Showing 81001 words to 84000 words out of 135096 words
sunanka ba fa"
"ƙawa zan gaya miki very soon insha Allah, dan Allah in an samu wani update ɗin ki sanar dani, sannan akwai ajiyata a wayarki ki kula sosai light"
"Ajiya kuma? Wace irin Ajiya?"
Murmushi Yusuf yayi yace
"Light, light tabbas ina da Ajiya a gurinki, dan Allah ki kula da kanki da kuma wayarki, idaan nazo zan nuna miki ajiyar"
"shikenan Aboki, amma dan Allah ka dena rufe wayarka"
"to shikenan insha Allah"
Tunda Yusuf yaji labarin nan hankalinsa ya tashi, ya shiga tunanin ya Widad take, ba shiri ya miƙe ya shiga shiryawa.
Ya fito tsakar gida, Umma ta kalle shi tace "se ina kuma?"
"zanje gidansu Widad ne?"
"yau kuma, to Adawo lafiya"
Ya amsa da Allah yasa.
Yana zuwa gidan Isa yace "Yusuf ina ka shigane ka dena zuwa gidan nan kusan kwana tara, me gida yasa an kiraka a waya shima ya kira amma layinka baya shiga, ka dena zuwa ba tare da wani dalili ba"
Bece komai ba ya shiga cikin gidan da sauri, yana zuwa ɓangarenta ya nufa ya tarar bata nan, ya fito babban falo yaga Amal.
"Amal dan Allah ina Widad ne"
Banza tayi masa taƙi ce masa komai Anwar ne ya shigo hannunsa riƙe da leda yana ganin Yusuf yace "bawan Allah kwana da kwanaki ake nemanka baka zuwa, daga samun saɓani ka ɗauke ƙafa Uwar ɗakinka na neman rasa ranta.
Ba ƙaramin razana Yusuf yayi ba yace " tana ina? "
Anwar yace " tana ɓangaren Daddy "
Da sauri Yusuf ya nufi sashin na Alhaji Nasir yana shiga ya tarar da Widad a zaune Daddy yana ta aikin rarrashi tace Abinci amma taƙi se kuka take.
Daddy na ganin Yusuf yace "Alhamdilillah, Yusuf ashe zaka dawo saura ƙiris in fita nemanka da kaina"
Yusuf seda ya firgita Widad ta zabge gaba ɗaya, ta rame sosai ta ƙara haske idanunta a kumbure, juyawa tayi gaba ɗaya taƙi kallon inda Yusuf yake.
Yusuf yace "Yallaɓai bata da lafiya ne?"
"ciwonta ne ya tashi, ta fara samun sauƙi naga baka zuwa na tambaya, tace min rigima kukayi ka dena zuwa, na mata faɗa naga ta sake shiga damuwa ga kuma batun Auren nan, ta dena cin Abinci ko magana taƙiyi, se kuka munyi magana da wani abokina a Abuja yace akwai babban likitan Ƙwaƙwalwa a international Hospital yana zuwa ranar Talata, idan ba zaka damu ba dan Allah ina so ka temakamin ku tafi tare, na yadda da kai Yusuf nasan ba zaka cutar dani ko 'yata ba, tafiyar tazo daidai da taronmu na shekara idan banje ba akwai matsala, seku sauka a gidan Abokin nawa kuje Asibitin daga nan duk abunda kukayi kuka gama ranar Monday jirginta ze ɗaga Zuwa England, ta koma taje ta ɗan huta, kafin in san me ya kamata inyi, naga tafi samun nutsuwa a can"
Jiki a sanyaye Yusuf yace " Shikenan an fasa Auren nata?"
"eh munyi magana da Bulama, mun yanke shawarar ɗaga Auren se ta samu sauƙi, idan babu matsala baka da wani abunda zakayi ban takura ka ba seku tafi"
"Shikenan Yallaɓai zanje in shirya insha Allah, Allah ya bata lafiya ko nan da birnin Sin ne zanje insha Allah "
"to shikenan masha Allah, nagode sosai Allah yayi Albarka ya jiƙan mahaifa, tafiyar safe nake son kuyi dan kuje da wuri, jibi in Allah ya kaimu zamu kwana a gidan gona, da an idar da sallar Asuba seku tafi, nace kubi jirgi tace A'a"
"Ameen ya Allah Bakomai Yallaɓai, zanje in shirya insha Allah"
Yusuf a ransa yace 'dole inje wannan tafiya, duk cikin aikina ne'
Kallon Widad yake amma sam taƙi kallon inda Yusuf yake.
Miƙewa tayi ta bar ɗakin daddyn gaba ɗaya.
Alhaji Nasir yace "Yusuf tabbas nasan kana da haƙuri, shiyasa kuka daɗe tare da 'yata, kana da matuƙar tasiri a rayuwarta ko yanzu ka canza mata abubuwa da dama na rayuwarta nagode da wannan namijin ƙoƙari da sadaukarwa ga' yata"
"bakomai Yallaɓai Allah yasa a dace, Allah ya bata lafiya"
********************* **************
"Masha Allah, komai yana tafiya yadda muka tsara, komai zezo ƙarshe koda tsiya koda tsiya tsiya se mun mallaki abunda muke so" cewar Alhaji Munir
Alhaji Musa ya kwashe da dariya yace "tabbas haka maganar ka take, nayiwa yaran nan jan kunne yadda yakamata baza'a samu matsala ba Saleh yace ze sanar damu duk wani abu da ake ciki"
Alhaji Munir yace "ƙunrunƙus, yayin da muka ɗauke hankalinsa ta ɓangare ɗaya, ɓangare ɗaya kuma baze halarci taron kasuwanci ba"
Suka ƙyalƙyale da dariya gaba ɗaya.
(RASHIN SANI......)
Share and share please 🙏 🙏 🙏 🙏
Domin gyara sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1
Page 22_23
Yusuf yaso yabi bayan Widad dan ya duba ta, amma yasan halinta tsaf zata yanƙwanashi, dan haka ya yanke shawarar tafiya kawai.
Office ya wuce kai tsaye, ya tarar da Suleiman yana shirin fita suka gaisa Suleiman yace "Yusuf akwai wani update ne"?
"Eh yallaɓai gurinka ma nazo"
"shikenan mu koma ciki" suka juya zuwa cikin office ɗin gaba ɗayansu.
Nan Yusuf ya zayyanewa Oga Suleiman komai da yake wakana, akan harkar binciken da batun tafiyar da za suyi, da abunda Nurat ta sanar dashi.
Suleiman yace "Amma baka ganin mu haɗaka da abokan aiki, suyi muku rakiya a wata motar gudun samun matsala?"
Yusuf yace "Insha Allah babu wata matsala Oga, kasan a slide mistake yarinyar nan zata iya ganewa nikuma bana son ta gane komai a yanzu har bincikenmu ya kammala".
"shikenan Yusuf Allah yayi mana jagora, Insha Allah zakayi Nasara ana ta samun haske akan lamarin, bari ni zan fita ne yanzu zanje headquarter"
"to shikenan Yallaɓai a sauka lafiya"
Bayan tafiyar Suleiman Yusuf ya fito yana shirin tafiya, Suka haɗu da Sakina, Sakina tace
"Ashe yau ka samu ka shigo, ban samu na maka murnar ƙarin matsayi ba, Allah ya tayaka riƙo"
Yusuf yace "Ameen nagode"
"sannan ina tayaka murnar rabuwa da mugun aboki wato Abbas"
Cikin mamaki da rashin fahimta yace "kamar yaya?"
"Kamar yadda na gaya maka, Allah ne ya dube ka ya rabaku, a baya nasan koda na faɗa ba zaka yadda ba, yanzunma ban sa ran ka yadda ba amma wataran zaka ce na gaya maka, Allah ya bada sa'a ya tayaka riƙo"
Tayi gaba ta bar Yusuf a gurin yayinda ya bita da kallo.
Da Yusuf ya koma gida yayiwa Umma bayanin tafiyar da zasu yi ya raka Widad, da farko taƙi yadda tace sam bata san zance ba.
Yusuf yace "haba Umma, ya za'ayi nida na ɗau Alƙawarin Yiwa jama'a aiki aikin ya taso kice baza'ayi ba, bayan ke kike cewa inyi gaskiya a aikina? Kina so in bari a cutar da ita ne, ba zan iya jure in ga wani mummunan abu ya sameta ba"
"nifa na kasa gane meke wakana tsakaninka da wannan uwar ɗakin, ka damu da ita dayawa"
"ba wani abu da yake wakana Umman Yusuf, kawai dai mahaifinta na mutuntani ne sosai"
"shikenan Yusuf, Allah ya bada sa'a zanyi kewarka zakayi kwanaki ba tare da Umma ba"
Yusuf yace "nikaina ina tunanin hakan, Amma insha Allah ba abunda ze faru kwana biyar ne kawai tafiyar"
"to Allah ya bada sa'a"
Ya amsa da "Ameen"
Haka nan Umman Yusuf take jin kamar akwai wani abu daze faru dalilin tafiyar nan, sedai ta kasa gane na daɗine ko akasin hakan.
Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, Yusuf ya shirya jakarsa da kayansa da ze dinga sawa da ɗan sauran kayan buƙatarsa a traveling bag.
Yaje gaban Ummansa yace "Umma na fito zan tafi, zan kwana a gidan gobe in Allah ya kaimu da Asuba zamu tafi"
Umma ta riƙo hannun Yusuf tace "ka kula da kanka Yusuf, kai kaɗai ka ragemin, Allah yayi maka Albarka ya sadaka da dukkan Alkhairi, Allah yayi maganin maƙiyanka ya karemin kai.."
Kasa ƙarasawa tayi ta fashe da kuka, gaba ɗaya jikin Yusuf yayi sanyi yace "Umma ko in fasa tafiyar nan?"
Ta girgiza kai da sauri tace "A'a bakomai yi tafiyarka, ban san kayi nesa dani ba shiyasa naji ba daɗi"
Haka sukayi Sallama ya tafi.
A can gidansu Widad da yaje, yaje ya sameta a ɗakinta tana ta aikin kuka, magenta se kewayata take itama tana kuka gwanin ban tausayi.
A sanyaye Yusuf yace "waike abun kuka baya miki wahala, kiyi ta azabtar da rayuwarki, kiyi haƙuri ki dena kuka koma meye yake damun ki Allah yana sane dake"
Sallamar Alhaji Nasir ce ta katse Yusuf daga maganar da yake yi
"Yusuf ka shirya ne?"
"Eh ranka ya daɗe na shirya ni"
"to shikenan ta haɗa nata kayan, bayan la'asar semu tafi can farm house"
Yusuf yace "to shikenan ranka ya daɗe"
Alhaji Nasir yace "daughter ki tashi ki haɗa kayan naki, ya kaiki gidan daddynki Bulama kuyi sallama"
Cikin kuka Widad tace "bazan ƙara zuwa inda yake ba, baya sona yafi san ɗansa"
Alhaji Nasir yace "Allah ya baki haƙuri tashi ki hada kayan, ko inyiwa Halima magana tasa a haɗa miki"
"Ni ba wanda ze haɗamin, zanyi da kaina"
Haka Widad taita daru san ranta, Daddy ya dena mata faɗa lallaɓata yake yanzu.
************************************
"Daddy wai yanzu shikenan an fasa ɗaura mana Auren?"
Bulama yace "Eh, an ɗaga dai akwai buƙatar taga likita, har yanzu bata da lafiya"
"Daddy wane irin likita kuma? Naga dai da hankalinta ba hauka take tuburan ba"
"eh mahaifinta ne yacemin akwai buƙatar a barta ta ɗan huta, dan gaba ɗaya tana nema ta illata kanta, ta damu sosai bata son Auren nan, dan haka ma zata Wuce England ta huta"
"wace irin maganace wannan, an samin rai kuma ace an fasa?"
Mahaifiyar Fahad dake gefe, tunda suka fara magana ba tace komai ba se yanzu tace
"kai Dalla Allah ya rufa maka Asiri kana nema ka tonawa kanka, Allah ya rabaka da Auren mara tarbiyya mahaukaciya"
Fahad yace "Ni gaskiya ina sonta a haka, kuma nasan Anwar ne yaje ya kai gulma ta gurin Alhaji Nasir, shiyasa yace haka, ko yana so ko baya so se anyi auren nan dani mu zuba mu gani"
Bulama na ƙoƙarin dakatar da Fahad, amma yaƙi tsayawa ya fice.
Yana fita ya ɗau mota ya nufi unguwar su Widad, yana zuwa beyi wata wata ba ya nufi boys quarters inda Sashin Anwar yake, Anwar yana zaune yana kallon labarai Fahad ya shigo bako sallama.
Anwar yace "Lafiya zaka shigomin ba sallama?"
"dole ka tambayi lafiya mana, ai ban san haka kake ba, ban san ka iya munafunci ba se yau, saboda rashin son cigabana shine ka shiga ka fita aka ɗaga Aurena da Widad bayan ina can inata shiri"
"kamar yaya kenan? Waye ya gaya maka ni na hana aurenku ko nace a ɗaga?"
"Au kai tunaninka wanine ya gayamin, bayan da bakinka kazo ka faɗamin, kayi Nasara Amma kasani Aure yana nan daram tsakanina da ita kuma se nayi maganinka"
Anwar yace "Yanzu Fahad akan Mace kakemin wannan cin mutuncin? Ina ɗan uwanka kuma abokinka?"
"na maka ɗin, haifata kayi da ba zan maka ba?"
"Ni bam rufe ido maci mutuncinka ba saboda cin amanar abota na amincewa da Auren Yarinyar da nake so, se kaine zakamin?"
Fahad yace "Ai ban ma yi maka komai ba, kuma wallahi ko bangon duniya zata zan bita sena Aure ta"
Anwar ya kashingiɗa a jikin kujera yace "Ashe dai haɗin da'akayi ita za'afi cuta, saboda naka haukan yafi nata fitowa"
"Anwar ni kake cewa mahaukaci?"
Banza Anwar yayi masa be kuma ce masa komai ba
"zakaga ƙarshen rashin mutunci kuwa"
"Ya ƙare akanka" Anwar ya bashi Amsa
A fusace Fahad ya baro part ɗin Anwar yana huci, yana ƙoƙarin shiga motarsa Ramlah ta ƙaraso da sauri tana faɗin haba "Fahad yanzu har kazo gidan nan amma ka tafi ba tare da ka ganni ba"
"Am sorry, zuwan gaggawa ne shiyasa yakike?"
Ramlah tace "gaskiya ban yadda ba, kazo mu shiga ciki"
"A'a Ramlah ina sauri ne, zamu haɗe insha Allah"
Ya shige mota ya bar Ramlah a gurin.
Da Yamma ƙarfe huɗu Yusuf ya shiga gidan, sedai yaga Hajiya Halima na masa wani irin mugun kallo, wanda be gane dalilin hakan ba, ko kulata beba ya wuce part ɗin Widad.
Tana zaune a gefen gado tana shafa jikin magenta, tayi shiru kana kallonta zaka san ɗauke take da damuwa.
Yusuf yace "Ya jiki kuma?"
Wata uwar harara ta aika masa ta ɗauke kanta.
Akwatunan ta data shirya manya guda biyu da ƙarama, abun har mamaki ya bawa Yusuf me zata yi da wannan uban kayan haka oho?
Ya ɗauki trolleys ɗin ɗaya bayan ɗaya ya kaisu Mota.
Alhaji Nasir ya fito cikin shirinsa tsaf, yaje ya fito da Gimbiyar 'yar tasa a falo yana shirin fitowa Hajiya Halima ta tarar da shi tace "Nifa Alhaji ban gane ba? Ina zaka ne haka ba bayani, naga har ana fita da akwatuna"
Alhaji Nasir yace "eh zamu ɗan fita ne, ba zamu kwana a gida ba Lovely zataje Abuja ganin likita daga nan kuma zata wuce UK"
"Amma shine baka gayamin ba se yanzu, sekace kana zaman gaba dani? Ace Widad zata tafi amma baka gayamin ba"
Wata uwar harara Widad ta aikamata dashi haɗe da tsaki tayi waje abunta, Yusuf ma be tsaya a gurin ba yabi bayan Widad a hanyar da zasu fita harabar gidan Amal tace "Allah ya raka taki gona, ma huta na kwana biyu kafin ki dawo, kai kuma ka dawo ka sameni"
Daga Yusuf har Widad ba wanda ya tanka mata sukayi gaba, kamar kullum gaban motar ya buɗe mata ta shiga, shima ya zagaya ya shiga suna jiran fitowar Alhaji Nasir.
Kusan mintuna sha biyar sannan ya fito shima ya shiga motar, Anwar ne ya fito ya ƙaraso da sauri yace "ina zakuje ne haka Daddy?"
Alhaji Nasir yace "zamuje farm house ne, gobe in Allah ya kaimu Yusuf ze raka Lovely zataje ganin likita Abuja, idan ta gama zata koma England ta huta"
Turus Anwar yayi yana kallon su, jiki a sanyaye yace "Shikenan, A dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya"
Ya juya ze koma BQ, da sauri Widad ta buɗe motar ta kira sunansa, ya tsaya ta ƙarasa da sauri inda yake ta kalle shi tace "Anwar lafiya kuwa?"
Anwar ya ƙaƙalo murmushi yace "lafiya ƙalau Widad"
"Amma naga mood ɗinka ya canza"
"zanyi missing ɗinki ne"
Ɗan tsayawa tayi tana kallon sa, jiki a sanyaye tace "Anwar haka kurum naji bana son tafiyar nan, ji nake kamar akwai abunda ze faru a tafiyar nan, dan Allah idan na tafi ka kularmin da Daddy dan Allah ji nake kamar wani abu ze sameshi idan na tafi "
Tai maganar hawaye na bin fuskarta.
Anwar yace "Widad akwai matsala ne?"
Girgiza masa kai tayi tace "ni dai ka riƙemin Amana dan Allah"
"shikenan karki damu, Insha Allah zan kula dashi, zakije ki dawo ki sameshi lafiya"
Ta jinjina masa kai tayi murmushi tace "Nagode Anwar"
Ta juya ta koma mota, shikam Yusuf wani takaici ne ya ƙule shi yadda taje ta tsaya tana magana da Anwar.
Yusuf yaja motar suka nufi gidan gona, tunda ma'aikatan suka ga tare da Alhaji Nasir ne suka dinga tururuwar zuwa kwasar gaisuwa, dan ya daɗe beje gidan gonar ba, nan ya dinga musu fara'a ya zolayi wannan ya zolayi wancan yana musu kyautar kuɗi.
Saleh ne ya shigo harabar gidan ya ƙaraso gaban Alhaji Nasir yana murmushi yace "Barka da sauka Alhajin Allah yaushe rabonka damu a gidan nan, sedai muji labarin kazo gari
"
Alhaji Nasir yace "Abubuwa ne sunyi yawa Saleh ya aikin, ya haƙuri damu?"
Saleh yayi murmushi yace "Yallaɓai ai kuke haƙuri damu"
"to Allah ya ƙara mana haƙuri da juna, zan maka transfer ɗin kuɗi aje ayo order Abinci gaba ɗaya ma'aikatan gidan nan Vip kowa yaci ya ƙoshi"
"Allah ya temakeka Alhaji namu, Allah ya ƙara nisan kwana da Arziki me Amfani"
Alhaji Nasir yace "Ameen Saleh, soja marmari daga nesa"
Saleh yayi murmushi ya fita, yana fita ya samu wani guri ya laɓe ya ɗakko wayarsa ya daddana yasa a kunnensa
"Oga sunzo, kuma da alama a gidan nan zasu kwana gaba ɗaya"
"shikenan kasa mana ido akansu sosai, sannan ka lura da motar da zasu yi tafiyar a cikinta kasa tracker dan karsu tafi kafin su Dage suje"
Saleh yace "shikenan as you wish, amma dan Allah karku saɓa Alƙawari"
"karka damu kai dai kayi abunda muka ce"
Alhaji Nasir ya turawa Seh kuɗi, yayo order Abincin ma'aikatan gidan nan kowa yaci yasha yana walwala, aka kaiwa Alhaji Nasir nasu, Alhaji Nasir ya haɗe nasa da na Yusuf yace suci tare, ba ƙaramin mamaki abun ya bawa Yusuf ba, ace babban mutum kamar Alhaji Nasir yace zeci Abinci kwano ɗaya da ma'aikacin 'yarsa lallai be ɗau duniya da zafi ba.
Widad kam sam bata walwala, Ƙarewa ma ɗaki ta ɗaya ta samu ta shige tayi kwanciyar ta.
Yusuf kam suka zauna da Alhaji Nasir suna ta hira, kamar ɗa da Uba yana bashi labarin tafiye tafiyen da yayi da ƙalubalen kasuwanci da kuma nasarorin daya samu.
Can Alhaji Nasir ya nisa yace
"kaga gidan nan shine gidana na asali, ina jin daɗin unguwar nan amma tun bayan rasuwar mahaifiyar Widad naga bata son zaman gidan, saboda ita na canza gida, nan kuma aka zuba dabbobi a wani ɓangaren saboda tama son dabbobi"
Yusuf yace "Allah sarki, tabbas naga tana matuƙar son dabbobi kam"
Alhaji Nasir yace "Yusuf dan Allah ka ƙara haƙuri da 'yata, na yaba sosai da ƙoƙarin ka Allah ya saka maka da Alkhairi, dan Allah idan ta gama ganin likitan, ranar da zata bar ƙasar nan dan Allah ka tabattar jirgunta