Showing 78001 words to 81000 words out of 135096 words
da tuni tayi maganinsa ta ɗau mataki akansa.
A hankali ya furta "Ubangiji Allah ka shiga lamarina, Allah yasa har in kammala aikin nan yarinyar nan ba zata ganoni ba"
*****************************
"Amma ni tabbas ba'ayimin Adalci a wannan lamarin ba, nida ɗan uwana ku kusan halaka shi sannan ace bazan ganshi ba, wannan wane irin zalunci ne"
"zaka iya kiransa da duka abunda kaga dama, amma tabbas ba zaka ganshi ba, zamu ci gaba da ajiye shi a ɓoyayyen guri har se sakamakon binciken nan yazo hannun mu"
Saleh yace "binciken nan bani na yake yi ba, kun san hukumar da sukeyi meze sa ku cigaba da azabtar min da ɗan uwa"
"saboda shi kaɗai ne hujjar daze fallasa komai a kotu, kuma yana nan shirin tona mana Asiri dan haka gara muyi maganinsa"
Cike da damuwa Saleh yace "to ai wanda yake ƙoƙarin samo min sakamakon anyi masa transfer ya kuke so inyi, ni ko ganinsa inyi shikenan"
Alhaji Musa yace "baja da wannan damar Saleh, kayi abunda muka ce kawai"
A fusace Saleh ya miƙe ya bar gurin zuciyarsa na masa zugi, tabbas su Alhaji Musa masifa ne a rayuwarsa da ɗan uwansa.
Anwar a cikin ɓacin rai yaje ya samu Fahad a gida, Fahad na ganinsa yace "Ohh God, Anwar ai namanta gaba ɗaya jiya zaka dawo am so sorry brother"
Jiki a sanyaye Anwar ya kalli Fahad yace "Am disappointed Fahad, dole kace ka manta jiya zan dawo, yanzu Fahad yarinyar dana daɗe ina mafarkin aura ita zaka aura?"
Ajiyar zuciya Fahad yayi yace "am sorry, nima bani nace ina son ta ba cusa min ita akayi akace sena Aureta dan anga tana da taɓun hankali"
"Fahad, Widad ba irin matan da za'a cusawa mutum bane, sannan idan har cusa maka ita akayi saboda taɓin hankali, ni ka barmin ita in aura tunda ni ina son ta"
"nice maka akayi bana sonta? Ko kuma so kake in kalli mahaifina ince zan bijirewa umarninsa"
Anwar yace "ni bahaka nake nufi ba amma nasani ka sani Baka dace da Widad ba, nasan halinka gaba da baya"
"kasan halina amma ka barni nake soyayya da ƙanwarka? Ko abun naka son zuciya ne?"
"son zuciya be wuce wanda ake shirin yiwa Widad ba, Ramla tasan dai dai tasan abunda take yi dan haka idan ta zaɓeka a matsayin miji ita taso hakan, Amma Widad fa Yarinya ce sannan...
"kaga Anwar ya isheni haka" Fahad yai maganar a tsawace
"Idan har ba so kake abotarmu ta samu matsala ba ka ƙyaleni, ka fita daga batun Auren nan"
"Idan kuma naƙifa?"
"Komai ze iya faruwa"
Anwar yace "to sonake koman ya fary Fahad, naga baka gane rarrashi zan ɓullo maka ta inda ya dace"
Fahad yace "Anwar karka kuskura kaje ka faɗi wani mummunan abu a kaina a gurin mahaifin Widad"
"Fahad dani da kai a ƙarƙashin kulawarsa mukayi karatu, ba abunda be mana na gata a rayuwa ba, bana jin Widad kanta ta moreshi kamar yadda muka moreshi, idan har aka lulluɓe kura da fatar Akuya ba muyiwa Alhaji Nasir Adalci ba, kaima kasan baka dace sa Auren 'yarsa ba"
"Amma Anwar kasan taimakawa zan in Aureta tunda mahaukaciya ce?"
"kabar taimakon naka mana, kaje ka auri Ramlah"
"Amma Anwar meyasa kake fifita Bare akan ƙanwarka? Idan har dagaske kake Ramla yakamata kace bazan Aura ba"
"Fahad ba goyon bayan bare nake ba, goyon bayan gaskiya nake kuma kaima ka sani"
Yana gama maganar ya fice a fusace cikin sauri.
**********************************
Ɓangarren Nurat kam lamarin mahaifinta yana bata mamaki, gaba ɗaya babu wanda ya gane inda yasa gaba daga ita har mahaifiyarta, ga ta'amali da wasu irin ƙarti da yakeyi wanda daka gansu zaka san ba mutanen kirki bane, suyita musu zirga zirga a gida, babu me ikon cewa uffan saboda duk tsoronsa suke ji.
Gefe guda kam tunanin Abokinta ya cika mata zuciya, zuciyar ta na matuƙar begen ta ganshi amma abu ya gagara, tasan ko giyar wake tasha bata isa taje gidansu Widad ba, tunda ta dena ɗaga wayarta tasan akwai wata a ƙasa haɗuwarta sa Widad ze iya haifar mata da matsala ne kawai.
Ba zata iya ƙirga adadin saƙonni da kuma kiran da tayiwa Yusuf ba, gefe guda kuma dai zuciyar ta na kwaɗai mata son sanin me mahaifinta ke ƙullawa wanda yasa shi yin mu'amala da wannan mutanen haka, suke ta musu sintiri a gida.
************************************
Anwar ne ya shiga ɗakin Alhaji Nasir da Sallama, cikin sakin fuska ya amsa masa, sedai mahaifiyarsa tana tare da Alhaji Nasir ɗin a wannan lokacin, fuskarsa ta nuna yana cikin damuwa kuma yana son yin magana ne.
Alhaji Nasir yace "shigo mana Anwar"
Anwar ya ƙarasa ya zauna a ƙasan carfet yana sunkuyar da kai, can yace
"Daddy, naji ka yanke wani hukunci, wai dagaske nan da ƙarshen wata zaka aurar da Widad?"
"eh hakane Anwar, halin ƙanwar taka ne se ita, gashi har yanzu ciwon ta yakan tashi, bekamata ace mamanku ta cigaba da ɗawainiya da ita ba, akwai buƙatar itama tayi Aure tunda ta girma"
"Amma Daddy kayi bincike akan wanda zaka bawan kuwa?"
Alhaji Nasir yace "bafa wani ne ba, Fahad ne ba wai wani guri aka samo mata mijin ba, Fahad ne Abokin ka ɗan gidan Bulama"
Irin mugun kallon da mahaifiyarsa ke jifansa dashi ne yasa ya kasa cewa komai yace "shikenan Daddy, Allah ya Sanya alkhairi ya kaimu lokacin"
Ya tashi gwiwa a saɓule yana kallon mahaifiyarsa ya bar ɗakina.
Alhaji Nasir yace "Halima kaman akwai abunda yake damun Anwar amma ya kasa faɗa"
"ba abunda yake damunsa, naga dai kamar ya ɗan damu ne da batun Auren Widad"
"ko dai yana sonta ne?"
Da sauri tace "A'a kasan halinsa dai da tausayi, da yana son ta ai da tuntuni ya faɗa"
"hakane, aikam da ban bawa Fahad ba da Anwar zan bawa, dukda gaba ɗayansu 'ya' yana ne, amma wata kusan ai tafi wata"
"hakane kam, Allah ya wuce mana gaba"
Bayan ta sallami Alhaji Nasir, ta fito ta tafi ɗakin Anwar, yana zaune a bakin gado ya dafe kai yana tunani, jin motsin shigowarta ne yasa shi ɗagowa ya kalleta, Hajiya Halima tace
"kaga Anwar zuwa nayi in sake yi maka kashedi, wallahi tun wuri ka fita daga harkar Auren nan, wai ƙanwar uwarkace ita kota ubanka? Ka shiga hankalin ka na gaya maka"
Fahad yace "Allah ya baki haƙuri, Insha Allah zan kiyaye, amma dai Fahad be dace da Aurenta ba"
"da anyi magana ka iya bada haƙuri ai, ko waze aurawa ina ruwanka, shi ya haifeta ba in ya ga dama yaje ya aurawa kare ita mana ina ruwan wani?"
"Amma Mummy ya zakiyi da Ramla da take mutuwar son Fahad?"
"Ai magana ta ƙare tunda Fahad ze auri mahaukaciya, Allah ya bata wanda ya fishi seta haƙura"
"Amma ba kya tunanin yadda take son shi hakan ya haifar da matsala?"
"Kai rufemin baki, Allah ya tsaremu da matsala ina sake jan kunnenka ka fita daga sabgar yarinyar nan, in kuma kaƙi ji baka ƙi gani ba"
Anwar ya bita da kallo yayin da ta bar ɗakin, ya girgiza kai tare da sauke ajiyar zuciya.
Yusuf yana zaune a mota yana ɗan danna wayarsa yana jiran fitowar Widad, be san ta taho ba kawai yaji ta buɗe motar, da sauri ya ɗago ya kalleta, wato abun nata kullum ƙara gaba yake, yau shigar tata tafi ta kullum muni, kamar yadda ta saba gaban mota ta shiga garin zama seda jikinsu ya gogi juna, amma kowannensu ya basar.
Shiru Yusuf yayi bece komai ba, ta ɗakko wayarta ta miƙa masa, ya karɓa ya duba, kwatancen idan zasuje ne ya sake duba agogon hannunsa ƙarfe tara daidai na dare, zuba mata idanun yayi yayinda itakuma take kallon wani gurin.
Ba zato yaji ta fizge wayarta daga hannunsa tace
"malam bana son kallo"
"Aikuwa kallo kin gamu dashi muddin da wannan shigar zaki fita" ya bata amsa
"shikenan cigaba da kallona karka fasa, wallahi kasa na makara zuwa inda zanje se nayi mummunan ɓata maka rai"
Ta faɗa in a very serious tone, haka yaja motar suka fita, gaba ɗaya jikinsa babu ƙwari yake tuƙin.
Yusuf be tsinke al'amarin ba seda yaga sun iso wani katafaren Club a cikin sabon garin Kano, kallon Widad yake yaga me zata yi ganin yadda zaratan karuwai da 'yan iska ke shiga suna fita a gurin.
Yunƙurawa tayi da nufin buɗe ƙofar taji yasa lock, ta kalle shi tace "buɗeni zan fita"
"kije ina?"
"inda ka aikeni" ta faɗa cikin fushi
Gyara zama yayi ya ɗauke kansa daga kallon ta.
"magana fa nake maka"
"idan har na bari kika shiga wannan gurin a haka, ba yiwa kaina adalci ba kuma Allah ze kamani da laifin cin Amana"
"Dalla ka rufemin baki, ina ruwanka da nine? Ina ruwanka da rayuwata na gaya maka kadenamin shishshigi fa bana so, ina kunyar Daddy ne ba dan haka ba da tuni na daɗe da karta maka rashin mutunci"
Kashingiɗa Yusuf yayi yace "kin daɗe baki yi ba, rashin mutunci wanne ne bakimin ba, ba wanda ban gani ba, dan haka duk wanda kika yi zan shanye amma ba zaki shiga gurin nan ba"
A cikin matuƙar hasala tace "ka buɗemin ƙofa Malam, nima karuwanci nazo yi gurin nan ka ƙyaleni inyi rayuwar da naga dama"
"Aikuwa da ajinki ya zube beb, duk yadda kike yanƙwana gayu kizo nan kiyi karuwanci ba class, ki canza guri mana"
Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyarta, wai ita Widad yau direbanta yake yanƙwanawa yana raina mata hankali yadda yake so, hakan be taɓa faruwa ba a tarihin rayuwar ta
"Naji ajin nawa ya zube, malam ka buɗen ƙofa nace"
Ramawa Yusuf yayi kamar yadda takewa mutane, yayi kamar baya jin me take faɗa.
Jikinta har rawa yake saboda masifa tana zazzagawa Yusuf faɗa, a zafafe ta miƙa hannu zata yi unlocking ɗin motar Yusuf ya riƙeta, a tare suka ji wata irin faɗuwar gaba, Jikin Yusuf har rawa yake dan besan yadda akayi ya riƙeta ba, yayin da nata ƙirjin ya dinga bugawa fiye dana Yusuf.
Tattaro Jarumtarsa yayi ya maida ita seat ɗinta, ya saka mata seat belt yaja motar ya bar gurin.
Widad zata iya cewa tunda take bata taɓa haɗuwa da mutumin daya raina mata hankali kamar Yusuf ba, dukda yana matuƙar yi mata biyayya tabbas yau ya tsallake iyakarsa, da yasan me tazo yi a Club ɗin da be mata haka ba, dole ta nuna masa munin kuskuren daya aikata yau, bata kuma ce masa uffan ba.
Ta naji tana ganin ya maida ita gida, zuciyarta na cigaba da tafasa kamar ta tsaga ƙirjinta.
Seda suka koma gida sannan yayi parking, ya fito ya buɗe mata ƙofar motar, ta fito ta tsaya ta saka idonta a nasa tace
"ban taɓa sanin baka da hankali ba se yau, kana tunanin na manta da contract ɗin daka sawa hannu? Harka samu damae da zaka nunamin ban isaba, saboda jahilci da rashin tunani irin na talaka, kasan me na jeyi gurin? Har zaka nunamin isa da Izza, ina ruwanka dani meyasa kake son zaƙewa cikin al'amuran rayuwa ta?, ko dan ina ɗaga maka ƙafa shiyasa kake ƙoƙarin takani, yau zan nuna maka ka saɓamin doka kuma dole ka karɓi hukuncin abunda kayi, banza mara amfani ka lalata min komai saboda Jahilci da son nuna kai wani ne, kamin hauka da wauta ka wargazamin komai saboda ƙaramin tunaninka, Amfaninka shine kamin aiki in biyaka amma ka zaƙe, dan haka zan nuna maka kai ba wata tsiyar bane a gurina kuma ka tsallake gona da iri "
Shiru Yusuf tayi seda ta gama sannan ya kakmeta yace " da bani da amfani da Allah be halicceni ba, babu wata halitta da Allah yayi wadda bata da amfani, tunda bani da Amfani zan ƙyaleki ki amfani kanki, tabbas da Allah yayi kowa me kuɗi da babu wanda zeji daɗi, kuma babu wanda ze mori wani, talaka yana da amfani, muma ba laifi mukayi wa Allah yayi mu a ƙarƙashin ku ba"
Yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko key ɗin motar, ya kamo hannunta yace "bani da Amfani, dan haka ki nemo me Amfani ya cigaba da yi miki aiki, idan harni ɗan halak ne bazan ƙara miki aiki ba, ga mukullayenki nan talaka mutum ne kuma yana da zuciya tunda iyayene suka haifemu kamar yadda aka haifeki"
. Ya ɗanƙa mata key ɗinta a hannu, jifa tayi da mukullayen tace "baka isa ba, wallahi yadda kasa hannu a takardar yarjejeniyar ka fara aikin seka kammala shi, se anje ƙarshe da kai"
"sedai ki nemo me Amfani yayi miki amma bani ba"
cikin gida da sauri, hakan yayi daidai da shigowar motar Anwar.
Tana zuwa ɗaki tayi jifa da kayan hannunta ta shiga sintiri hawaye na bin idonta tace "shikenan babu wanda ze fahimci halin da nake ciki? Wannan banzan ya ɓata min shirina ya wargaza komai, me yake tunani ne? Har na bashi damar daze shiga rayuwata haka ya yanke min hukunci, yanzu ina hukunta shi kuma Daddy ni ze ɗorawa laifi"
Anwar ne ya shigo da sauri ɗakin yace "Widad lafiya kuwa? Meke faruwane?"
Girgiza masa kai tayi tace "bakomai"
"a'a ya bakomai naga kamar kuna cacar baki da direbanki, kuma gashi kina kuka meyafaru"
Shiru tayi masa ta wuce kan gadonta tayi zamanta.
Kusa da ita yaje ya zauna yace "dawowata naga abubuwa daban daban wanda suka bani mamakiba gidan nan, wanda ban gane kansu ba, gashi Daddy yace wai Aure ze miki, meyasa zaki Auri Fahad"
Kallon Anwar tayi amma taƙi cewa komai.
"Say something please"
Lumshe ido tayi taƙi magana, duk yadda Anwar yayi taƙi magana haka ya ƙyaleta ya bar ɗakin jiki ba ƙwari.
Yusuf kam har ya koma gida zuciyarsa na tafasa, wai shine mara Amfani a tarihin rayuwarsa babu irin kalar cin zarafin da ba'ayi masa ba ya jure, Amma yau na Widad yaji zafinsu sosai.
Haka ya ƙarasa gida, Umma ta lura tunda ya dawo baya walwala sosai dan haka tace "tilo meke faruwane? Naga kamar ranka a ɓace yake"
"bakomai Umma"
"bana son fulatanci fa, ko kana da wanda zaka gayawa damuwar ka bayan ni?"
Girgiza kai yayi yace "Umma na rasa abunyi gaba ɗaya, Anyiwa Abbas transfer, yarinyar da nake wa aiki mun samu matsala na ajiye aikin, gashi ban sanar da shugabanni na ba kafin in yanke hukuncin, kuma ba aikin direba kawai nake mata ba kare lafiyar ta nake, ba ƙaramin hatsari take ciki ba ga mahaifinta wai Aurar da ita zeyi, Umma abubuwan dayawa nama rasa me zanyi "
"Allah sarki Jarumin ɗana, tun tasaowarka da jarumta na sanka da juriya meze sa ka karaya a wannan lokacin? Ni kaina ina jin tausayinka amma kasa Allah a lamarin ka sannan kayi haƙuri da komai, ɗaukaka bata zuwa ana kwance ba zato Aka ƙara maka matsayi a gurin aiki, jajircewarka ce tasa suka baka, dan haka ka zama Jarumi Yusufa, nan gaba iyali zaka riƙe kaga zama da mata se kayi haƙuri se Jarumin gaske, lokuta da dama bama gane Amfanin mutum se bayan ya matsa daga kusa damu"
Kallon Ummansa yayi yace "wani irin iyali kuma?"
"kayi Aure mana kaima ka hayayyafa, nima inga jikokin tilon ɗana"
Girgiza mata kai yayi yace "na yanke ƙauna Umma, kiyi haƙuri mu ƙarasa rayuwar mu a haka, nima na isheki"
"haba Yusuf, me rai ai baya yanke ƙauna daga rahamar ubangiji, dole kayi Aure wataran"
"Umma bana son tarihi ya maimaita kansa, bana son abunda ze sake ɗaga mana hankali, dan haka mu bar wannan maganar seda safe"
Ya miƙe yana tafiya a hankali ya bar ɗakin, Umman Yusuf ta dafe kai tace "Allah ka kawo mafita da sauyi na alkhairi ga rayuwar wannan bawa naka, Allah ka kawo masa mafita ka yaye masa damuwarsa"
Yusuf ya kashe wayoyinsa gaba ɗaya, baya fita ko'ina kullum yana gida, Dama bashi da wasu abokai a unguwar, dan haka baya zuwa ko ina.
Umma bata takura masa ba ta ƙyaleshi.
Widad kam tun daga ranar ko falo ta dena fitowa, Daddy kam dama ba shiga harkarta yake ba, se bayan tafiyar Yusuf ta gane Amfaninsa ta ɓangarori daban daban, gashi taga dagaske Yusuf ya dena zuwa gidan kwata kwata.
Haka nan Alhaji Nasir yaji ya damu da son ganin 'yar tasa dan ba ƙaramin missing ɗinta yake ba, yanzun ma ya danne zuciyarsa ne kawai dan ya samu ta saduda amma abun ba sauyi.
Part ɗinta ya tafi domin ya ganta, sedai yana zuwa bedroom ɗinta ya tarar ta rurrufe ko'ina, da sauri ya ƙarasa ya tura ƙofar ɗakin nata, ɗakin duhu ta kashe fitulun ɗakin, kunna fitilar ɗakin yayi haske ya gauraye ko ina, yana kunna fitila ta saka ihu ta shige cikin bargo.
Da sauri Daddy ya ƙarasa yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Babyna nine fa Daddy ne ɗago ki ganni"
Dunƙulewa ta sake yi tana karkarwa, a hankali ya ƙarasa ya ɗagota sedai taƙi yadda su haɗa ido.
Daddy ya girgiza kai yace "ciwon ne ya dawo again? Kalli Yadda kika rame lovely, subhanallah meke damunki ne haka?"
Ba tace komai ba sedai kwantar da kanta da tayi a jikin Daddyn nata, jikinta kamar ana girgizata.
Yusuf ya ɗakko tsohon layinsa yasa a waya, sedai yana sakawa yaga saƙonnin Nurat na shigowa, messages ɗin ya shiga dubawa ɗaya bayan ɗaya sedai yana cikin dubawar kiran Nurat ya shigo wayar, kamar kar ya ɗaga amma ya ɗaga yace
"Assalamu Alaikum"
Wata nannauyar ajiyar zuciya Nurat tayi tace "Aboki anya duniya da gaskiya, ka manta dani ko?"
"haba ƙawata, ya zan manta dake light, wayata ce ta lalace shiyasa"
"Allah sarki, duk hankalina ya tashi na zata wani abun ne ya same ka"
"ba abunda ya sameni light fatan kina lafiya"
"Lafiya ƙalau, amma ina son ganinka ne Aboki"
"me zaki bani in kin ganni?"
"magana nake so muyi"
"muyi ta a waya mana light, abubuwa sunmin yawa sosai"
Ajiyar zuciya tayi tace "zefi kyau dai in ganka, mahaifina ne naga yana harka da wasu irin mutane wanda da ganinsu kaga marasa kirki, ga yawan zuwa gidanmu dasu Alhaji Musa suke yi, kace idan naji wani abu wanda zesa a cutar da Widad in gaya maka, amma dai ban san meke faruwa ba"
Gaban Yusuf ne ya faɗi cikin sauri yace "a ina zamu haɗune Nurat?"
"nace ina son ganinka kace ba lokaci, amma da yake nayi maganar Widad shine kace zaka zo"
"yi haƙuri Light"
Nurat tace "sedai kazo gidanmu, babana yana gari baze yuwu mu haɗu ba"
"shikenan insha Allah, zan san yadda zanyi mu haɗu"
"Aboki baka gayamin