Showing 114001 words to 117000 words out of 135096 words
ace mamanki bahaushiya mahaifinki wani yaren, ko mahaifinki bahaushe mamanki wata yaren"
Widad ta ɗanyi jim sannan ta murmusa tace "dukkansu Hausawa ne, mazauna Kano"
Hindu tace "kano, dan Allah a kano kike?"
Widad tace "kin taɓa zuwa ne?"
"Ni waze kaini kano? Muna dai jin labarin kano, ance garin yana da kyau sosai, kuma mutanen kano suna da kirki"
Widad tace "Insha Allah wataran zaki kano, ba laifi kam kano tana da kyau, nikam ya sunanki ne"
Hindu tace "sunana Hindu"
Widad tace "Masha Allah, Hindatu"
Gwaggo ce ta fito hannunta ɗauke da ƙwarya da rariya tace "Amarya yau hira ake haka? Badan da kaina naga kina surutu ba, da zance bake bace"
Widad tace "Wallahi gwaggo bani da surutu, amma ina magana sosai ai"
Hanne kuwa dake bakin rijiya tana wanke wanke ko kulasu ba tayi ba.
Itakuwa Hari fitowa tayi da gero, ta zuba a turmi ta fara daka tana habaice habaicenta, basu kulata ba suka cigaba da hira.
Gwaggo tace "Ai Amarya mutum rahama ne, ko yaya idan kina ɗan fitowa ana hira zaki rage kaɗaici, amma ace ke mijinki kawai kika sani"
Widad tace "Mama kenan, to ai shikaɗai ɗin kawai na sani, kawo in tayaki tankaɗawa"
Gwaggo tace "A'a kar in takura miki"
Widad tace "ni baki takuramin ba"
Ta ɗaga kai ta kalli Hari tace "dan Allah malama kiyi ɗaya, ko dakan kokuma waƙe waƙen haba dan Allah, da wanne za muji ƙarar daka ko kuma na wannan hayaniyar da kike yi"
Hari tace "Allah ya haɗani da Baƙar Jaraba ni Hari jikar Hama, na kulaki ne ko tsabar jan bala'i ne? Wallahi ki fita a sabgata, tun kafin in miki wulaƙanci"
Widad ta sunkuyar da kai tana dariya, dama abunda take so kenan, ta zungurota taita masifa, dan ita yanzu ta maida Hari comedy.
Widad ta karɓi tankaɗe kamar abun Arziki, ta riƙe rariyar da hannu ɗaya, ta ɗaga hannun sama tana girgiza rariyar, garin kuwa se kama gabansa yake, dan haka iska ta dinga kwashe shi, gwaggo kuma takasa yi mata magana saboda kawaici.
Yusuf ne yayi sallama hannunsa ɗauke da ledar viva, hango Widad yayi tayi buɗu buɗu a cikin gari, gashi a ƙarƙashin bishiya take tankaɗen, iska duk ta kwashe garin.
Hanne na ganinsa ta wani fara mutsu mutsu da gyare2, tace "sannu da zuwa" Yusuf be kula da ita ba
Da sauri ya ƙarasa inda Widad take yace 'Subhanallah Widad waye ya saki wannan aikin "
Gwaggo tace "seda nace base tayi ba, tace in bata tayi"
Yusuf yace "wa yace ki bata, Mama bata iya bafa, kalli yadda tayi miki Asarar gari"
Murmushi gwaggo tayi, ta ɗauke kai daga kallonsu.
Widad tace "Na iya, ba gashi inayi ba, kai komai nayi seka gwalemin"
Yusuf yace "Ni na isa kiyi abu in gwale, amma kalli yadda kika ɓata gurin"
"Ni dai ka ƙyaleni in cigaba da aikina"
Yace "Naji, amma kawo in nuna miki yadda akeyi"
"A'a ni naga yadda akeyi ai, shine nima nake gwadawa"
Gwaggo kam gaba ɗaya kunya suka bata, dan haka ta miƙe ta bar musu gurin gaba ɗaya.
Yusuf yayi ƙasa da murya yace "dan Allah kiyi haƙuri ki kawo, wallahi baki iya ba kawaici kawai tayi miki, amma wannan aika aika kike mata"
Sakar masa rariyar tayi, ya shiga gwada mata yadda ake yi, kawai ta kwashe da dariya, ya kalle ta yace "lafiya kuwa?"
"A'a gani nayi ka iya sosai"
Ba ƙaramin kyau tayi ba dariyar da tayi, karon farko da tayi fara'a haka sosai ya gani.
Kawai ya shagala da kallonta, ya ɗanyi murmushi ya cigaba da nuna mata yadda akeyi.
Hanne kuwa ji tayi ta tsani Widad gaba ɗaya, ko ganinta bata son yi ganin Yadda Yusuf ke wani ƙure Widad da ido se taji kamar tayi kuka.
Megari ne yayi sallama ya shigo, yace "Malam Yusuf ka dawo kenan?"
Yusuf yace "eh Baba na dawo" Megari yana jin daɗin yadda Yusuf yake girmamashi
Yace "ya kasuwar kuwa?"
Yusuf yace "Alhamdilillah, naje harna dawo"
Megari yace "to masha Allah"
Widad kam ko kallon Megari ba tayi ba, balle tace masa wani abu, Megari ya ƙaraso inda take yace "wannan 'ya tawa akwai miskilanci, tunda ba zata kula baban nata ba, toga tsaraba na kawo mata, Allah ya ƙara ƙarfin jiki"
Ya ajiye mata dabino rabin kwano a gabanta, Yusuf yace "Mungode sosai Baba, Allah yasaka da alkhairi"
Megari yace "A' a bakomai Yusufa, Allah ne ya haɗa mu zama tare, kuma naji harga Allah kun kwantamin, Allah yayi muku Albarka"
Yusuf yace "Ameen"
Yusuf ya ɗau ledae daya shigo da ita, da wadda Megari ya bawa Widad, ya shige gaba Widad na binsa a baya, gwaggo tace
"Amarya karɓi kayan hannun nasa mana"
Widad tace "Ai ze iya ɗauka, ni yamin nauyi"
Gwaggo ta jinjinawa gaɓunta irinta Widad, akwai buƙatar a zaunar da ita ayi mata takara akan zama da miji.
Suna shiga ɗaki Yusuf yace "yanzu uwaɗakina abaki abu amma ki kasa cewa kin gode, baze ji daɗi ba fa"
Maimakon tayi magana, sema sosa kai data hauyi tana wasa da gashin kanta ta wuce inda katifarta take, Yusuf ya bita da ido, wato se yanzu yake ganin tsabar yarintar Widad, wato a da ɗinma tsabar izzarta da jin kaine yake sa ka ganta kamar wata babba amma kwanan nan wautar da Widad keyi wasu lokutan, suke ƙara fito da yarintar ta, sedai har yanzu wannan izzar da jin kan basu barta ba.
Yusuf yace yakamata kidinga gaida Megari, kinga yana mana ƙoƙari shima kinji gimbiyata.
Aikuwa nan da nan ta haɗa rai , Yusuf yace "meye kuma na haɗe ran?"
"Ai kafini sanin abunda ka faɗa, kuma kasan bana so"
Hindu ce tayi sallama a ɗakin nasu Yusuf ya amsa, ta shigo da kwano ta durƙusa ta gaida Yusuf, Yusuf ya amsa mata, tace "Amarya gashi inji Gwaggo"
Widad tace "to Nagode"
Hindu ta juya ta fita, Widad ta buɗe kaanon tace "yau kuma meye wannan?"
Yusuf ya karɓa ya duba yace "kwaɗon rama ne"
Ta kalle shi tace "meke nan?"
Yusuf yace "kici kiji mana"
Tashi tayi taje ta wanke hannu tazo ta zauna, ta ɗiba takai bakinta, yatsine fuska tayi tana taunawa da ƙyar, kamar tayi kuka tace
"Wai su mutanen nan basa girka abunda akeci ne?"
Yusuf kamar ya tintsire da dariya yace "wannan me ake dashi in ba ciba"
"to naji tsami, ga gishiri da kamar sugar"
Yusuf yace "kyaji dashi, nidai bari inje inyi salla" ya miƙe ya fita.
Abu kamar wasa, sa 'yan sanda suka tashi suka kama Anwar da Doctor Sufyan, wai za' ayi bincike a kansu akan ɓatan Alhaji Nasir Daula, aka kama wasu daga ma'aikatan Asibitin sannan aka rufe Asibitin. Tun ana ɓoye ɓoye har abu ya fara bayyana cewar wai Alhaji Nasir Daula ya ɓata a Asibiti.
Hankalin Hajiya Halima ya tashi, jin an kama mata ɗa an kai shi police station, gidan Bulama ta shirya ta tafi bagazan bagazan ta ɗau mota ta fice.
Tana fita Isa yace "Matsiyaciyar mata, da yake ɗanta aka kama kalli yadda ta fita afujajan, amma mijinta na kwance a Asibiti ko a jikinta, ni ɗanne ma yake bani tausayi da nace Allah yasa baza'a sake shi ba"
Murtalah yace "ai Matsiyaciya ɗaya kenan, kalli yadda ta saida fiye da rabin motocin gidan nan, kalli Yadda tabi ta rage mana albashi dan Azzaluma ce, Allah sarki Yusuf da uwaɗakinsa, ko a wane hali suke oho?"
Nura yace "Ai wallahi se yanzu nake ganin ranar yarinyar nan, duk wulaƙancinta haƙƙinmu baya ciwo koda megida baya nan, ubangiji Allah ya bayyana Alhaji Daula"
Isa yace "Ameen dai abubuwa se faruwa suke kamar almara wai anemi mutum a gadon Asibiti a rasa, Allah ya kyauta"
Suka haɗa baki sukace "Ameen"
Yusuf ya dawo daga salla, yaga kwanon rama a rufe, yace "kaddai baki ci ba"?
Dabinonta take ci tace "ni bazan iya cin wannan Abunba"
Yana duba kwanon yaga ta tattare ƙuli ƙulin, da tumatir da Albasar da gurjin dake kai ta cinye abunta, ta bar gayan ramar duk ta lashe ƙulin jiki.
Murmushi yayi bece komai ba, ya ci ramar nan a haka, se jikinta yayi sanyi taga bata kyauta ba.
"Gimbiyata, ga wake nan na siyo mana a kasuwa yau da yamma za'a kawo kayan tea harda bredi"
Da sauri ta kalle shi tace "dan Allah dagaske hadda bredi?"
"ya zan miki ƙarya, inje ki hukunta ni, dagaske nake"
"Yau zanci bredi"
Yusuf yace "hadda shayi makuwa, bari inje in watsa ruwa na gaji sosai"
Widad tace "to, ba zaka ci dabinon ba?"
"bari in wanka tukuna"
Ya tashi ya ɗau bokiti ya fita, seda taga ta kassara dabinon nan, ta masa cin ƙoshi sannan ta ajiyewa Yusuf sauran.
Ta miƙe ta tattare ƙwallyen ta tafi taje ta zubar, gwaggo na ganin Widad tace "Amarya zo kinji yarinyar kirki"
Widad ta ƙarasa inda take, gwaggo tace "Amarya, daga yanzu idan mijinki ya dawo in yazo da kaya duk abunda kike ki tashi ki karɓi kayan hannunsa kinji?"
Widad a ranta tace 'wai nan duk zatonsu wani Auren kirki mukayi?'
A fili tace "To Mama zan dinga yi, amma gaskiya banda kaya me nauyi"
Gwaggo tayi murmushi tace "dama bance dame nauyi ba, amma ki dinga kula dashi sosai, ko so kike yayi miki amarya?"
Widad dariya kawai tayi tace "Mama kenan, to in yayi meye a ciki, nidai fatana mu koma gida"
Gwaggo tace "hakane amma yakamata kidinga nuna kishi akansa, zeji daɗi ko Auren dolene kukayi?"
Ganin kamar Widad bata son zancen ne, yasa Widad tace "jeki abunki ɗiyata"
Widad ta juya ta tafi ɗaki, tana zuwa ta tarar Yusuf ya fito daga wankan, yana tsaye da gajeren wando a jikinsa yana goge ruwan wankan jikinsa, wasu irin dogayen gashi ne a jikin Yusuf, taga yayi mata wani irin girma da kwarjini.
A ɗan gigice tace "Yoseef meye haka?"
Da sauri ya waigo ya kalleta yace "meyafaru?"
"meyasa zaka shigomin ɗaki a haka? Kalleka fa tsirara"
Yusuf ya kalli kansa yace "Niba tsirara nake ba"
"to meye haka, naga a can banɗakin kake sa kayanka"
Yusuf yace "Ramawa nakeyi, Allah ya bani haƙuri in dai a haka tsirara nake, toke ban san a ya kike yawo ba"
Tsaki tayi ta shige can lungun ɗaki, ta juya masa baya ya juyo ya kalleta, yayi murmushi ya gama tsane jikinsa, ya zura riga, ya ɗakko man shafawa yazo kusa da ita yace
"dan Allah ki tayani shafawa a bayana mana"
"Allah ya kiyaye, ni ka tashi daga kusa dani" ƙememe taƙi kallonsa.
Yusuf yace "kalli kiga"
Rintse ido ta sake yi tace "ni bazan Kalleka ba, seka sa kaya wallahi ko inyi ihu da ƙarfi"
"Aina saka kayan"
A hankali ta buɗe idonta tana kallonsa, Wani irin kallo yake mata, wanda ta kasa gane ma'anar kallon da yake mata.
Zamewa yayi ya kwanta akan cinyarta, yace "Wash na gaji bayana ciwo yake kamar zan ɓalle"
Itadai kamar Yusuf ya ɗaureta yau, ta kasa magana sam balle ta motsa, hannunta ya kama yana ta murzawa a hankali, har bacci ya ɗaukeshi.
Har yanzu hannunsa yana cikin nata, Ƙura masa ido Widad tayi, gaba ɗaya Yusuf tausayi yake bata mussman idan ta tuna beji ba be gani ba tsautsayi ya ritsa dashi, se wahala yake faman sha, kuma be taɓa nuna mata ya gaza ba.
Riƙe hannunsa ta sake yi, ta toshe bakinta tana kuka, hawayen tausayinsu ya kamata.
Yusuf da bacci ya ɗauke shi, ya buɗe idonsa jin saukar hawayenta a fuskarsa, a gigice ya miƙe zaune yace "subhanallah meyafaru? Nine me nayi miki"?
Bata iya bashi amsa ba se kuka data cigaba dayi, Yusuf yace
"yi haƙuri na ɗagaki, tunda bakyaso bazan sake kwanciya a jikinki ba, yi haƙuri"
Ta lura baya son yaga tana kuka, dan haka ta basar dan karya gane acikin damuwa take yasa tace "Kuma idan muka koma gida sena gayawa Daddy taɓani ka dingayi"
Yusuf yace "Yi haƙuri bazan sake ba, goge hawayenki bazan sake ba insha Allah, bari in sauka ma daga kan katifar"
"A'a ka kwanta anan, amma idan ka sake taɓani se nayi kuka, kuma Daddy zan gayawa idan muka koma gida"
"To shikenan naji"
Ya kwanta ya juya mata baya, murmushi ta dingayi ta miƙe ta tsallake shi tayi waje.
Alhaji Munir yace "Impossible, ta yaya Alhaji Nasir ze ɓata a gadon Asibiti, sekace ɓatan rigar sawa"
Alhaji Haruna yace "Abun da mamaki, a yadda yake dai be isa ya gudu da ƙafafunsa ba akwai wata a ƙasa"
Alhaji Munir yace "tabbas akwai lauje cikin naɗi, inma dai akwai wanda yake gefe yake mana manaƙisa, amma kowaye idan muka tono shi abun baze masa da daɗi ba"
Babu ko sallama Hajiya Halima ta shiga Falon Hajiya Sarah, a fusace ta kalli Sarah tace "ina megidan nan yake?"
Hajiya Sarah tace "lafiya kuwa, maman Anwar?"
"bani da lokacin baki wannan amsar, kije ki gaya masa ina son ganinsa"
Bulama yace "Ai gani nan ina kusa"
Hajiya Halima ta kalleshi tace "da sanin ka aka kama min ɗana?"
Bulama yace "haka labari yazomin an kama shi"
"to ba labari bane ba, an kama min ɗana, to wallahi baze yuwu ba, daga abun Arziki seya koma na tsiya, daga yayi jinyarsa an sace shi a Asibiti se'a kamamin yaro akanme?"
Bulama yace "yanzu sace mijin naki be dameki ba?"
"Dalla karka gayamin maganar banza ko ka rainamin hankali mana, kai sace shin damunka yayi?"
"Yaya za'a sacemin Aminina ɗan uwana, sannan kizo kina tayarmin da hankali akan an kama ɗanki? Ki bar doka tayi aikinta, in sunga bashi da laifi zasu sake shi"
"dokar banza dokar wofi, ni zaka gayawa doka, doka nawa kayi amfani da kuɗi kayi fatali da ita a ƙasar nan? Ina son kayi Amfani da wannan damar taka da ikon kayi fatali da wannan dokar kasa a sakarmin ɗana, in bahaka ba you know what am capable of doing"
Godiya me tarin yawa Fans ina godiya 😍 😍 😍 😍 😍 😍
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1
Page 38_39
Shi kansa Saleh abun ya ɗaure masa kai, ta yaya za'a je har Asibiti a sace mara lafiya, kuma bayan da jam'ian tsaro a cikin Asibitin da suke tsaron lafiyarsa, koda yake ba abun mamaki bane a haɗa baki dasu a sace shin, saboda da yawa mutanen yanzu suna iya yin komai saboda kuɗi.
Maman Nurat ce ta shigo ɗakinta, ta tarar da Nurat tana kan system tana danne danne, ta ɗago ta kalli Mahaifiyarta tace "Mummy lafiya kuwa?"
Mummy tace "Mhmm, wani labari naji"
Nurat tace "labarin me?"
"wai an nemi Alhaji Daula an rasa a Asibiti, yanzu haka an kama Shugaban Asibitin doctor Sufyan da kuma Anwar"
Zare farin glashin idonta Nurat tayi tace "What are serious Mum?"
"did I ever lie to you?"
Cikin kaɗuwa Nurat ta girgiza kai tace "Na shiga uku da wannan masifa, daga wannan se wannan ana ƙoƙarin a kashe wannan amma se waccan ta faru, an sace masa 'ya har yanzu ba wanda yasan inda suke, yana kwance yana fama da jinya an bishi gadon Asibiti an sace shi, innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Mummy me Anwar yayi aka kama shi to? "
Mummy tace " ina zan sani, ance dai har dashi a cikin suspect "
Nurat tace" idan harda sa hannun Yaya Anwar a ɓatan baban Widad, to tabbas beyi hakan dan cutar dashi ba, akwai dalili yakamata in ganshi "
Zare ido Mummy tayi tace " kiga wa? Ba dani ba Wallahi idan kika sake kika fita duk abunda yayi miki ke kika siya, na gaya miki babu ruwanki ki koma gefe ki taya su da Addu'a yafi "
Shiru Nurat tayi bata kuma cewa komai ba, Mummy ta gama mitarta ta tashi ta fita, ita kuwa Nurat ta shiga tunanin yadda zata yi ta fita.
Yanzu duk lokacin da aka idar da sallar Asuba, se Yusuf ya tsaya sunyi karatu a masallaci, aikuwa gasu da son karatun babu girman kai a lamarin su, dan haka yake jin daɗin koyar dasu, kuma ya basu damar yi masa tambayoyi, wasu tambayoyin idan kajisu sam bazaka ce musulmi ne ba, saboda tsagwaron Jahilci, Yusuf baya kyararsu ko hantararsu, haka yake amsa musu.
Akwai wanda yake tambayar Yusuf bayan an watse daga gurin karatun, wai shi ya zata in mutum ya kwanta da iyalinsa ba'a wanka se ranar Juma'a, Yusuf yayi masa bayani dalla dalla, kuma ya ƙudurce babu batun kunya, shine maudu'in daze musu gobe in Allah ya kai rai a gurin karatu "
Ya koma gida ya tarar da hakimar tanata kwasar baccinta, ya nemi guri shima ya ɗan kwanta, nannauyan bacci ne ya ɗauke shi, can cikin baccin nasa ya jiyo ihun Widad a tsakar gida, aikuwa a gigice ya tashi ya fita, wata kazar harice Widad tazo wucewa ta zata 'ya' yanta zata taɓa mata, dan haka ta fara bin Widad tana kai baki zata cije ta, shine take ta wannan ihun tana zagaye, ita kuma kazar na cigaba da binta.
Hari na kallonta, ta dinga tintsira dariya, a gigice Yusuf ya fito, yazo da sauri ya kori kazar ya kalli Widad yace "haba my queen, gaskiya kin ban kunya kaza ce fa kawai "
Widad tace "to ba cizona take son tayi ba, kuma wlh idan ta sake bina sena kamata na tura ta a cikin wutar can ta ƙone kowa ya huta"
Hari tace "kan bala'i, kazar tawa zaki saka a murhu? Aikuwa dana miki rashin mutunci kuma wallahi da sekin biyani"
Yusuf yace "yi haƙuri bama iyawa zata yi ba, tana faɗane kawai yanzun ma tanawa kazar ihu, ta ina zata iya kamawa balle tasa a murhu?"
Widad tai farat tace "to sena buga mata wannan icen ta mutu, ko in Takata da ƙafata harta mutu, garama kija mata kunne"
"Kazar zan jawa kunne ko kuma wa?"
"Eh ita kazar"
"ta yaya zanjawa kaza kunne? Ko nima