Showing 45001 words to 48000 words out of 382522 words
kalli Galadima, amma saiyaga ko motsawa baiyiba, bashima da niyyar tanka musu.
Itama Munaya saita maida kallon nata ga Galadima, a kuma lokacinne yad'ago kansa zai gyara zama.
Wata razananniyar k'ara Munaya tasaki saboda tsorata, da Sauri Galadima ya toshe kunnensa, shima tsawar ya Daka mata wadda tasakata nutsuwar dole.
“k!!! Dalla karki ciremana dodon kunni!!!!”.
Dole Munaya tayi shiru jikinta na 6ari da k'yarma.
Yaja wani wawan tsaki, tare da janye hannayensa daga kunnensa yana harara Munaya. “k wace irin shashashace ne?”.
Sukda halin da take ciki saida ta watsa masa harara, amma bata iya cewa komaiba.
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya FASA, komi yatuna oho.
Komawa yayi inda yataso ya zauna, ya maida k'afafunsa yay crossing d'insu.
Shi dai Muftahu yana kallonsu yakasa cewa komai, bakajin motsin komai saina shashshekar kukan Munaya Dana k'arar AC.
Cikin kuka tace “minamaka kasa aka kawoni nanan? ko sokake kakuma jamin wani sabon 6atancin bayan Wanda yafaru abaya? wane Abu na tare maka waishin aduniyarnan dan ALLAH bawan ALLAH?”. takuma rushewa da kuka mai tsuma rai.
Bakinsa ya ta6e a zuciyarsa yake fad'in daganin yarinyarnan akwai tsiwa dai, saikuma uban tsoro kamar farar kura. banza yamata, azahiri idonsa a lumshe suke, amma kuma abad'ini yana kallon Munaya ne, kukanta Neman saka masa ciwon kai yakeyi, dan haka yay maganar cikeda izza da mulki.
“kinutsu muyi abinda ya kawomu, inba hakaba zaki kwana anan gidan ne”.
Da Sauri Munaya ta share hawayenta, “indai kukane na daina wlhy, kayi hak'uri ka sanarmin, dan ALLAH ka maidani gida kafin hankalin innarmu ya tashi”. tak'are maganar da share hawaye.
Dariya taso bashi amma saiya gimtse, saikace ba itace tagama tsiwa ba yanzun.
Muftahu dai kasa hak'uri yayi saida yad'an dara, Galadima ya balla masa harara, hakanne yasashi yin shiru ya had'iye dariyar.
“kin shirya tafiya kenan?”. ‘galadima yafad'a tamkar an masa dole sai yayi maganar’.
Munaya tace, “wlhy na shirya ranka ya dad'e”.
Yace “good girl” yana ta6e baki.
“ki fad'amin waye yasaki aikin nan?”.
Cikeda rashin fahimta Munaya tace, “wane aikin?”.
Shiru Galadima yayi bai tanka ba, sai Muftahu ne yaymata bayani dalla-dalla akan abinda yafaru a plaza kwanakin baya”.
Cikeda k'unar zuciya Munaya tace “ni babu Wanda yasakani, saima tozarci da hakan ya jawo mana muda mahaifiyarmu, bansan komaiba, amma tunda al amarinan yafaru muka kuma tsintar kanmu a k'unci, kullum da irin abin kuka dazamu gani agidanmu, yanzu haka akan waccan abin maganar aurena sau biyu tana lalacewa, yanzu haka satina guda kenan da baro asibiti saboda tashin hankalin dana shiga a dalilin fasa aurena da cin zarafi dana fuskanta daga Wanda yafasa aurena nawa, wlhy Ku yarda dani bansan komaiba”.
Muftahu ya juya yana kallon Galadima da idonsa ke a rufe, amma yana sauraren Munayar.
Kusan mintuna 3 sannan ya bud'e idonsa, akan Munaya ya zubasu, bazata iya jurar kallon kwayar idonsa ba dan haka tayi azamar janye nata, shima janye nasa yayi ya gyara zamansa. “kince babu hannunki? amma miya kaiki plaza a wannan time d'in daya kamata duk yarinyar kwarai tana gidansu?”.
“Muna bikine, bayan munkai amare mun dawo sai fu'aad yamatsa akan saimun shiga, ba dan nasoba nayarda, kuma bani kad'ai baceba, harda 'yan uwana su uku”.
“waye shi Fu'aad d'in?”.
“Saurayinane, awajen bikin muka had'u dashi”.
da sauri Galadima yace “miye kamaninsa? kuma ya kukayi dashi bayan abin ya faru?”.
A nutse Munaya tabasu labarin komai, sannan ta zano musu kamannin Fu'aad dalla-dalla, danma bawani kallon tsaf tamasa ba a cikin kwana biyun.
Muftahu yace “kozamu iya samun Horton shi Fu'aad d'in?”.
“banida hotonsa, dan bai yarda munyi ko photo d'aya ba awajen bikin, amma zamu iya samu a video d'in da akayi maybe awajen dinner? ”.
“galadima yace “a ina zamu CD d'in yanzu?”.
“gaskiya wannan shine mai wahala, dan bansan taka maimai cikin angunan waye yasaka ayiba”.
Galadima ya cije lips d'insa da k'arfi, sai kace zai hudasune.
Kusan mintuna 3 kowa baice komaiba, sai can munaya tace “kunji na fad'a muku gaskiya, Ku maidani kafin afara nemana”.
“zamu maidaki bisa sharad'i guda d'aya”. ‘cewar Muftahu ’.
“wane sharad'ine?”. ‘Munaya ta tambaya’.
“Sharad'in shine zakuyi auren 1year keda Galadima”.
Cikin zaro idanu waje munaya tace “kamar ya? ban fahim cekaba fa?”.
“ina nufin Auren yarjejeniya zakuyi na shekara 1 ko 2, ta wannan hanyarne kawai zamu iya kamo bakin zaren, sannan kekuma zaki sama ma iyayenki kwanciyar hankali, nanda kafin adadin da aka d'ibama auren yacika kinga komai ya wuce, saiya sakeki kiyi idda ki sami Wanda kikeso sannan kuje gida a d'aura miki aure dashi, Galadima ma zai iya sawa har auren a d'aura muku, daga baya sai kuje ya warwarema iyayenki komai, yakika gani?”.
“tabd'i, wannan wace irin maganace saikace labarin Novels ko films? to tayayama za'ayi hakan yafaru? bayan nama sanarma iyayena banida wata alak'a dashi”.
Murmuahi Muftahu yayi, yace “dan wannan duk mai sauk'ine, kedai amincewarki kawai muke nema”.
“amma dai kun maidani wawuya wlhy, to ban aminceba, gara na dawwama banyi aureba ai”.
Baki Muftahu ya bud'e zai k'ara magana Galadima ya d'aga masa hannu alamar yayi shiru ya barta.
“kinga tashi kije kawai, amma wannan maganar tazama iyamu ukunnan, idan najita awani waje saina zubar miki da hanjin ciki waje, duk shawarar dakika Yanke da zuciyarki zaki iya nemanmu daga nan zuwa kwana biyu kawai”.
Da sauri Munaya tazaro idanu waje tana kallon Galadima.
Harara ya zuba mata yace “karki cinyeni”.
Baki ta zun6ura gaba tana k'unk'uni, bayajin mitake fad'a, sai motsin la66anta kawai yake gani.
Sai da aka rufemin iso sannan aka baro gidan dani, bankuma kwanceba saida motar ta tsaya, Wanda yake tare dani yacire k'yallen sannan yace na fita.
Ko kallonsa banyiba saboda tsoro nafice amotar da sassarfa.
Gudu-gudu sauri-sauri na Isa gidanmu, mutane sai kallona sukeyi, ALLAH ma yasoni babu kowa a tsakar gida, inaga matan gidan duk sun shige sallar magriba yaran kuma basu dawo daga islamiyya ba.
A 6angarenmu ma innarmu na d'akinta, hakanne yabani damar shigewa d'akinmu wuff, na iske Munubiya na barci itama, na sauke ajiyar zuciya mai k'arfi ganin ALLAH ya tsareni babu Wanda ya ganni, kayana nacire daketa kamshin turaren Galadima, bayi nashige nida kayan, nayi wanka sannan suma na wankesu na shanya a bathroom d'in.
Harna fito Munubiya bata tashiba, nayi sallar magriba sannan nafito wajen innarmu.
Da mamaki take kallona, “yoni har ina shirin kiranki naji lfy baki dawoba had dare yarufa?”.
Zama nayi ina murmushin yak'e, dan abinda yafaru tsakanina dasu Galadima d'anzu ya min kane-kane a zuciya. ganin abin nakeyi kamar a mafarki. “ayya innarmu ai tun d'azun nashigo, lokacin kina salla, harfa nayi wanka ma nad'an huta. tace tana gidaki, yaya jikin Munubiya?”.
Jikinta Alhmdllh, tad'an watsa ruwa takoma ta kwanta bayan taci d'an abinci”.
To Almdllh, ALLAH yak'ara afuwa.
Amin innarmu ta amsamin, daganan muka koma hirar gidan Inna lami.
Munkai tsawon lokaci afalon muna hira da innarmu, sai dai nifa bama fahimtar hirar nakeba, dan fili kawai nakeson samu nayin tunanin maganar su galadima.
★★★★
Tun bayan tafiyar Munaya Galadima yakoma kan doguwar kujerar yay kwanciyarsa tamkar mai barci.
Muftahu dake kallonsa yace, “Amma miyasa kace ta tafi? batareda ta bamu gamsashshiyar amsa ba kuma?”.
Shiru Galadima bai amsaba tsawon mintuna uku, sai zuwa can yabud'e idonsa yana kallon Muftahu, baki yad'an ta6e “karka damu kanka, tama yarda, amsa ce kawai bata bamuba, itama kuma zata bayarne, tuni naga yardarta cikin kwayar idonta, akwai abinda take shakku akansa shiyyasa tak'i amsa mana”.
Kai Muftahu ya jinjina kawai, yasan tunda Galadima yafad'i haka to hakanne kuwa, amma sai yace “to amma bamu bata koda number ba, tayaya zata sanar damu amincewar tata kenan?”.
Murmushi kawai Galadima yayi baice komaiba.
Hakanne ya tabbatarma Muftahu murmushin Galadima shine amsar tambayarsa. Daga nan bai sake cemasa komaiba shima.
Falon yay tsit.
★★★★
Gaba d'aya a kwanaki biyunan banida wani sukuni, tunanin maganar yak'i barin zuciyata, a kowacce dak'ik'a zuciyata tunzurani takeyi akan Na amince kawai, dan banida wata mafita sai wannan, ni kaina inason sanin Wanda ya aikata mana wannan abun, sannan bana fata sauran 'yan uwana suyi aure su barni a gidannan, hakan ba k'aramin tozarci zai zamarminba, ga Munubiya tadage akan innarmu ta sanarma Abba itama ad'aga bikinta har saina samu miji nima ahad'a ni da ita, na nuna mata 6acin raina akan maganar amma abanza, tanuna Sam ita tana a kan bakanta, nikuma harga ALLAH ba zanso hakan ta kasanceba.
Ita kanta innarmu nakula danne zuciyata kawai takeyi akan fasa aurena, amma tana cikin matsananciyar damuwa.
Yanzu yazanyi kenan? Na amince ko karna amince? gashi ya gargad'eni akan kadda Na nemi shawarar kowa, ni kaina nama kasa sanarma koda Munubiya, kuma kullum cikin tanbayata take mike damuna? duk da ita zatonta akan maganar Haidar ne har yanzu nake cikin damuwar.
Yau dai kwanaki biyu kenan da faruwar abin, har yanzu kuma nakasa tsayawa a matsaya d'aya.
Kusan tashin hantsi muna tsakar gida a baranda muduka 'yan matan gidan, kowa da hidimar dayakeyi, sai wasu daga cikin k'annenmu dake wasa agefenmu, iyayenmu kuma Na daga can k'arshen barandar suma kowa da hidimarta, innarmu ce kawai babu tana gidan mama Rabi'a taje duba feena da jikinta yad'an motsa.
Tsayuwar mota mukaji a k'ofar gida, yara suka tafi da gudu dansuga wanene? azatonsu cikin su Dady ne.
Mintuna baifi 10 ba saigasu suna shigowa da ledoji, saikuma ga Zarah tashigo cikin kwalliyar kece raini, tana taku d'ai-d'ai, daka ganta kaga mai yaron ciki, cikeda muran muka hau mata sannu dazuwa, itako saiwani ciccijewa take tana kuma Jan kai, ita adole matar manya.
Abin kallo bai k'areba saida mamansu yaa Hameed ta iso da d'an gudu ta rungume Zarah a jikinta, duk mukai galala muna kallon wannan sabon salo.
“masha ALLAHU Zarah sarkin haske, kinganki kuwa, da anganki anga matar manya yarinyata, kai ai aure Ni'ima ce babba, duk wacce ALLAH yabama 'yarta miji matan gidannan ta godema ALLAH, Dan wlhy yana sonta”.
Caraf Momy Hadiza ta kar6e da fad'in “wlhy kuwa Yaya, ai babu babban bak'inciki irin kanada gandamemiyar budurwa a d'aki tayi kwantai takasa auruwa, aimu sai godiyar ubangiji wlhy, babu ta inda ni'ima bata saukar manaba, Zarah zoki zauna ki huta kinji 'yar albarka”.
Maman safara'u da gwaggon haleema da maman su Fiddausi suka kwashe da dariya.
Kowa yasan damu ake wannan gugar zanar, amma sai mukayi murmushi kawai bamuce komaiba, maman fauziyya ma batace komaiba, nama godema ALLAH da innarmu bata nan balle ranta ya 6aci.
Tsam namik'e nabar wajen zuciyata Na suya, Na danne kukan dake shirin tahomin...
Maman Safara'u tace, “to yanzu ke bazaki iya danne zuciyarki ba saikin nuna hasaadarki a filin ALLAH?, to Ashe ranar auren 'yan uwanki mutuwa kuwa zakiyi?, dan kina gani za'a d'auke kowacce abarki agidan.
Wani k'arfine yazomin a zuciyata, Na had'iye kukana, najuyo ina kallonta ido cikin ido, wani murmushin takaici nasaki, sannan nace “maman Safara'u ke uwace agareni, sannan innarmu takoya mana tarbiyyar girmama kowacce mace agidannan, badan hakaba dana fad'a miki maganar dabazaki ta6a mantawaba, kuma ba hassadar tasani tashiba kamar yanda tunaninki yabaki, natashine Na d'aukama Zarah ruwansha, naga tashawo rana kuma babu Wanda yayi yink'urin bata”.
Ina gama fad'ar haka nabar wajen. tsit banji kowa yasake maganar ba, bansan miyasa ba, maganar tawace tasakasu yin shiru kokuwa oho.
Ina shiga falonmu Na fashe da kuka, anzo ga6ar da kawai zan amince da buk'atar Galadima, insha ALLAHU aranar datake fad'ar za'a tafi abarni, aranar nima zanbar gidan, Na gwammace nayi auren shekara d'ayan nafito.
Tunanin tawace hanya zanbi Na fad'ar musu Na amince na farayi, dan basu bani number ko wata hanyaba dazan iya nemansu, gashi kuma bazan iya gane gidan dasuka kainiba.
Tunawa dawata farar takarda nayi, wadda nagani a bag d'in dana fita da ita a ranar, kuma nasan ni bani Na ajiyeba.
Da Sauri Na d'auki bag d'in na zazage, saiga takardar tafad'o, na d'auka na bud'e, Number wayace ajiki kawai.
Jikina har rawa takeyi na d'auki wayata na kwafe number, sai kuma nakasa kira, na fara zagaye d'akin.
Motsi naji kamar na tafiya, da Sauri na shige bathroom d'inmu dan nasan Munubiya ce.
fanfo na kunna yanda zata d'auka wanka nakeyi.
Sha warar tura massage kawai na yanke. dan haka na rubuta
*_“na amince inhar bazai zama ka wulak'anta rayuwa taba”._*
Haka kawai natura masa na cire kayana nafara wankan gaskiya...........✍🏼
⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀time d'in wasa yafara.🤸🏻♀
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*👏🏻😭
*_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻1⃣7⃣
.........Cikeda girmamawa yace, “Ranka ya dad'e barka da dare?”.
“barkan ka dai Muhammad. dama kashigo k'asar kenan?”.
Gabansa yad'an fad'i, danshifa yama manta mai martaba baisan yazo k'asarba, dakiyar dole ya aro yace, “wlhy kuwa nashigo d'azun yin wani aiki, amma gobema idan ALLAH ya kaimu zan koma”.
“tofa, gobe gobe? kuma gashi inason ganinka a goben”.
d'an jimm yayi, irin tamkar baisan komaiba, cikeda shakku yace, “ranka ya dad'e lafiya dai ko?”.
“lafiya k'alau, wata muhimmiyar magana nakeson muyine”.
“to shikenan, zanshigo insha ALLAH ”.
“to madalla saina ganka”.
Dafe kai Galadima yayi yana mamakin kansa, anya kuwa baima kansa d'aurin gorobo? koda yake idanfa yayi hak'uri shekara 1 ne ko 2 kacal, inma komai yafito kafin cikar shekarar zai sawwak'a matane, yad'an murmusa sannan yakoma ya kwanta abinsa cikeda tunani barkatai.
★★★★★
Rashin reply d'in Galadima ya dameni, haka dai naita danne zuciyata dankar innarmu da Munubiya su fahimta, nacigaba da harkokina tamkar banida wata damuwa a zuciya, saima sallar dare damuka fara dagewa da tashi nida Munubiya, gakuma azumin damuka tashi dashi yau litinin.
Duk da innarmu ta fahimci inada damuwa batacemin uffanba, saidai tausayina na damun zuciyarta, tana dannewane kawai.
Munubiya kam tsaf tagama fahimta ta, amma itama saita nuna bata fahimci komaiba, taje tasamu innarmu da maganar son a d'aga bikinta again.
“munubiya ba wannan yakamata muyiba, addu'a yakamata muyima 'Yar uwarki, idan da rabo saikiga ALLAH ya kawo mata miji a cikin watanni 2nan dasuka rage kinji. nima nasan tana acikin damuwa, amma tana dannewa a zuciyarta saboda farin cikinmu. addu'ar dazamu mata itace tsantsar k'aunarta a garemu”.
“shikenan innarmu, insha ALLAH zamu kuma dagewa da fad'ama ALLAH, itama ALLAH ya kawo mata ta hanyar da batayi zatoba, ya sakanka mata fiyeda sadaukarwar datayi, innarmu nasan sadaukarwar da 'Yar uwata tayine yasakata a wannan halin, ta sadaukar da farincikinta saboda ni, mizanyi na biyata nikam”.