Showing 75001 words to 78000 words out of 382522 words

Chapter 26 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2948

sai naji tausayin kaina ya kamani, domin nafahimci nanma akwai mai irin halin innaro kenan. Wasu hawaye suka silalomin a kumatu, sauk'i nama auren 1year ne Na kama gabana.
Daga ni har shi babu Wanda yaci wani Abu har aka tashi a taron, lokacin 12pm, yanzuma mom ce takama hannuna muka koma 6angaren da aka fara kaini, muna shiga kwanciya nayi, bayan mom tasakani cire alk'yabbar jikina, duk kunya ta rufeni, ganin haka yasata ajiyemin kayan barci masu kauri ta fita, a hanzarce na shirya na saka hijjab sannan na kwanta, saida ta kintaci time sannan suka shigo itada aunty Mimi da Galadima sai wani ba'indiye, Ashe abokinsa ne dayazo biki, kuma doctor ne.
Galadima ya zauna a bakin gadon kusada kaina, dayake na juya musu bayane, bargon Dana rufa har fuskata yad'an janye, Idan Akash yay tambaya saishi ya d'an rankwafo Dan yaji amsar da zan bada, saiya maimaita masa abinda na fad'a.
Bayan gama tambayoyin Akash yace damuwa ce da gajiya kawai, ya rubuta maganin daza'a sayo min, (duk cikin harshen ingilishi suke maganar).
Kar6a Galadima yayi ya d'auki waya yakira Harun, sunan maganin ya Sanar masa sannan ya yanke wayar, mintuna 10 saiga Samha takawo maganin.
Ya kalli mom yace, “amma bataci abinciba ai”.
Kallon Samha mom yayi, tace “taje ta had'o min tea.
Samha na kawowa duk sai suka fice suka barni dagani sai shi, shima Akash fita yayi.
Bargon jikina ya yaye gaba d'aya, muryarsa a dake yace “tashi kisha”.
Shiru na masa, hakkane yasakashi kausasa muryarsa, “wai bak'ya jinane?”.
Yun k'urawa nayi na tashi da k'yar, kad'an na saci kallonsa, harya cice kayansa na d'azu, yana sanye da dogon bak'in wando da T-shirt mai gajeren hannu, gefen wandon anmasa zane layi 2 da farin zare. fuskarshi babu walwala kamar kulum.
Mug d'in tea n ya mik'omin bayan na gyara zamana na jingina da gado, ALLAH ma ya soni sanye nake da hijjab.
Kar6a nayi dan nima nasan harda yunwa ke cina, inaga rabona dawani abincin kirki tun ana jibi d'aurin aurenmu, (ranar kamu).
Nasha rabin cup d'in na mik'a masa, bai kar6aba yashiga hararata, cikeda k'asaitarsa yace “cup d'in kawai nake buk'atar gani, kina 6atamin lokaci zanje na kwantane”.
Tamkar na makeshi haka naji, na harareshi nima a k'asan ido, muryata na rawa nace “wlhy na k'oshi, zanyi amaine”.
Bai tanka minba kuma bai k'ar6i mug d'inba, hakan ya nunamin dole dai saina shaye kenan, haka na rumtse idanu na shanye na mik'a masa mug d'in.
Kar6a yayi ya ajiye saman table glass d'in dake gabansa, sannan yad'auki magungunan ya 6alla min, bana tsoron Magani sai allura, dan haka babu musu na kar6a nasha tareda ruwan daya bani a cup.
Ina gamawa na zame na kwanta, mik'ewa yayi yaja bargon ya lullu6a min sannan ya fice batareda ya tanka minba.

Babu dad'ewa barci ya kwasheni, bamma San su Ayusher sun shigo sun kwantaba suma. da yake gadon babbane duk sai ya d'aukemu.


Washe gari natashi dad'an sauk'i, sai dai kewar munubiya data innarmu, harma data gayyar tsiyar 'yan gidanmu, sauk'i nama d'aya ina ganin su Feena.
Break fast mai rai da lafiya aka kawo mana, su Ameera sai zuba santi sukeyi, nidai uffan bance da suba, nad'an tsakura kad'an na turo, maganin jiya na d'auka nasha na safe, dan har lokacin kaina na ciwo kad'an-kad'an, babu dad'ewa barci yay awon gaba dani.
Ban farkaba sai 12, shima tadani akayi, wai za'ayi ko hawan mi, nidai wannan bidi'a ta isheni hakanan wlhy.
Shiri akamin yanzuma cikin farin less, sanan aka samin alk'yabba, yanzun ma fuskar tawa a rufe take.
Gaskiya gidan sarauta akwai girma, dan shimafa dole akirasa da suna wani gari guda kam.
A mota aka sakamu zuwa inda za'a gudanar da hawan, dukda kuwa acikin gidanne fa, nida Samha ne kawai a mortar, tana ta zubamin surutu har muka isa.
Wata daban santa bace ta fitar dani daga motar, tana rik'e da hannuna har gurin da aka tanada domin zamana, yanzun fuskata a bud'e take, ba'a sakamin hular alk'yabba d'inba, dan muna zama awajen matar data fidoni ta ciremin, sai dai kunya tasani kasa kallon kowa, duk tsiwata inada tsananin kunya da rashin son zama wajen da mutane suka cika yawa.
Aunty Mimi ce a gefena na haggu.
Ban iya kallonba saida ta min magana tana kamo hannuna, dole babu yanda na iya na kallesu, su Galadima ne a saman dokuna shida samari kusan biyar duk da irin shigarsa ta sarauta, dokunan suna a tsaitsaye, da alama umarni suke jiran abasu, dan kamar gasace zasuyi.
Caraf muka had'a ido dashi, murmushin gefen baki ya sakarmin, cikeda mamaki na janye idona daga kallonsa.
Ana busa wani k'aho kowa yabama dokinsa k'aimi suka rera da gudu, nanfa hankalin kowa yakoma kansu ana zufa tafi, babu wata hayaniya dan bawani yawane damuba, kusan ma wajen duk 'yan matane sai abokan Galadima dasuke son ganin al'adar dabasu saniba. Saikuma yayunsa mata irinsu aunty Mimi, amma babu manya kamar su mom awajen.
Ni ban saniba Ashe wannan tafiya saisun zagaye masarautar su dawo, Wanda yafara zuwa shine na d'aya.
Muna nan kusan mintuna 30 saigasu aguje suna tada k'ura, ko ganin fuskarsu ma ba'ayi sosai bare kagane wanene a gaba.
Jinai kawai ansaki tafi kowa na ambatar Galadima! Galadima!!, wai Ashe shine yafara isowa. ya diro akan dokin yana murmushi da goge hannunasa da handkerchief d'insa daya zaro aljihu, sannan yagoge fuskarsa.
Ruwa wani dogari ya mik'a masa, ya d'auka daga saman tired'in da aka d'oro yabud'e Goran, batareda ya saka kofiba ya hau shan kayansa, tas ya shanye ya jefar da robar, suma sauran duk ruwan suke sha.
Daga nan hotuna akayi, sannan yazo har inda muke ya kama hannuna, wai Ashe nima yanzu dole saina hau dokin, ahakane zamuje sashe-sashe, dan kowa yanacan yafito waje yana jiran zuwanmu.
Banta6a hawa dokiba sai yau, dan haka jikina yakama rawa. Muryarsa can k'asan mak'oshi yace “k bak'auya ki nutsu”.
Maganarsa saida tabani haushi amma ya zanyi, da taimakonsa na hau dokin bayan dogarai sun baza rigunansu yanda baza'a ga hawa naba.
Saida na hau da k'yau sannan shima yaje ya hau nasa, kuyangine a gabanmu suna zuba flowers, a bayanmu kuma dogarai, gefe da gefenmu ma dogaraine, wasu suna busa algaita wasu suna kid'an taushi, sai gayyar abokansa biye damu abaya dasu Ayusher da 'yammatan masarautar.
Ahaka muka dinga zuwa sashe -sashe inda duk sun firfito, duk muna akan dokin bamu saukaba, sai dai mukan risina alamar gaisuwa. fuskata kuma tana abud'e yanzun kowa Na ganina, saida muka zagaye ko ina a masarautar sannan aka maidani wajensu mom. Lokacin la'asar tayi.

Dukna damu saboda kiran munubiya danaketa yi wayar akashe, tsakin danakeyine ya saka Ayusher tambayata, na fad'a mata.
Dariya tayi, “yo banda abunki ina zakiji munubiya kuwa, yaa marwan nacan nashan amarci kema kin sani ai, kema zuwa gobe wazai kiraki ya samu, Galadima nacan yana kwa.....”.
Filo na d'auka Na jefa mata a fusaka, suka sanyamin dariya kuwa.


★★★★

Nasha kuka yayin tafiyarsu Ayusher, inaji ina gani suka tafi suka barni nikad'ai cikin wad'anda ban saniba.
Tun magriba aka shiryani tsaf cikin wata tattausar atanfa, sannan aka d'oramin alk'yabba, wlhy nagaji da saka alk'yabba r nan, saboda nauyi sukemin, har mamaki nakeyi yanda su basu damuba.
Zan iya cemuku nidai yau wanka akamin da turare dan kowane lungu da sak'o na jikina saida yasha ruwan turare, ruwan danayi wanka dashi kansa na musamman ne, nayi k'yau harna gaji.
An fiddoni aka sakani cikin mota, sannan aka nufi sashen Galadima dani. Dukda nasan auren Contract nayi, hakan bai hana zuciyata luguden dakaba, tunda bamuyi wata yarjejeniya dashiba ta zaman da zamuyi, addu'a natayi a zuciyata ina tunano innarmu da munubiyata da kewarta ta gallabeni, jinake tamkar mun shekara 5 bamuga junaba, bamu ta6a yini ba'a tareba, saigashi yau munyi kwana da yinima, ko'a waya bamuji muryar junaba.
Duk da fuskata a rufe take hakan bai hanani shaida 6angaren Galadima ya had'uba, dan k'amshinsa ma da banne.
Muryar wata na tsinkayo a cikinsu tana fad'in wai falon Galadima za'a kaini, gabana yakuma fad'uwa.
Nidai naji mun iso inda turaren Galadima yafi ko ina yawa, inaga nanne falon nasa, gawani lallausan Abu danake takawa a k'afata, sun zaunar dani akan wani laushin dayafi Wanda nake takawar, sannan sukayi addu'a suka fice.
Tunda suka fita ban iya d'ago kainaba, dukda falon tsitt yake alamar babu kowa cikinsa, sai k'arar AC kawai da ni'im taccen k'amshin dake tashi, a falon, sai TV dake magana can k'asa an rage k'arar sosai, hawayen danaketa rik'ewa tun d'azun suka shiga ziraro min a kumatu. a hankali nakejin takun takalmi na tunkaro falon.........✍🏼


Muhad'u tomorrow idan munkai da rai da lafiya, yau kaina namin ciyo kuyi manage da wannan please🤦🏻‍♀.


Ko Galadima zai angwance oho mar😜🥳.
⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu👏🏻😭_*
*_Typing📲_*



*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_




*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_




*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



👉🏻2⃣2⃣


..........Takun takalminsa yana bada sautine dai-dai da kowacce dak'ik'a na bugawar zuciyata, gaba d'aya saina nemi jarumtata na rasa, musamman da firarsu a Ayusher tashiga dawomin a zuciya.
Zuciyata tashiga tsitstsinkewa, saikace ba Munaya mai tsiwarnan ba da rashin barin kota kwana, kululu cikina yabada sauti lokacin da aka murd'a handle d'in k'ofar. kamshinsa ne ya buso min har cikin hancina.
Shikam cak yatsaya yana kallona da mamaki, yasan wannan aikin aunty Mimi ne ko mom, yakuma tamke face saboda tsaro ba tsoroba😎.
Oho ni bamma san yanayiba, nima tawa ta isheni a zuciya, dan wani tsoronsa ALLAH ya dasamin lokaci d'aya. kusan mintuna 2 yana a tsaye tamkar bak'on falon, yayinda k'amshin turarena ke dukan hancinsa, yau da ace auren soyayya yayi da wadda yakeso, babu abinda zai hanasa sauke nauyin daya damesa tsawon shekaru. a hankali yacigaba da takowa har cikin falon, ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu cikeda izza, k'afarsa d'aya a kan d'aya yana wani kallona a k'asan idanu, shiru kakeji tamkar bama a cikin falon.......
Muryata a sanyaye nace “ina yini”.
tamkar bazai amsaba, saikuma yace “lafiya”.
Daga nan kowa yay shiru.
Knocking d'in k'ofar da akayine yasakashi sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, cikin muryarsa mai kama da anmasa dole ya tambayi wanene?.
Cikeda girmamawa sarkin k'ofar yace, “nime ranka ya dad'e, dama an kawo sak'one”.
Kansa ya jingina da kujera, sannan yace “su shigo”.
Kuyangi kusan biyarne suka shiga falon da sallama, duk muka amsa akan la66a, suka dire kayan hannunsu sannan suka zube suna kwasar gaisuwa agaremu, hannu kawai ya d'aga musu, nidai koma motsi banyiba, dan nima kunyama nakeji idan naga sun durk'usa suna gaidani, danfa wasuma sun girmeni sosai wlhy, wasuma sun haifeni, kai sarauta dabance gaskiya, al'amuransu sunada wahalar gaske, nidai harma yanzu ban fahim ci komaiba wlhy.
Bayan fitarsu da kusan mintuna 4 naji alamar mik'ewarsa, yanzu ma baice dani uffan ba yashige wani d'aki danake k'yautata zaton bedroom d'in sane a wajen.
Guntun tsaki naja, a raina nace ALLAH ka rabamu da girman kai dai wlhy.
Ban damu da cire hular alk'yabba d'inba, dan sanyin Ac yasa ban takura ba, sai zamana dana gyara sosai yanda zanji dad'i da k'yau a saman lallausar kujerar, duk da har yanzun a tsoracen nake kuwa. dan wannan d'an jinkan yafi k'arfina, zai iya amfani da k'arfinsa ya cutamin batareda yayi la'akari da matsayin auren namuba.

Shikam yana shiga d'akin nasa yafara k'ok'arin cire bottom d'in rigarsa, idon sane ya sauka akan gadonsa dake lailaye da zanin gado blue, dan komai nasa na nan white and blue ne, sa6anin na India dasuke White and Golden, kuma matsawa yayi sosai saboda ganin farin k'yalle dake saman bedsheets d'in.
Tsaki yaja yana fad'in “waisu wad'annan mi suke nufi da shinfid'amin wannan farin abun a saman gado? samazo su d'auki kayansu yanda suka ajiye, motsww”. Yakuma jan tsaki sannan ya shige bathroom.
Acanma yana wankan yana jera tagwayen tsoki, bai wani dad'eba yafito sanye da bathrobe milk, hannunsa rik'eda k'aramin towel yana goge fuskarsa zuwa kansa.
Bai shafa maiba, wando yasaka da t-shirt duk milk color marasa nauyi, da alama yayi shirin barci kenan, ya d'auki turarensa na barci mai sanyin k'amshin ya faffeshe jikinsa, sannan ya saka silifas bak'ak'e a k'afarsa yakuma fitowa..
Kallona yayi da mamaki ganin ko fuskarta na kasa bud'ewa, ya ta6e baki da cije lips nashi saman ya zauna bisa tattausan carpet d'in tsakkiyar falon inda kuyangin suka ajiye kayan d'azun.
Tankwashe kafafunsa yayi yashiga bud'e kwanikan domin duba abinda ke ciki. “halan kekam bak'ya jin zafi?”.
Yayi maganar yana zuba fruits salad a k'aramin bowl na tangaran mai k'yau.
Shiru nayi tamkar ban jishiba, shima saiya shareni yaja bowl d'in gabansa yafara sha a hankali tamkar bayaso.
Duk abinda yakeyi ina kallonsa ta k'asan ido, saboda kaina Dana jingina da kujera.
Kusan mintuna 5 yana shan fruits salad d'in tamkar wani k'aramin yaro, dan ko Rabin Wanda yazuba baiyiba, araina nace abincinma sai an masa sarauta kenan.
Idanunsa ya d'ago yana kallona, “k wai bakijin ana Miki maganane? bazaki bud'e face nakiba?”.
Saida naja kusan seconds 20 sannan na janye hular alk'yabba d'in.
Janye idonsa yayi yacigaba da shan kayansa, nikuwa saima na zame na kwanta a kujera, dama 3setter ce, idanuna na maida na lumshe saboda ciwon da kaina yakeyi kad'an-kad'an, ga kewar innarmu da munubiya dasu Aryaan na damuna, ga wannan auren na fargaba na addabar zuciyata.

Dukda yaga kwanciyar danayi bai tankaba, ya kammala shan fruits salad d'in yamik'e, saman kujera yakoma ya zauna, ya d'auki wayarsa yana latsawa, saikuma ya ajiye ya d'auki remote ya canja tasha zuwa labarai.
Haka muka zauna tamkar kurame, shi yana kallon labarai yayinda nikuma barci 6arawo ya saceni batareda na shirya ba, to gajiya na nuk'urk'usata.
Shi duk bai farga barci nakeba harya kammala kallon labaransa ya kashe tvn, kallona yayi da nufin min magana saiyaga kamarma nayi barci a haka.
Yay d'an jim yana tunanin tayaya zai tasheni, danshi soyake ya shige yayi shafa'i da wutiri ya kwanta, a ganinsa kuma bai kamata ya barni a wajenba.
Matsowa yayi kusada kujerar, ya d'an bubbuga hannun kujerar, dama barcin nawa baiyi nisaba, na bud'e idanuna dasukayi d'an jaa a hankali, saboda barcin dana fara.
“tashi muje ki kwanta”.
Gabana ya fad'i, amma saina yunk'ura da k'yar natashi zaune.
Ganin ya nufi k'ofar futa sainaji d'an sanyi, tashi nayi nabi bayansa muka fita, bakowa falon alamun duk suntafi makwanci. Wani falon muka shiga daban kuma, gaskiya shima ya had'u, komai na cikinsa lemon green ne da milk, sai tashin k'amshin turaren wuta da air fresheners masu dad'i yake. bai tsaya ananba yay gaba, nidai ina binsa abaya kawai, munshiga k'aton bedroom tamkar nasa, saidaifa aganina nasan yafi had'uwa duk da ban ganiba, nanma komai lemon green ne acikinsa, sai labuloli milk kamar falon, shima yanata tashin k'amshin.
Juyowa yayi ya kalleni “nan shine d'akinki”. ‘yayi maganar tamkar an masa tilas’.
Uffan bance masaba, sai d'aga masa kai nayi alamar naji, shima bai sake cewa komaiba ya fice abinsa.
d'akin na shiga bi da kallo, yamin k'yau sosai, na cire alk'yabba jikina ina sauke numfashi, sanan na cire sark'a da 'yankunne da bangles d'in duk na zube saman madubi. Suma kayan na hau cirewa dan bazan iya barci da suba, sai kuma na shiga tunanin inda zan samu kayan barci? tunda lefena suna gidanmu ba'a kawoba, akwatin da'a kawoni dashi kuma jiya ban Ganshi a d'akinba, zuciyatace tabani shawarar duba wardrobe d'in dake d'akin, banyi musuba naje na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login