Showing 39001 words to 42000 words out of 382522 words
saida na binciko gidanku, sunana Haidar Mustapha”.
Shiru nayi ban tanka masaba.
Yay murmushi yana matsowa kusa dani, “please mana baby, kimin magana?”.
Da k'yar ya sami na amsashi sannan nima nafad'a masa nawa sunan. abinda na fuskanta da haidar shi mutumne mai sauk'in kai, sannan ko kad'an banga alamun yaudara ba tattare dashi.
Cikin kwanaki kad'an mungama sabawa da haidar, sabawa maiban mamaki, wadda nikaina har mamakin kaina nakeyi wlhy.
Alokacinne kuma yaa Marwan shima ya nuna yanason Munubiya, wayyo zokuga farin ciki wajen iyayenmu, tamkar su zuba ruwa a k'asa susha dan dad'i.
Wannan Abu fa ya bak'anta ran 'yan gidanmu, sunso ace munyi kwantai, har agama sakama 'ya'yansu rana mu babu mazaje a hannu, amma ALLAH ya fisu ai.
Kud'in Munubiya aka fara kawowa gidanmu, daga nan saina Safara'u. nima saiga iyayen Haidar sunzo, ranar har kukan dad'i mukayi muda innarmu, duk wani masoyinmu zai tayamu murna akan wannan al'amari, dan ba'a ta6a tunanin zamu iya samun mazaje da wuri ba saboda abinda yafaru.
Sauran 'yan uwanmu ma duk ankawo kud'ad'en aurensu, dandanan aka tsaida ranar aure, watanni uku kacal, bayan salla babba da wata biyu.
Zuwa yanzu kam hankalinmu ya kwanta, sai dai matsaloli na gidanmu da basa k'arewa, saikuma abinda yafaru tsakaninmu da Galadima, wani lokacin mukan fuskanci tozarci daga wasu jama'a idan mun fita, tunma muna zama muyi kuka har zukatanmu suka fara dakewa.
Galadima kam bamu sake koda jin d'uriyar saba, hakama Fu'aad, tunima Haidar ya mantar dani wani Fu'aad gaba d'aya.
Ahaka babbar Salla tafara gabatowa. Masu shiri natayi, nikam dai babu mu aciki, dagani har Munubiya munyi alk'awarin babu inda zamuje sai gidan mama Rabi'a........
Munshiga bikin salla lafiya, inda iyayenmu sukayi layya kamar yanda kowacce shekara suka saba, itama innaro anmata, babu inda mukaje wannan karon, su Safara'u dai ansha yawo, ranar suyar nama kuma saiga dukkanin amare sunzo yawon salla, abin tamkar had'in baki, kowaccensu tayi 6ul-6ul da ita, harma damasu tsarabar ciki.
Kowacce jinta take a sama, mijinta yafi na kowa, iyayensu kam anata baza hak'wara da tink'aho ana zuba mana habaici.
Babu Wanda ya tanka musu acikinmu, dan innarmu ta hana.
wajen Ayusher mukejin wai babu Galadima a hawan salla wannan karon, hakan bai dameniba, danni baya gabana, nama manta dawani Galadima can.
Bayan gama bikin salla da kwanaki uku saiga wani tashin hankali.
Iyayen Haidar sunzo wai abasu kayansu sun fasa, ance musu ni 'Yar iskace.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Yau munga tashin hankali muda innarmu, kuka da hawaye innarmu keyi itada mama Rabi'a, haka aka had'a kayansu aka basu.
Innaro tashigo tafara tata tsiya babuji babu gani, sai zuba cin mutunci takeyi ga innarmu, 'yan gidanmu natajin dad'i, jisuke kamar anmusu gafara da fasa aurennan nawa, aganinsu yaza'ayi 'ya'yansu suna auren masu kud'i nima na auri mai kud'i, ai bazai yuwuba..
Cikin kuka nakira Haidar ina tanbayarsa miyasa zaimin haka, yasan tun farko ba sona yakeba miyasa yazo gidanmu har iyayensa suka shiga.
“k dalla malama yimin shiru, ni mahaukacine zan auri yarinyar da aka buga hotonta jikin jarida wani na kissing d'inta, ok da an 6oyemin za'a bani sauran wani Ashe ked'in karuwar Galadima ce, to ALLAH ya toni asirinku dagake har iyayen naki, ko a hanya muka had'u karki kuma nuna kin sanni ma”.
Baki na bud'e da nufin maida masa murtani ya yanke wayar, nayi saurin kuma kira amma sai najita arufe.
Kuka na fashe dashi, bansan miya faruba sai dai najini ak'asa kawai.
Cikeda tashin hankali Munubiya tayo kaina tana kuka da girgizani.
Dandanan d'akin yacika dasu Dady, babu alamar rai atare dani, hakan yasa aka d'aukeni da gaggawa sai asibiti.........
★★★★★
A 6angaren Galadima kuwa wasu ayyukane suka d'auke hankalinsa, gaba d'aya yayi busy saboda kamfaninsu na k'ok'arin fidda wata waya sabuwar k'ira.
Abinda ya faru kuwa a Nigeria ya watsar dashi gefe, saboda gargad'in da doctor d'insa yamasa akan yarage yawan damuwa, saboda ciwonsa yana k'ok'arin tashi.
Haka yadage yacire komai d'in, amma har yanzu yasaka amasa aikin bincike ta k'ark'ashin k'asa, sannan iyalan manager sun ku6uta suma, yabar Nigeria da sati biyu suka sakosu.
Gaba d'aya ya ajiye duk wani abinda yashafi Nigeria a gefe, ko bikin salla bai hakarta ba, sannan zuwan dayankan yi duk karshen wata ma ya daina, Momma batace dashi komaiba akan k'in zuwan nasa.
Dan lokacin da mai martaba (mahaifin momma) yazo sun tattauna sosai akan abinda yafaru, shine yace Galadima yad'an tsahirta da zuwa Nigeria nawani lokaci, idan komai ya lafa sai acigaba da bincike, dan wad'anda suka aikata sumafa baza suyi barciba, yanzu idonsu abud'e yake akan komai, amma idan anyi burus dasu komai ya lafa sai a d'auki mataki. Wannan yasa bai sake zuwaba, gameda business d'insa nacan kuwa Harun yana tsaye akan komai.
Fitowarsa kenan daga office zaije gida yad'an kimtsa sannan yaje asibi, wayarsa tashi ruri, zarota yayi daga aljihu ya duba, ganin Muftahu a kan layi saiya maida wayar cikin aljihu kawai batare da ya amsaba.
Hannu yabama beejay abokin aikinsa sukayi sallama akan saikuma gobe. yana k'ok'arin shiga motar kiran yakuma shigowa, shiga yayi ya zauna sannan ya d'aga, suka gaisa da Muftahu, ya tambayesa jikin Abie.
Shikuma ya amsa da Alhmdllh.
Muftahu yace, “ALLAH yasa ban takuraka ba? Inason muyi magana ne dama”.
Kwantar da kansa yayi jikin kujera ya lumshe idanunsa, cikeda k'asaita ya furta “ina saurarenka”.
Daga can Muftahu yay murmushi, sannan yace “dama akan yarannan ne, d'aya daga cikinsu an fasa aurenta, wai Wanda zai auretan yace yafasa sabo...da sa... sa.... yakasa fad'a saboda maganar tamasa nauyi abaki”
Galadina yace “kafad'a mana, kasanfa bana son kwana-kwana a magana ni”.
“wlhy maganarce babu dad'in ji, ca yayfa wai ita karuwarka ce, yanzu haka yarinyar tana asibitima”.
Da k'arfi ya cije lips d'insa, zuciyarsa na suya, saikuma ya saki guntun murmushin takaci, yatashi zaune yana bud'e idonsa, “humm Muftahu waye shi yaron dazata aura d'in?”.
“wlhy ban saniba nima”.
“o right karka damu, zanyi tunani akan lamarin, ni bamma duba bayanai daka turomin akan yarinyarba fa, abubuwa sunmun yawane wlhy. amma masu bibiyar tata basuga wani abunda ya shafi waccan maganarba?”.
“Gaskiya basuga wani abuba sa6anin tunaninmu, ammafa bama yarinya d'aya bace ba, twins ne, kaduba bayanan kagani”.
“ok sai munyi magana kenan”.
Bayan sunyi sallama yay shiru yana tunani a ransa, da gani kasan ransa a6ace yake, ya furzar da huci daga bakinsa sannan ya tada motar yatafi. idonsa yayi jajir saboda bak'in ciki, yanzun har takai wani yafasa auren wata akansa? waye yamasa wannan abin? miya masa ne da zafi haka ya tozartashi? wlhy yayi alk'awarin duk Wanda keda hannu akan wannan tozarcin da akai masa bazai d'aga masa k'afaba, dolene yayi dana sanin saninsa.
Da wannan tunanin ya k'arasa gida.
Babu kowa a gidan sai jakadiya, su Sauban suna makaranta, Aunty Mimi da Momma kuma suna asibiti, jakadiya ta rissina tana gaidashi, hannu kawai ya iya d'aga mata ya haye sama.
Binsa tayi da kallon tausayi, hakan da yayi mata ya nuna ransa a 6ace yake, danshi mutum ne mai girmama nagaba dashi, dukda tana a k'ark'ashinsu bai ta6a wulak'antata ba, wannan tarbiyar mahaifiyarsu ce kuma.
Koda yashiga rigarsa kawai yacire ya zauna a bakin gado, medical glasses d'insa yasaka sannan yajawo System yabud'e, Emailil na Muftahu ya shiga.
Dukkan bayanai da tarihin su Munaya ne awajen.
Gaba d'aya ya nutsu ga abinda yake karantawar, shi mamakima abin yabashi, sukuma wane irin gida wad'annan yaran suka fito haka? Wani abun yakan bashi dariya (sai dai yakanyi dariyar ne a zuciyarsa), wani kuma haushi, tsaf yagama karanta tarihin yaran masu kama da juna.
Ya mik'e yana zagaye d'akin da tunanin miye mafita, har yanzu zuciyarsa bata bar karanta masa da hannun wad'an yaran aka masa wannan abunba, sai dai shi kansa yana tambayar kanasa mizaisa su aikata? miye kuma ribarsu bayan suma hardasu aka tozarta?. yanzu kuma zuciyarsa na masa wani tunani daban bayan yaji tarihinsu.
Zuciyarsa na cigaba da tunzurashi akan yayi amfani da damar k'arshe wajen bincikensa, tunda yabi dukkanin sauran bai samu wani bakin zareba.
To amma kuma wannan ai ba tarbiyyar Malam bahaushe baceba, daga baya kuma idan komai yafitofa? wane kallo kuma za'a masa?, shinma zata iya fahimtarsa kuwa? dan irin wannan abun yakan farune a labaran films ko Novels, to amma wannan ce damarsa ta k'arshe ai kawai, dolene ya jefi tsuntsu biyu da dutsi d'aya kenan?.............✍🏼
Tirk'ashi, Nikam dai nakasa fahimtar wannan cirkud'ad'd'en tunanin na Galadima☹, fan's koku kun fahimta Ku fassara mana🤔?.
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu😭👏🏻_*
Qanwata don Allah ki karo min irin wa'innan hotunan,Tare kuma da na twins maza daban mata daban amman manya da kuma wanda duk suke a hade
*_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻1⃣5⃣
.......Tunda yafara tafiya bai tsaya ko inaba sai a wata sabuwar anguwa, shiru anguwar take babu yawan hayaniya, dan gidajenma tsilli-tsilli suke tamkar rugar Fulani, wani gida dakecan nesa da sauran gidajen yanufa, gidane babba mai k'aton bak'in gate, yay horn sau biyu akazo aka bud'e masa. a babbar harabar gidan yay parking, yana cikin motar bai fitoba har kusan 10 minutes bayan yagama waya yace ya iso.
Idanu na zaro waje saboda ganin Muftahu yafito daga wata k'ofa yanufo motar, gaba d'aya mamaki yahanani kwakwkwaran motsi harya k'araso.
Mai taxi yafito ya risina ya gaidashi, sannan yace nagama aikina Oga.
Murmushi Muftahu yayi, sannan ya lek'a Munaya dake barci kashir6an ta glass, janye kansa yayi sannan ya zaro wayarsa daga aljihu yay kiran wani.
“Umh yalla6ai akwai 'Yar matsala fa, dan barci takeyi sosai, kona d'akkota”.
Da sauri yace “No ina zuwa, amma wannan driver dayay aikin yabar wajen, dan bana buk'atar ya ganni”.
Murmuahi Muftahu yayi, tare da fad'in “angama ranka ya dad'e”.
Muftahu ya sallami drivern daya kawo Munaya, yace zai kirashi ya maidata zuwa anjima, yaje yabar motar anan.
“babu damuwa Oga, saina jika”.
Bayan tafiyar driver Galadima yafito, dama duk yana kallon abinda ke faruwa ta window.
Taku yake cikin tsantsar nuna jinin mulki dake yawo ajikinsa, ga wata izza ta zamowarsa cikakken namiji mai isashshiyar lafiya. fusakarnan babu walwala kamar kullum, ahaka ya k'araso wajen motar, Muftahu ya bud'e masa murfin inda Munaya ke kwance tana kwasar barcinta.
Kallonta yayi na tsayin mintuna uku, sannan ya janye idonsa ya rankwafo da kansa cikin motar, saida yad'an cije lips d'insa sannan yasaka hannayensa biyu ya tallafota ahankali ya fito da ita, tamkar 'Yar baby haka ya d'akkota acikin hannayensa, sai wani kuma d'aure fuska yakeyi yana kauda kai, kaikace anmasa dolene ya d'auketa.
Hannu Muftahu yasaka yatoshe bakinsa saboda dariyar dake Neman kwace masa.
Wai yau Galadima gudane d'auke da mace a hannu, mutumin da ko kallon mata bai cika yiba, inkaga yana walwala ko dariya wa mace to Momma ce ko aunty Mimi.
Jakarta ya d'auka shima yabi bayansa.
Ya iske harya shinfid'eta a doguwar kujerar dake falon, yana gyara hannun rigarsa daya nannad'e yana jan k'aramin tsaki, ganin Muftahu na murmushi saiya kuma had'e fuska, Muftahu ya ajiye bag d'in yana had'iye dariyar da k'yar saboda gudun yin laifi.
Hannu yamik'ama Muftahu.
Muftahu yabashi handkerchief d'in daya zaro a aljihu, rankwafowa yayi kanta ya d'ora Handkerchief d'in bisa hancinta, tsayin minti 2 ya janye.
Tari tafarayi, saikuma ta fara k'ok'arin bud'e idanunta tana lumshewa, Muftahu ya mik'o masa gorar ruwa mai d'an sanyi.
Cikin hannunsa ya tsiyaya kad'an ya shafa mata a fuska, ahankali ta fara bud'e idanun ta, shikuma yaja da baya yakoma ya zauna bisa kujerar mai zaman mutum d'aya.
d'ora k'afa yayi d'aya kan d'aya ya jingina kansa jikin kujerar ya lumshe idanu, saika rantse idonsa arufe suke, amma ya zubasune akan Munaya dake ta mutsu-mutsun tashi zaune.
Da k'yar ta iya tashi ta samu ta jingina da kujerar tana k'arema falon kallo, yayinda hawaye ke zirara a kumatunta.
Ruwa Muftahu ya mik'a mata, babu musu ta kar6a dan wata kishirwa takeji, tunda tafara shan ruwan bata ajiyeba saida ta shanye tas, nan wata zufa tafara karyo mata kuma.
Mik'ewa Muftahu yayi yak'ara gudun AC n.
Ahankali zufar tafara tsanewa, saikuma tad'anji k'arfin jikinta, Muryarta na rawa alamun kuka tace, “Please Ku suwaye? miyasa kuka kawoni nan? dan ALLAH kuyi hak'uri karku cutar dani, karku lalatamin rayuwa dan girman ALLAH, Ku tausayama mahaifiyata, damuwar damuke ciki kad'ai ta ishemu, wlhy daku keta mutuncina gwamma Ku kasheni yafimin sauk'i”.
Daga Muftahu har uban gayyar kallonta kawai sukeyi, ita ko kad'anma bata gane Galadima ba, saboda yayi sama da fuskarsa.
Muftahu ne yace “ki kwantar da hankalinki, kuma ba abinda yasa muka d'akkokiba kenan”.
“to miyasa kuka d'akkoni? bawan ALLAH, mina muku?”.
Muftahu ya juya ya kalli Galadima, amma saiyaga ko motsawa baiyiba, bashima da niyyar tanka musu.
Itama Munaya saita maida kallon nata ga Galadima, a kuma lokacinne yad'ago kansa zai gyara zama.
Wata razananniyar k'ara Munaya tasaki saboda tsorata, da Sauri Galadima ya toshe kunnensa, shima tsawar ya Daka mata wadda tasakata nutsuwar dole.
“k!!! Dalla karki ciremana dodon kunni!!!!”.
Dole Munaya tayi shiru jikinta na 6ari da k'yarma.
Yaja wani wawan tsaki, tare da janye hannayensa daga kunnensa yana harara Munaya. “k wace irin shashashace ne?”.
Sukda halin da take ciki saida ta watsa masa harara, amma bata iya cewa komaiba.
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya FASA, komi yatuna oho.
Komawa yayi inda yataso ya zauna, ya maida k'afafunsa yay crossing d'insu.
Shi dai Muftahu yana kallonsu yakasa cewa komai, bakajin motsin komai saina shashshekar kukan Munaya Dana k'arar AC.
Cikin kuka tace “minamaka kasa aka kawoni nanan? ko sokake kakuma jamin wani sabon 6atancin bayan Wanda yafaru abaya? wane Abu na tare maka waishin aduniyarnan dan ALLAH bawan ALLAH?”. takuma rushewa da kuka mai tsuma rai.
Bakinsa ya ta6e a zuciyarsa yake fad'in daganin yarinyarnan akwai tsiwa dai, saikuma uban tsoro kamar farar kura. banza yamata, azahiri idonsa a lumshe suke, amma kuma abad'ini yana kallon Munaya ne, kukanta Neman saka masa ciwon kai yakeyi, dan haka yay maganar cikeda izza da mulki.
“kinutsu muyi abinda ya kawomu, inba hakaba zaki kwana anan gidan ne”.
Da Sauri Munaya ta share hawayenta, “indai kukane na daina wlhy, kayi hak'uri ka sanarmin, dan ALLAH ka maidani gida kafin hankalin innarmu ya tashi”. tak'are maganar da share hawaye.
Dariya taso bashi amma saiya gimtse, saikace ba itace tagama tsiwa ba yanzun.
Muftahu dai kasa hak'uri yayi saida yad'an dara, Galadima ya balla masa harara, hakanne yasashi yin shiru ya had'iye dariyar.
“kin shirya tafiya kenan?”. ‘galadima yafad'a tamkar an masa dole sai yayi maganar’.
Munaya tace, “wlhy na shirya ranka ya dad'e”.