Showing 93001 words to 96000 words out of 135096 words
ze fashe, Wayyo Allah Daddy na"
Yusuf yace "kiyi haƙuri insha Allah komai ze daidaita, zakiji sauƙi mun taho da magunguna"
Shiru tayi ta sake kwantar da jikinta a ƙirjin Yusuf, hawaye na bin gefen idonta.
Tun Yusuf yana sa ran tafiyar ta ƙare har yayi shiru ya zubawa sarautar Allah ido.
A hankali Yusuf ya fara ganin gidaje tsilla tsilla a gurin, gine gine na tsurar ƙasa haka Gidajen suke, wasuma ko katanga babu a haka suke, yayi mamakin wannan irin ƙasurgumin ƙauye haka da yadda mutane ke rayuwa a cikinsa, suka baro duk bakin hanya suka shigo wannan surƙuƙin guri sukayi ginin Gidaje.
A hankali suna cigaba da tafiya, yaga ƙauyene sosai me ɗauke da gidaje da mutane a ciki, sedai sunyi hannun riga da duk wani abun more rayuwa da jin daɗi, kama daga Makaranta, Asibiti, ko wani abu me kama da borehole tunda suka shiga ƙauyen Yusuf be ganshi ba.
A ƙofar wani babban gidan ƙasa, an shafawa ƙofar gidan farar ƙasa, alama dai mamallakin gidan yana riƙe da wata sarauta ne a ƙauyen.
Saleh yace "Yusuf ina zuwa"
Ya sauka daga motar ya shiga cikin gidan, Yusuf yana ta ƙarewa gurin kallo yana tunanin anya Widad zata iya rayuwa a cikin gurin nan?
A hankali yaji tace "Ka yadda da Saleh, kana da tabbacin shima ba cutar damu zeba?"
"Ko ban yadda dashi ba, Allah baze bashi damae cutar damu ba, nidai fatana inga kinji sauƙi gaba ɗaya"
Ajiyar zuciya tayi, tai shiru ba tace komai ba can Saleh ya fito shida wani dattijon Mutum, kansa ɗauke sa rawani.
Suka ƙaraso gaban akori kurar, dattijon yace "sannu dai ɗan samari"
Yusuf yace yawwa Baba, barka da yamma
"Yawwa barka" mutumin ya kalli Saleh yace "sune wannan?"
"Eh sune wanda na gaya maka, ina son su zauna a gidanka na wani lokaci, kafin komai ya lafa su koma"
"Amma kana ganin babu wata matsala Saleh, nifa bana son abunda zezo ya ɗagawa Al'ummar garina hankali, kasan ku mutan binni se a hankali"
Saleh yace "Haba dai, wane irin matsala taimako zakayi, baka ga yadda suke a galabaice ba, babu wata matsala insha Allah"
"Shikenan, shigo dasu se a kaisu ɗakin daka gyara musun"
Yanzu ma Widad ba zata iya tafiya ba, Yusuf ne ya ɗauke ta zuwa cikin gidan.
Duk da rabi tana hayyacin ta rabi bata hayyacin ta, tana mamakin mutane ne ke rayuwa a wannan gidan, roofing gidan kansa na Azarane, ta dinga kallon roofing tana tunanin menene wannan?
Yayin da wasu ɗakunan roofing danga ne.
Tunda suka shigo gidan, mutan gidan maza da mata suka fito suka yi cirko cirko kamar zakaru suna binsu Yusuf da kallo kamar sunga baƙin halitta.
Wani ɗakine a can ƙarshen gidan, Saleh yasa mukulli ya buɗe ƙofar katakon dake ɗakin ya shiga yacewa Yusuf "bismillah"
Ba lefi ɗakin yana da girma amma ba sosai ba, yana da taga guda ɗaya wadda akayi ta da katako da kuma langa langa, ɗakin ginin ƙasa ne tsura, sedai anyiwa ƙasan floor, aka shimfiɗa buhu a ƙasa sannan aka kawo tabarma duk aka shimfiɗa.
Akwai matsaikaciyar katifa a shimfiɗe a ƙasa, da bargo guda biyu se fula guda ɗaya duk sababbi.
Gefe ga tulu, da wani ƙaramin kwandon kwanuka da 'yan kwanuka a ciki, gefe ga sababbun bokitai guda biyu, da sabuwar buta.
Akan katifar Yusuf ya kwantar da Widad, da duk inda ya motsa ta ciwo yake mata.
Dattijon yace "wannan bata da lafiya ne haka?"
Saleh yace "Eh bata da lafiya, a hannun masu garkuwa fa na karɓo su, na maka bayanin komai, dan Allah Baba a kula dasu, duk abunda suke buƙata ayi musu"
"Shikenan, indai nine baka da matsala, ko baka kawo kowa ya zauna a gidan nan ba, gidan nan na jama'a ne, Allah ya basu lafiya"
Ya juya ya fita, yana kora yaran da suka yi dandazo a ƙofar ɗakin suna leƙen su Widad.
Idon Yusuf ne ya sauka akan akwatunan Widad data shirya domin tafiyar da zasuyi, da traveling bag ɗinsa da suka bari a motar da'aka sace su.
Yusuf ya zare ido yace "Nifa Saleh ina buƙatar kamin bayanin abubuwa, ya akayi ka samu jakunkunan mu na tafiya? Ya akayi kasan idan muke kaje ka tseratar damu?"
Saleh yace "Nasan zakayi mamaki, kuma dole ku tambaya, Amma yanzu ina sauri saboda zan koma kano kar su gane wani abu a ƙasa su fara zargina, duk yadda aka shirya sace ku dani akayi shi, Tun bayan sace ku ni kuma na fara shirin yadda zaku tsira, amma ka sani koda wasa karka kuskura kayi gangancin barin ƙauyen nan in bani na fita daku ba, dan wallahi suka ganku sekun kasheku"
Yusuf yace "wai tsaya, wai inane nan ma tukuna?"
"Nan wani ƙauye ne a cikin garin Bauchi, Zan dinga zuwa ina duba ku, a waccan jakar na ajiye muku abubuwan da ba'a rasa ba da zaku buƙata kafin ku saba da irin rayuwar da suke yi, ga kuma kayanku can dana kawo nan, nan gidan ƙanin kakana ne dan haka insha Allah baku da wata matsala, idan ma dawo za kaji komai "
Saleh ya fita tsakar gida ya kalli wata dattijuwa yace "Gwaggo dan Allah Amana nan, a kula da baƙin nan dan manyane duk abunda suke buƙata ayi musu"
Gwaggo tace "Lallai kam, baƙin suna da girma a gurinka, tunda sanadinsu gashi kana leƙo mu"
Wata mata a tsakar gidan tace "Eh aimu da yake cinyesu zamuyi shiyasa ba'a bamu amanar baƙin ba se ita"
Saleh yace "Aifa kedai halinki yana nan bazaki canza ba" yayi gaba abunsa, ya tafi gurin me gari suka sake tattaunawa sannan ya tafi.
Haka Saleh ya tafi ya bar su Yusuf a cikin wannan ƙasurgumin ƙauye.
A hankali Widad tayi juyi, ta ƙarewa ɗakin da take ciki kallo, wai anan zata zauna ita da suka zo sam bata zaci wai nan mutane ne ke rayuwa a cikin gurin ba se yanzu.
Yusuf yaje yayo Alwala, yazo ya tada salla sedai duk inda yayi se mutanen gidan su bishi da kallo.
Widad ta cire hijjabin jikinta, jikinta se faman ƙaiƙayi yake mata, Yusuf ya idar da salla zeyi magana ta riga shi ta hanyar cewa "zanyi wanka"
Ɗan zare ido yayi yace "to shikenan, bari inwa mutan gidan magana"
Ya fito tsakar gidan, yaga wadda Saleh ya kira da Gwaggo ɗazu tana ta aiki a tsakar gida, yace mata "dan Allah Mama ko zamu samu ruwan ɗumi, mara lafiyar zata yi wanka, nikuma ko na sanyi ne na samu se inyi Amfani da shi"
Tayi murmushi tace "bakomai, na zuba ruwan tuwon dare dama, bari in ɗibar maka"
Yusuf yace "to nagode"
Ya tafi ɗakin su, ya ɗakko sabon bokiti, aka zuba ruwa aka sirka Yusuf ya koma ɗakin yace "An haɗa ruwan"
Ta tashi zaune ta fara kiciniyar cire rigar jikinta, sedai hannunta na hagu shine wanda aka harbeta, na dama kuma yana ciwo saboda duka da wahalar mota.
Yusuf ya juya mata baya da nufin ta kintsa ya kaita banɗakin.
"Zoka tayani cire wannan rigar na kasa cirewa....
(Akwa ƙura fa🚶 🚶 🚶 🚶 🚶)
Share, share and share please 🙏
Domin, gyara sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1
Page 28_29
Gaba ɗaya dirircewa Yusuf yayi, se yayi kamar beji me tace ba, ganin yaƙi magana yasa itama tai shiru ta nemi guri ta kashingiɗa.
Yusuf ya waigo yace "Kin gama kintsawar ne?"
Kawai ya ganta a zaune.
"Ya haka kuma? Se ruwan ya huce?"
"Ban sani ba, ai kana jina ina magana kayi min shiru, nace kazo ka tayani in cire rigar nan, amma kayi kamar baka jiba"
Ikon Allah bata da lafiyar ma, an tsira da ƙyar bakinta be mutu ba, gashi da ƙyar take maganar.
Yusuf yace "bari inyiwa mutanen gidan magana, se suzo su cire miki"
"Wallahi babu matar da zata taɓani" tai maganar tana kuka
Seda Yusuf yayi shiru, sannan ya tako a hankali kan katifar da take, ya zagaya bayanta hannunsa rawa yake ya zuge zip ɗin doguwar rigar tata ƙasa.
Farar fatarta ta bayyana cikin wata baƙar vest, shiru yayi yana kallonta, ta janyo hijjabi ta mayar ta yunƙura zata miƙe tsaye amma jiri ya kwashe ta.
Yusuf yace "ki dena gaggawa, a halin da kike ciki ɗin nan, idan kika faɗi zaki ji ciwo fa"
Ya duba ya ɗakko soson wankanta dake cikin Akwatinta, sedai babu sabulu haka ya riƙota suka fito, Gwaggo na ganin haka ta taho da sauri da nufin ta taya Yusuf, Amma Widad ta maƙale hannunta, ta manne a jikin Yusuf tabi gwaggo da ido, gwaggo ta tsaya sororo tana kallonsu.
Yusuf yace "Mama karki damu, kiyi haƙuri haka halinta yake bata da yadda ne"
Matar dake gaban murhu ta juyo ta kallesu tace "yau nake ganin ikon Allah, wannan gwandamemiyar matar ce take ƙyuya se kace me shan Nono, taɓ amma lamari ya ɓaci, koda yake wannan kamar ma ba irin tamuce ta nan ƙasar ba"
Widad tabi matar gaban murhun da kallo, haƙoranta yellow shar ga haƙorannata wasu sunyi goyon kura, gata baƙa sosai ga fuskarta duk tsagu, gashi se ƙara baje hanci take.
Gwaggo tace "Haba Hari, ina ruwanki da ita irinku ne ke sawa adinga cewa Hausawa basu da kirki, yanzu da taji abunda kike faɗa ba"
Zatonsu duk Widad bata jin hausa, gwaggo ta kalli Yusuf tace "ga banɗakin can seka kaita"
Suna zuwa ƙofar banɗakin Widad tayi tiris taƙi gaba taƙi baya.
Yusuf yace "muje mana seki shiga kiyi wankan"
Girgiza masa kai tayi tace "Ni wallahi tsoro nake ji bazan iya shiga ba" sam Widad gurin be mata kama da banɗaki ba, kamar wani gidan horo haka taga gurin.
"meye abun tsoron, zan jiraki anan gurin kiyi ki fito"
Riƙe shi tayi tsam tana girgiza kai tace "Ni na fasa wankan, bazan shiga nan ba"
Gwaggo tace "ɗan nan ya naga bata shiga ba, lafiya kuwa?"
Yusuf yace "wai tsoro take ji ba zata iya shiga ba"
Gwaggo tace "Allah sarki, ƙasashenku babu irin wannan banɗakin ko? Abun duk se haƙuri ai, akwai wani ɗaki da babu komai a ciki ta shiga tayi a ciki kawai"
Yusuf yace "mungode Mama"
"A'a bakomai"
Ta nuna musu ɗakin, duk yadda Yusuf ya tsani roƙo, haka ya karya billensa ya tambayi sabulun wanka, sedai Sabulun da suke wanka da shi irin sabulun nan ne kore na wanki me ƙarnin tsiya, Yusuf ya miƙawa Widad, tasa hannu ta karɓi sabulun ta kalli Yusuf kawai yaga Hawaye a idonta.
Tausayinta ya kama shi, amma ya basar kamar bega hawayen idonta ba, haka ta shiga ɗakin da siminti a ƙasan ɗakin, tayi wankan nan tsigar jikinta na tashi saboda yadda ruwan in ya zuba a ƙasa yake taɓata, ga tashin zuciya saboda ƙarnin sabulun, ba shiri ta ajiye sabulun tayi wankan a haja, sedai taji daɗin ruwan zafin sosai "
Ta fito tana kama bango, Yusuf ya riƙeta ya maida ita ɗaki, ya duba Akwatinta ya ɗakko kaya ya bata, ta saka itama tayi salla.
Saleh beje gida ba se bayan sha biyu na dare, yayi tunanin ko yaje yayi magana da doctor Safwan amma wata zuciyar ta hana shi, saboda yadda Safwan ya dinga rawar jiki da yaji batun kuɗi tsaf zeje ya gaya musu, yaje ya sameshi.
Gaba ɗaya tunaninsa ya koma kan yaze ƙwaci Alhaji Nasir a gurin wannan Azzaluman mutanen? Dan ba ƙaramin shiri suke dashi ba.
Me Adda suka koma inda suka ajiye su Widad, da niyyar ayita ta ƙare, suna zuwa suka buɗe gidan, suka shiga suka saka mukulli suka buɗe ɗakin suka ga wayam ba kowa a ciki, a kiɗime ɗayan yace "Me Adda bafa kowa a ɗakin nan"
Ƙarasawa yayi da sauri ya shiga ɗakin shima amma ba kowa a ciki, nan da nan suka gigice suka shiga lalauben su Widad.
Me Adda yace "Mutanen da ko iya takawa basayi, ta yaya zasu gudu? Duk matakan tsaron dake gurin nan ina sukabi suka fita?"
Cam ɗaya daga cikinsu ya ɗaga kai ya kalli Roofing ɗakin yace "me Adda kalli ta nan suka fice" yai maganar yana nuna musu saman roofing ɗakin
Me Adda a gigice yace "ya zama dole mu bazama neman su, amma ta yaya suka samu abu sukayi hanya har suka fita?"
Ɗaya daga cikinsu yace "Allah ne ya san yadda suka gudu"
Me Adda yace "bamu da lokacin ɓatawa, maza maza mubi sahun su yadda suke a galabaice ba lallai su iya tafiya me nisa ba"
Haka kuwa akayi suka rarraba kansu a cikin daji.
Saleh yaje duba Alhaji Nasir a Asibiti, ya tarar da Anwar a gurinsa, suka gaisa yayi masa ya me jiki, ya ɗan dubi Anwar yace
"Amma meyasa baza'a fita da Alhaji waje a nema masa magani ba?"
Anwar yace "Nayi duk me yuwuwa inga an fita da shi, amma Mummy da Alhaji Bulama sunce nan ma ana kula da shi"
Saleh yace "Abunda za'ayi yanzu shi ne, ka ɗauke shi ka canza masa Asibiti ba tare da ka sanar dasu ba, ko ba'a fita dashi waje ba a camza masa Asibiti, sedai kawai suga ka canza maaa Asibiti"
Anwar yace "Amma zasuji babu daɗi idan nayi hakan, suna ganin nanma ana ƙoƙari akansa amma inyi haka kamar ban kyauta ba"
"Anwar zamanku a Asibitin nan yaci ace jikinsa yana karɓar treatment yadda yakamata, amma har yanzu babu wani cigaba, mu canza masa wani Asibitin kawai"
Anwar yace "Kana ganin babu matsala idan muka yi hakan?"
"eh babu matsala, Amma karkace ni nace ka canza masa Asibiti"
Anwae yace "shikenan, ka kawo shawara me kyau insha Allah gobe in Allah ya kaimu da Safe, sedai suzo su tarar na canza masa Asibiti ni kaina rashin samun sauƙin nan nasa yana bani mamaki"
Doctor Sufyan ne yake ta zagaye acikin Office ɗinsa, yana tunanin me yakamata yayi akan batun su Alhaji Haruna, yana tuno irin halacci da kirkin Alhaji Daula, idan aka haɗa kai dashi aka cutar dashi to tabbas mesa Adalci ba, Amma wani mataki Alhaji Musa zasu ɗauka akansa idan har be abunda sukace ba?.
Fitowa yayi da sauri daga office ɗin nasa ya nufi ɗakin da Alhaji Nasir yake, yana zuwa shiga suka haɗu da Saleh, suka yi kallon kallo babu wanda ya cewa kowa komai suka wuce.
Ya shiga ɗakin da Sallama, Anwar ya amsa masa, doctor Sufyan yace "Anwar yame jikin kuwa?"
"Jiki sedai muce Alhamdilillah, amma doctor na fara karaya da yanayin jikin sa, babu wani cigaba fa gashi nayiwa su Mummy magana a fita dashi amma sunƙi amincewa, na rasa dalili"
Sufyan yace "ka kwantar da hankalinka Anwar, treatments ɗin dai da muke masa anan, shi za suyi masa a can, komai ze tafi dai dai ze warke in Allah ya yarda"
Anwar yace "Shikenan Allah yasa"
Haka Widad ta kwanta akan katifar, Yusuf ya ɗau bargo ɗaya ya koma bakin ƙofa ya shimfiɗa ya kwanta, shiru Widad ta kasa bacci, tana tunanin wai itace zata kwana a gurin nan, ga sauro se kururuwa yake mata a kunne, ga zafi ga jikinta da yake ciwo, ga rashin lafiya tana fama.
Ɓangaren Yusuf ma shiru Yayi yana saƙe saƙe, yana tunanin wani hali Ummansa take ciki, yasan duk inda take hankalin ta a tashe yake, dan tun tasowarsa be taɓa nesa da ita ba, wani ɓangare na zuciyar sa yana tunanin Alhaji Nasir yasan tabbas shima yana cikin damuwa, ko wani haki yake ciki Allah masani, ga zamansa da Widad a ɗaki ɗaya baze yuwu ba, tunda ba muharramarsa bace, gashi ba ta yadda da kowa se shi, ga wasu abubuwan se anyi mata saboda bata da lafiya, dole idan Saleh yazo yayi masa magana asama masa wani ɗakin, dan gudun afkawa tarkon sheɗan.
Yana nan kwancw sauro yana cizonsa, yana masa hada hada aka, ga cinnaka da yake ta gasa masa cizo a gurin nan, tunani yake Allah yasa kae cinnakan ya ciji Widad.
Katsam ya jiyo sheshsheƙar Widad tana kuka, da yayi kamar ya basar amma ya dinga jin kukan nata a zuciyar sa, tabbas yakamata a tausaya mata.
Ɗakin baƙiƙirin da duhu, ko tafin hannu ba'a iya gani saboda duhu, haka yaja jikinsa cikin lalube yaje gefen katifar ta yace "uwa ɗakina kukan me kike?"
Maimakon tayi magana seta sake fashewa da kuka, Yusuf yace "Am sorry, i feel your pain kiyi haƙuri ki karɓi hakan a matsayin ƙaddarar mu, yakamata ki gode Allah da yasa muka tsira daga hannun mutanen nan, kuma insha Allah zamu koma gida ki dena kuka, kiyi bacci zaki ji daɗin jikin ki"
"I can't sleep, sauro ya dameni zafi nake ji, kuma ina tunanin Daddy na"
Tai maganar tana sake fashewa da kuka.
"kiyi hakuri, Insha Allah Daddy yana nan lafiya, komai ze wuce kamar be faru ba, ki dena kuka kinga baki da lafiya"
Ajiyar zuciya kawai tayi, ta lumshe idinta tana jin yadda zuciyarta ke raɗaɗi.
Da Asuba yayi Alwala yazo ya tada Salla, bacci take dan sam bata samu bacci ba da daddare, seda ya idar sannan ya tashe ta ya kaita tayi alwala tazo ta tada salla.
Da gari ya fara haske me gari da kansa yayi sallama a ƙofar ɗakin su Yusuf, Yusuf ya fita ya durƙusa ya gaishe shi.
Ya amsa cikin mutuntawa yace "Ya me jikin kuwa?"
Yusuf yace "Jikinta da sauƙi Alhamdilillah"
"Masha Allah, Allah ya ƙara afuwa ya bata lafiya,