Showing 30001 words to 33000 words out of 382522 words

Chapter 11 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2909

bayani dalla-dalla. “tad'ora da fad'in kinsani ko saboda galadiman yayi?”.
“to amma Dan zaima Galadima mu miye Na had'awa damu kuma?”.
“wannan amasar tana wajen Fu'aad sister ”.
Hankalin Munaya yatashi ainun, itafa ko kad'an bata ta6a kawo Fu'aad acikin wad'anda take zargiba, amma maganar Ayusher tasata dogon nazari yanzu, duk da dai bawai tama yarda baneba kwata-kwata..



★★★★★★★★★★

Lokacin da harun ya iso sashen Galadima bai wani jira isoba yashiga, kwance ya iskeshi bisa 3seaters sam6al, hannunsa d'aya dafe da k'irji, d'aya dafe da kansa.
Da sassarfa ya k'arasa gabansa “Sameer lafiya kuwa?”.
Da hannu Galadima yamasa nuni da k'irjinsa da Kansa.
“ya salam, Sameer! Shiyyasa naketa cemaka kacire abunnan a ranka, kafasan matsalarka batason yawan takura da tunani”. Wayarsa dake ringing ya Ciro a aljihu, Momma Ce ke kiransa.
Cikeda girmamawa ya amsa sallamar data masa, sannan naji yace, “wlhy Momma bashida lfy, kuma k'irjinsa yake complain akai”.
“ok Momma ”.
Yana yanke wayar sai yayi kiran Dr Jalal.
“Jaalal please kana gida kuwa?”.
Bansan wace amsa ya bashi ba daga can, naji dai yace, “please kazo kaduba Galadima”.

Babu dad'ewa saiga Dr Jaalal, damuwa sosai Nagano a fuskarshi saboda ganin halin da Galadima yake ciki.
Harun ya taimaka masa suka kaishi bedroom, sannan yamasa allurar barci.
Babu dad'ewa kuwa barcin ya kwasheshi.
Su duka ajiyar zuciya suka sauke, Dr jaalal yama harun sallama yatafi.
Yana fita Muftahu Na shigowa, gaisawa sukayi da Harun, sannan ya tambayi jikin Galadima d'in.
Harun ya amsa masa Cesar da sauk'i.

Anan sashen Galadima suka kwana, sai dai kowanne acikinsu da dalilin kwannan nasa.

*_Washe gari_*

Alhmdllh Galadima yatashi jikinsa da d'an sauk'i, yakuma ji dad'in ganin Harun da Muftahu a tare dashi. bai iya zuwa masallaciba sai a d'aki yayi salla.
Yana zaune akan sallayar yana azkar su Muftahu suka shigo, zama sukayi bisa Sofa suna jiran yak'arasa azkar d'in nasa.
Bayan ya k'arasa ya juyo garesu, hannu ya mik'a musu sukayi musabaha, suka tamyashi jikinsa.
Yace da sauk'i Alhmddlh, sannan yace, “Muftahu inason ticket, dan yau zan wuce India, ina buk'atar ganin doctor d'ina”.
“ok babu damuwa, bara na bincika idan akwai jirgi mai zuwa India daret”.
Harun yamik'e yana fad'in “bara ahad'a maka ruwan wanka to”.
Kai ya d'agama harun, ya maida idonsa ya lumshe tareda jingina da Waldrop.
Muftahu dake latsa waya yad'ago ya kallesa, “babu jirgin dazai tashi a yau, sai gobe 1:30pm”.
Batareda ya bud'e idonsa ba yace, “bincika min ta Abuja ko legos. dan bazan iya kuma kwana a k'asar nanba yau, ina buk'atar ganin lilita”.
Kai Muftahu ya jinjina ya cigaba da latse-latsensa a wayar, kusan mintuna 4 sannan yad'ago, “an samu, amma zai biya Abu-Dhabi ya sauke Passenger's, daga nan zasuyi hutun kamar na 1hour”.
Idomsa a lumshen yace “yaushe zai tashi daga Nan?”.
“12pm, yanzu na saya maka ticket d'in zuwa Abuja, jirgin zai tashi 8am ne”.
“Ok bara na shirya to”.
Harun dake tsaye yana saurarensu yace “bara naje Na watsa ruwa nima”.
Shima Muftahu mik'ewa yayi suka fita tare.
Galadima yashiga bathroom, kusan mintunansa 40 sannan ya fito, dauriya kawai yakeyi, amma shi kad'ai yasan irin suyar da zuciyarsa ke masa. tsaf ya shirya cikin Suit blue, rigarshi ta ciki Orange, yayi k'yau sosai, yana zaune bakin gado yana saka takalminsa Muftahu yashigo da sallama.
d'ago idanunsa yayi akan Muftahu, sannan yatashi tsaye yana gyara belt nashi, “ya maganar binciko yarinyar nan?”.
“Nagama komai, inason kasami nutsuwane sai muyi maganar daman”.
Galadima dake gyara 'yar sumarsa da bawani yatarata da uban yawa bane yace “ok, katura min komai zan duba, sannan inason kaje kuyi magana da commisshiner of police akan iyalan Manager d'innan”.
“ok yalla6ai angama insha ALLAH”.
Sallamar Harun suka amsa gaba d'aya, ya zauna kan sofa sannan yace “amma yakamata ma'aikatan plaza su koma aikinsu, naga jama'a kamar suna fassara abin dawani Abu daban kuma”.
Murmushin gefen baki galadima yayi, ya ajiye Cumb d'in hannunsa yajiyo yana kallonsa “aini yanzun kuma babu kuma ta sigar dabaza'a fassara ni ba, inaga akan mace kawai yarage jaridu su buga duniya ta ganni, so sukoma aikin su kawai”.
Daga Harun har Muftahu kallonsa suke cike da tausayawa. Muftahu yace wannan d'inma kansu sukai mawa, kuma ALLAH bazai barsuba”.
“insha ALLAHU”. ‘cewar Harun’.
Galadima baice komaiba, sai d'an kimtse kimtsen da ba'a rasabane ya k'arasa, su Harun kam suka fice suka bashi waje.
Baifi mintuna 10 ba yafito suka fice, bayan yatsaya da bayinsa na mintuna biyar, bansan miya fad'a musuba, naga dai sunata faman godiya damasa addu'a.
Aka bud'e masa mota yashiga, duk wanda yake k'ark'ashimsa saikaga fuskarsa ta canja alamun baya son tafiyar tasa.

Kai tsaye fada suka nufa, bayan motocin sun tsaya aka bud'e masa yafito.
Shi kad'ai yashiga fadan, cike take da dukkan masu ruwa da tsaki anata fadanci.
Saida ya gaida sarki, sannan ya zauna mazauninsa kusada sarkin, sauran fadawan suka gaidashi cikin girmamawa, shima ya amsa cikeda mutuntawa.
“ya adalin sarkinmu yau zan koma inda na fito, saboda inason ganin likitana”.
Murmushi sarki yayi, sannan ya gyad'a kai bare da yayi maganaba.
Da sauri Dogarawa suka d'auka da fad'in Sarki yajika Galadima, Yakuma amsa, yana maka addu'ar sauka lfy kuma.
“ina godiya da wannan alfarma”. ‘galadima yafad'a cikin rissinar da kai alamun girmamawa”.
Sarki yad'an gyara zamansa, ahankali ya furta “ka gaidamin da d'an uwana da gimbiya Zeenah, insha ALLAH nima nextweek ina nan zuwa”.
“ina godiya ranka shi dad'e, insha ALLAH d'an uwanka zaiji”.
“gyad'a kai kawai sarki yayi”.
“An gaisheka galasima, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka, ALLAH ya kaika lafiya yabama adalin tsohon sarki lafiya, Alkairin ALLAH da ni'ima sukai a garesa, gaba dai gaba dai Galadima mai jiran gado, d'an sarki jikan sarakuna k.....”.
Hannu ya d'aga musu alamar ya Isa.
Ya risinar da Kansa domin girmamawa ga fada sannan yamik'e suna jera masa addu'oi, yayinda shikuma yake amsawa asaman la66ansa.

Bai shiga sashen kowaba yay tafiyarsa, suna isa filin jirgi ko 20 minutes basuyiba jirgin su yatashi zuwa Abuja.
Muftahu da Harun da dogaransa suka dawo cikeda kewarsa.
Koda ya isa Abuja hotel yanufa kai tsaye, yakama d'aki danya huta, akwai kusan 3hours nan gaba kafin jirginsu ya tashi. Rigar suit d'insa yacire tareda tie d'in, sannan ya zame wandon da rigar cikin ya kwanta dagashi sai boxer da vest.
Juyi kawai yakeyi agadon, Dan barci yakasa d'aukarsa, abinda yafaru a kwanaki biyunnan yakasa barin zuciyarsa, yarasa wane irin hasashe zaiyi ga masu aikata masa hakan... Ringing d'in da phone nasa tayine yasakashi bud'e idanunsa, wayar yajawo yana kallon mai kiran. *_Sweet papi_* yagani ajikin wayar, yay saurin d'agawa kafin ta tsike.
Cikeda girmamawa tamkar yana a gabansa ya rissinar da kansa bayan yatashi zaune, “Barka da hantsi ranka ya dad'e”.
Daga can aka amsa “da yauwa Muhammad, ina fata kana lfy?”.
“Alhmdllh ranka ya dad'e”.
“To masha ALLAH, dama mamanka Ce takirani takemin wasu bayani, duk da kafin kiran nata dama naga zantukan dake yawo a jaridu da yanar gizo, zuciyata bata yarda zaka aikata hakanba Muhammad, amma inason sanin gaskiyar zancen?”.
“wlhy ranka ya dad'e sunyi hakanne kawai domin 6atamin suna, amma ainahin abunda yafaru shine.............”
Nan Galadima ya zayyane masa komai.
Murmushi mai sauti tsohon yayi, har Galadima Na jiyosa, sannan yace, “hummm! to yanzu kai kana wace nahiya ne?”.
“Ina Abuja zan koma India, saboda jikina yana Neman motsawa”.
“to to, hakanma dakayi dai-daine, amma a kwantar da hankali, komai mai wucewane, komai kaga yafaru da d'an Adam rubutaccene a littafinsa, dama ita rayuwa tana tafiyane da k'addara, yanzu zan isa fada, bayan kasamu nutsuwa idan kaje zamuyi magana, duk da watak'ilma nashigo ganin mahaifin naka k'arshen watannan”.
“to shikenan, ngd sosai, ALLAH yak'ara tsahon rai da lafiya mai amfani”.
“amin ya rabbi Muhammad” cikin tsokana tsohon yace “kaga d'annema, duk kabi ka susuce akan k'aramin Abu, kazo Na sanmaka jarumtata mana”.
Dariya Galadima yayai (karon farko danaga yayi dariya🙊😂) cikin tausasa harshe yace “haba dai, ai sai dai Na sammaka tawa, nifa sabon jinine, ta ina mai shekaru 80+ zai fi mai 29 jarumta?”.
Daga canma Sarki dariya yayi, cikeda k'aunar jikan nasa, “uhmyim tunda kace haka idan kazo saimu gwada kwanji ai”.
“hhh tom kafad'ama inno ta tsumaka sosai, inba hakaba zatayi takaba”.
“ja'irin gora zan kamakane ai, ALLAH ya tsare hanya, ka gaida iyayen naka”.
“zasuji ranka ya dad'e, a gaidamin inno, tayi hak'uri wannan karon ban shigo naci tuwon taba, nazo k'asarne da uzurori dayawa, gashima banyi ko d'ayaba”.
“zataji insha ALLAHU, babu komai, adage dai da addu'a watarana sai labari, *zakaran da ALLAH ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai yayi jikana kaji*.
Murmushi Galadima yayi dan jin maganar kakan nasa, sukayi sallama cikeda k'aunar juna”.

Ajiye wayar yayi yakoma ya kwanta fuskarsa d'auke da murmushi, yana k'aunar kakansa (mahaifin Momma) saboda shima yana nuna masa k'auna da kulawa, akan la66ansa ya furata “ALLAH ya k'aramaka tsawon rai my sweet papi”.


Amin Galadima.
⛹🏻‍♀bara nalek'o su munaya.




★★★★*★★★*★★★★

Bansan yanda zan musalta muku irin bak'in cikin danakeba a yau, tundaga kiran Fu'aad zuwa yanzu zuciyata sai suya takemin, banida wata walwala, sai dai ina dannewa kodan kwanciyar hankalin innarmu da 'Yar uwata Munubiya, dama tun randa abunnan ya faru bamu sake fita koda tsakar gidaba dagani har 'yar uwata, abinci sai dai innarmu kosu Aryaan su kar6o mana.
Habaici dai da gugar zana muna shanshi acikin gidanmu, innarmu bata cemusu uffan, nikuma mai maida murtanin damuwa ta hanani iya cewa komai, 'yan biki dai zuwa yau kowa yakama gabansa, yanzu dagamu sai mune agidan.
Sauk'inmu d'aya tun ranar innaro bata sake shigowa gidanba, inaga baba mai kanwa yahanata.
Babu Wanda yay mana maganar komawa makaranta, muma kuma bamuyi yunk'urin zuwanba, kullum dai innarmu NATA k'ok'arin ganin munkwantar da hankalinmu, a koda yaushe cikin mana nasiha take dayimana kwatance da rayuwarta itada mama Rabi'a, takan Nuna mana muhimmancin hak'uri da amfanin yinsa, koda baka ci ribarsa anan gidan duniyaba zakaci ribarsa a lahira inda kowa ke rububin tara ayyukan alkairi.
Alhmdllh muma mun fara rage damuwar kodan ganin farin cikinta, Abu d'ayane kecin zukatanmu shine maganar fidda miji da Abbamu yace nayi acikin sati biyu kacal, gashi kuma babu wani tsayayye a hannu.
Duk mun rame mun zuge nida munubiya, dama gamunan bawani aukin kirkiba, ahaka muka cinye satin da abin yafaru.

Yau ta kasance lahadi, wasu a yaran gidanmu sunata shirin ziyartar gidajen amare, kaf sa'aninmu 'yan matan gidan sunyi shirinsu, Fauziyya, Fiddausi, Safara'u, Haleematu, amma ban da mu, Dan kogaya mana mu shirya ba'ayiba, saima Fauziyya Ce data tashigo da safe gaida innarmu take sanar damu wai mushirya zamuje gidajen amare.
Dagani har Munubiya bamuce da ita komaiba, sai 'yar dariya damukayi.
Koda suka gama shirinsu basu nememu ba, sai Fauziyya Ce tashigo danta mana magana akan mufito.
Turus tayi Dan ganinmu babu wani shiri, hasalima muna falo zaunene, Munubiya ta kwantar da kanta bisa cinyata ina kwance mata kai, innarmu kuma Na zaune gefe suna waya da mama Rabi'a, sai Aiyaan da Aryaan daketa faman buga game.
Hira mukeyi da Munubiya akan wasu write-ups datake dubawa a Instagram da akayi akan maganarmu da galadima, cikin damuwa take karanta writeup d'in, shiyyasa bamuga shigiwar Fauziyya ba saida tayi magana...
“wai sisters kuna nufin ma ko shiryawa bakuyiba?”.
Gaba d'aya muka kalleta, nayi murmushi ina fad'i “kiyi hak'uri Fauziyya, kutafi kawai, har yanzu fita bata kamacemu ba, dan abubuwa basu gama daidaitaba tukunna”.
Cikeda damuwa ta gyad'a kai, jiki a sanyaye tace “shikenan saimun dawo”.
“ok to Ku gaida mana amare”.
Kanta ta jinjina nanama tana ficewa.

Munubiya tace, “ALLAH Sarki Fauziyya, itadai tana sonmu”.
Nad'an murmusa ina taje mata Wanda Na tsefe, “Munu.... nima ina k'aunar Fauziyya wlhy itada mamansu, sune kad'ai suke sonmu agidannan, Na tabbata wannan fitar dama ba'a sota damuba, itace kawai taketa k'ok'arin taga munje d'in”.
“wlhy hakane sweetheart ”. ‘cewar Munubiya’.

Innarmu dai tanata waya, Dan haka batace mana komaiba.....



★★★★★★★★★

Lokaci na gabatowa yay shiri yabar hotel d'in, zuwansa airport babu dad'ewa jirginsu yad'aga, sun tsaya a Dubai Abu-dhabi sukayi hutun 1hour sannan suka nufi India.
Tunkan jirginsu ya sauka Sauban da Samha sukazo d'aukarsa.
Dan haka yana fara taka matakalar jirgin suka hangosa, cikeda jin dad'i suka nufo gareshi.
Duk da fuskarsa babu walwala hakan bai hanasu nuna farincikin ganinsa ba, shima dai yayi farin cikin ganinsu, duk da kwanaki 4 kacal kenan da barinsa k'asar.
Sauban ya kar6i bag d'in hannunsa yana fad'in yaya welcome”.
Kansa ya shafa yana lumshe ido alamun amsawa.
Samha ma tace “Wellcom back Uncle Sam”.
Ahankali ya furta Thanks you dear, ya school?”.
“Alhmdllh Uncle, ya kabaro Nigeria? ”.
Murmushi kawai yayi batareda ya amsa mata ba, yasan surutun Samha bamai k'arewa bane, yana amsa wannan wata zata jeho masa.

Sauban ya bud'e masa back seat ya zauna, sannan yarufe shi yakoma mazaunin driver, Samha Na gefensa.
Idonsa ya lumshe ya maida Kansa ya jingina da kujera.
Wani madaidaici Gida suka isa, Wanda baza'a kirashi k'aramiba, sannan ba k'ato baneba, sai dai muce tsaka tsaki.
Samha ce tafita da kanta tabud'e gate d'in, Wanda ana ganin komai dake farfajiyar gidan ta jikinsa daga waje. Sauban ya ida shiga da motar, kusada wasu motoci uku yay parking, Samha data k'araso tabud'ema Galadima yafita.
Kusan atare suka shiga falon gidan, yana gaba suna baya.
Masha ALLAH nafad'a saboda ganin tsaruwar falon, sai dai shiru gidan alamun babu kowa a ciki.
Ya zube bisa rukunin kujerun farko dasuka kasance golden color and white. Isaka yad'an turo daga bakinsa sannan ya kalli Sauban dake shirin zama shima.
“yanaji gidan shiru? inasu Momma ne?”.
“duk suna hospital, har jakadiya ma, zamu tafi d'akko kanema Aunty Mimi tatafi itama, dama ita kad'aice agidan saboda mu muna school ”.
“Ok, ya jikin Abie?”.
“hummm da sauk'i yaya”.
“mik'ewa yayi yana guntun murmushi, tunda yafara girma yafahimci mahaifinsa Na kwance yakejin idan antanbaya Momma jikin Abie tana cewa da sauk'i, amma shi shekaru kusan 25 Abie Na kwance amma shifa baiga wannan sauk'inba, kawai suna dai fad'ane, sauk'i d'ayane


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login