Showing 108001 words to 111000 words out of 135096 words
kicin kicin da fuska yace "ga kayan nan na wankesu, sun bushe ma gaba ɗaya"
Tasa hannu ta ciro kayan daga bokiti, taga kayan a haɗe dana Yusuf, kwashe nata tayi ta zube masa nasa a gurin, Yusuf yasa hannu ya kwashe ya zuba a jakarsa.
Ya kalleta yace "kinci Abinci kuwa?"
"ni banci wani Abinci ba, kaga fa abunda aka kawo"
Kwano ta miƙa masa, yasa hannu ya buɗe dafaffiyar masarace a ciki da ɓawonta da komai, Yusuf yace "to me yasa baki ciba?"
"ta ina zanci ? Kawai se in kama cin masara, ni ban taɓa ganin anci masara ba, nidai kawai nasan Abinci akeyi da ita, amma ba'aci"
Yusuf yace "ikon Allah, wannan wace irin hausa ce? Waye ya gaya miki ba'a cin masara"
Ya zauna ya ɓare masarar tsaf, ya ɗaurayeta, yace "nasan kece baki taɓa ciba, amma ana cin masara dafaffiya ko gasashiya, ci kiji"
Ɗauke kai tayi taƙi karɓa, Yusuf kuwa yasa masara a gaba ya fara ci, zuba masa ido tayi tana kallon ikon Allah, yana nufin itama haka zata ɗau masarar ta dinga wannan kokawar haka sekace wata saniya.
Plate ya ɗakko ya shiga ɓanɓarowa yana tara mata a plate yace "gashi na ciro miki ɗauki kici"
Ba kunya tasa hannu ta fara tsinta tana kaiwa bakinta, dan bilhaƙƙi ita bata taɓa ganin ana cin masara a haka ba, amma kuma tabbas da daɗi, ya dinga cirowa yana tara mata tana tsinta tana ci, kamar wata 'yar yaye, cikin ikon Allah a haka kuma ta ƙoshi.
Shiru tayi ta tuna lokacin da sukaje restaurant cin Abinci, Yusuf yake gayamata Naira ɗarin cin Abinci tana gagarar wasu, take ganin kamar ƙarya yake, se gashi yanzu ta gani da idonta, da wanine ya bata labarin ana dafa masara aci a matsayin Abinci zata ce ƙaryane dan bata taɓa gani ba.
Can Yusuf yace "inda ƙwaron ya cijeki ya dena zafin?"
Ta gyaɗa masa kai alamar eh, yace "hannun da'aka harbe ki fa?"
"yayi sauƙi, ina iya motsa hannun sosai, sedai idan ma bige ne nake jin zafin"
Yusuf yace "masha Allah, Allah ya ƙara miki ingantacciyar lafiya"
Shiru tayi kamar ba taji ba, Yusuf yace "Addu'ar ma bakya so?"
Shiru tayi masa tana sake ƙarewa roofing ɗin ɗakin kallo, tana son gane dame akayi shi.
Yusuf yace "me kike kallone?"
Widad tace "kai subhanallah, wallahi ka dameni da surutu haba, sekace waccan matar me haƙora"
Yusuf yace "to shikenan na dena gimbiyata"
Ɗagowa tayi ta masa wani irin kallo, ba shiri ya miƙe yayi waje ya bar mata ɗakin yana murmushi.
Wasa2 Ramlah ta ganewa shaye2, bata salla se wajen ƙarfe takwas na safe, da ta idar zata ɗakko Coca-Cola tasha, seta kai ƙarfe biyun rana tana bacci.
Yanzuma Amal ce ta shiga ɗakin Ramlah, ta tarar da ita tana girgiza jarkar Coca-Cola.
Amal tace "Ramlah, wai me yake damunki ne haka? Wane irin coc ne kike sha ba yau ba gobe ga shegen bacci kamae kin haɗiyi kasa"
Ramlah ta kalleta tace "kina da matsala da hakanne?"
"ba wai batun ina da matsala da hakan bane, sedai cewa kina ganganci da rayuwar ki, baccin da kike ya wuce ƙa'ida, kuma wannan coc da kike sha yayi yawa sosai, nifa na fara zargin wani abu kike sha a cikin coc ɗin nan"
"Ke Amal! Ki kiyayeni, dalla wuce ki barmin ɗaki, ina ruwanki dani idanma wani abun nake sha?"
Amal tace "shawara ce nake baki, amma
" wallahi Amal in baki barmin ɗaki ba sena miki rashin mutunci, Dalla ƙara gaba kije kiji da kanki"
Amal tace "shikenan Kije ki ƙarata" ta fito daga ɗakin.
Yanzu kusan kullum se Ramlah ta fita, ko tare da Fahad ko ita kaɗai, kuma Hajiya Halima bata taɓa yi mata magana akan hakan ba.
Anwar kam ya tattara yasa musu ido, ya maida hankali akan kula da Alhaji Nasir, kwata kwata ya dena shiga sabgarsu ma.
Abubuwa suka fara cakuɗewa su Alhaji Musa, suka kuma hayar wasu 'yan ta' addan domin a nemo musu su Me Adda, yayin da Alhaji Haruna ya keta tunani akan maganar da Saleh ya gaya masa game da tserewar Su Yusuf.
Meeting suke akai akai akan yadda zasu ɓullowa al'amarin,
Alhaji Munir yace "tabbas idan har yaran nan suka kuɓuta suka dawo Asirinmu ze iya tonuwa"
Alhaji Musa yace "yakamata ku kwantar da hankalinku, babu yadda za'ayi Asirinmu ya tonu, yanzu naga Likitan nan yana aikin da muka sashi, dan yanzu baya gane waye akansa sam"
Alhaji Haruna yace "hakane Daula ya zama abun tausayi, talakawan da yake fafutuka akansu, an hana kowa zuwa inda yake, manyan ƙasar nan ma kowa yayi watsi da lamarinsa, yanzu haka nasa Jam'ian tsaro su hana kowa shiga inda yake, se ɗan matar nan tasa, shi kuma wannan soko ne, ba abunda yake ganewa, shekaranjiya wasu baƙin turawa sunzo duba shi, amma an hana su ganinsa ance yana ƙarƙashin kulawar likita baza'a ganshi ba"
Alhaji Musa yace "Good hakanma yayi, a hana kowa zuwa inda yake muyi yadda muke so, Amma Nifa har yanzu ina mamaki akan guduwar yaran nan, kuma da suka kuɓuta aida zasu dawo a gari a gansu, amma har yanzu babu wanda yaji ɗuriyarsu"
Alhaji Munir yace "ni kaina abunda yake ɗauremin kai kenan, zuwa yanzu ai yaci ace anji labarin sun dawo, amma babu wanda yaji hakan"
Alhaji Musa yace "shiyasa nake tunanin akwai wata a ƙasa ruwa baya tsami banza, akwai munafiki a cikin mu"
Alhaji Haruna yace "kamarya? Kana nufin a tsakaninmu munafikin yake kokuwa?"
Alhaji Munir yace "kunga ya isa haka, nima nayi zargin haka amma babu lallai da munafuki a tsakaninmu, sedai a wanda suke mana aiki tabbas, kokuma akwai wani a gefe daya ke farautar abunda muke nema"
Alhj Haruna yace "ba abunda baze iya faruwa ba, Amma kar mu ɗora komai akan zargi semun tabattar"
Kamar yadda Saleh ya bada umarni, aka ginawa Widad nata banɗakin, akwai wata ƙatuwar rijiya a gidan ruwan sam bashi da kyau, haka nan ake amfani dashi a gidan, ko kuma mutum yayi tafiyayyiya yaje rafi ya Ɗebo.
Yusuf kuwa tafiya yake me nisa, yaje ya ɗebo ruwa a wannan borehole guda ɗaya tal ta garin, yazo gida ya tafasa idan ya huce seya zuba a randarsu suke amfani da shi a matsayin na sha.
Har yanzu Widad bata saba da kowa a gidan ba, ba ruwanta dasu sedai in sun haɗu a tsakar gida suka mata sannu ta amsa, amma bata shiga sabgar Hari sam, saboda Hari baƙar magana take gaya mata.
Yanzu ma tana tsugune tana brush da yamma, yaran Hari suka kewaye Widad suna kallonta, mussman dogon gashinta dake ɗaukar ido, gata ba ma'abociyar saka kallabi ba, abun haushi hadda 'yan matan gidan da suka tasa, se kallonta suke ita ta rasa se yaushe zasu saba da ganinta su dena mata wannan kallon haka?.
Widad tace "kai me kuke kallone, haba bana son kallon nan da kuke min, did i look like a beast?"
Hari tace "yo sunga abunda basu saba gani ba, kin fito tiɓitiɓi da wasu irin kaya ai dole su kalleki ni wallahi da ban zaci ma musulma ce ke kina jin hausa ba"
Widad tace "eh ba musulma bace ni, gunki nake bautawa yana ɗaki idan kina so ki ganshi"
Sam hari bata zaci Widad tana da baki hadda baƙar magana ba.
Gwaggo tace "Amarya ƙyaleta kiyi haƙuri"
Sannan ta kalli Hari tace "haba Hari, kin fiye magana wallahi duk haƙurin yarinyar nan kinsa ta fara tanka miki"
Hari tace "yo Yaya yara sunga abunda basu saba gani ba ba dole su kalla ba"
Yusuf yana ta tunanin wace sana'ar ze ɗan fara, saboda ya saukewa mutan gidan ɗawainiyar da'ake dasu, ga Widad bakomai take ciba duk ta rame, ya dawo daga sallar Azahar ya tarar an kawowa Widad gujjiya, tanaci hadda ɓawon, Yusuf yace "mekike ci ne?"
Ta ɗan taɓe baki tace "na manta sunanshi, amma inaga wake ne wannan maman ce ta bani"
Yusuf ya kwashe da dariya, ta haɗe rai tana kallonsa, yace "haba Madam, wannan ne waken? Kuma da ɓawo kike ci bari kiga"
Ya zauna yana ɓarewa yana bata, ita tunda take bata san wata gujjiya ba, da taci a baki se taji kamar wake, ta zata ma wake ne yazo a haka.
Tun Yusuf yana mamakin bata san abubuwa da yawa ba, har ya dena mussman duba da yanayin rayuwarta, ita ba sakewa take da mutane ba, kuma mafi yawa a waje tayi rayuwarta, dan haka yake mata uzuri a wasu abubuwan.
Yusuf yace "Ina son in fara zuwa kasuwar garin nan, inga me zan fara siyarwa saboda mu ragewa mutanen gidan nan ɗawainiyar da suke damu"
"dama akwai kasuwa a dajin nan?"
"daji kuma?"
"Eh mana" ta bashi amsa
Yusuf yace "eh akwai kasuwa amma se anyi tafiya me nisa sosai, nayi magana da megari ya haɗani da yaronsa tare zamuje kasuwar gobe in Allah ya kaimu inga yanayin abubuwan"
Tace "Shikenan" tana ci gaba da cin gujjiyarta, seda ta gama ta kalle shi tace "Wanka"
Yusuf yace "to" ya haɗa mata ruwa sannan ya fita sallar la'asar
A gurin salla Yusuf yaga abun mamaki, akwai ƙaramin gurin da suke jam'in salla, akwai ƙarancin ilimi ga mutan ƙauyen, liman ya makara wani yaja salla a raka'ar ƙarshe liman yazo, raka'ar ƙarshe kawai ya samu, itama an ɗago daga ruku'u, da'aka idar Yusuf yana jira yaga liman ya tashi ya kawo wadda be samu ba amma yaga liman yayi ƙyam yaja gefe yana laziminsa.
Yusuf ya dinga kallonsa ko ze tashi ya canza sallane, amma yaga aka jima liman ya shafa addu'a ya miƙe ya gaisa da mutane ya ƙara gaba.
Yusuf yayi shiru a ransa yace "wannan mutumin dabe san hukuncin salla ba, shine kuma yake jan salla? Tabbas akwai matsala babba, mutanen garin nan suna buƙatar ilimin Addini, ya barwa ransa cewa zeyi wa megari magana, yaga ta inda ze iya basu gudunmuwa.
Ya shiga cikin gida ya shiga ɗakinsu da sallama, Widad ta fito daga wankan tana shafa mai, ba tare da ta kalle shi ba ta amsa ƙasa ƙasa, ta cigaba da abunda take.
Kusa da ita yaje ya zauna yana kallonta, duk cikin salon son yasa ta kula shi, dan idan har bashi yayi mata magana ba in zasu kwana idan ba wani abu take buƙata ba, ba zata kula shi ba.
Tana jin yadda ya zauna daf da ita ya ƙureta da ido, kamar tasan maganar yake so tayi, taƙi magana.
Cike da fargaba dan yasan ze sha masifa, amma ya maze ya kai hannunsa gashin kanta yace
"wannan gashin yaushe rabonsa da a taje shi? Insha Allah idan na fara zuwa kasuwa indai naga comb zan siyo, in taje shi da kaina"
Bige hannunsa tayi tace "wai kai meye haka? Me yasa kake son taɓani ne? Na gaya maka bana son karka ƙara taɓani na gaya maka, in ba haka ba duk abunda nayi maka kai ka siya, haba sekace baka da zuciya, ko baka gane magana"
Shiru yayi kawai yana kallonta yadda take ta masa masifa, shi yaga tana magana ma se yaji daɗi a ransa, dan yaga ta rage yawan kukan da take yi.
Ga mamakinta murmushi yayi maimakon taga yaji haushi.
"kawo man in tayaki shafawa" yai maganar yana ɗaukar robar man, ƙwacewa tayi tace
"bana so na gama"
Yusuf yace"Shikenan bari in baki guri kisa kaya"
"inma baka bani gurin ba baze hanani sa kayana ba"
Yayi murmushi ya miƙe cike da jin daɗin yasa ta magana, bayansa tabi kallo yana fita ta ajiye abunda ke hannunta ta shiga goge hawayen da ita kaɗai tasan dalilinsu.
Doctor Sufyan yana Office ɗinsa, yana jiran lokaci yayi ze shiga tiyata, wayarsa yaji ta fara ringin, ya tsaya ya ɗaga tareda yin sallama.
"Sufyan ne?"
"Eh nine"
"ina son ka kasa kunne ka saurareni dakyau, dukda nasan baka san dawa kake magana ba, hakan ya faru ne sakamakon sanin wanda kake maganar dashi a gurinka bashi da amfani, ina son ka saurareni da kyau kaji abunda zan gaya maka, kana jina ko?"
Sufyan yace "ina jinka"
"kamar yadda aka baka kwangilar sake kwantar da Daula, aka baka miliyoyin kuɗi akan karya warke, kuma kayi dan tuni wani percentage ya shiga hannunka, to nima aiki nake son kayi min, niba kwantar da Daula nake so kayi ba, kawar da Daula nake son kayi!!!"
Miƙewa doctor Sufyan yayi tsaye ya shiga waige waige karya je wani yaji abunda ake faɗa masa a waya, cikin rawar murya yace "amm.. Ban gane me kake fada ba fa"
"ƙarya ka keyi ka gane, kuma kaji me nace tunda ka iya karɓar kuɗi kake bashi wrong treatment, to zaka iya karɓar kuɗi ka kasheshi, likita ne kai babu me zarginka, tunda kowa yasan condition ɗinsa yayi worse, bazance ga abunda zan bi yaka ba, sedai da kanka nakeso ka yanke abunda zan bi yaka "
Wani wahallalen gumine ya dinga ratsowa Sufyan, gumi yake ji har tsakanin cinyoyinsa, yace " Amma kisan Alhaji Daula hatsari ne, dole se anyi bincike akan gawar sa, don a tabattar da abunda ya kashe shi, idan aka ganoni fa, ina da iyali da ƙananan yara nasan kasheni za'ayi, Daula babban Attajiri ne"
"meye marabar abunda kake masa yanzu da wanda nace kayi masa, sanin kanka ne wrong treatment ɗinma ze iya kasheshi, baka da damar cewa ba zakayi ba, saboda na maka tarko ta ko'ina, ina da duk yadda akayi ka karɓi kuɗi kake bashi wrong treatment, duk wata hujja daza'a kamaka ina dashi, idan kuma naga dama zan saka ɗauke ɗaya daga
'ya' yan naka ko kayi ko kuma ransa ya salwanta, zaɓi ya rage naka, sannan idan kaga dama ka gayawa wani"
Ƙit aka katse kiran, gaba ɗaya doctor Sufyan yaji kamar an zare masa laka, jikinsa se rawa yake ya duba wayarsa yaga anyi hiding ɗin lambar, dan ko unknown number be fito ba, duk sanyin Ac dake office ɗin shi gumi yake, kamar wanda ya tuƙa tuwon gidan biki a tsakae rana.
Yau da wuri Yusuf ya shirya, dan zebi ɗan megari kasuwa, ɗan megarin shima matashi ne be kai Yusuf ba, a bayan gidan megari nasa gidan yake, da matarsa da 'ya' yansa shida.
Har Yusuf ya gama shirinsa, aka kawo musu Abincin safe Widad bacci take, a hankali ya ƙarasa gaban katifarta ya janye bargon jikinta, bacci take hankalinta kwance, se yarintarta ta sake fitowa ta ƙara kyau a idon Yusuf, yayi shiru yana kallonta.
A hankali ya ɗan daki pillow ɗin da take kai, amma bata motsa ba, ya sake taɓa pillow amma still bata motsa ba, hannu yasa ya ɗan daddaki nata hannun, kamar me tashin ƙaramin yaro, juyi tayi amma taƙi buɗe ido.
"Widad" karo na farko a rayuwarta data ji ya kira sunanta, taji zuciyar ta ta buga da ƙarfi, ta buɗe ido ta kalle shi
Yace "ga breakfast an kawo karya huce, kuma inason zan fita ni"
"shine zaka wani durƙuso kaina haka? Kamar zaka shige cikina"
"ke komai nayi miki lefi ne? To sorry tashi karya huce kinji gimbiyar..
Kallonsa take taji meze ƙarasa, maimakon ya ƙarasa se yayi murmushi yace "tashi kije kiyi brush, muci Abinci "
Ta miƙe ta ɗau brush tayi waje, Yusuf ya gyara mata shimfiɗa, ya gyara ɗakin.
Widad ta fita tsakar gida, gwaggo tace "Amarya ina kwana"
Widad tace "lafiya ƙalau"
Gwaggo tace "Alhamdilillah ya ƙarfin jiki?"
"Naji sauƙi"
Gwaggo tace "to madalla"
Hari ta ƙurowa Widad ido tana so tayi magana, Widad tace
"idan baki dena kallona ba, sena saka butar hannuna na ɓallo miki wannan haƙorin da yake leƙowa idan kina magana"
Hari tace "ke hudas kike ko wudas, yau dai ban kulaki ba balle ace na shiga harkarki"
Widad ta Harareta ta wuce banɗakinta.
Data fito ta manta da batun Yusuf dake jiranta, ta tsaya gurin da take leƙen zomaye.
Seda tayi me isarta, sannan ta koma ɗaki.
seda taga Yusuf sannan ta tuna ashe ita yake jira suci Abinci, yace "naga kin daɗe?"
Kai tsaye tace "kallon zomaye nayi" , ta ajiye kayan brush ɗinta, tazo ta zauna ta buɗe kwanon farko, dakakken ƙuli ƙuli ne a ciki, ta rufe ta buɗe ɗayan dafaffen dankalin hausa ne a ciki da ɓawonsa da komai manya guda uku.
Ta kalli Yusuf tace "meye wannan?"
"Dankali" ya bata amsa
"kuma a haka? Ta yaya za'aci"
Yusuf yace "ga mahaɗin nan ƙuliƙuli a wannan kwanon"
Widad tace "ta yaya za'aci wannan abun ba tea?"
Yusuf yace "seki kora da ruwa" yai maganar tare da fara ɓare dankalin.
ta zuba masa ido, ya ɓare tsaf ya yayyanka shi a kwano, ya ɗebo ruwa ya ajiye mata yace "bismillah"
Tsayawa tayi tana kallonsa kamar wata sokuwa, ya ɗakko ɗaya ya dangwala da ƙuli ƙuli ya kai bakinta, ɗauke kanta tayi tasa hannu ta karɓa tasa a bakinta.
Ba zata ce babu daɗi ba, sedai gurin haɗiyewa ne daƙyar take yi, dan kasa haɗiyewa tayi seda ta haɗa da ruwa.
Dan haka shima ba taci dayawa ba tace ita bazata iya cin wannan abun ba, shaƙe mata wuya yake.
Yusuf ne yaci sauran, sannan yayi mata sallama ya tafi.
Sufyan abun duniya ya dameshi, ya rasa inda ze saka ransa, ba ƙaramin hatsari bane kashe shahararren mutum kamar Daula, amma kowa se saka rayuwarsa yake a hatsari saboda suna taƙamar suna da kuɗi, shiba abun ya kaisu gurin 'yan sanda ba, shi ze kwana a ciki.
Gaba ɗaya daren nan yakasa bacci, sedai juyi dafa da Asuba aka kuma sake kiransa, bashi da zaɓin daya wuce ya amsa wayar.
"baka da isasheshen lokacin ɓatawa gurin aiwatar sa wannan aikin, kana da yau zuwa gobe in Allah ya kaimu ne kawai, idan baka yi ba ni zan aikata maka abunda nace"
Aka katse layin, Doctor Sufyan yayi jifa da wayar ya dafe kai, matarsa ta lura da yana cikin damuwa ta tambaye shi ko lafiya, yace mata babu komai.
Widad bata taɓa shiga damuwa ba, tsawon lokacin data ɗauka tana rayuwar kaɗaici a rayuwarta se wannan karon, tunda Yusuf ya fita be dawo ba taji gaba ɗaya duniyar ta mata faɗi, gashi ita bata saba da kowa ba se shi, seta ji ta wani iri kamar ita kaɗaice a duniyar, koba komai ganin motsinsa yana rage mata damuwa.
Yau wuni guda tana ɗaki, ba