Showing 45001 words to 48000 words out of 135096 words
zafin nama Yusuf zama shamaki da faruwar hakan, ta hanyar riƙeta ta faɗa a jikinsa.
Ƙirjinsa ya dinga bugawa da ƙarfi, saboda jin hakan wani irin abu daban, Isa me gadi ne ya zaro ido ganin abunda yake faruwa, Yusuf kamar me raɗa yace "Are you ok?"
Jinjina masa kai tayi ta sake ƙoƙarin miƙewa, amma still jiri ke kuma ɗibarta, tafiya take tana tangaɗi kamar wadda tasha wani abu, Yusuf yabi bayanta ya mata rakiya har cikin babban falo, hannunsa riƙe da ƙaramar jakarta da kuma wayar ta.
A babban falon ta zauna tana riƙe kai, hawaye nata zarya a fuskar ta, ƙoƙarin cire takalmin ƙafarta take, amma abu ya gagara, se kokawa take da takalmin.
Yusuf ya taka inda take ya durƙusa ya kwance igiyar takalmin nata me tsinin tsiya ya cire mata.
Ta gyara kwanciyar ta sosai ta miƙe ƙafafunta akan doguwar kujerar tare da lumshe idonta, don bawa hawayen idon nata damar gangarowa.
Yusuf a ransa yace 'Ikon Allah, wannan wane irin kuka ne?'
"ko za'a kira likita ne?"
"Ni lafiya ta ƙalau" ta bashi amsa idonta a rufe.
"Jikinki yana rawafa, kamar zazzaɓi ze kamaki fa"
"to ina ruwan ka? Jikin ka ne ko nawa? Ni kaimin kayana ɗaki ka tafi ka ban guri"
Ɗan girgiza kai Yusuf yayi yaje ya ajiye mata kayan ta ya fito, tana nan inda ya barta, yasa kai ya fice.
Yana fitowa ƙofar da zata sa dashi da harabar gidan yaji an riƙo rigarsa, waigawa yayi yaga waye wannan.
Amal ce tsaye tana huci,
"Amal lafiya kuwa?"
"dole kace lafiya mana? Yusuf daga ina kake kai da Widad?, saboda tsabar abu harda cire mata takalmi, Yusuf wai kai wani irin mutum ne dan Allah? Me kake aikatawa ne haka Yusuf? me yasa lallai seka yi abunda zaka birgeta, bayan kullum baka da kima a idon ta? Sau nawa nake gaya maka kusanci da ita tamkar kusanci da mutuwarka ne? "
Yusuf yace " look Amal niba wani abu nake nema a gurin Widad ba, kuma ba neman kusanci nake da ita ba, kawai ina tausayinta ne, kuma ina jin daɗin yadda mahaifinta ke mutuntani"
"kace tausayi Yusuf? Yusuf daga tausayi so yake shiga, ban taɓa ganin mutumin daya samu damar da ka samu a gurin ta ba, Yusuf a gidan nan ba kowa keda ikon zuwa inda take ba in bada izinin ta ba, kai kuwa kana iya zuwa gurin ta duk lokacin da kake so a matsayin ka na direbanta, Yusuf ina kishin ka, Yusuf sonka nake wallahi bazan zuba ido abubuwa su cigaba da gudana tsakanin ka da Widad a haka ba"
"Amal, Soyayya tsakanina dake ba zata yuwu ba, Mahaifiyarki bata ƙaunar talaka, kuma ni talaka ne inani ina iya Soyayya dake Amal?Hausawa suka ce ƙwarya tabi ƙwarya, idan tabi akushi zata fashe"
"dakata Yusuf" Amal ta katse shi, hawaye tuni ya fara sintiri a idon ta, tace "bazaka iya Soyayya dani ba, amma zaka iya da Widad ko?"
"Amal ni ba Soyayya nake da Widad ba, inani ina son mace kamar ta, ita a kanta bata yarda da wata soyayya ba, Amal nayi Soyayya a baya, abun da na fuskanta a soyayya bazan ƙara yadda in sake fuskantar sa ba, ke kanki da kin san wayeni bazaki soni ba, ba zaki so kasancewa da mutum kamar ni ba, kiyi hakuri "
"ba abunda ya shafeni, what I know is that ba zan zuba ido ka faɗa soyayya da mahaukaciya mara tarbiyya ba, kuma bari in gaya maka ba zaka taɓa kuɓucemin ba kasa wannan a ranka"
Tana gama faɗar haka ta juya da sauri ciki tana kuka, jikin Yusuf yayi sanyi a haka ya ja jiki ya fito.
Masallaci ya wuce yai sallolinsa, sannan ya zauna yana karatun Al'qur'ani mai girma, ya daɗe yana addu'a sannan ya miƙe ya nufi titi dan samun abun hawa zuwa gida.
Abunka da unguwar masu kuɗi, tuni unguwar tayi tsit se sanyi bishiyoyi dake kaɗawa, yana ta tafiya a ƙasa yana tunanin abubuwa da dama, ya baro layin su Widad sosai inda security suke, ba tsammani se gani yayi ansha gaban
sa da mota, tsayawa yayi cak yaga ikon Allah.
Wasu ƙarti ne suka fito daga motar suka zagaye shi, ɗayan yace "kaine direban 'yar gidan Alhaji Nasir?"
Ba tare da tsoro ko shakka ba Yusuf yace "Eh nine"
"Good labari ya ishemu cewar akwai kusanci tsakanin ka da ita, duk inda zata tare kuke zuwa, an samu mu ɗakkota kwanaki amma ka hana, bari in gaya maka wani abu, zamu ƙyaleka ne saboda zakayi mana amfani, zamu ci gaba da bibiyar ka saboda akwai wani abu da muke so ka karɓo mana a gurin ta" cewar ɗaya daga cikin ƙartin
Yusuf yace "Babu wani kusanci tsakanin mu, aiki nake mata tana biyana, ko meye kuje ku tambaye ta ta baku mana"
Ɗaya daga cikin sune ya sakarwa Yusuf wani mummunan naushi, da seda jini ya fito daga bakin sa, a zuciye Yusuf ya ɗago yana kallonsu, babban yace
"Wallahi idan baka kawo mana abun nan ba se mun kasheka, akwai wasu mahimman abubuwa da muke so ka karɓo mana a gurinta idan kaƙi semun maka yankan rago"
"Bayan yankan ragon se kuma me?" Yusuf ya faɗa babu alamar tsoro
Wani naushin suka ƙara masa a gefen ido,
Maimakon Yusuf ya tsorata, ko ya nuna jin zafin naushin, se yayi murmushi yace
"idan kunmin yankan rago, ku kuma ku zauna a naɗe duniya daku?, babu wani mahaluki daya isa yasa Yusuf yin wani abu dan son zuciya da zalunci, kuje ku gayawa wanda ya aiko ku cewar karya kuskura yayi gangancin cin iyakar gonar da ba tasa ba, idan kuma yaƙi zanwa shukokin feshi in ƙone nawa da nashi, kowa ya rasa, wannan saƙon Yusuf ne ga uban gidanku ko wayeshi"
Wani naushin suka yi niyyar kai masa amma ya riƙe hannun ɗayan.
"Waye kai? Waye ya gaya maka wanine ya turomu?" cewar ɗaya daga cikin su
"yadda kuka binciko kuka gano nine direban Widad, haka yakamata ku bincika kusan wayeni, nasani aikoku akayi ku koma ku ƙara tabbatarwa wanda ya aikoku nina ɗauke Widad lokacin da yasa a sace ta, ni aikina tuƙata a mota dan haka ya kiyayi yunƙurin cutar dani"
Hausawa sukace 'sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, sun daki Yusuf sosai, yaso yayi amfani da bindigar sa, amma yin hakan ze rusa masa da yawa daga shirinsa, dan haka ya fasa ɗaukar bindigar, suka daddake shi, wani yana iya ramawa wani kuma baya iyawa.
"zamu cigaba da bibiyarka, harse ka bamu abunda muke nema, zaka gane baka da wayo, Uban taurin kai, Ubangidanmu yafi ƙarfinka"
haka suka barshi a gurin suka tafi.
Da ƙyar Yusuf yaja jikin sa ya hau Napep ya tafi, hancinsa yana ta zubar da jini, jiri ne yake ta ɗibarsa saboda jinin da yake zubarwa da yawa, da ƙyar yaje gida, Allah ya temake shi Umma tayi bacci.
ya cire kayan jikinsa yana goge jinin fuskarsa, Aljihun wandonsa ya taɓa yaji wayar da Widad ta bashi ɗazu.
Hannu yasa ya ɗakko ta yana jujjuya ta "Ka ɓoye ta kamar yadda zaka ɓoye ranka, wannan wayar tamkar rayuwar ka ce"
Maganar Widad ta dawo masa, kunna wayar yayi, Amma akwai password akai shiru yayi yana nazarin kamar yaya wayar nan tamkar rayuwar sa take? Ajiye wayar yayi ya shiga yayi wanka ya fito, nan ya shiga aikin nasa na tunani dan abubuwa da dama sun faru da suke buƙatar nazari.
"Me Widad taje yi Hotel? Me ta gani ya sata kuka? Waye ya turo mutanen nan? Ko waye akwai sa hannun wani a gidan su Widad? Amma dagaske Tausayin Widad zesa ya fara sonta? Me yasa tasa a durƙusa a bashi haƙuri yau? Tabbas zata iya yuwuwa akwai Alaƙa tsakanin wani a gidansu Widad da mahaifin Nurat"
Ji yayi kansa kamar ze fashe, dan haka ya rintse idon sa yana addu'a da fatan bacci ya ɗauke shi koze ɗan samu nutsuwa, Amal ta faɗo masa a rai itama, wai ita bilhaƙƙi son shi take.
Wani tunani ya shigayi watanni shida da suka gabata, da yanzu yana nan da Auren sa, katsam a dalilin irin tasa ƙaddarar aka fasa wannan Aure, bayan cin zarafi da wulaƙanci daya fuskanta daga iyayen matar daze Aura, bacci dai se ɓarawo ne ya ɗauke shi.
*******************************
Da safe Yusuf ya tashi da matsanancin zazzabi, kansa har sarawa yake sosai saboda dukan da yasha jiya, juyi kawai yake akan gadon gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, ganin har kusan ƙarfe tara be fito ba yasa Umma leƙawa ɗakin sa, ta tarar da shi kwance a kan gadon sa, ƙarasawa tayi ta taɓa jikin sa tace "Yusuf lafiya kuwa? Naga har ƙarfe tara baka fito ba?"
"Bana jin daɗi ne Umma"
"dan baka jin daɗi seka zo ka kwanta kana juyi, ka tashi ka watsa ruwa, ka karya seka sha magani"
"to Umma"
Yusuf ya miƙe ya shiga yai wanka, kayan breakfast ɗin ta kawo masa ɗaki, ta kalle shi tace
"Yusuf kamar kumburi nake gani a gefen idonka da bakin ka"
Yusuf yace "Mun faɗi akan babur ne jiya da daddare"
"Amma ka kasa gayamin? Meye amfanin hakan, haba Yusuf"
Yusuf yace "Yi haƙuri Umma, bana son ɗaga miki hankali ne"
"Amma ina fatan ba wani mummunan ciwo daka ji?" tai maganar cike da damuwa
"Eh banji ciwo me yawa ba"
Da kanta ta zauna tana bashi Abinci a baki, ta ɗakko masa first aid box ɗinsa ya ɗau magani ya sha, ya koma ya kwanta.
Kwanciyar sa ba daɗewa Abbas ya kira shi, da ƙyar Yusuf ya ɗaga wayar, Abbas yace "Mutumina kana ina ne? Ina son ganin ka"
"Ina gida bana jin daɗi ne"
"Subhanallah, meya sameka?"
"Zazzabi ne" Yusuf ya bashi amsa
"Shikenan gani nan zuwa"
Su kayi sallama
**************************
Hajiya Halima na zaune falon ta tana shan tea, Isa mai gadi yazo yana kwaɗa sallama a ƙofar falon ta, A fusace tace "wai meye hakane? Lafiya kame do kamin wannan sallama kamar kana bina bashi?"
"Hajiya nine, Isa ne"
"to ya a kayi?"
"Hajiya gurin ki nazo"
Ta ɗanyi tsaki sannan tace "shigo"
Ya shiga falon ya durƙusa yace
"Ina kwana?"
"Kai bana son doguwar gaisuwar nan meke tafe da kai?"
"to Hajiya kin san shi sha'ani na rayuwa kiwon mutum ake ba dabba ba koba haka ba?"
"kai nifa bana son wannan surutam banzae, ka faɗamin kanka tsaye meke tafe da kai"
Isa ya gyara zama yace "game da sabon direban nan ne Yusuf, gaskiya Hajiya akwai buƙatar kisa ido, jiya yadda na gansu Allah ya nuna min Annabi salallahu alaihi wassalam, kin san dai irin shigar da take yi, bayan kin fita ita dashi suka fita, basu dawo ba se ƙarfe tara na dare, bayan sun dawo a gabana da idanun nan nawa" yai maganar yana gwalo idon nasa ya cigaba da cewa
"da idanu na naga suna rungume juna, Hajiya a saka ido, kina gani idan ba kiranmu akayi ba bamu da damar shigowa kiga yadda take hantarar mu, Amma shi ba yau ba gobe cikin sintiri yake har cikin ɗakin kwanan ta, Allah kaɗai yasan me suke yi, gaki da 'yan mata kema kyawawa bekamata yana gardi baligi ya dinga wucewa yana kalle miki su ba, shiyasa nace bari inzo in sanar dake abunda ake ciki "
Dire kofin hannun ta tayi, taja wata nannauyar Ajiyar zuciya tace " Hmm naji maganganun ka, kuma kazo da magana abun dubawa, tashi kaje zan san abunda zanyi "
Isa ya miƙe yana murna yace
"shikenan Hajiya na barki lafiya "
Shiru Hajiya Halima tayi tana zake nazartar kalaman Isa megadi, tabbas Widad bata yadda wani ya Wulaƙanta Yusuf ba, lokacin da ciwon ta ya tashi taƙi yadda da kowa se Yusuf, idan har dagaske wani abu na faruwa a tsakanin su to tabbas akwai yuwuwar ta gayawa Yusuf inda abunda suke nema yake.
**************************
Widad kwana tayi da zazzabi da ciwon kai, da ƙyar ta samu tayi bacci.
Jikin ta sam babu ƙwari ta miƙe domin haɗawa magen ta abunda zeci.
Widad na matuƙar son dabbobi, tana tausayin su fiye da yadda take tausayin mutane, akwai shaƙuwa me ƙarfi tsakaninta da dabbobinta, mussman ma wannan magen nata pita, da kuma karen ta dake gidan gona, tana jin daɗin kasancewa da su, dan ba ƙaramin ɗebe mata kewa sukeyi ba.
Ta samu container ta zuba masa madara, ta samo wani ta zuba masa gugguru, ta koma gefe tana kallon magen, maimakon magen yaci seya koma jikin ta ya kwanta, dan ya saba idan lokacin cin Abinci yayi, ta zuba masa nasa yana ci itama tana cin nata
**********************************
Abbas ne yayi Sallama ɗakin Yusuf, da ƙyar Yusuf ya iya amsawa, ya miƙe zaune suka gaisa da Abbas.
"Sannu Yusuf, ko Asibiti za muje in sauke ka"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a na sha magani kawai, ya kake ya aikin?"
"Alhamdilillah, jiya Oga Suleiman yake neman ka, shine kiran da nayi maka, kuma se kace baka jin daɗi, yanzu yau ba zaka gidan su mutuniyar taka ba?"
Yusuf yace "bazani ba gaskiya, sedai zuwa gobe in Allah ya kaimu idan naji sauƙi"
Abbas yayi ƙasa da murya yace
"Ya kuɗin nan waye ya turo dasu kuwa?"
"itace wai Albashi na ne na watanni uku da bata bani ba, nace mata yayi yawa ta rage taƙi"
"Taɓɗijan kaima Yusuf da wani abu, kamarya ta rage? Malam kawai kaci kuɗi, meye labari kuma?"
Yusuf ya gaya masa Hotel da suka je, da yadda suka dawo tana kuka, Amma be gaya masa zancen wayar nan ba data bashi.
Nan suka cigaba da tattaunawa zuwa wani lokaci Abbas yace ze tafi, Naira dubu ɗari Yusuf yayi masa transfer a cikin kuɗin, Abbas yaita murna yana godiya suka yi sallama.
Amma ƙasan zuciyar Abbas kamar ya fasa ihu
'dana san wannan alherin Yusuf zeje ya dinga samu da tun farko nina karɓi aikin nan, ya samu dubu ɗari biyar amma ya bani wata shegiyar dubu ɗari, ga danƙareriyar waya ya samu, na tura shi dan ina gudun wulaƙanci amma yaje yana samo abun Arziki, dole in san yadda zanyi a cire shi daga kan aika ni maye ni"
'Amma hatsari da kasadar dake cikin aikin fa?' wata zuciyar ta tambaye shi, tsaki yayi yana ci gaba da surutai.
*******************************
Shafa jikin magen take a hankali tana lallaɓashi yaci Abinci, wayarta ce ta fara ringing, muzurun nan ya kasa a guje yaje ya ɗakko ta a bakin sa ya kawo mata, shafa kan muzurun tayi tace "thank you Roux"
Ta amsa wayar tasa a kunnen ta
"Ranki ya daɗe Bala fa babu lafiya, an ɗauke shi rai a hannun Allah an kai shi Babban Asibitin cikin gari, dan besan waye a kansa ba"
Miƙewa tayi tsaye tace "what? How comes? Wace irin rashin lafiya ce wannan?"
"Nima ban sani ba gaskiya, Amma an fita da shi daga Asibitin cikin kurkukun gaba ɗaya"
Bata kashe wayar ba ta miƙe, da sauri ta shiga bedroom ɗinta ta canza kaya, dukda yanayi na rashin lafiya da take ciki, wayar ta ta koma ta ɗakko ta fara daddanawa sannan tasa a kunnen ta.
Yusuf yana jin wayarsa tana ringing ya ƙi ɗagawa yasa ta a silent, ya ajiye wayar ya cigaba da kwanciyar sa.
Jifa tayi da wayar akan kujera ta fice harabar gidan, gurin su Nura ta nufa, tana zuwa suna gaishe ta amma bata kula suba tace
"Ku kiramin driver yanzu"
Jiki na rawa suja shiga kiran Yusuf babu ƙaƙƙautawa, Amma be ɗaga ba.
Ta kalli Nura tace "ɗakko mota da sauri, zaka fita dani"
Cike da washe baki yaje ya ɗakko mota, ta shiga Nura yaja motar suka fita, gaba ɗaya ji take kamar tayi Amai, dukda a bayan motar ta zauna amma warin hammatar Nura ya cika motar, se tsaki take yi badan ya zama urgent ta fita ba babu yadda za'ayi ta yadda wannan ƙazamin ya jata a mota, suna tafe tana masa tsawa gami da hantararsa, Amma Yusuf ze gane kurensa na ƙin zuwa da yayi yau sannan yaƙi ɗaga waya.
Prison tasa ya kaita, suna zuwa ta fita ta shiga, kai tsaye ofishin Hisham ta wuce.
Yana ganin ta yai murmushi ya sallami kowa daga office ɗin sannan yace "barka da zuwa lady boss, Ashe kin dawo Nigeria?"
"Ya aka yi Bala ya kamu da rashin lafiya da har ta kai shi ga kwanciya, seda aka fita da shi daga gidan nan?"
"Ranki ya daɗe gaskiya dama yana ɗanyin rashin lafiyar a tsai tsaye, Kawai se ɗan uwansa ya kawo masa ziyara, bayan ya tafi jikin sa ya rikice"
"yanzu kana nufin kace min Ɗan uwansa ne ya kawo masa abunda yaci, jikin sa ya rikice kenan? Saboda sakaci da rashin sanin aikin ku?"
"A'a ranki ya daɗe kin san?...
"Yimin shiru malam, saura sati ɗaya tal a koma kotu, kawai se inji wannan banzar maganar mara tushe, shikenan amma kasani idan har rashin lafiyar Bala haɗin baki ne, duk wanda yake da hannu a ciki shima abunda ya samu bala ze sameshi. "
Ta miƙe a fusace ta fito, Hashim ya biyo ta da sauri amma ta shiga mota da niyyar ta ta wuce gurin lawyern Daddy, amma ba zata iya jure wannan tsamin da Nura yake ba, dan haka tace ya nsida ita gida, tana mamakin ƙoƙari irin na Daddy da yake iya shaƙe wannan warin hammatar, Yusuf kullum tsaf dashi cikin ƙamshi, amma wannan ƙazamin kamar baya jin yadda yake wari, seda ta bari sun koma gida, sannan tayi wa Nura ta tas akan ƙazanta da warin da yake yi a gaban sauran ma'aikatam.
Gaba ɗaya ranta a ɓace, ga jikin ta ba ƙwari gashi a ƙule take da Yusuf, tana shiga babban falo ta tarar da Hajiya Halima, bata kula ta ba tasa kai zata wuce
"Widad ina son Magana dake"
Widad ta tsaya ta juyo ta kalleta ba tare da tace komai ba.
"Widad bekamata ace kina fita lokacin da kike so ki dawo lokacin da kike so ba a matsayin ki na mace, sannan ki dinga dawowa sanda kika ga dama ba, Alhalin nida nake zaune tare dake ban san idan kike zuwa ba, Sannan wannan yaron da yake sintiri gurin ki har ƙuryar ɗakin ki, Sam be dace ba"
"kinga dakata Malama, zamanki nake a cikin gidan nan? Koke kika ajiyeni? In kun tashi taku yawon gayamin kuke? Kisawa ranki gidan nan tamkar bariki yake, kowa yayi abunda yaga dama