Showing 6001 words to 9000 words out of 135096 words
wannan ma shiriricin ke gadi"
Abbas yace "Sani dai ba Abbas ba"
Yusuf yace "Am sorry, Sani"
Abbas yace "duk yana cikin binciken da za kayi, ka kula kayi taka tsan2, banda sakin jiki da kowa dama nasan kai ba me son hayaniya bane"
Isa ya dawo yace "bismillah ku taho mu shiga, Alhaji yace a shiga daku"
Tunda suka kama hanyar shiga cikin gidan Yusuf yake ƙarewa ko ina kallo, an danƙarawa gidan dukiya kaman ba'a san ciwon ta ba.
Wasu irin faluka suka dinga ratsawa, kowanne da kalar sa da irin tsaruwar da yayi, shikan sa Abbas be san haka cikin gidan yake ba.
Sunyi doguwar tafiya kafin su iso wata ƙatuwar ƙofar glashi,Isa yasa hannu ya murɗa suka shiga da sallama.
Iya girman falon nan ya ishi wani talakan gina wadataccen gidan da ze zauna, Yusuf ya fara tambayar kansa shi kuwa wannan wane irin sana'a yake yi da har ya gina wannan gidan kamar baze mutu ba?
Babban mutum ne a zaune akan wata luntsumemiyar kujera yana karanta jarida gefen sa da wata mata, se 'yan mata biyu zaune akan kujerar dake facing ɗin su.
Aka amsa musu Sallamar, cikin girmamawa suka gaisa da me gidan tare da iyalan sa, yanayin gaisawar tasu ze nuna maka mutum ne me fara' a, dan kuwa fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa musu.
Isa yace "Yallaɓai sabon driver ne da kace a samo, shine suka zo yanzu"
Ya ajiye Jaridar hannun sa yace "Masha Allah wanne ne daga cikin su?"
Cikin girmamawa Yusuf yace "Nine"
Alhaji Nasir ya ɗan ƙura masa ido yace "masha Allah, ya sunan ka?"
"Suna na Yusuf"
Alhaji Nasir ya jinjina kai yace "Hajiya Halima kinji me sunan Yaya na ko?"
"Aikam dai me sunan shi" ta amsa
Alhaji Nasir yace "Allah sarki, Allah yasa me irin halin sa ne, ni duk Yusuf ɗin dana sani mutanen kirki ne, ina fatan kaima haka?"
Abbas yace "Alhaji ba ganin ido ba Shima mutumin kirki ne sosai"
Alhaji yace "ai dama na sani, ban taɓa ganin Yusuf mutumin kawai ba"
Ya kalli 'yan matan nan dake zaune yace "Amal jeki part ɗin gimbiya ta, ki gani idan idon ta biyu bata komai ki gaya mata Daddy na son ganin ta, idan kuma da abunda take yi ki ƙyaleta"
Wadda aka kira Amal ta miƙe tare da cewa "to Daddy" .
Babban abunda ya bawa Yusuf mamaki be wuce tun lokacin da' aka ce shine ze zama direban, matar da 'yan matan nan suke binsa da kallo ba, mussman wadda aka kira Amal yadda ta tsare shi da idanuwa.
Seda akayi Minti goma sha biyu da tafiyar Amal, sannan ta dawo tace "Daddy tace tana zuwa"
Alhaji Nasir yace "to babu laifi"
Wasa2 seda sukayi minti Arba'in ba suga Alamar wadda aka kira ɗin zata fito ba, iyalan suka ci gaba da hirar su aka bar su Yusuf shiru kamar mayu.
Gaba ɗaya Yusuf ya gaji da zaman, ga sanyin A. C da kallon ƙurillar da'ake masa duk yabi ya takure.
Alhaji Nasir ya kuma cewa "Ramla bawa baƙin nan Abinci kafin ta zo"
Ba tare da Ramla tace komai ba ta miƙe ta fice, ruwa da fruits ta kawo ta ajiye musu.
Abbas da Isa suka dinga ɗauka suna ci suna kallon tv, shikam Yusuf ya kasa cin komai, gaba ɗaya a takure yake, gashi ko ɗaga kai baya son yi saboda kallon da'ake masa.
Kaman ance ya ɗaga kai idonsa yayi tozali da wata irin kyakywar halitta, babu shakka itace a jikin hoton da Abbas ya tura masa, Amma a zahiri tafi haka kyau, gabansa ne ya dinga faɗuwa ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi, yarinya ce sharaf amma se kwarjini fara ce ƙal tana sanye da skin tied iya gwiwarta, se wata over size shirt data saka har wajen gwiwarta, kanta babu ɗan kwali gashin ta a hargitse babu ribbon, ta sake shi a kafaɗun ta.
Fuskarta a haɗe babu annuri, ta ƙaraso cikin falon ta zauna kusa da mahaifin ta. Tana zama Hajiya Halima ta miƙe ta canza wata kujerar
Alhaji Nasir yace "Lovely daughter ina fatan ba'a takura miki ba?"
Girgiza masa kai tayi alamar A'a
Alhaji Nasir yace "Sabon driver ne gashi nan, yazo ki gani in yayi miki"
Kamar baza tace komai ba ta ɗago ta kalle su ɗaya bayan ɗaya ta tsaida idon ta akan Yusuf ta ɗan ɗau lokaci tana kallon sa kaman tana ƙoƙarin gano wani abu.
Ɗauke kai tayi ta haɗe rai cikin isa tace
"Ramla kawo min madara da cup, sannan kije falona ki kawomin wata folder akan kujera"
Waigawa Yusuf yayi ya Kalli wadda aka kira Ramla, ta girmi yarinyar da har yanzu be san sunan ta banesa ba kusa ba, dan shi har yanzu beji wanda ya faɗi sunan ta ba, ramla ta miƙe ta tafi cika umarnin ta.
Yarinyar da dudu bata fi shekaru sha takwas zuwa sha tara ba, a idon ta da yadda take magana zaka gano tsabar izza, da isa, Ta kalli Abbas tace "kai kaman na sanka ko?"
Abbas yace "eh ni abokin Bala ne, ina zuwa gurin sa"
"good, kai Bala meye aikin ka?"
Cikin Rawar jiki yace "gadi ranki ya daɗe"
"to ka tashi da kai da shi ku fita ka koma kan aikin ka"
Ba musu bala ya miƙe, Abbas ma ya miƙe, kafin su bar falon ta kalli Hajiya Halima tace
"Madam i need privacy you can leave"
Ɗan taɓe baki Hajiya Halima tayi ta miƙe ta nufi wata ƙofar daban.
Ta kalli inda Amal take ta mata wani kallo, tun kafin ta furta komai Amal ita ma ta miƙe ta nufi barin falon.
Gaba ɗaya mamaki ya cika Yusuf, yadda take wannan izzar take wa manya magana babu respect kuma a gaban mahaifin ta amma bece komai ba, ya ma maida hankali akan jaridar sa kaman be san me take yi ba.
Ramlah ta dawo ɗakin ɗauke da cup da madara tazo ta ajiye, sannan ta miƙa mata folder, taje ta nemi guri akan kujerar da ta tashi zata zauna, Amma suka jiyo zazzaƙara muryar ta tace
"wait don't sit, get out from here, bana buƙatar wani a falon zan gana da shi"
Wata irin Ajiyar zuciya Ramlah tayi ta ɗan jinjina kai ba tare da ta waigo ba ta miƙe ta fita ta bar falon itama.
Madarar ta ɗauka ta zuba a cup tana sha, tana kaɗa ƙafa kaman tama manta da Yusuf a gurin.
Alhaji Nasir ya kalle ta yace "gimbiyar Daddy bari inje in ɗan watsa ruwa zan fita anjima, yadda kuka yi dashi kya gayamin in na dawo, in yayi miki.
Ɗan ɗaga girar ta ɗaya tayi ta lumshe ido ba tare da tace komai ba.
Bayan tafiyar mahaifinta haka suka ci gaba da zaman kurame ita da Yusuf
Can ba zato ba tsammani yaji tace
"what's the level of your Education?"
Yusuf ya ɗanyi jim sannan yace "secondary school" yai maganar ƙirjinsa na bugawa
Shiru ta kuma yi tana kallon tv seda aka kuma jan wani lokacin sannan ta kuma cewa
"Meye sana'arka?"
Gumi ne ya fara tsatstsafo masa dukda sanyin AC da yake ɗakin, Yusuf baya son kuma yin ƙarya, Amma yace
"Eh ina ɗan zuwa kasuwa ne ina yaron shago"
Cikin Tsara magana da take daki daki, da muryarta me sanyi tace
"Anyway naga kaman za kayi hankali, zan iya yadda ka zama direba na amma ina da sharuɗai"
Ta ɗanyi shiru kaman ba zata kuma magana ba, sannan ta ɗora
"bana son ƙarya, duk ranar da na gano kayi min ƙarya zaka fuskanci hukunci me tsauri, bana son sa ido da shishigi a cikin lamurana, bana yafewa maƙaryaci ko wanda yaci amana ta, babu ruwan ka da irin mutanen da nake hulɗa dasu, bana yadda da mutum kowaye ni kaina wani lokacin bana yadda da kaina balle wani, dan haka duk lokacin da kayi motsin da ban yadda da shi bama zan iya sawa a kulle ka, ban yadda da saɓa lokaci ko Alƙawari ba, sannan lokacin dana ɗauke ka aiki mallaki na ne bana ka ba, ibada kaɗai kake da 'yancin yi, bayan wannan baka da hurumin yin wani aiki idan ba nawa ba, se dai idan ni na baka dama, in ka amince da sharuɗai na" ta ajiye wata takadda
"kayi signing anan, salary 200k and your hard work determines your salary promotions"
Shiruu Yusuf yayi yana tunani, gaba ɗaya ya rasa abun yi
Yusuf yace
"ranki ya daɗe ko zaki iya bani dama inje inyi shawara"
"I don't gives second chance, and I don't want too much waste of time" ta bashi amsa tana maida hankalinta kan talabijin
Shiru Yusuf ya kuma yi ya ɗauki takardar yana jujjuya ta ba tare da ya karanta meye a jiki ba, gumi se karyo masa yake ya ciro biro a Aljihun sa, hannun sa na rawa ze sa hannu yaji tace
"that means you accept the terms and conditions i have mentioned?"
Jinjina kai yayi alamar yana ƙoƙarin ya saka hannu tace
"if you are here to spy don't sign this paper"
(idan kazo nan ne dan leƙen Asiri kar kasa hannu a takardar nan)
Ras! Gaban Yusuf ya faɗi, Anya babu wata a ƙasa, yarinyar nan bata san komai ba? Cikin ƙwarewar Aikin sa ya dake yace
"ranki ya daɗe menene Spy kuma?"
Banza tayi masa ba tace komai ba.
Seda Yusuf yayi Addu'a a zuciyar sa sannaan yasa hannu akan takardar.
Ta sa hannu ta ɗauki takardar ta jujjuya ta sannan tace
"signing this paper is like signing on your death contract!!! Jeka sena neme ka"
Tana gama faɗin haka ta miƙe ta bar falon
Ras! Ras!! Ras!!! Gaban Yusuf ya faɗi
A fili yace "My death Contract kuma?"!!!
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDA TA*_
*PART1*
_Page 3_
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Special thanks to my Association Members
Perfect writers Association
Maimaita death contract Yusuf ya dinga yi, ya rasa abunda ya kamata yayi, a hankali ya miƙe ya biyo hanyar da Isa ya biyo da su ya fice.
Abbas yana tare da Isa yana jiran fitowar Yusuf, kallo ɗaya Abbas yayi masa yasan akwai matsala, da ƙyar Yusuf yake ɗaga ƙafarsa, Isa da Abbas suka dinga tambayar sa meyafaru? Amma yaƙi cewa uffan, Abbas yayi wa Isa Sallama ya ja Yusuf suka tafi, be ƙara tambayar Yusuf ba har suka je gidan su Yusuf.
Da suka je gidan ma Yusuf yai mursisi yaƙi faɗa wa Abbas yadda suka yi, daga ƙarshe dai Abbas ya ƙyale Yusuf ya ɗauka ire iren wulaƙanci ya fara fuskanta, dan haka yaita bashi haƙuri yana kuma rarrashin sa kan ya daure kar ya karaya.
Sam hankalin Yusuf baya kan Abbas, gaba ɗaya ƙwaƙwalwar sa ta shiga lissafe lissafe daban2, a karon farko da shigar sa Aiki wannan ne aiki me matuƙar wahala da sarƙaƙiya a gare shi, yana buƙatar nutsuwa da taka tsantsan akan komai.
"Yusuf naga kaman hankalin ka baya kaina fa?"
Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "ta yaya zaka samu hankali na, tace ba'a mata ƙarya bata yafe wa wanda yayi mata ƙarya, Nikuma akan ƙaryar ma naje nake aikin, yanzu idan ta gane gaskiya fa?"
Abbas yace "karka damu kayi abunda ya kamata kawai tana ƙoƙarin yi maka ba razana ne, idan kabi a hankali ba zata gane komai ba"
"to Allah yasa?"
Abbas yace "Ameen"
Bayan tafiyar Abbas fa tunani ya auri Yusuf, kasa jurewa yayi seda ya gayawa Umman sa aikin daze jeyi a matsayin direba gidan Alhaji Nasir Daula amma ya ɓoye mata gaskiyar halin yarinyar da sharuɗai da ta saka masa.
"Yusuf wace irin lalacewa ce kana aikin ka gwanin sha'awa zaka koma wani direba?"
"Umma ba lalacewa bace, harkar aiki ce ta kawo haka"
"hakane amma ni bana son sabga da masu kuɗin nan yaran su ba tarbiyya suka cika ba, bana so a wulaƙanta min ɗa a banza, gurin aikin naku babu wanda zasu saka se kai"
Yusuf yace "Umma Addu'arki da goyon bayanki nake buƙata, idan kika soki abun zaki kashe mun gwiwa ne"
Umma ta numfasa tace "shikenan Allah ya tabattar da Alkhairi, Allah yabada sa'a, ka kula da kanka"
"insha Allah umma na nagode sosai"
'yan kwankin nan Gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idaniyar ta, duk motsin da zata yi surar Yusuf take gani, rashin walwalarta da yawan son kaɗai cewa ne yasa 'yar uwatta lura da akwai abunda yake damun ta kasancewar ta me surutu da san hira.
Ramla ta dubi yadda' yar uwar tata tayi shiru tana jujjuya spoon a cikin cup ko sau ɗaya bata kai abunda ke kofin bakin ta ba, bayan shafe kusan mintuna goma da zaman da tayi da niyyar cin Abinci.
"Amal wai me yake damunki haka ne, na lura tun jiya kin zama wata iri"
Amal ta ajiye spoon ɗin hannun ta a ranta tace "Mhmm Yaya Ramla ina cikin damuwa tabbas, kuma na shiga damuwa ne domin ƙoƙarin samo mafita akan gagarumin lamarin dake barazanar jefani wani bigire da be kamata ba, Amma nasan bazaki taɓa bani goyon baya ba" Amma a zahiri tace
"karki damu bana jin daɗi ne kawai"
"Amma yakamata kije kiga likita"
Amal tace "ba abun damuwa bane, zan ware Insha Allah"
Tun Yusuf yana fama da tunani tareda sauraren kira daga uwaɗakkinsa har ya fidda rai, ya fara mantawa ya shiga sabgogin sa.
Kusan sati uku kenan da zuwan Yusuf gidan daga nan Amal bata ƙara saka shi a idon ta ba, wasa wasa abu ya ci gaba da damun zuciyar ta, gashi abu na ta faman damun zuciyar ta.
Alhaji Nasir Daula ne zaune a wani ƙaton falo shida wani mutum wanda zeyi sa' ansa, sukw hira tareda ƙyaƙyata dariya kai da gani kasan akwai kyakkyawan kusanci da fahimtar juna a tsakanin su.
"Alhaji Nasir nikam daughter tunda ta dawo ƙasar nan bata zo mun gaisa ba, kota manta dani ne?"
Alhaji Nasir yace "haba Bulama yaza'ayi daughter ta manta da kai, kawai dai kasan halin ta ne Nason kaɗaici har yanzu a haka take, Amma insha Allah zan turo maka ita har gida ku gaisa"
Alhaji Bulama yace "kana nufin har yanzu bata dena wannan ɗabi'ar ba, ba ta warke ba kenan?"
"kai dai bari kawai, lamarin daughter yana damuna, ace kaf rayuwar ɗan adam be yadda da kowa ba, ba za ta sake da kowa ba, to koni wataran ina ƙasar nan idan bata ga dama ba se tace bata son inje inda take, narasa menene mafita "
Jinjina kai Alhaji bulama yayi yace" "wai shekarun ta nawa ne yanzun?"
"18 to 19, amma menene ma fitar?"
Alhaji Bulama yace "mafita ɗaya ce shine kayi mata Aure, idan har aka yi mata Aure zata dena wannan halin nata"
Alhaji Nasir yace "Aure kuma? Dudu du guda nawa daughter take? Yarinya ce ƙarama kuma waze iya jure halayen ta?"
Alhaji Bulama yayi murmushi yace "kai kake ganin yarintarta idan ka aurar da ita daram zata zauna, samun wanda ze zauna da ita da halin ta abune me sauƙi, semu haɗa ta Aure da Fahad yaron guri na da yake karatu a china, dama bata sanshi ba kaga se a haɗa su, hakan ze ƙara zumunci dake tsakanin mu, kuma kaga tunda ita kaɗai Allah ya baka seka samu 'yan jikoki"
"Masha Allah gaskiya naji daɗin wannan shawarar taka, amma kasan semun bi a sannu idan nace zan tursa sata, za' a iya samun matsala"
"bakomai mu bi komai a sannu insha Allah babu wata matsala"
Suka cigaba da hirarrakin su.
Misalin ƙarfe goma na dare Yusuf yayi shirin sa tsaf ze kwan ta, wayar sa ta fara ringing, Sunan Abbas ne akan screen ɗin wayar, ya ɗaga suka gaisa
Abbas yace "Yusuf ɗazu Isa megadi ya kirani, yace min yarinyar nan ta bada saƙo tace zaka kaita unguwa gobe misalin ƙarfe goma na safe, ta jadadda goma na safen nan dan haka ka kiyaye"
"Shikenan zan je Insha Allah"
Tunda Yusuf ya kwanta ya gagara cikakken bacci, da yaje sallar Asuba sam be koma bacci ba, ya zauna ya ci gaba da lazumi, da sassafe ya tashi yayi wa mahaifiyarsa aikace2, kaman yadda 'ya mace za tayi haka Yusuf ya share ko' ina yai wanke2 yai girkin karin kumallo.
Koda Ummansa ta tashi tayi mamakin inda Yusuf yake gaggawar zuwa, bata son yawan takura masa dan haka ta ƙyaleshi.
Ƙarfe tara dai2 na safe Yusuf ya isa gidan Alhaji Nasir.
Isa na ganin sa yace "kai sannu da ƙoƙari Allah yasa ka ɗore, idan ka ɗore da zuwa akan lokaci saura kuma ƙalubale na gaba"
Yusuf yayi murmushi yace "Malam Isa kenan, Kowace sana'a tana da ƙalubale, sedai fatan Allah ya bamu ikon aikata dai2"
Da yake Isa akwai surutu kaman an ƙona shi aka, haka ya dinga zubawa Yusuf surutu kuma surutun nasa ba'aakan kowa bane se kan 'yar masu gida
Yusuf yace "wai ya sunan ta ne?, nifa har yanzu ko sunan ta ban sani ba"
Isa yace "Ai abune me wuya kaji sun kira sunan ta, ban san sunan ta na gaskiya ba, amma sunan ma dai da' ake kiran ta dashi akwai wuya dan ban riƙe ba"
Yusuf yace "ikon Allah wahalar sunan ta kai ka kasa riƙewa"
"haba Malam Yusuf kaman baka san iyayinku na 'yan binni ba? Wasu sunayen ma karasa sunan tumakine kona taurari"
Ba ƙaramin dariya Isa ya bawa Yusuf ba.
Suna ta ɗan taɓa taɗi, Isa yace "Aff gata can ta fito"
Yusuf ya ɗaga kai ya hango ta, ba ƙaramin kwarjini take da shi ba, taku take na ƙasaita akan wani dogon takalmi, dogon wando ne a jikin ta dark blue da riga light blue me dogon hannu, ta ɗaure kanta da ɗan kwali, amma gashin ta seda ya fito ta baya, fuskarta sanye da wani ƙaton glashi, wayar tace kawai a hannun ta babu jaka se key ɗin