Showing 99001 words to 102000 words out of 382522 words

Chapter 34 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2966

naje”. ‘nayi maganar tamkar zanyi kuka’.
Banza yamin, saida yamula dan kamsa sannan yabud'e idonsa a kaina yana hararata, “ki nutsufa, ko an fad'a miki haka akeyi?”.
Baki na tunzuro gaba.
Ya janye idonsa daga kallona yana kuma matse hannuna cikin nasa.
Ni ban saniba Ashe wai dole sai an nema masa ison shiga gidan namu, sarkin mota dai tuni yafita dama.
'Yan anguwarmu sunyi cirko-cirko suna kallon motocin, jira kawai suke suga Wanda zai fito aciki, dukda sunga masu jajayen riguna a tsaitsaye, alamar daga masarauta ne.
Muna a haka saiga yaa hameed yafito daga cikin gidanmu dad'an hanzarinsa, inaga yazo gaidasune, dan kullum Safiya duk sai sunzo shidasu yaa Shafi'u.
Jikin motar damuke ya k'araso, sarkin k'ofa yay knocking d'in glass d'in 6angaren Galadima. duk da yasan yana kallonsu shi.
Sauke glass d'in yayi a hankali, sannan yama sarkin k'ofa nuni daya bud'esa, har yanzu hannuna yana cikin nasa kuma. Ya d'auki hularsa ya saka.
Cikeda fara'a Yaa Hameed yake masa barka da zuwa, sai lokacin ya saki hannuna, sannan yazura k'afarsa d'aya yafito, nima dogari d'aya yazagayo da sauri yabud'emin, na fito, handbag d'in hannuna dogarin ya kar6a yana zubomin kirari.
Kallofa Yakoma sama ga 'yan anguwarmu, kowa sai kallona yake yana fad'in ashe munaya Ce, kai masha ALLAH, kugafa auren sati d'aya harta canja kamanni, lallai sarauta dad'i.
Inda yaa Hameed da Galadima suke na zagayo, suna rik'e da hannun juna sunyi musabaha, fuskar yaa Hameed a washe, yayinda ta Galadima ke d'ukeda wani munafukin murmushi.
Cikin murna nace “yaa Hameed I miss u”.
“miss u too Darling sister. bismilla ranka ya dad'e kumuje ciki to”.
Atare muka shiga ciki, ina gaba suna bina a baya shida yaa Hameed.
Matan gidanmu kowacce na mak'ale jikin window d'inta tanason ganin Galadima, yayinda Aryaan da Aiyaan suka shek'o da gudu kaina, ganin haka suma sauran yaran sai suka shek'o, duk na tarbesu cikeda farinciki da kewa.
Ni nama manta dawani Galadima muke tare, Ashe shi yanata kallonmu cikeda sha'awa.
yaa Hameed yamasa jagora zuwa falon Dady.
Nikam ai d'akin Innarmu sha, tareda gayyar 'yan tarbata.
A zaune na iske innarmu tana ninke kayan su Aryaan, da alama wankewa tayi, sai tausayinta ya kamani, yanzufa kowanne aiki dole itace zatakeyi, babu mai tayata, jikinta na fad'a ina hawaye.
Itakam tace “kajimin ja'irar yarinya, to miye abin kukan kuma? wai nikam yaushe kika lalace da sauri kuka haka Munaya?”.
“innarmu kewarku cefa wlhy”. nashiga gaidata, cikeda farincikin yanda na koma a kwana 6 kacal take amsamin, sai jero hamdala take a zuciyarta.
Zainab k'anwar Fauziyya tashigo d'auke da tire an d'oro zo6o da ruwa akai.
“inyee, kaga su zee anzama 'yan matafa, kace bad'i sai aure kenan?”.
Fuskarta ta rufe tana fad'in kai Aunty kibari please, innarmu kice ta daina”.
Innarmu dariya take mana itakam, saiga Rahma itama tashigo, saiga Ameenatu da Khadija ma, lallai bad'ima Ashe zamu aurar da yawa, a kwana ki 6 d'innan sainaga yaran duk sunmin girma a ido. Nasha mamakin su na zuwa gaisheni, dan bansa akaba nikam, araina nace ko jama'ar gidanmu dun fara canja haline dai?.
Muna haka saiga innaro tamkar an jehota, kowa ido ya zuba mata, dan shigowa tayi tana masifar wai bamu fara shiga gidan taba nida Galadima.
Na kalleta a d'age ina ta6e baki, “yo banda abinki innaro ai sai nafara ganin Uwata, dan banida kamarta kaf duniya”.
Ha6a tarik'e tana kallona “eh lallai kam, yo ai Dama ke halin uwarki gareki, ba mutuncine dakeba, ballan tana yanzun kuma ido yak'ara fetsarewa ansan komai na aure”.
Zan maida mata murtani innarmu ta harareni, shiru nayi na k'yaleta badan nasoba.

Shima Galadima yana falon Dady yasamu tarbar mutunci daga maman Fauziyya, dan matan gidanmu babu wadda ta aika masa dako ruwa, yaji dad'in tarbar daya samu kuwa, musamman yanda su Abba suka nuna masa tamkar d'ansu, baiyi dubi da sarautar dake kansaba ya duk'a har k'asa yakwashi gaisuwa wajen iyayena uku.
Hakan yamusu dad'i, domin ya mutuntasu, kuma sun kuma tabbatarwa shid'in mai tarbiyyane.
Anan yamusu bayanin munzo musu sallama ne zamu tafi India.
Fatan alkairi su abbanmu sukai mana da k'yak'k'yawar addu'a, daga nan sukad'an ta6a hira dashi, dukda yana nonnok'ewa saboda kunya irin ta jinin hausa Fulani.
Nikam can innarmu ta iza k'eyata nashiga kowanne d'aki na gaidasu, sai kallon k'urulla suke bina dashi, anason ganin wata makusa a jikina, amma sai basuganiba kuwa, komai sai sambarka. Aikam bak'in ciki tamkar ya karsu, kowa hassada nacin zuciyarsu (kai jama'a ALLAH yarabamu da cutar hassada komai k'ank'artatta😢🙏🏻)
Na dad'e d'akin maman Fauziyya sosai, dan acanma naci abinda tad'an girka mana mara nauyi, yaa Hameed yazo ya d'auki na Galadima da kansa.
Sashenmu na dawo inatama innarmu shagwa6a, duk nabi na nanik'e mata, dukda tureni datakeyi. Nashiga tsohon d'akinmu harda kukana, komai nanan yanda yake, harma dawasu 'yan tarkacenmu daba a gama badawa ba, haka kawai bamu mutuba d'akinmu Yakoma kango, anan na d'akko cajata da wayar Galadima daya barmin a filin idi, sai wad'ansu 'yan abubuwa danake buk'ata.

Na fito ina tambayar innarmu waye ya d'auki wani hotonmu dake saman mirror nida Munaya?, tacemin maybe Ameeran inna lami Ce ko Bilkisu, dan taji suna rigima akan d'aukar Horton.
Shigowar Galadima da yaa Hameed tasaka innarmu yin shiru, nikam ban daina daddaga k'afa k'asaba ina k'unk'unin miyasa tabari suka d'auka?.
Galadima dake k'ok'arin zama yad'ago ido yad'an kalleni sannan ya janye.
Yaa Hameed ne yace kekuma lafiya?.
Fad'a masa nayi tamkar zanyi kuka, yace “to kuka zakiyi?”.
“ALLAH yaa Hameed inason hotonfa”.
“ai saiki hak'ura yanzun tunda sun d'auka ko?”.
Innarmu da Galadima dai gaisuwa sukeyi, babu Wanda ya tanka mani. shi saima mamakin ta6arar danakeyi yake a zuciyarsa.
Nikam bansan yana yiba.
Sosai yaji innarmu ta burgesa, yakula ko kad'an ba halinta nabiyoba, dan ita tanada sanyi, dagani batada hayaniya, amma nikam ai sai addu'a.

Yad'an jima anan dukda ba hira sukeba, kowa kunya na cinsa, a raina nace dama yanda kunya guy d'inan ashe?.

Alkairi mai yawa ya ajiyema innarmu, dawata leda da yaa Hameed yabiyosa da ita, sannan yafita innarmu na saka masa albarka yana amsawa cikeda jin dad'i, jinta yake tamkar Momma d'insa.
Daga nan saida yashiga kowanne d'aki, sannan yaa Hameed ya rakashi gidan innaro.
Abba ne yashigo yana fad'in a tattaro lefena muwuce da kayanmu.
Na marairaice fuska nace Abba abarsu anan, kagaba tafiya zamuyi can d'in babu kowa.
“a'a Munaya bazai yuwuba, idan mun ajiyesu anan mizamuyi dasu?, kitafi da kayanki, duk randa dai kuka dawo suna d'akinki ai.
Badan nasoba na amince, amma naje wajen kayan ina fitar da wasu, ni saima yau naga lefen, gaskiya su Galadima sun zuba kud'i a wajennan.
Duk matan gidanmu atanfofi na fidda musu, maman fauziyya kam guda biyu, sannan yaran gidanmu 'yan matan yanzu kowa nafidda masa wani abun, su Aryaan ma dukda mazane kowa na fidda masa abinda zai iya amfani dashi.
Sai su Ayusher da inna lami da Ameera, Bilkeesu ma da nata, hakama mama rabia, na ware akwati guda na lodama Munubiya kaya sosai aciki, aunty salamah ma da nata, sai gwaggo Safiyya da yaranta mata, itama innaro jarabatu na fidda mata, su Abbanmu ne dai narasa mizan basu aciki.
Innarmu na kira tagani, ta kalleni tana fad'in “munaya bazasuga an kwashe kayanba?”.
“a'a wlhy innarmu bazasu ganiba, kowafa da sashensa a gidan, kuma babu mai shiga harkar wani, idan na barsu mizanyi dasu? Kayan sunmin yawa ai”.
“to shikenan, ALLAH ya saka da alkairi”.
Na amsa da ameen ina fad'in “ganaku nan keda su Aiyaan innarmu”.
“a'a ni bazan d'auki komaiba, bakiga yama kawomin abuba, ga kud'i dama bansan ko nawa bane”.
Kuka na Sanya mata akan saita kar6a, babu yanda ta iya ta amsa, amma saida tarage. Sai dai tana fita na maida mata harda k'arima.
Zainab Ce ta kaima kowa nasa, kowacce rai babu dad'i ta amsa, sotayi ace daga 'ya'yantane wannan abun arzik'in yafito bawai innarmu ba, (basusan shi Ubangiji babu ruwansaba, yakan azurta Wanda yaso Yakuma k'ask'antar da Wanda yaso a lokacin dayaso).
Babu wadda tazo godiya sai maman fauziyya, nace “oho dai, aikin banza wai talaka ya girmi sarki🤷🏻‍♀”.
Banyi maganar su d'auki motarba, dan sonake nasami cikon d'ayar nabasu su duka ukun.
Nima naje na gaida innaro, dasu Abbanmu, naje gidan innaro lokacin su Galadima harsun fito,, na iske Ashe gwaggo Safiyya tama koma jiya, sai d'iyarta Habiba datake zawarci aka bari anan.
Munsha hira da ita, tanata yaba k'yan da nayi.
Innaro kam dukda jana datake ajiki sai basar da ita nakeyi, amma hakan bai hanata yaba Galadima ba, catake wai na more miji, nafi kowa morewa a gidanmu.
Nidai banda ta6e mata baki da bak'ar magana babu abinda nakeyi, bata damuba saboda neman gindin zama take ajikina.

Bamu baro gidanmu ba sai gab daza'a shiga sallar juma'a, an taho da motata da lefena, duk kayan daza'a bana mutane kuma na barsu a can, harna Munubiya.
Su Abba sunsha alkairi awajen Galadima Ashe, hakama matan gidanmu d'akin kowacce daya shiga saida ya ajiye alkairi, sunata kukan zuci da fad'in inama-inama 'ya'yansu ne a wannan daular🤣🥴.
Zamu shiga motane ina sharar kwalla baba k'arami yace namusu godiya wajen Galadima, kaina kawai na iya d'aga masa.
Innarmu bayan tafiyarmu har 'yan kwalla tayi, matan gidanmu kam duk haushinta sukeji, idan kacire maman fauziyya.

Daga nan gidan Munubiya muka nufa, amma anan bai shigaba, yace naje zuwa anjima zai dawo mutafi, dan yanzu zaije sallar juma'a.
Kai na kawai na d'aga masa, nafita bayan dogari d'aya yabud'emin k'ofa, basu bar gate d'inba saida sukaga na shige ciki, ya maida kansa jikin kujera ya kwantar tareda lumshe ido, abinda yafaru a gidanmu kawai yake tariyowa, yakula family nawama sai a hankali dai. Sunada shigen irin halallayyar family d'insa.

Nikam da gudu nashiga ina kwala kiran sunan Munubiya, itama yafito aguje muka rungume juna, sai muka fashe da kuka kawai, ALLAH ma ya somu yaa Marwan yarigada yafita masallaci.................✍🏼



*_Masoya bansan yanda zan nuna muku tsantsar farin cikinaba, amma tabbas inajin dad'in Comments naku, kuyi hak'uri da rashin amsawata d'ai-d'ai, kunmin yawane wlhy, ga massages na PC, idan kuma nagama typing d'inan kaina d'aukar zafi yake, ko son ta6a waya banayi wlhy, naga wasu suna d'auka kamar wulak'ancine rashin amsawar, wlhy ba haka bane, kumin afuwa da uzuri please & please, duk da nasan bazan iya k'yautatama kowa acikinku yanda yakamata ba, dole wani yaga gazawata koyayane tawani fannin😄._*






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*



*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_




*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_




*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



👉🏻2⃣8⃣


...........Bansan yanda zan musalta muku farin cikin damuka tsinci kanmuba nida 'yar uwata Munubiya, abin kawai ba'a magana.
Duk da bata yarda zan zo d'inba amma bata fasa tanadar min duk abinda tasan inasoba, tarasa inda zata sakani dan dad'i, gaskiya gidan munu yayi k'yau sosai, gashi an cika ko ina da kaya, kasancewar harda nawa aka had'a mata, muna yin salla muka 6arke da hirar yaushe gamo, a haka yaa marwan yazo ya samemu, yaukam abin mamaki naga fara'a a fuskarsa, nace lallai aure yayi citta kenan, yanda yake bama Munubiya kulawa sai abin ya birgeni, kamar Na lashesu kuwa Dan dad'i. Haka muka yini muna tad'i har lokacin sallar la'asar yafita salla.
A lokacinne aunty Salamah tazo gidan, Ashe Munubiya ce takirata ta fad'a mata zamu tafi India yau da daddare, mun tarbeta da murna sosai, yayinda ita kuma taketa yaba wai munyi k'yau. mukaita rufe fuska alamar kunya.
Shawarwari taita bamu akan rayuwar aure da yanda zamu tattali mazanmu, babu ko kunya take 6aro mana komai, sai mune muketa sunkuy da kai, itakam ko a jikinta, ta rarraba mana wasu buks da ke d'auke da abubuwa masu amfani dazasu bada gudunmawa a zaman takewar aure, nidai bawai na d'auki nawa da muhimmanci baneba.
Wajen 5 tatafi, tafiyarta babu dad'ewa saiga Galadima da yaa marwan sun shigo, Ashe wai ya dad'e a k'ofar gida zaune, ya kira yaa marwan yace baya gida amma gashinan zuwa.
Shine yajirashi amota harya iso suka shigo tare. Sun gaisa da Munubiya a mutunce, ta shirya musu abinci, da yace yagode sauri yakeyi, amma munu ta marairaice wai yaza'ayi mijin 'Yar uwarta yak'i cin abincin gidanta, in baimasa baneba ta sake masa.
Murmushi yayi ya zauna yaci kad'an, yayinda mukuma muka shiga d'aki dan mu basu waje suci abincin, d'an kuskus d'inmu mukayi muma, takuma kwantar min da hankali akan auren nawa da wasu 'yan shawarwari, da nunamin fushinta akan abinda nace nama Galadima d'in, ta nunamin wannan ba tarbiyyar da iyayenmu suka bamu baneba, gaskiya karna sake irin haka, kuma nabashi hak'uri akan hakan, nace “to amma tayaya zan basa hakurin?”.
'Yar takarda ta d'auka tayi rubutun tabani wai nabashi.
Na kar6ane kawai badan ina tunanin zan bayar d'inba, duk da nasiharta ta shigine gaskiya, kuma nima tun a ranar nayi nadamar ce masa azzalumin gaskiya, Duk da nasan a cikin fushine Nima Na fad'a, Dan nashiga rud'ani sosai akan abinda yayimin daban zataba.
tabani kayan da aunty salamah takawo a Leda, batareda na dubaba na amsa.
Itama k'yauta mai tsoka yamata sannan muka fito, nida ita kowa yana sharar kwalla, bamason rabuwa da juna, amma yazamuyi? aure ya rabamu.
Daga nan gz yaa marwan muka nufa gaida mama rabi'a, namayi mamakin yanda yasanta, nankam tare muka shiga, su Ayusher suka rukunkumeni cikin tsantsar farinciki da kewa.
Bamu dad'e sosaiba itama ya ajiye mata alkairi muka fito, su Feena ma yabasu kud'i wai su sai kayan kwalliya, hakama Ahmad, yaa Fadeel dai mun tarar baya nan, yakoma inda yake bautar k'asa.
Nanma saida nayi kuka dazamu taho.
Saida muka shiga mota ina sharar hawaye sannan ya kalleni cikeda k'asaita yana ta6e baki, “ke wai bak'ya tsoron hawayenki su k'are ne?”.
Bance masa komaiba nacigaba da kukana, shima saiya shareni.


★★★***★★★


Koda muka isa Masarauta bamu wuce sashenmu kai tsaye ba, wasu 6angarorin gidan mukaje mukai musu sallama, harda sashen mama Fulani, yauma dai babu magana mai dad'i tsakaninta da Galadima, nifa lamarin nasu na d'aure kaina gaskiya.
Mai martaba kam munsha addu'a a wajensa, sannan muka fito.
Mun shiga sashenmu ana kiran sallar magriba, zan shige yace “kiyi azamar shirya kayanki trolley d'aya, karki wani kwashi kaya dayawa”.
Da to kawai na amsa nayi shigewata ciki.


*_7:30pm_* Muka bar masarautar, nida shi da Samha motarmu d'aya, muna baya tana gaba.
d'ayar motar kuma Sauban da aunty Mimi da khaleel ne aciki.
Mun sami rakkiyar Harun da Muftahu sai wasu k'alilan daga masarautar.
Tom nidai ba k'auyace a airport, dan banta6a shiga jirgiba, amma kunsan mutuniyar taku da Jan aji,🤨 saina Fiske abina nima inajan citta tamkar wadda ta saba.
Duk abinda yadace ayi anyi mana, musamman ma ni danake sabuwar fita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login