Showing 54001 words to 57000 words out of 135096 words

Chapter 19 - Akidata Book 1 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

755

naje har prison dan in duba shi, amma akace min an fita da shi zuwa babban Asibiti dan be san wake kansa ba, ban kai ga zuwa duba shi ba har sena je naga lawyer na tukuna "

A gigice Sale ya kalle ta yace " ya za'ayi ace yana rashin lafiya, harta kai ga baya gane mutane? Shekaranjiya fa naje duba shi, na sameshii lafiya ƙalau, taya haka zata faru? "

"Nima abunda na gaza ganewa kenan, ace beyi rashin lafiya ba se daya rage 'yan kwanaki a cigaba da shari'a, Babban Albishir ɗin dana zo maka da shi shine, muddin na tabbatar da sa hannun ka, zaka maye gurbinsa ne"

Saleh ya kalleta da sauri, bata bari yace komai ba, ta juya ta tafi. Turus Saleh yayi yana nazarin maganganun Widad.
Tunda Yusuf ya fara aiki da Widad, a kullum se yaga abun mamakin daze kulle masa kai.

Ya kunna motar suna shirin tafiya wayar ta ta ɗau ruri, tana kallon screen ɗin wayar ta ɗan ɓata rai ta tura baki, ɗaga wayar tayi tasa a hansfree  "Hello Daddy"

"lovely fushi kike dani ko?"

"A'a"

"Fushi kike mana, Daddynki yace ya aiko a kira masa ke kince ace bazakiyi zo ba, Baby Why meyasa kike haka?" shiru tayi taƙi cewa komai.

"Yanzu haka munyi waya, ina so kije kiji meze ce miki"

"Daddy nifa yanzu wani gurin zani, Na gaya maka ina cikin damuwa kunƙi saurara ta, sema kawomin wasu abubuwa da bana buƙata yake, na gaya maka akwai matsala amma kunƙi saurara ta"

"Ba shawara nake baki ba, Umarni ne kije gurin Bulama yana son ganin ki"

Tura baki tayi ta ajiye wayar tana haɗe rai, Yusuf be nemi shawarar ta ba ya kaita gidan Bulama, Ranta a ɓace ta buɗe motar ta fita tana tura baki, har tayi gaba ta tsaya ta juya taga Yusuf yana rufe mota
"Malam ni ka hanzarta ba zaman jiranka zan tsaya yiba"

Yusuf ya biyo bayanta, suna shiga katafaren falon suka tarar da Iman, ƙanwar Ramadan, Iman tai murmushi tace  "Ohhh beb, ashe zaki zo yanzu Ramadan ya dawo"

Hannu kawai ta ɗagawa Iman ta nufi matattakalr bene.
Iman tace "Widad, Nurat ta kirani tace min tun ranar da kika bar gurin birthday ɗinta baki ƙara ɗaga wayarta ba, i hope ba saɓani kuka samu ba, dukda nasan halinki dai"

Shiru Widad tayi ta tsaya, saboda yadda abubuwa suka yi mata yawa, sam bata cigaba da bibiyar meyasa meta a gurin birthday ɗin Nurat ba, dan tafi tunanin ko ciwonta ne ya tashi a gurin, shiyasa ta kasa tuna komai, juyawa tayi tana kallon inda Yusuf yake, ya ɗauke kai yaƙi kallon ta.

Still ba tace komai ba ta cigaba da tafiya Yusuf na binta.

A babban falon dake saman benen wanda ya kasance na Bulama anan suka tarar da Bulama shida matarsa.

Yusuf ya gaishe su suka amsa, Widad kam kyam ta tsaya tana ƙare musu kallo, sannan ta nemi guri ta zauna abunta tana hura hanci, wata uwar harara matar Bulama take wa Widad.

Bulama yace "lovely ba gaisuwa?"

Tura baki gaba ta sake yi tana ƙunƙuni, Bulama yayi murmushi yace

"Ikon Allah, ƙiri2 'ya na fushi da babanta, har in tura a kiraki kiƙi zuwa ko? Duk dan nace a miki Aure kike wannan fushin dani haka?"

Cike da tsiwa tace "Eh dan kace ayimin Aure ne, nace maka bana so, bana so, Amma kaƙi ban sani ba ko kaima da wata manufar a ranka, nace a min Visa in koma inda na fito shima kace A'a, ba dole inyi fushi ba"

"Widad meyasa baki da kunya ne? Sam baki da ta ido" cewar matar Bulama.

"Ba dake nake magana ba, ina magana da mijin ki ne karki sake shiga harka ta" Widad tai maganar a fusace

Bulama yayi murmushi yace 
"Ummu Ramadan excuse us please"

A fusace Matar Bulama ta tashi ta bar ɗakin tana mita, Bulama ya kalli Yusuf yace 
"Young man can you excuse us please?"
Yusuf yace  "ok sir" ya juya ze fita

"ba inda zeje, ko mene faɗi a gaban sa"

"wow daughter kin yarda dashi haka yaji abubuwan da suka shafi rayuwar ki? Lallai sauƙi yana samuwa"

"ba wani sauƙi daya samu, ina nan a mahaukaciya ta kamar yadda kuka saba faɗa"

"waya isa yace miki mahaukaciya, ba mahaukaciya bace ke Daughter"

"Eh amma kuke kaini gurin likitocin mahaukata"

Alhaji Bulama yace  "Daughter a bar wannan maganar, magana ce Maman ki tazo min da ita"

"ni uwata ta mutu, an kasheta bani da wata uwa, ta haifi dai wanda ta haifa"

Bulama ya girgiza kai yace  "What ever dai, ta kawomin ƙorafi akan ki, kina fita lokacin da bata sani ba, ki koma bata sani ba, kuma kinsan babu tsaro haka kike yawo ga rayuwar ki a hatsari, kuma tayi koke akan wannan direban naki, bata jin daɗin yadda direban ki yake sintiri a sashenki, gaki budurwa ga ta da manyan yara mata, bekamata ya dinga sintiri kuna keɓewa dashi ba, daughter meyasa ba kya ɗaukarta kamar mahaifiya ne? "

Shiru Widad tayi tana jinjina kai, Yusuf kam gaba ɗaya ji yayi kamar ƙasa ta tsage ya nutse, dan shi kansa baya jin daɗin yadda yake shiga inda Widad take, yana ganin rashin dacewar hakan.

Bulama yace " Daughter baki ce komai ba"

"so nake ka gama tukuna"

"Na gama feedback ɗinki nake jira"

Widad ta gyara zama tace "Ka gaya mata wanda ze iya zama a gidanmu a ƙarƙashin mulkina shikenan, wanda baze iya ba ƙofa a buɗe take ya ƙara gaba, tunda basu da zuciya dole su zauna su cigaba da zama, yadda ba ruwana dasu to sudena samun ido, idan zargin da takemin kenan, to ka gaya mata idan maza nake son kawowa bata isa ta hanani ba, tunda gidan mu ne, sannan ni bani da uwa, Uwata ta bar duniya an kasheta, bazan ƙara yadda da wani ba, ban yadda da kowa ba kuma bazan yarda da wani ba, i start loosing trust on you Bulama, bani da uwa an kashe uwata! Karta ƙara kiran kanta uwata, ni bani da uwa! Bana son kowa ya raɓeni, ban yadda da kowa ba wannan AƘIDATA ce"

Jikin ta ne ya fara rawa, wasu irin hawaye na zuba daga idon ta, da sauri Yusuf ya tashi suna rige rige da Bulama zuwa ga Widad, Numfashi take da ƙyar tana kuka, Yusuf yazo kanta da sauri yace
"Are you ok?" jinjina masa kai tayi
Bulama jiki a sanyaye yace 
"daughter, ban faɗi wannan maganar dan in ɓata miki rai ba, Nayi ne dan in tunasar dake mahimmancin haƙuri, kuma koba komai matar mahaifinki ce sannan.. Ɗagawa Bulama hannu tayi ta miƙe ta nufi waje da sauri.

Bata tsaya ba seda taje mota, gaba ɗaya rayuwar Widad abun tausayi ce, tunda Yusuf yasan ta bata cikakken sati bata zubar da hawaye ba, Amma ina dangin mahaifinta kona mahaifiyar ta? "

A haka ya kaita gida, yana tuƙi kamar baya so, saboda yadda yake jin kukan ta me ban tausayi, kamar yadda ta saba indai sukaje guri suka dawo, kame tazo dashi a motar zata barshi, se Yusuf ya kawo mata.
Dan haka yana parking ta buɗe ta fice, ya ɗakko jakar da Wayar ta ya bita.
Sedai yana shiga Falon ya jiyo sautin kukan Widad cikin gurɓatcciyar hausar ta take faɗa
"danme zaki dinga zuwa kina kai ƙarata, bafa ki haifeni ba, keba uwata ce ba, kin sani meyasa kike shisshigi a al'amura na, idan baki dena min haka ba zan ɗau mataki mafi muni akanki, ki ƙyaleni inji da abunda nake ji, ki ƙyaleni inji da ƙunci da baƙin cikin dana ke ciki tsawon shekaru mana, danme zaki dinga min haka?"

Masifa take sosai kamar zata shaƙe Hajiya Halima, Abun na Widad ya fara wuce gona da iri.

Yusuf yace  "kina hayyacinki kuwa? Meyasa kike haka?, a haife ta haife ki, bekamata kidinga gaya mata wannan maganganun ba"

Ta juyo kan Yusuf cikin faɗa tace "Bana hayyacina, ni mahaukaciya ce, idan baka sani ba yau in gaya maka, bani da hankali har ƙasar waje ake kaini ganin likitan mahaukata, Amma baka san me nakeji a zuciya ta ba, An kashe mamana ban san kowa ba se ita, aka kashe ta ba wanda ya damu dani se Babana da Bulama, kowa kansa ya sani babu wanda ya damu da abunda Widad take ciki, kasan me nake ji a raina idan na tuna lokacin da aka kashe mahaifiyata? Wannan tabin baze bar zuciyata ba, a ƙyaleni inyi rayuwar da naga dama mana, "

Yusuf yayi ƙasa da murya yace
" is alright I feel your pain "

" you don't feel my pain, your mum is still alive but me... Kasa ƙarasawa tayi se sake fashewa da tayi da kuka, ta tafi part ɗinta da sauri, Yusuf kam kasa bin bayan ta yayi wannan karon,  Hajiya Halima kam ƙamewa tayi ta zubawa sarautar Allah ido.

Yusuf ya juya ze fice Hajiya Halima tace  "Ina zaka tsohon munafuki, zuwan ka gidan nan shiya hargitsa komai, da yarinyar nan duk rashin mutuncinta bata fiye magana ba, seda kazo kana hure mata kunne, to idan ma wani ne ya turoka to tabbas zanyi maganin ka, dan da zarar Alhaji ya dawo zansa ya sallameka, matsiyaci banza dana wofi kawai "

" Niba matsiyaci bane, Amma talaka ne me wadatar zuci, sannan kafin kisa a koreni da kaina nayi deciding yin resigning, zan bar aikin nan dan nima abunda yake faruwa ba daɗi yake min ba ko dan tsira da mutuncina, dole in bar aikin nan tunda bana shiga aljanna bane"

Fitowar Amal yai daidai da maganganun Yusuf da yace ze bar aikin, sakin ƙaramin plate ɗin hannun ta tayi, tabi bayan sa da sauri tana kiran sunan sa.

" Idan kika bar ƙofar falon nan da sunan bin bayan sa, zan sallamawa duniya ke in bar masa ke, tunda haka kike so"

Juyowa tayi tana kallon Mummy, ta juya da sauri part ɗinta tana kuka.

************************************

Abbas se juyi yake akan kujera yayi shiru, gaba ɗaya abun alherin da Yusuf ke samu a hannun Widad ya tsaya masa a zuciya, yaji meyasa yasa aka tura Yusuf aikin shi beje ba? Yayi gudun kar yaje a dinga masa wulaƙanci yasa aka tura Yusuf, yanzu gashi kuɗin data bashi Yayi Albashinsa uku, ga gefe ana biyan sa Albashinsa, Sallamar Sakina ce ta dawo da shi hayyacin sa, ya amsa mata sallamar ta kalle shi tace 
"lafiya kuwa Yallaɓai?"
"lafiya ya bata amsa"

Ta ɗan taɓe baki tace 

"dama zuwa nayi in tambaye ka, dan Allah meyasa Yusuf baya zama a office yanzu? Wane irin aiki ne aka bashi haka?"

Abbas dama a ƙule yake yana neman wanda ze gayawa matsalar sa, dan haka ya zayyane mata komai, ciki harda Aibata Yusuf, ba ƙaramin mamaki ne ya kamata ba, ganin duk headquarter nan babu wanda Yusuf yake sakin jiki dashi kamar Abbas, Amma ace Abbas ne da bakin sa yake faɗar wannan mahanga akan Yusuf, lallai ɗan Adam ba abun yarda bane.
A zahiri ta maze tace
"gaskiya kai yakamata ace kana samun wannan sha tara ta Arziki ba shi ba, yanzu kayi duk yadda zakai kasa a maye gurbin sa da kai, a karɓe aikin daga hannun sa, idan kana buƙatar taimakona ma zan maka, kasan mu mata akwai iya makirci"

Abbas ya washe baki yace 
"ƙwarai kuwa, amma fa nagode sosai Sakina"

************************************

Har Yusuf ya kama hanyar gida, kawai ya ɗakko wayarsa ya kira Manager Hotel ɗin nan, ai kuwa wayar ta shiga, Yusuf ya tambaye shi idan yana son ganin sa ya zasu haɗu? Ya gayawa Yusuf inda zasu haɗu a gidan sa, beyi wata wata ba yaje har gidan nasa.

Da ganin manager Hotel ɗinma kaga ɗan duniya, suka gaisa da Yusuf, Yusuf yace  "dama wata buƙata ce ke tafe dani, ina son ka nunamin mutanen da suka kama ɗaki a hotel ɗinku, tun daga farkon wannan watan"

Manager yace  "Kai Malam, ni na zata ma wata harkar cigaba ka kawo, wannan abun da kake tambaya sirri ne bama fitar dashi, manyan mutane ke zuwa Hotel ɗinmu, ba zamuyi exposing ɗinsu ba dan duniya babu yarda"

"ze kasance sirri ne tsakanina da kai, kasa a bani babu wanda ze sani"

"Malam bazan iyaba, ka tashi ka tafi kawai"

"zan baka dubu ɗari biyar, zaka bani akan wannan farashin?"

(Abunda yasa Yusuf baya son nuna shi waye, ma'aikaci ne na sirri, no need asan shi waye)

Murmushi mutumin yayi yace "yanzu naji batu, Amma tsakani da Allah turoka akayi, kokuma ma'aikaci ne kai?"

Girgiza kai Yusuf yayi yace 

"Dani ma'aikaci ne ko sisi bazan baka ba, sedai inyi amfani da ƙarfin aiki na, Matata nake zargi ina so in kamata red handed, kuma kona kamata bazan taɓa sako sunan ku a lamarin ba"

"Shikenan, Amma dan Allah ya zama sirri tsakaninmu"

"in Allah ya yarda babu meji, da gani se kai"

"shikenan muje se a baka"

Yusuf yace  "No bana son yawan zuwa gurin bana son a ganni a gurin, ta Email ɗina nake so ka turamin, zan baka ɗaya bisa huɗu na kuɗin seka turomin zan baka sauran, bana saɓa Alƙawari dan haka kaima karka saɓa"

Haka ya amince da wannan yarjejeniyar.

*********************************

Saleh ne yake kaiwa yana komowa, Alhaji Bukar ya fito ya sa meshi, ya kalle shi ya yatsuna fuska yace  "lafiya?"

A fusace Saleh yace  "dole ka tambaye ni lafiya, me kasa akayiwa ɗan uwana? Ta yaya zanje in ganshi lafiya ƙalau kawai labari ya isheni wai bashi da lafiya"

Alhaji Bukar yace  "dakata! Da ina son ganin bayan ɗan wanka da tun a shekarun baya gudun karya tona min Asiri da tuni ya bar duniya, zaman kotu daza'a koma bani da fargaba sam, inada ƙwararrun lawyoyi da na biya su wanda zasu tsayamin, dan haka ba abunda zesa in yiwa ɗanuwanka wani abu"

"Au haka ma zakece? Wato kai a wanke ka shikuma ya cigaba da zama a prison ko? Ga wannan mahaukaciyar Yarinyar taje ta sameni, tace muddin wani abu ya samu Bala ni zan maye gurbin sa, me kake tunani ne wai? Yarinyar nan tana da kuɗi zata iya aikata duk abunda taso"

Alhaji Bukar ya ɗan daki kafaɗar Saleh yace 

"shiyasa nace kazo mu haɗa kai mu raba ta da dukiyar, mu mallaki gundurin dukiyar da muke ta farauta muga ta tsiya"

Saleh ya make hannun Bukar yace  "Niba dukiyar tace a gabana ba, babu irin kyautatawar da mahaifinta be minba, ni dukiyar sa bata gabana, ni burina a wanke ɗan uwana a fito da shi daga kurkuku tunda bashi da laifi"

Wata uwar dariya Alhaji Bukar ya saki yace  "ubanwa yace maka bashi da laifi? Lallai har yanzu kanka a kwano yake, ka ƙyaleshi ya girbi abunda ya shuka, kazo a haɗa kai a nemi Arziki".

Yana gama maganar ya wuce ya bar Saleh a gurin.

************************************

Yusuf yaita safa da Marwa yana duba wayar sa, ba zato Sega abunda ya nema an turo masa ta Email ɗinsa, message ɗin na shigowa Manager ya kira Yusuf, Yusuf yayi masa godiya sannan ya tura masa sauran kuɗin, wanda kuɗaɗen da Widad take bashi ne, dan wani lokacin idan ta bushi iska se yaga alert.

Yusuf ya tura message ɗin cikin System ɗinsa da sauran wayyoyinsa, nan Yafara aiki akan bayanan da aka turo masa, ba ƙaramin mamaki ne ya kamashi ba ganin mutanen da suka ka kama ɗakuna a wannan watan zuwa ranar da suka je Hotel ɗin tare da Widad, wanda ya kama ɗaki ranar da sukaje shida Widad yafi bashi mamaki, Abun tambayar anan shine 'ya akayi Widad tasan da zuwan mutumin gurin? Me Widad taje yi? Gurinwa taje?' me ta gani ya sata kuka? '
Yusuf zuciyarsa ɗaya baya jin Widad zata aikata wani mummunan aiki na alfasha, amma akwai wani ɓoyayyen abu da yakamata ace ya sani.

Kamar wanda aka mintsina ya miƙe ya shirya, ya duba agogonsa ƙarfe takwas na dare, haka ya fita ya tari abun hawa ya tafi unguwar su Nurat.

Unguwar tasu shiru, amma haske ko ina da yake rukunin Gidajen masu kuɗi ne, har ƙofar gidan aka kaishi aka sauke.
Ya sauka ya nufin gidan su Nurat, ya tsaya suka gaisa da megadin, Yusuf yace  "Dan Allah gurin Nurat nazo"

Maigadin ya kalle shi yace "tasan da zuwanka ne?"

"A'a, bata sani ba, Amma ka gaya mata tayi baƙo"

Mai gadi ya kira Nurat a waya yasa a hansfreee ya gayamata tayi baƙo.

"Babu wanda zan haɗu dashi yau, dan haka ba zanga kowa ba"

Yusuf yace "kace mata Widad ce ta aiko ni"

Aida jin Widad ce tayo aiken Nurat ta rikice, tace "Kaishi guest room, ina zuwa"

Maigadin yayiwa Yusuf jagora, har wani katafaren Falo, Yusuf ya zauna yana jiran fitowarta.
Ko mintuna goma ba'ayi ba se gata ta fito, ta ƙaraso cikin falon da hanzari, sedai tana arba da Yusuf ta rikice ta buɗe baki zata yi ihu ta gudu, Cikin zafin nama Yusuf ya riƙeta tare da toshe mata baki.

"Meye haka kamar kinga wani aljani ko mugu? Kinga fa mutum ne ni"

Fizgewa tayi, ta shiga Ja da baya ta kwaɓe fuska zata yi kuka tace
"Nifa wallahi tun ranar da kuka bar nan, Widad bata ƙara zuwa gidan mu ba"

Gaba ɗaya Nurat ba tafi sa'ar Widad ba, sedai Widad tafi Nurat jiki sannan Izzarta da jin kanta yake sa ka ganta kamar Babba.

Yusuf yace  "Haba Nur, nifa ba wani abu zanyi miki ba kawai tambayoyi zan miki in tafi"

Girgiza kai ta shiga yi tana kiran sunan Daddy a hankali.

"Daddyn yana nan ne?" ya tambaye ta

Ta girgiza masa kai alamar A'a

"to ki nutsu ki zauna, hira za muyi in tafi"

A hankali ta zauna, tana rarraba ido dan a tsorace take da Yusuf, dan ba zata manta randa Yusuf ya shaƙeta ba, har yayi barazanar sace taba.

Yusuf yace "Calm down dear, hira zamuyi kawai in tafi"

Ganin taƙi sakin jikin ta yasa Yusuf ya miƙe ya zaro komai na Aljihunsa, dan ya tabattar mata da babu wani makami a tare dashi.

Ya kalleta yana ɗan nazarin ta sannan yace 
"ko ki tambaye ni ina Widad ko? Tun ranar da ta bar nan baki sake neman ta ba"

"Na kirata bata ɗaga wayata ne, nasan bazata sake yarda dani ba"

"Waye yace miki ba zata sake yarda dake ba? She's very simple and kind, but why do you attempt

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login