Showing 33001 words to 36000 words out of 135096 words
niba mahaukaciya bace"
Gaba ɗaya Yusuf ya rikice, yace "is Ok ai dama ke ba mahaukaciya bace, ki kwantar da hankalin ki"
Amal ta kalli Widad tace "kina wannan tamɓelen kike cewa ke ba mahaukaciya bace? Kalli fa abunda kike yi mahaukaciya ce ke tuburan, dan me hankali baze abunda kike ba"
Yusuf yace "Haba Amal, ya ana ƙoƙarin kwantar mata da hankali Amma kike tinzira ta"
Amal ta zumɓura baki tace "kaga ni karɓi kayan nan, kalli yadda take wani riƙe ka aikin banza kawai"
Widad ta shammace ta, tasa hannu ta kifar da farantin ruwan zafin, aikuwa ya zube a ƙafar Amal, Ihu Amal ta saki, wanda ya janyo hankalin Mahaifiyar ta da Ramlah suka taho da sauri.
Idan ba gizo idon Yusuf yake masa ba, tabbas kamar ragowar ƙwayar magani ya gani a ƙasan kofin da'aka zuba tea ɗin, sedai kafin yayi wani yuƙuri
Hajiya Halima taƙarsaso tana cewa "lafiya, meye haka?"
Cikin kuka da azaba Amal tace "Mummy, Widad ta ƙonani da ruwan zafi, Mummy ƙafata"
Mummy ta kalli inda Yusuf ke tsaye, Widad na riƙe da shi tace
"To maye Jarababbe, ka lallaɓa ka Asirce ta ita da uban ta, shine ka koma da baya zaka illatamin 'ya ko? Wallahi ka kiyayeni, kuma kafin kasa kwaɓata tayi ruwa ni zanyi maganin ka, ke kuma" ta nuna Widad dake bayan Yusuf tace
"dan Ubanki ba dai hauka ba, a haka zaki ƙare, Hauka yanzu kika fara shi, daga nan har ƙarshen rayuwar ki, keda hankali sedai ki ganshi a gurin wasu, wannan haukan haka zaki mutu kina yinsa"
Widad ta Jijjiga Yusuf tace "kai ka gaya musu niba mahaukaciya bace, kuma wallahi idan ta kasheni itama sena kashe ta, gaba ɗayansu sune zasu kasheni, suna tace min mahaukaciya zasu kasheni, wallahi in baka hana su ba ni zan kashe su"
Ramla tace "kaga Malam dalla cikata kazo ka bar gidan nan, tunda babu gadon ka a ciki, ba'a haɗa kuɗi da matsiyacin uban ka an gina ba"
Wani irin kallo Widad takewa Ramla daga bayan Yusuf.
Kallon da Widad kewa Ramla ne yasa taga kamar Widad ta dawo hankalin ta.
Widad tace "idan ka tafi ka barni kasheni za suyi, kashe mutane suke yi fa"
Mummy tace "uwarwa muka kashe miki? Mu bama kisa kumako bamu kashe ki ba mutanen da kike Wulaƙantawa suna nan suna bibiyar ki zasu kashe ki, Mahaukaciyar banza da ta wofi, Allah kaɗai yasan me sukeyi da harta yarda da shi haka, dalla kuzo mu tafi suje su ƙarata, Allah ya ƙara birkita ƙwaƙwalwar ki zauna a haka koma samu mu huta, in ƙwaƙwalwar ki ta birki ce ta Ubanki ma ta birkice kowa ya huta da iskancin ki"
Ramla tace " Mummy watch your words fa, kina ta sakin layi mu tafi kema Amal Allah ya ƙara, maganinki kina ma wannan ɗan isakan direban shisshigi, gashi ai sun ƙonaki a banza nan gaba ma illataki zasuyi"
Shiru Yusuf yayi yabi bayan su da kallo, gaba ɗaya tausayin Widad da Mahaifinta ya kama shi.
Ya lallaɓa Widad ya bata youghurt da ƙyar ta sha, tana sha tana masa surutai na shirme, irin na masu taɓin hankali.
"Menene dalilin samun taɓun hankalin Widad?" Yusuf ya tambayi kansa
Kwanciya tayi a jikin sa tana lumshe ido alamar bacci take ji, ƙirjin Yusuf se bugun uku uku yake, Kasancewar ya keɓance da Widad, abunda be taɓa yi ba, a duk lokacin da yayi yunƙurin rabata da jikin sa seta saka ihu kamar ƙaramar yarinya.
Yusuf yayi mamakin iri maganganun da Hajiya Halima da 'ya' yanta suka dinga faɗa akan Widad, koda yake ba abun mamaki bane, duba da Yadda Widad ɗin ke Wulaƙanta su, Amma me sukayi mata take musu haka? " Yusuf yayi Alwashin tone duk wani abubuwa da ake ɓoyewa, kuma ya ƙudurce a ransa zeyi duk me yuwuwa ya jure wulaƙancin Widad yaga ta ina ze temaki rayuwar ta.
Yusuf yai shiru yayi zurfi a cikin tunani, yaji Widad tana ajiyar zuciya alamun tayi bacci, a hankali ya zame ta daga jikin sa, ya kwantar da ita ya lulluɓeta ya fita ya kulle ta a ɗakin yaje yai salla.
Ana idar da Salla Isa yace " Yusuf ashe uwar ɗakinka ce babu lafiya? Ance taƙi buɗewa kowa ƙofa amma tana jin muryar ka ta buɗe, gaskiya kai ɗan baiwa ne, Amma naji ance haukan nata ne ya tashi ko?"
Yusuf ji yayi kamar ya kwaɗawa Isa mari, Amma ya ƙyaleshi ba tare da yace masa komai ba.
Ya koma ɗakin nata ya tarar bata farka daga baccin ba.
Falon ta ya koma yana tunani, Ba zato ba tsammani yaji sallamar Mahaifin Widad a falon, Amsawa Yusuf yayi cikin girmamawa tare da risinawa.
Alhaji Nasir a ɗan ruɗe yace "Sannu babban Mutum, ya me jikin kuma?"
"Alhamdilillah, ta samu bacci"
"Masha Allah"
Yasa kai ya shiga bedroom ɗin, ya taka a hankali zuwa gaban gadon Widad ya zauna a gefen ta ya ɗagota, idon ta a rufe tana bacci, ya shafa kanta yace
"Allah ya baki lafiya my daughter" ya kalli Yusuf yace "Nayi mamaki data iya yadda da kai, idan ciwon nan ya tayar mata bata yadda da kowa seni, ko Bulama wani lokacin muɗinma bata yadda damu gaba ɗaya se an mata allurai"
Yusuf yace "Wane irin ciwo ne haka?"
Alhaji Nasir ya ɗan na Numfashi cike da damuwa yace
"Yusuf, nasan mutane da yawa suna mata kallon bata da kirki, wasu suna zargina da barin 'yata ta lalace, kawai ina kallon sune, ba tare da nace wa kowa komai ba, Yusuf Widad ita kaɗaice' yata dana mallaka, larurar nan ta same ta ne sakamakon kashe mahaifiyar ta akan idon ta"
Zaro ido Yusuf yayi yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
Alhaji Nasir ya jinjina kai yace "ƙwarai kuwa, Akwai abunda ya faru da Widad, wanda tun daga lokacin take gudun mutane, ta haɗu da larurar ƙwaƙwalwa, dukda partially ne larurar tata da farko, Amma daga depression ya zarce mata ta samu Arthropophobia,
larurar ƙwaƙwalwa me sa mutum ya dinga jin tsoron mutane, ba mutane ba wani lokacin idan tana cikin larurar ko haske bata so, muna ta magani Sedai har yanzu na gaza samun abunda zesa ta farinciki, kana gani ko fara'ar kirki ba tayi, na yanke shawarar in mata Aure amma tace bata so, dan Allah Yusuf na san kana haƙuri haka nan naji ka kwantamin, dan Allah ka tayani Addu'a, Allah ya bawa 'yata lafiya, ita kaɗai nake da ita, ba uwa ba uba"
Gaba ɗaya tausayin Alhaji Nasir da' yar sa suka cika shi, Yusuf ya numfasa yace "Insha Allah Alhaji, Amma ba kayi......
"Yallaɓai ya akayi harka shigo ban sani ba? muna can part ɗina muna fafutukar a kira likita yazo ya duba ta, gaba ɗaya yau kwana mukayi ba muyi bacci ba saboda yadda jikin Widad ya rikice, ko Abinci ba wanda ya iya ci yanzu ma mun shiga muyi salla ne ka dawo ban sani ba" Hajiya Halima ke wannan maganar cike da salon bariki da Kissa.
Alhaji Nasir yace "Allah sarki, nasan kina ƙoƙari akan Yarinyar nan, Allah ya saka miki da Alkhairi, ina su Baby Amal ɗinne ko basu san na dawo ba?"
"Amal ma bata jin daɗi, Ramla kuma salla take, ina jiran Widad ta farka ne a bata Abinci, mun samu da ƙyar tayi bacci"
Yusuf kam bin Hajiya Halima yayi da kallo, yana mamakin wannan iya salon barikanci nata, gaba ɗaya ta juye kamar tana cikin damuwar gaske.
Yusuf yace "Bari inje gida Alhaji tunda ka dawo"
"Shikenan Yusuf ka gaida gida, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi"
"A'a bakomai Yallaɓai" Yusuf yasa kai ya fice, Hajiya Halima tabi bayan sa da harara.
Kan Yusuf ya ƙara ɗaurewa da maganganun da Alhaji Nasir ya gaya masa, yana daf da fita kawai yaga Ramla ta sha gaban sa.
Tsayawa yayi yana kallon ta, ta kalle shi cikin Isa tace
"Bani mukullayen Motar Widad dana ɗakin ta dake gurin ka"
Yusuf ya tsuke Fuska yace
"ɗan bani hanya zan wuce mana"
"Ni kake kallo kakewa wannan gadarar haka? Zaka bani ko sena maka rashin mutunci?"
"bake kika bani ba, ba kuma ke nakewa aiki ba, dan haka babu ruwan ki dani"
"Kai kalli tsabar Idona, karka kuskura kace zakayi Jayayya dani, naga se wani shisshigi kake kana cusa kai a gurin waccan Mahaukaciyar da ita da Ubanta, to bari kaji in gaya maka, idan ma wani abu kake kwaɗayin samu wallahi ba zaka samu ba, Kuma hauka yanzu Widad ta fara shi daga nan har ƙarshen Rayuwar ta, ba zata sake moruwa ba, gara ka cire wa kanka ƙwalamar wannan daular da dukiyar, yadda kazo a talaka haka zaka koma a matsiyaci, idan kaga dama kaje ka faɗawa duk wanda zaka faɗawa, shawara ta ƙarshe da zan iya baka itace, ka gaggauta Ajiye aikin nan ka ƙara gaba ya fiye maka Alkhairi akan wasa da rayuwar ka"
Murmushi Yusuf yayi ya dubi Ramla yace "in kinga na bar aiki a gidan nan wanda nakewa aikin ne suka sallameni, kina wani iƙrarin dukiya, dukiya nawace taki a dukiyar nan? Ki kiyayi Yusuf, matsi da takura babu wanda Yusuf be gani ba a rayuwar sa, dan haka ƙaramar barazana irin taki ba zata hanani Aiki na ba, ni babu ruwana da rayuwar da kuke a cikin gidan nan ni aikina kawai nasani, ban guri in wuce ko in hankaɗeki"
Galala tabi Yusuf da kallo, da ma akwai Yadda yake mata magana cikin Izza shima, Me yasa ba yayiwa Widad da take Wulaƙanta shi, lallai maganar Mummy gaskiya ce, ya kamata ayi maganin Yusuf.
Yusuf fa kai ya sake ɗaukar wuta, abun da ya faru yau, ya ƙara tabbatarwa Yusuf akwai wani mugun nufi a zuciyar Hajiya Halima da 'ya' yanta.
Umman Yusuf ta lura da yanayin Yusuf ko iya sakewa yaci Abinci ba yayi, Umma ta kalle shi tace
"Yusuf wai meke damunka ne haka? Naga gaba ɗaya kwanan nan na kasa gane kanka, Allah yasa ba wani abun aka kuma yi maka ba?"
"Umma ni a rayuwa ta wani irin ƙalubale ne ban gani ba? Aini lamarin rayuwa ta na miƙawa Allah, aikin da aka bani ne me matuƙar rikitarwa"
Nan ya kwashe komai ya gayawa Umman sa, Umms tayi shiru na wasu 'yan mintuna sannan tace
"lallai wannan lamarine me sarƙaƙiya, nidai fatana ka kula da kanka Yusuf, kayi taka tsan tsan ka cigaba da Addu'a, Amma waye yazo ya nemi da a dinga bawa ita Yarinyar kariya?"
Shiruu Yusuf yayi sannan ya girgiza kai yace "Wallahi Umma ban sani ba"
"Ta yaya za'a bawa mutum kariya ba tare da sanin sa ba? Kaima kamar baka san aikin naka ba?"
"Umma nasan aiki na, Amma nima umarnin manya na nake bi, wataƙila be kamata in sani bane"
"Hakane amma kayi taka tsan tsan, naji tausayin yarinyar nan, Amma ni jikina yana bani wani abu game da aikin nan da aka saka, Amma kasa gane ko menene, ina dai yi maka addu'a a duk inda kake Yusuf, ni dai fatana ka kula da kyau"
"Insha Allah Umma na"
Haka suka cigaba da taɓa hirarrakin su na ɗa da uwa.
Sosai tunani ya auri Yusuf, maganar Umma tana bisa hanya, waye wannan da ya nemi a bawa Widad kariya a ɓoye, dole akwai wata a ƙasa.
*******************
Washegari da safe, Yusuf ya koma gidan su Widad, bayan sun gaisa da su Nura, Yusuf yace "Nura ya jikin uwa ɗakina kuwa?"
Nura yace "ta yaya zamu sani? Kaine dama aka ɗauka mutum a gidan nan, da kai ake komai mu ina zamu san wani abu? Ai kaine mutum a cikin mu"
Yusuf yayi Murmushi ya samu guri ya zauna. Murtalah ya ƙaraso inda Yusuf yake yana faɗin "Malam Yusuf, ɗazu Alhaji ya leƙo yana tambayar ko kazo, dama yace in kazo a shiga da kai ɓangaren sa"
Yusuf yace "shikenan babu laifi, muje"
Murtalah yayi gaba Yusuf ya bishi a baya, Sam Yusuf be taɓa sanin da wannan ɓangaren a cikin gidan ba, gjda se kace ba'a duniya ba, Yusuf ya buɗe ido yana bawa idonsa Abinci.
Suna shiga Ƙaton falon, Murtalah yace
"to ni na tsaya daga nan, dan bani da ikon ƙarasawa ciki, seka fito"
Seda Yusuf ya gama waige2 sannan ya kalli ƙatuwar ƙofar dake cikin falon, a hankali ya taka yaje ƙofar ɗakin ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama.
Alhaji Nasir ne ya amsa tare da cewa "Shigo"
Yusuf ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, Alhaji Nasir ne zaune Widad ta ɗora kanta akan cinyar sa, idonta biyu tana ta jujjuya ƙwayar idon ta, gefe kuma Alhaji Bulama ne zaune a kusa da Alhaji Nasir.
Yusuf ya durƙusa yana gaishe su, Alhaji Nasir ya faɗaɗa murmushinsa yace "Me babban suna, ashe kazo?"
"Eh nazo ranka ya daɗe, yame jiki"
Alhaji Nasir yace
"Jiki da sauƙi, Alhamdilillah an samu ta dawo hayyacin ta, Amma taƙi magana sam"
Yusuf ya kalle ta yace "Sannu ya jikin naki?"
Haɗe rai tayi ta tura baki tace "Malam ni lafiya ta ƙalau"
Alhaji Bulama ya jinjina kai yace
"gaskiya akwai ka da sa'a, tun ɗazu muke magana taƙi kulamu amma kai gashi tayi maka magana"
Alhaji Nasir yace "My lovely, kin san wannan?" yai maganar yana nuna mata Yusuf
"Daddy nifa ba mahaukaciya bace"
Daddy yace "Ai na sani Babyna, tambayar ki kawai nayi"
Ta tura baki tace "Nasan shi"
Alhaji Bulama yace "to waye?"
"Direba ne" ta bashi amsa a taƙaice.
Daddy yace "direban wanne daga ciki?"
Maimakon ta basu amsa seta kalli Yusuf tace
"kai ka gaya musu niba mahaukaciya bace, naga suna yadda da maganar ka, wallahi ni ina da hankali"
Yusuf yace "ai dama basu ce ke mahaukaciya bace, kina da hankali"
Ta kuma cewa "ka gaya musu wani na ƙoƙarin kasheni a gidan nan, ka cewa Daddy dan Allah ya ƙyaleni in koma England"
Yusuf yace "Shikenan ki kwantar da hankalin ki, zan gaya musu Insha Allah"
Alhaji Nasir yace
"Naga taku tazo ɗaya da Yusuf Lovely, kamar shi kin yadda da shi ko?"
"Allah ya kiyaye, direba ne kawai, yana nan a matsayin sa na direba, karma ka faɗi wani abu da zesa yaji cewa shi na musamman ne, ko yana da wani matsayi, i don't trust anyone"
Alhaji Nasir ya girgiza kai yace "Yusuf nagode sosai, zaka iya tafiya abunka kaje ka huta, dama na kiraka ne in ƙara maka godiya nagode"
Yusuf yace "Ai babu wani abun godiya da nayi Yallaɓai, Allah ya bata lafiya"
Suka yi Sallama ze tafi, sedai yana ƙoƙarin barin ɗakin, Hajiya Halima ta shigo da tray da kayan marmari a kai, tana ganin Yusuf ta haɗe rai ta bishi da wata uwar harara ba tare da ta bari Alhaji Nasir yaga hakan ba.
Yusuf ya kama hanyar fita, yaji ance "Yusuf ashe kazo?"
Ya juyo ya kalli inda Amal ke masa magana yace "Eh nazo, tun ina ciki na duba jikin Madam ne"
Amal tace "shikenan ɗan jirani ina zuwa"
"to shikenan bari in jiraki a waje" Yusuf ya koma harabar gidan yana jiran fitowar Amal, mintuna kaɗan sega Amal tazo, kaya ne a jikin ta wanda sukai matuƙar matsarta, ta dube shi tace
"dan Allah so nake muje gurin shan ice cream tare, Akwai maganar da nake so muyi"
"Kina ganin ba matsala kuwa? Kinga wancan karon, Madam bata ji daɗin fita da mukayi tare ba"
"Shikenan idan ba zaka iya min Alfarma ba, na fasa zuwa"
Ɗan shiru Yusuf yayi yana nazari a ransa, tabbas Amal bata da wayo sosai, idan ya bugi cikin ta ze samu bayanai, dan haka ze iya shanye masifa da tsiwar Widad, a fili yace "shikenan kawo car keys ɗin naki mu tafi"
Ta kalle shi tayi fari da ido tace "Dan Allah meye matakin karatun ka ne? Ka iya turanci Yusuf"
Ɗan basarwa kawai yayi murmushi ya nufi inda motocin suke.
Wani Joint tasa ya kaita, tayi ordering Pizza da tea, ta tambayi Yusuf me zeci yace shi baya cin komai.
Yusuf ya kalleta yace "Wai ya naganki duk wata iri ne yau?"
Ɗan taɓe baki tayi tace "ba lafiya ba, shine ko ka tambayeni ya jikina? bayan a gabanka Widad ta ƙonani jiya ba abunda kayi, baka damu dani ba, Amma nasan saboda rashin lafiyar ta yasa kazo da wuri yau" ta ƙarasa maganar tana tura baki
Yusuf ya ɗanyi Murmushi yace
"kiyi haƙuri, kinga bata da lafiya wani mataki zan ɗauka akanta? kuma kinga kaman mamanki da Yayar ki basa Son ina yawan shiga al'amuran gidan ku"
Amal tace "ba Al'amuran gidan nan ne basa son kana shiga ba, Al'amarin Widad ne da kake nuna damuwa dashi sosai ne basa so, ko baka ga Yadda take Wulaƙanta mutane ba?"
"Eh amma, ita ina maman ta ne take rayuwa ita kaɗai?"
Amal ta ɗan taɓe baki tace "Kashe ta akayi fa, shine dalilin da yasa ta zama mahaukaciya bata son mutane"
Zare ido Yusuf yayi kamar besan komai ba yace "waye ya kashe ta?"
Amal ta taɓe baki tace "Oho wayasani? Kana gani dukda mahaifinta yana da kuɗi amma a binciko wanda yayi laifin abu ya gagara, shi ne ita kuma tace zata nemo wanda suka kashe mahaifiyar ta, akwai mutanen data sa aka kama aka kulle a prison ba tare data nada wata cikkakiyar hujja ba, dan haka itama ake farmakinta, sannan akwai wani abu da'ake so a karɓa a gurin ta wanda nima ban san komenene ba, Shiyasa nake gujemaka yawan Shiga lamarin ta bayan Aƙidarta ta Wulaƙanta mutane, duk randa ka bari wani kusanci me ƙarfi ya shiga tsakanin ka da ita, ba shakka za'a fara farmakin rayuwar ka domin za'ace kasan inda abunda ake nema a gurin ta yake, shine death Contract ɗin data gaya maka ai!!!"
IN AN KARANTA AYI SHARHI PLEASE
SANNAN AYI SHARE
07063065680
Ayshercool.
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
ELEGANT ONLINE WRITER'S
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
PART1