Showing 375001 words to 378000 words out of 382522 words

Chapter 126 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2988

ta tsaya iya haka, karmu sake jayayya a kanta”.
Shiru kowa ya kasa motsi, domin wannan rikici yazama na manya, hakanne ya saka papi mik'ewa ya sallami kowa, ya rage daga shi sai mai martaba da Abie a d'akin taron.


***********

Na fito wanka na iske Galadima zaune a bakin gado hannunsa dafe da kai, da sasaarfa na k'araso dan nasan akwai matsala kenan, musamman da acikin y'an watannin nan sau biyu ciwonsa na tashi, duk da akowane bayan watanni uku sai munje India ganin likita shida Abdurraheem, dayake yanzu hankalinsa yana nan Nigeria akan Company da suketa k'ok'arin ginawa, zuwa India saiya zame masa sai time to time kokuma wani gagarumin Abu ya taso daya zama tilas saiyaje.
Laimar ruwa da yaji a jikinsa ya sashi d'agowa da hanzari ya kalleni, kafin nace wani Abu sai kawai ya rungumeni tsam a jikinsa, sai kace zai maidani cikine, kusan mintuna 3 muna a haka, sai sauke tagwayen ajiyar zuciya yakeyi, nikam ina shafa gadon bayansa a hankali.
Nutsuwar daya samu ta sakashi d'ago muka zubama juna ido, murmushi mai kashe zuciya namasa ina shafa sajensa, cikin sanyin murya nace, “Waye ya ta6amin Barden gagara badau ne?”.
Lips d'insa ya ciza yana rik'e hannuna, cikeda damuwa yace, “Munaya sosuke kawai sudawo da abinda ya wuce”.
Nace, “Mikenan?”.
Ya sauke nannauyan numfashi ya zamewa ya kwanta, kansa bisa cinyata muna kallon juna yacigaba da fad'in, “Akan mulki mana, tun sanda Abie ya dawo na fuskanci Abba nason maida masa mulki, amma mama Fulani na hanashi, sannan a gefe mahaifiyar su Matawalle tana nata k'ulle-k'ulle, dama kwanaki mun fara maganar ni da Momma da Abie, saboda rikicin dake Neman 6arkewa tsakanin mama Fulani da mai martaba, a lokacin bansan kuma miya dakushe lamarinba, sai yau da rana tsakarnan mai martaba yace zai maidama Abie sarauta, wannan shine mak'asudun zaman gaggawar, kinsan kuwa wannan kujerar itace ke hana kowacce masarautar zaman lafiya da hargitse-hargitse, harta kai ga asarar rayuka, shiyyasa da Sarki yafara ciwo burin kowa ya mutu hattada y'ay'ansa da matarsa mai manyan y'ay'a saboda burin y'ay'anta su gaji mulki? Wlhy ina cikin tashin hankali, hankalinmu ya kwanta kowa yasamu nutsuwa a masarautar nan gawani bala'innan zasu 6alloma mutane, inaga kawai zamu tattara mu koma India harsu Abie da zaran anyi bikin Sauban. Da aunty mimi”.
“Ina bayanka wlhy my king, wannan itace babbar mafita kawai, domin cigaba da samun zaman lafiya mai d'orewa, hukuncin daka yanke yayi sosai”.
Ya lumshe idanu da shafo fuskata saboda jin dad'in goyon bayan dana bashi, domin k'ara masa nutsuwa saina d'ora bakina akan nashi nashiga masa wani salo mai cikeda kwarewa fiyeda yanda ya koya min, tamkar jira yake ya birkicemin, kafin kicemi labari ya canja salo, saigani da sake sabon wanka babu shiri.🤭

Tun daga ranar bamu sake jin maganarba daga bakin manya, sai munafunce-munafunce da sukaita wanzuwa, bakuma mujiba daga bakin Abie ko papi, dan aranarma ya koma inda ya fito, wannan dalilin Galadima ya samu yafara shirin komawarmu India da Zarar an kammala bikin Sauban daya rage sati biyu kacal.
Ana saura kwana biyu d'aurin aure ya zauna da bayin ALLAH da suka hidimta masa akan su tanderu.
Baffi, Baba Rabilu, Badi, Muftahu, Nuren, Saleem, Sir isa, su Ameer.
Dukansu ya bisu da k'yauta ta girma, tare da musu godiya ta musamman mara iyaka, yakuma y'anta Badi tare da k'yautar muhallin zama mai nagarta a cikin masarauta, hakama sarkin mota, ya basu hak'uri bisa ga jinsa shiru, abaya tattalin arzik'insa ya raunana ne, koyace zai karramasu bashida k'arfin hakan, amma yanzu kam alhmdllh komai ya dai-daita.
Suma sun masa godiya ta musamman a garesa da k'yak'yawar Addu'a, daga k'arshe ya kaisu ga Abie da Momma, sunci abincin rana tare da adalin tsohon Sarki wato Abie, sannan suka sha hira, dama kowa yasan Shiba mutum bane mai girman kai, ga yawan tsokana, shima yamusu k'ayuta ta musamman, hakama Momma tayi nata.

Washe gari ana gobe d'aurin aure kenan da tashin hantsi yasakani shiryawa wai namasa rakiya wani waje.
Kamar ko yaushe Sarkin Montane ke Jammu, yayinda dogaransa ke binmu a baya.
Mun Isa wani waje kusada birnin gayu plaza, wajen ya had'u iyakar had'uwa, a da shagunane kawai a wajen, amma yanzu kamar an rushe anyi wani gini na musamman. An saka k'aton allo mai d'aukeda hotunan kayan gyaran gashi dana kwalliya, an rubuta *_LADIES MIRROR_* da manyan haruffa, hakama jikin k'ofar wajen dayasha glass, an saka babban allo a sama mai kawo wuta da d'aukewa, shima dai irin rubutun farkone a nan, wato *ladies mirror*, abin ya k'ayatar dani, yana rik'e da hannu na muka shiga.
Ashe wajene na musamman na gyaran irin duk Wanda mace take buk'ata, gyaran jiki, saloon, kwalliya, kunshi, dakuma waje na musamman da kayan shafe-shafe na kwalliyar mata ake siyarwa, da glasses aka rarraba shagon, kowanne da 6angarensa, bayan ka fara iske reception a farko, sai office dayaji komai zam dake can k'arshen shagon, shima dai duk glass d'inne, amma daga ciki zagaye yake da labuloli, ba'a buk'atar ganin Wanda zai zauna a ciki kenan.
Bayan mun gama zagaya ko ina muka Isa Office d'in, Galadima ya saka hannu ya yaye wani allo da aka lullu6e da farin k'yalle.
Kallonsu nayi da mamaki, saiya nunamin rubutun jikin allon..
*_“Wannan tukuycine a gareki my mata, badan biyanki hidimar da kike daniba, dan idan biya zanyi abinda na mallaka kaf bazai iya biyankiba matata abar k'aunata, bugun zuciyata komaina Munaaya”._*

Da tsantsar mamaki na d'ago ina kallonsa, yad'an ta6e baki da d'agamin kafad'a alamar gaskiyar kenan.
Kawai jinai hawaye sun gangaromin, na fad'a jikinsa ina sakin wani kukan farin ciki.
Hannu biyu ya saka ya rungumeni yana murmushi, sannan ya jani muka zauna bisa sofa guda d'aya dake a office d'in, ban tsaya wata-wataba na manna la66ana saman .....🤭.
Caraf ya cafke tamkar dama jira yakeyi, gaba d'ayama mun manta a inda Muke, mun tsunduma duniyar masoya wad'anda suka soyu a soyayyarma, saida naji yana Neman kauce hanya sannan na dawo hayyacina.
Na kuma rungumarsa tsam ina jero masa godiya wadda nama rasa wace iriya zanyi masa yasan naji dad'i.
Ya rik'e fuskata cikin tafin hannunsa yana bina da kallo, “My mata babu godiya a tsakaninmu, inma akwaita to nine ya cancanci nayi miki, domin kinmin abubuwa da baki bazai iya lisafosuba, kedai kawai ki rik'eni Amana ni da yaranna da k'anensu masu zuwa, idan kinkai hakan kin gamawa Muhammad Sameer komai, na haramta miki yimin godiya inhar akan wannan d'an wajenne”. Ya kamo hannuna yana zaro key d'in mota a aljihu ya d'oran a hannu.
Kallonsa nayi sannan na kalli hannayenmu, ya d'aga min gira da cije lips sannan ya mik'e.
Tamkar sokuwa haka na bisa da kallo, gaban loka k'arama dake office d'in ya nufa, ya kwaso wasu file ya dawo inda ya barni tamkar wata gunki, d'ayan hannun nawa ya kamo yana d'oran files d'in, “Wannan sune bayanai da form na ma'aikatanki, angama d'aukar kwararru a kowanne fanni, wannan takardun wajene da kowanne lasisinsa, ko gobe kika shirya ma'aikata zasu fara aikinsu.................✍🏻






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼
[8/21, 8:44 PM] 0mmer Farouk: *_Typing📲_*



*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*


*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BOOK 3_* 👉🏻3⃣2⃣


*_🔚END!! 😢✋🏻_*


...............Ban San yanda zan musalta muku halin dana tsinci kainaba bisa ga wannan tukuyci na Galadima, saidaifa kafin wani dogon lokaci dukkan Wanda keda alak'a dani yasan da zaman wannan k'yauta, y'an uwa sai tayani murna sukeyi.
Y'an gidanmu dai saida sukaji wannan bak'ar al'adar tasu ta hassada, amma sun d'an danne zukatansu sukaimin murna.

Washe gari bayan d'aura auren Sauban da aunty mimi Galadima yaja gayyar abokansa da yayuna sukaje aka bud'e wajen saloon d'ina. Akuma ranar ma'aikata suka fara gudanar da aiki, dan a can naje na iske Galadima ni da tawa tawagar, na gana da dukkan ma'aikatana tare da basu umarnin duk Wanda ya shigo wajen a ranar amasa abinda yakeso k'yauta, Washe gari sai a fara na kudi.

Bikin Sauban ya gudana cikin k'ayatarwa, itadai aunty mimi koda aka d'aura auren shikenan, tace wane biki kuma a shekarunta, ana gama shagalin na Sauban tareda amaryarsa Ni'imatullah d'iyar Mom da biyu, itama ta tare gidan mijinta professor Ibraheem Macid'o, musalta muku yanda mukasha shagali 6ata lokacine.

Bayan bikin da kwana biyu Galadima ya fara koya min mota, koya motar da taso zama shiririta, wai dole saidai na zauna a cinyarsa ahaka za'a koyan, banida yanda na iya dole nayi hakan, cikin amincin ALLAH a sati biyu nagama kwarewa, kwana biyu da faruwar hakan na yaye su Amaturrahman bisa dagewar Ubansu akan shima k'annensu yakeso, danga Munubiya da ciki🤭🤣.
Dole nayi wannan yaye yara suka koma wajen Momma.
Kwanaki 10 cif dayin yayen saiga bak'ona yazo, karkuso kuga murna wajen Galadima, wai hanyar samuwar ciki ta bud'e.
Ni dai shiru namasa ban tankaba. Randa kuwa nayi wanka ai babu d'aga k'afa, ALLAH mai iko da falala kuma ya amince masa, koda wata ya dawo babu jini babu alamarsa, hankalina ya tashi na birkice masa, sai yayta tuntsuramin dariya da fad'in “Yarinya an fad'a miki nid'in na wasane, zan zama Abbu a karo na biyu, ALLAH yasa su zama 3+3=6”.
Tashinai nabar masa falon ina zun6ure-zun6ure, shikam yayta tuntsura dariya.
Nima nayi farin ciki da samuwar cikin, tunda naga hakan shine burin mijina da farin cikinsa, sai kuma fatan ALLAH ya sauke mu lafiya, dan wannan karon dai mun sa6a ni da Munubiya.



*_BAYAN WATA 6_*

Cikina ya fito sosai, ina samun tattali da kulawar mijina, kai kace wannan shine cikin farko daza'a Haifa masa, ga shak'uwa mai yawa dake tsakaninsa da yaransa, abin akwai birgewa mai yawan gaske.

Ranar wata juma'a kawai mukaga an tashi da wani gagarumin biki dabamusan na miye ba a masarautar, dama kusan kwanaki uku kenan bak'i nata sauka, ni dai harna kasa hak'uri na tambayi Galadima, yace, wlhy shima bai saniba.

Ana sakkowa daga massalaci sallar juma'a aka hana Galadima shigowa gida, papi ya umarcesa da zuwa ya zauna inda aka tanada dominsa.
Mamaki ya kamasa ganin gurin dank'am da jama'a, addu'a kawai aka gudanar papi yabada umarnin fara abinda ya tara mutane, daga baya koma mikenan jawabi zai biyo baya.
An umarci Galadima da tasowa zuwa saman daddumar dasu Abie da manyan sarakuna ke zaune, ya zauna a tsakkiya shidai zuciyarsa na faman tsitstsinkewa da bugun mamaki.

Turaki ya mik'e a tsanake zuwa gaban mai martaba Sarki Jalaludden Abubakar, yay gaisuwa tare da risinawa sannan ya zare rawanim dake kansa, gaba d'aga wajen aka d'auki kabbara, Abie yay k'asa da kansa yana share hawaye, shidai dan anfi k'arfinsane kawai, amma daba yanke wannan hukuncinba wlhy.

tuni bugun zuciyar Galadima ya k'aru ganin Turaki ya nufo garesa, zaiyi maganar papi yay masa alamar yay shiru🤫.
Dole ya maida bakinsa ya tsuke yana had'iyar yawu da k'yar.
Tsohon Sarki Jalaludden ya taso da taimakonsa Turaki ya cire hular saman kan Galadima aka d'ora masa sabuwa dal, sannan aka fara nad'a masa rawani akai, jikin Galadima sai tsuma yakeyi, ya kafe papi da Abie da ido ko k'yaftawa bayayi, shikad'ai yasan a halin dayake ciki, zufa sai tsatstsafo masa take a kowacce mahudar gashi dake a jikinsa.
Tsaf aka gama nad'a masa rawani jama'ar wajen suka d'auki kabbara, yayinda za'a saka masa alk'yabba sai dogarai suka baza riguna ana masa kirari.
Galadima yay k'asa dakai idonsa na kwararar hawaye lokacin da kunuwansa ke jiyo masa jawabai daga bakin sank'ira.

*_“ALLAH ya d'auki rawani ya maida bisa kan matashi kuma adali tsohon Galadima a yau yazama Sarkin wannan masarauta ta gagara badau bisaga adalcin tsohon Sarki mai murabus a yau, masarautar gagara badau tayi sabuwar amarya, a halin yanzu Mai martaba Muhammad Sameer Saifudden Abubakar shine Sarkin wannan adalar masarauta, ALLAH ya tayashi rik'o, yabashi ikon koyi da k'yawawan halaye irinna manyan wannan gida”._*

Tuni waje ya harmutse da surutai, kowa na fad'in albarkacin bakinsa.
Galadima kam saida papi ya rungumesa a jikinsa sannan yafara samun nutsuwa, yayinda aka kawo Matawalle shima aka zaunar aka nad'a masa rawanin wazirci, shine zai zama wazirin d'an uwansa Sarki Muhammad Sameer Saifudden Abubakar.
Ai tuni guri ya rinca6e, babu maijin zancen wani, kafafen yad'a labarai da social media duksun d'auka, masu murna nayi masu bak'in cikin nayi, (kusan shigabanci, dolene kasamu masoya da mak'iya😭).

Mama Fulani da labarin ya Isar mata zarewa tayi, sai surutai take Wanda ba kowa ke fahimtaba, Gimbiya zulfah kuwa yanke jiki tayi ta fad'i wanwar, koda aka zuba mata ruwa ta farfad'o saita kama aman jini zuciyarta yariga ya buga.
Ba'a katse su papi daga abinda sukeba aka nemo doctor dazai dubata, saidai bata d'auki wani dogon lokaci ba tare ga garinku nan.

Haka duniya take, lokacin da wani ke zuwa sannan wani ke ficewa, hakanne ga gimbiya Zulfah, tatafi a randa Galadima ya zama Sarkin gagara badau.🤴🏿😝😁👍🏻

Ni kaina da labarin zaman mijina Sarki yau babu zato ya zomin saina rikice, na rud'e, ganin lamarin nake tamkar tatsuniya ko mafarki, ga ciki, nama rasa murna zanyo ko kuka.
Ban fita a wannan magaginba saiga zancen halin da gimbiya zulfah take itada mama Fulani, saikuma ga abinda ya girgiza kowa shine mutuwarta.


*********

Koda aka buk'aci jawabi daga bakin Galadima kasawa yayi, shifa ganima yake a mafarki komai ke faruwa, shima Matawalle ya kasa cewa komai, sai zirar da hawaye kawai sukeyi Wanda hakan ya birge kowa da bada mamaki.
Abubuwa sun rinca6e fiye da yanda bakwa zato a masarautar gagara badau, bayan an sallaci gawar gimbiya zulfah aka kaita makawancinta na gaskiya y'ay'anta na kuka da y'an uwanta.

Kiri-k'iri ganin mijina ya gagareni har dare, Abdurraheem sakin k'ulafucin Uba sai kuka yake yak'iyin barci, su Amaturrahman da sukayi nasu na lallashesu sai suka kwanta, dan sunsaba da yayi sallar isha'i yana tare dasu, amma yau shiru babu amo babu labari.
Nikam sainaji abin yana cizon zuciyata, indai wannan mulki zaisa mijina yin nesa dani bana farin ciki, saigani da kuka rurus.

Sai misalin 12pm Sarki Muhammad Sameer yasamu rakkiyar zuwa sashenmu.
Ina zaune afalo nayi tagumi naji alamar mutum tsaye a kaina.
A firgice na d'ago kaina ganin mijina saina mik'e a firgice tare da fad'awa jikinsa na saki kuka.
Shima rungumeni yayi sosai yana sakin nasa kukan, sannan ya d'aukeni cak zuwa cikin bedroom d'in ya ajiyeni a saman gadon, kuma rungume juna mukayi muna cigaba da kukan mu.
Tsawon lokaci muna haka, sannan yafara dakatar da nashi yana lallashina. “Munaya kinga abinda su papi sukaimin ko, ni dai banason sarautarnan, amma sunk'i saurarena, wlhy banaso munaya, banaso nidai”.... Yakuma fashewa da kuka.
Tausayinsa saiya kuma kamani, nakuma rungumesa tsam a jikina, abinda kaga ya saka Galadima kuka aiba k'arami beneba kuwa. Daure zuciyata nayi na shiga lallashinsa.
Na kuma rungume sa sosai cikin nutsuwa ina fad'in, “Mijina ba komai ne ake tuntu6e dashi bisa shiryawa kaiba, wani abun tunkan kasan tuwarmu gudan tsoka rubutaccene a littafin k'addararmu, babu wani d'an Adam da alk'alamin k'addararsa ke a tafin hannunsa, gudun zuciya yafi na k'afafu sauri, idone kawai ke iya banbance fari da bak'i, baki kuwa d'and'ano kawai yake tantancewa, aikin kunne kuwa jine kawai da banbance k'arar sauti, baka tunanin duk mutum mai baiwa ALLAH ke ba damar banbancewar? Irinku kune kuka cancanci mulkin al'umma, domin kuwa bashine burinku ko damuwarkuba, kune zaku iya adalci da tausayin na k'asa daku, ka amince dayin wannan sadaukarwar ga iyayenka da al'ummarka, domin samun damar k'ar6ar sakamakonka wajen adalin Sarki mai tarin rahma da jin k'ai. Zuciya da tunani duk mallakar gangar jikice, haka gudanar jini da motsin ga6o6i, su papi sune sukasan tayaya ka cancanta kaida d'an uwanka, har suka d'auki wannan nauyin suka d'ora muku, Ku kar6i yau d'unku da hannu biyu, domin jiyanku tazama labari, Ku hidimtawa gobenku domin Ku ribantu da jibinku, wannan shine kawai masalaha mai k'ayatarwa ga mu ahalinku, masu ganin baka kaiba saisu ajiye makamansu su


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login