zama a bayan Mota.
Yusuf ya fara tuƙi ba tare da ta kalle shi ba tace "Muje Farm House" shima be ce mata komai ba, ya ɗauke kan motar zuwa hanyar gidan gona.
Suna tafe Yusuf yana tunanin wani dalili ne yasa kowa yake tsoron Widad haka? Take faɗawa kowa abunda ta ga dama komai tsufan sa kuwa? Indan Mahaifinta yana da kuɗi ne, suma ai masu kuɗi ne.
Bayan tafiyar su Widad Bulama na nan inda suka barshi yana zaune yayi shiru, Matarsa Hajiya Sarah ce ta fito da shirin ta tsaf, da alama fita zata yi.
Inda Alhaji Bulama ke zaune ta nufa, ta samu kujera ta zauna ta kalle shi tace
"Ya dai? Wannan dogon tunanin fa? Shekaru sun fara ja, dogon tunani be kamace ka ba"
Ya sauke Ajiyar zuciya ya kalle ta yace "dole inyi dogon tunani, Yanzun nnan Widad ta bar gidan nan, lamarin yarinyar nan kullum ƙara taɓarɓarewa yake, wai ita ba zata yi Aure ba kwata2, haka zata ci gaba da zama, Rayuwa zata yuwu a haka? "
Ɗan taɓe baki tayi tace "waini Alhaji meye nasa damuwar 'yar wani a ranka? Naga dai ba kaine ubanta ba, taje tayi abunda taga dama mana"
"A' a Sara, Kin san yadda nake da Mahaifinta, damuwata tasa ce, damuwar sa ta wace, kuma har yanzu ana kainata hari, nace a samo mata masu tsaron lafiyar ta, taƙi se wannan yaron da take yawo da shi, kome ze tsare mata oho?"
"to ku ƙyaleta tayi abunda ta ga dama mana, tunda bata san abun Arziki ba, dama ba dole a cigaba da kai mata hari ba wannan Wulaƙanta mutane da take, Yarinya ƙarama se baƙar Aƙida"
"A'a be kamata a ƙyaleta ba Sarah, nifa mun yanke shawarar zamu haɗa ta Aure ne da Fahad"
Kallon sa tayi galala sannan tace
"ban gane haɗa ta Aure da Fahad ba? Wannan Yarinyar mara tarbiyya da bata san Darajar mutane ba zaku haɗa da Fahad, ko manta Fahda ɗin shima yadda yake da saurin Fushi da