Showing 321001 words to 324000 words out of 382522 words
Chapter 108 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete
A koda yaushe Momma cikin kira take taji yaya jikinsu Munaya, koda wasa ba'a sanarma Abie komaiba, Dan ana ganin cigaba da haske game da jikinsa sosai, ba'a fatan wani abinda zai maido da hannun agogo baya game da ciwon nasa.
Addu'oi kam sosai aka duk'ufa yinsu game da Munaya, wadda har yanzu Galadima ne kawai keda alhakin shiga ya dubata, shima sau d'aya a rana kawai, yau dai duk ake saka ran farkowarta, Dan an dakata damata dukkan wata allura dake sakata barci, saidai kuma har dare babu wani bayani.
Zasu tayar da hankalinsu doctor yace suyi hak'uri, maybe zuwa dare ko safiyar gobe ta farka d'in, danba a sume takeba, barcine kawai da sune suka sakata ta hanyar mata allurar.
Badan hankalin nasu ya kwantaba sukai shirun, har lokacin barinsu asibitin yayi babu wani bayani game da farkawar tata.
*Washe gari*.
Duk dai yanda akaso farkawar Munaya a ranar sai a washe garine ALLAH ya amince da hakan, Alhmdllh anci nasarar farkawar tata yanda ake buk'ata, saidai ciwukan jikinta a halin yanzu.
Saida doctors suka gama dukkan kai kawonsu naganin komai ya ida daidaita sannan aka bama Galadima damar shiga.
Tamkar mai sand'a haka ya shiga d'akin, tana kwance amma idonta biyu, sai dai a lumshe suke, an kuma cire mata bandejin da aka zagaye mata fuska, sai kad'an aka bari inda ciwon yake.
Durk'usawa yay a gaban gadon, ya kamo hannunta Na haggu dakeda lafiya ya saka nashi ciki, a hankali ta bud'e idanunta saboda jin tattausan hannunsa cikin nata, ga k'amshin turarensa daya mamaye d'akin Wanda ya tabbatar mata da shid'inne, tana shak'a a hankali.
Idonta ta saka cikin nasa, kowanne yakasa koda kwakwkwaran motsi tsawon mintuna 2, a hankali Galadima ya bud'e baki tamkar mai rad'a ko gudun wani ya jisu yace, “Munaayaa I love you, I really love you, I love you more and more my Heartbeat..”
Lumshe idanu Munaya tayi, wasu hawaye suka gangaro daga cikin idanu zuwa gefen kunnuwanta, zuciyarta sai wani irin bugawa take da sauri-sauri, ta kuma damk'e hannunsa cikin nata tana maijin tsigar jikinta Na tashi, jininta sai yamutsawa yake a kowanne 6angare. Kuma bud'e idon tayi a kansa, suka sakarma juna lallausan murmushi ga hawaye Na zuba a idonta har yanzu, shima kwalla sun tarar masa a cikin ido sun saka idon wani k'yalli Na musamman daya kuma sakama munaya wata kasala da tsantsar k'aunarsa, ya lumshe idanunsa alamar tabbatar da abinda ya fad'a mata har cikin ransane ba iya fatar bakiba.
Itama hawayen ta kuma matsowa, ta bud'e baki da k'yar tana cigaba da kwararo hawaye. Tace, “i love you too yalla6ai, I love you so much...”. ‘takai k'arshen maganar wani kukan Na kwace mata.
Hannunta dake rik'e cikin nasa ya sumbata yanamai jin farin ciki, yace, “ki kasance dani Munaya, ki kasance dani har k'arshen rayuwata, ke Katanga tace, haskena ce, farinciki nace, duniyata ce, duk duniya kece mace ta farko bayan mahaifiyata da y'ar uwata danakema so Na musamman, please karki barni uwar y'ay'ana, karki gujeni komai rintsi, nima namiki alk'awarin kasantuwar mu tare har k'arshen numfashi, ki rayu dani, ki mutu dani bugun zuciyata, kamar yanda nima burina kenan a gareki tsawon lokaci”.
Lallai yau daba'a halin ciwo takeba har rawa sai tayi, Wanda bata ta6a tsammani ko tunanin zaisotaba shine yake furta wad'annan dad'ad'an kalamin agareta, shine yake rok'onta ta kasance dashi har k'arshen rayuwarsa?, shine yake kiranta katangarsa?, harskensa, bugun zuciyarsa? Koda a yau tabar duniya ta ribantu da nasarorin masu yawan da wahalar k'ididdiga wajen lissafi.
Galadima dake share mata hawaye da hannayensa ya duk'a ya manna mata kiss a goshi da saman la66a.
Ta kuma bud'e idonta da suke jajur akansa, murmushi suka kuma sakarma juna, ya girgiza mata kansa alamar tabar kukan, idanunta ta lumshe alamar amsawa.
Shikam ya tsura mata idanu ko k'yaftawa bayayi, y'ar ramar da tayi saiya k'ara mata k'yau da k'uruciya, ya shafa k'ananun kitson dake kanta ta kuma bud'e ido tana kallonsa.
Cikin d'age gira d'aya yace, “baki tambayi ina yaraba?”.
Lallausan murmushi ta kuma sakar masa, ta kwanto hannunsa dake sark'e da nata saitin bakinta ta sumbata, sannan ta d'orasa a saman k'irjinta.
Tausayinta ya kamashi sosai, domin jikinta akwai zafi har yanzu, ga abincinsu sunyi matuk'ar cika, Wanda zazza6in nata yanada nasaba da rashinsu gareta, dukda akwai Na zafin ciwo.
Hakan da tayi shima saiya fahimci mitake nufi, kuma duk'owa yay ya sumbaci goshinta, zaiyi magana doctor ya shigo.
Shiru Galadima yay ya juyo yana kallonsa, itama Munaya daga kwancen take kallon doctor ta k'asan ido.
Doctor dake gulma da zuciyarsa yana fad'in lallai ya yarda, duk sarautar Sarki a gaban matarsa bawane, matarce ke zama sarauniya..... (Ga naku Matan kwarai sarakin duniya👍🏻👌🏻😜)
Galadima ya katse tunaninsa ta hanyar buga yatsunsa biyu suka bada sautin d'as-d'as.
Doctor ya dawo hayyacinsa a kunyace. Yace, “sorry ranka ya dad'e, dama Nurse zata goge mata jikine da kuma gasa mata, Dan tasamu sauk'in nauyin da yay mata”.
Murmusawa Galadima yay, ya zare hannunsa daga cikin Na Munaya yana mik'ewa tsaye, hannayensa ya hard'e a k'irji yana kallon doctor da fad'in “Doctor da raina zan bar wasu ganarmin sirrina? Ku kawo kayan buk'ata kawai”.
Doctor daya fahimci Inda zancen Galadima ya nufa saiya murmusa yana cewa “Afuwan ranka ya dad'e”.
Hannu kawai Galadima ya d'aga masa, ya juyo suka had'a ido da Munaya ya d'aga mata gira da cizar lips d'insa.
Baki ta tunzuro masa tana yamutse fuska.
Ya d'aga kafad'a da ta6e baki alamar bashida matsala🤷🏿♂🤣.
Nurses biyu suka shigo da dukkan abinda ake buk'ata, Galadima Na tsaye ko kallon inda suke baiyiba, idonsa nakan matarsa k'yam, sukam sai satar kallonsa sukeyi, suka ajiye suna fad'in “Gashi Ranka ya dad'e”.
hannu kawai ya d'aga musu amma ko tari baiyiba.
Fita saukai cikin takaici, dan sunso yayi musu magana koda sau d'aya ne.
Takawa yay a hankali jikin k'ofar ya Mirza key, sannan ya dawo yana cire link d'in hannun rigar farar shaddarsa da tattarewa zuwa sama.
Suka had'a ido da Munaya tai azamar janyewa cike da kunya.
Murmushin gefen baki yayi yana zama bakin gadon kusa da k'ugumta.
Bottoms d'in jikin green d'in rigar asibitin yafara cirewa a hankali, itadai kunya ta hanata bud'e ido, gashi ya tsareta da idanu, Dan tanajin yanda idanunsa ke yawo cikin jininta, salon daya koma wajen cire bottoms d'in ya sakata dafe hannunsa da hannun haggunta, ta bud'e ido tana kwa6e fuska.
Gira ya d'aga mata, da wani mata salo da kwayar ido.
Babu shiri ta maida idonta ta rufe ruf, tsigar jikinta Na tashi.
A haka dai aka gama cire rigar, yaja bedsheet d'in da ake lullu6a mata a k'afafu ya rufa mata a jiki, sannan ya kuma gyara hannun rigarsa yana tsoma madaidaicin towel d'in cikin ruwan d'umin dake a boket, ya matsa dukda akwai d'an zafi ruwan haka yafara danna mata jiki dashi.
Tanajin zafi, amma kuma tanajin dad'in d'umin ruwan sosai, k'in yarda tayi su had'a ido har aka gama, ya d'auki wani d'an kwalba da mai ke ciki tamkar zaitun, karantawa yay yaga amfaninsa sannan ya zuba a tafin hannunsa yana murzawa, kumajin tattausan hannunsa daya had'u da sul6in mai tayi a k'afafunta, tad'an kuma bud'e ido tana kallonsa. Ganin ba ita yake kalloba saita shagala da kallonsa, babban mutum mai daraja jinin mulki yau shine ke mata hidima irin haka, itako badan kar ace tayi alfahari ba da cika baki da yawa da tace ta more fiye da kowacce mace (🙄nidai fa bandani, reader's Ku kun yarda harda Ku🤷🏻♀)?.
Sosai tafara jin dad'in tausar, Dan da salon nutsuwa yake mata, tuni tafara lumshe idanu, hardai barcin yaci galaba a kanta. Sai dai saukar numfashinta yaji a hankali.
Ya kalleta yana murmushi da lumshe idanu, bai bartaba saida ya tabbatar barcin yayi nisa, cikin dabara ya canja mata rigar da suka sakko a kayan domin canji. Ya duk'o ya sumbaci goshinta da bakinta yanajan bedsheets d'in sosai ya kuma lullu6a mata.
Kayan ya maida gefe, ya koma saman kujerar dake gefem gadon ya zauna ya zuba mata idanu, kai kace yaune ya fara ganinta, ya dad'e a haka kafin ya d'auka wayarsa yana dannawa.
A haka Nurses d'in suka masa Knocking, izinin shigowa yabasu, amma sai suka murd'a k'ofar a rufe.
K'aramin tsaki yaja yana muk'ewa, shi yama manta ya rufe. Bud'ewa yay yadawo ya zauna yana d'ora k'afa d'aga kan d'aya da kuma d'aure fuska.
Tuni Nurses d'in suka shiga hankalinsu, cikin risinawa d'aya tamasa bayanin zasu canjama Munaya bandejin jikinta ne.
Batareda ya kallesuba yace, “kuyi a hankali, Dan barci takeyi, idan kuma kunsan zata iya farkawa kubarsa saita tashi ”.
Kallon juna suka, kowacce tad'an ta6e baki, d'ayar tace, “insha ALLAHU bazata tashiba ranka ya dad'e”.
Nanma Kansa kawai ya jinjina musu yacigaba da latsa wayarsa.
Haka sukai wannan aiki a gabansa Dan yak'i fita, data motsa ya zuba musu uwar harara mai rikita hanjin ciki.
Dolensu suka bita a sannu har suka samu kammalawa lafiya, kowacce ta fice a tsorace.............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻2⃣1⃣
.................Kusan mintuna 7 da fitar Nurses d'in doctor yay Knocking, Galadima ya amsa ba tare da ya ajiye wayarba, doctor ya shigo abinsa, Nurse d'aya da sukai akin d'azun Na biye dashi.
Galadima ya d'ago yana kallonsu fuska babu walwala, Dan shifa yafara gajiya da wannan shigi da ficin, amma baice komaiba.
Doctor daya d'an tsargu yace, “Afuwan ranka ya dad'e, dama ina ganin yakamata tafara cin abincine, Dan ruwan da muke saka matane dama yake taimaka mata, to yanzu kuma zata fara shan magunguna insha ALLAH”.
Galadima yad'an sauke numfashi yana fad'in “ok, to amma yaranfa? za'a iya kawosu yanzu?”.
“eh to, sunkai nawa?”.
Yatsu uku Galadima ya d'agama doctor, dukda yayi mamaki saiya danne abinsa, musamman dayaga munayar y'ar k'arama da ita. yace, “Ranka ya dad'e dadai and'an k'ara mana lokaci koda kwana biyune, har yanzu zancen danake maka ba'ason abinda zai cika mata hayaniya a kai”.
Jinjina kai Galadima yayi kawai, alamar gamsuwa.
Daganan Doctor yay d'an dube-dubensa ya bama Galadima Drugs d'in Munayar akan Nurse zata dinga zuwa tana bata kullum.
Doctor Na fita shima ya ajiye wayarsa kusa da ita ya fito, d'akin da Nuren yake ya shiga, yana zaune Aunty Mimi Na bashi abinci a baki, Galadima yad'an hararesa yana fad'in “k'aton banza kacika shagwa6a”.
“Uhmyim” Nuren ya fad'a yana ta6e baki da rama Harar da Galadima ya masa.
Ita dai aunty Mimi murmushi kawai take da wannan rigima tasu dabata k'arewa, dama can inhar Nuren da Galadima Na waje sai kayi dariya, Dan kafin su rabu sai anyi kusan fad'a goma.
Galadima yace, “Ya jikin?”.
“Aini kam Alhmdllh, yanzu kawai maganar gaskiya amin aure, inda Na mutufa shikenan, kukan kwana uku zakuyi a wuce wajen, amma in mat......”
Hannu Galadima yakai zai bige bakinsa, yay saurin duk'ewa, Aunty Mimi ta sanya dariya, Galadima kuwa kwafa yay yana kallon Aunty Mimi, “oh ALLAH, maimakon kimasa fad'a dariyama kike masa? Wannan yaron wlhy fitsararrene, idan kunk'i masa aurenan zai iya zuwa yayi baku saniba ma”.
Nuren ya gyara zama yana hararsa, “Yo angaya maka ni irinkane, soyyaya Na cin zuciyata k'asaita ta hanani fad'e, Malam mufa dama munsan komai, munzuba idone muga yanda wasan zai k'are”.
Murmushin da Galadima bai niyyar yibane ya su6uce masa, ya mik'e da fad'in, “Duk iskancin da kamin ninaso, tunda nine nazo dubaka, idan nakuma zuwa d'akinnan kace ba sunanka Nureddin ba”.
“Ahaf, yo dama sunana Sameer ne?”.
Galadima bai kulashiba, ya kalli aunty Mimi daketa musu dariya, “Auntyna yakamata a sanarma gidansu ta farka, naga har yanzu babu Wanda ya iso”.
Murmushi Aunty Mimi ta masa, ta ajiye plate d'in datake bama Nuren Abinci tana cewa, “babu damuwa, mu barsu har zuwa yammar, tunda kaga har yau basu bada damar a shigaba”.
“Ok, hakan yayi”.
Harzai fice aunty Mimi tai saurin cewa “Abincinfa?”.
Kansa ya girgiza mata yay ficewarsa.
Nuren dake murmushi ya kalli Aunty Mimi yana fad'in “Auntynmu soyayya nacin Guy d'inan yak'i fahimta”.
Dariya tayi “Nuren kenan, ingaya maka sarai yasan yana sonta, shegen son girma da miskilancine kecinsa, amma ai naga alamar yanzu an wuce wajan”.
“A haba? Aunty da gaske?”.
“kwarai ma kuwa Nureddin”.
Hannu yabata suka tafa, yanajin wani sanyi a ransa, da sakama Muftahu albarka a zuciyarsa, danya zama aboki kuma d'an uwa Na k'warai.
Fitowar Galadima yaci karo dasu Yassar, ya fad'ad'a murmushinsa, shima yaran sun shiga ransa sosai, k'arasowa sukai gareshi, cikin girmamawa duk suka gaisheshi, ya amsa da kulawa.
“ku bakwa gajiya da yawo?”.
Soshe-soshen kunya suka farayi, Marcel yace, “ai daga gida muke, munzo muk'ara ganin jikin Aunty da Uncle ne”.
Galadima yad'an murmusa yana tura hannayensa duka a aljihu, cikin d'an lumshe ido yace, “kushiga to kugansa”.
“Uncle! Auntynfa? Ta farka itama?”. ‘Ahakam ne mai maganar’
Galadima ya jinjina kai. Yace, “ta farka Ahakam, amma tana barcine”.
Gaba d'ayansu farin cikine ya bayyana a fuskokinsu, kai kace y'ar uwarsuce ta jini, da wannan farin cikin suka shiga d'akin da Nuren yake, shikuma yakoma inda Munaya take murmushi d'auke a fuskarsa.
Dad'an hanzarinsa ya k'arasa gareta, ganin ta farka, zama yay a kujerar suna kallon juna, murya a sanyaye yace, “Kin tashi?”.
Da idanu ta amsashi.
Ya shafa kanta yana fad'in “Sannu, yanzu ina ke miki ciwo?”.
Fuska ta d'an yatsine, ta nuna masa hannunta da kanta.
Cikin tausayawa Yakuma mata sorry, sannan yace, “mizaki ci?”.
Kanta ta girgiza masa alamar babu komai.
Ya d'an 6ata fuska yana fad'in “Ban yarda ba, kinga kuwa yanda kika rame?”.
Murmusawa tayi, itama ta masa alamar wai ya rame shima.
Baki yad'an ta6e, amma baice komaiba ya d'auka wayarsa dake kusa da ita yay kiran Muftahu akan abinda za'a kawoma Munayar kozata d'anci.
Itadai kallonsa kawai takeyi. Ya yanke wayar yana kallonta shima da d'age mata gira d'aya alamar kallonfa?.
Dukda taji kunya saita yamutse fuska irin miye abin kallon anan.
Galadima yay wani miskilin murmushi cikin murya k'asa-k'asa yace, “Really?”.
Ta lumshe idonta alamun tabbabatarwa.
“zaki maimaitamin idan kin warke yarinya”. Yay maganar da wata siga harda cije lips.
Munaya ta kauda idonta tamkarma bata fahimci ina ya dosa ba.
A ranardai haka kowa ya yini cikin farincikin farfad'owar Munaya, gashi anbarsun sunshi sun gagganta, saidai anata musu gargad'in banda hayaniya, tausayin ta duk ya kamasu. Innaro harda hawayenta, aka saka bakin Zane ana sharewa da jemasu Alhaji balala ALLAH ya isa, harda cewa sai an koma kotu an sake sabuwar shari'a an kar6oma jikarta hak'inta.
Shi Galadima ma abin dariya ya bashi matuk'a, yadai had'iye yana duk'ar da kai