Showing 198001 words to 201000 words out of 382522 words

Chapter 67 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2997

Samha tana ta bani hak'uri, amma tamkar tana zuganine, saida Galadima ya harareta yana mata alamar tamasa shiru sannan tayi shiru, shikam ko sau d'aya baicemin uffanba..
Asibiti muka koma, tunda muka shigo Momma ta taso ta rungumeni a jikinta tana lallashi.
Galadima ya jingina da bango ya hard'e hannayensa yana kallonmu, a haka sauran suka shigo suka iskemu, Abie ma kallonmu yakeyi cike da tausayina.
Saida nasamu na tsagaita da kukan sannan nacema Momma zanci abinci.
Galadima yaje kusada Abie ya zauna yana k'aramar dariya, “dama kice yunwa kikeji kika zauna kinama mutane ta6ara?”.
Hararsa Momma tayi tana masa dak'uwa, hakama Abie, aunty Mimi kam saida ta rankwasheshi akai.
Gurin ya dafe yana fad'in “a'a yazaku tararmin ne kuma?, gaskiyafa na fad'a ko Samha?”.
Samha tace, “Uncle nima dai ina bayan aunty gimbiya”.
Idanu ya kwalalo alamar tak'aremin.
Muka had'a ido na hararaesa.
Lips d'insa ya ciza yanamin alamar zan kamakine da ido.
Na ta6e bakina nikuma. Dolenesa yatashi yanemomin abinda zanci.



★★★★★★★★★★

Tunda su Abba suka tafi lafiya tamin k'aranci, bana iya tsinanama kaina komai sai kwanciya, dukna fita hayyacina na canja kamanni, ga cikifa sai kuma bud'ewa yake yana k'ara girma. Kai kace ba halitta d'aya bane a cikinsa.
Galadima dole ya d'auki hutu a office, idan abinda yazama dolene saiyaje Office kam yakanyi shine ta yanar gizo.
Gakuma nasarar jikin Abie daketa k'ara k'yau, dan wasu sassan jikinsa suna nuna alamun fara aiki kamar yanda doctors d'insa suka sanar mana.
A kwana na 8 da tafiyarsu Innarmu ranar a asibiti na kwana, saboda jiki dai yak'i dad'i, ga masifaffen cin abinci abin babu arzik'i.


★★★★★★★

Su Abba sun gudanar da ibadar Umrah cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, ga Sauban dake nuna musu komai yanda bazasu wahala ba.
Suna cika kwanaki goma yasakasu a jirgi suka nufi k'asar haihuwa Nigeria kenan, sun rabu cikeda kewar juna suna saka masa albarka.

Sun isa Nigeria batareda sanin kowa namuba sai Yaa marwan da Galadima yakira ya sanarma yaje ya d'aukesu a airport.
Isowarsu gidanmu tazama a bazata, hakan yasaka gidan rikicewa da murna, dukda kishin daya cika matan gidan ganin innarsu munaya takoma wata d'anya shakaf saboda Hutu da canji wajen zama data samu, dandanan 'yan anguwa suka shiga shigowa taya murna dama Abba jajen ALLAH ya kiyaye gaba.
Innaro babu kunya taketa haba-haba da d'anta, kota innarsu munaya batayi, dan haushinta takeji taje ta zauna a India itako an maidota gida. (Babu mai iyama Innaro dai sai ALLAH🤦🏻‍♀🤣).

Su Ayusher da sukazo suka zage suka gyarama inna d'akinta, komai ya koma need, tamkar ba shineba ya had'a uban datti na tashin hankali.

Tafiyarsu Abba Nigeria da kwana 5 Sauban ma ya dawo India, ya iske ina asibiti, dan gado suka bani dole, babu ranar sallama ma, k'ila saina haihu.
Saidai randa mukayi waya da Munubiya nake fad'a mata tace ai gidama yakamata na dawo na haihu, itama batada lafiyar sosai.
Da to na amsa mata kawai, amma ina tunanin yanda Galadima da ahalinsa zasu amince da zuwana haihuwa Nigeria, kuma tunda 'Yar uwata ta ambata dolene hakan za'ayi, kona so koban soba kuwa.


___________________________


*_Two months ogo_*😬🤭


Watanni biyu kenan da tafiyarsu Abba, tunda sukatafi kuma babu wani Abu mara k'yau kona Sosa zuciya dayay gamo dashi, harma ya koma wajen aikinsa hankali kwance.
Jama'ar gidansu Munaya kuwa sunyi haushin da nuna hassadar ga inna harsun gaji sun bari, dan sudai san ba kulasu zatayiba, ita yanzu babbar damuwarta ma 'ya'yanta su sauka lafiya, dansu Safara'u duksun haihu sukam, kuma dab da dab sukaita kancamo 'ya'yan, ayanzu haka sunan d'an Fauziyyane kawai yarage gobe idan ALLAH ya kaimu, dan itace k'arshen haihuwa..
Su fiddausi duk suna gida sunzo wanka, iyayensu kowa ta zuba k'arya a hidimar sunan 'yarta, yanzu maman Fauziyya da innarsu munaya kawai aka zubama ido aga yanda zasuyi nasu.
Inna dai bata d'ad'ara kanta da k'asaba, iya abinda ALLAH ya hore mata iya shine tai k'udiri yi a hidamar sunansu Munubiya idan sun haihu. Fatantama su sauka lafiyar, dan gasu suna neman share watanni na goma haihuwa babu amo babu labari.
Mama Rabi'a cema kawai keta k'ok'arin ta na ganin sun tanadi dukkan abin fita kunya, sai Aunty Salamah dake taimaka musu, wadda a yanzu tazama 'Yar uwa agaresu makusanciya, dan komai nasu tana tsaye a akai tsakaninta ga ALLAH.

WASHE GARI akasha sunan d'an Fauziyya. Wanda mijinta da mamarta suka bada mamaki, masu shirin asha kunya sai aka barsu su dajin kunyar da shak'ar bak'inciki irinna masu hassada.
Itama tamkar su Haleematu gida ta taho wankan jego.



**************************


A wata ranar talata datai dai-dai da cikar cikunanmu wata goma da sati biyu natashi da matsanancin ciwo, Wanda ya rikita Galadima da ahalinsa, nan take doctors sukace haihuwace, aka fara shirin kar6arta amma ina, gadai haihuwar gadan-gadan da gaske amma kuma nagagara haihuwar har washe garin laraba.
Nayi masifar galabaita, Galadima yace sumin cs idan bazan iya haihuwa da kaina ba.
Amma sukace zan iya haihuwa.
Ranar laraba da daddare Galadima da Momma na kusadani suna ta tofamin addu'a saboda zufar danakeyi, nace su kiramin munubiya, babu musu Galadima ya kira Yaa marwan.
Shima dakaji muryarsa zakasan a rikice yake, hakan yasaka Galadima tambayarsa ko lafiya?.
Yaa Marwan yace, “dadai sauki ranka ya dad'e, tun daren jiya Munubiya ke nak'uda amma haihuwa shiru, sai sunan Munaya kawai taketa kira”.
Mik'ewa Galadima yayi tsaye, yace, “muma ai halin da ake ciki kenan, yanzuma itace tace akira mata ita, please kakai mata wayar”.
“ok”. Yaa marwan ya amsa yana nufar d'akinda Munubiya take...............✍🏻





Barkanmu da dawowa.🤩✋🏻








*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_typing📲_*


💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*


*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

_________________________

*_HASKE WRITERS...._*

_gaisuwarku ta musammance, alkairin ALLAH ya baibayeku aminan kwarai abokan tafiya👍🏻😽._

I love you manya-manya fa🥰🥰🥰🥰🤩🤸🏻‍♀

________________________


~book 2~👉🏻2⃣2⃣


................Cikin kuka Munubiya tace, “y'ar uwata ki taho gida please”.
Munaya dake saurarenta ta share nata hawayen itama, “insha ALLAH zan taho, ki kwantar da hankalinki, daga yau zuwa gobe ko yaushe zaki iya ganina sweetheart”.
Daga haka munaya ta mik'ama Galadima wayar tana cigaba da share hawaye.
Hankalinsa atashe yace, “miyasa zakimata alk'awarin zuwa? bayan kinsan ga halin da kike a ciki”.
“kayi hak'uri yalla6ai, gara ka barni Na tafi shine mafi a'ala, tun farko y'ar uwata bata 6oyeminba ta sanarmin naje gida Na haihu, idanma baka kainiba to wahala kawai zanta sha anan d'in tunda hakan take buk'ata”.
Galadima jiyay tamkar ya make Munaya, ya haukace mata da masifa kaikace zai cinyeta d'anya, “wannan ai canfin banzane da wofi, ALLAH shine kawai maiyi ai bawani alk'awarinku ba, shin Ku bazaku tausayama kanku baneba? yaufa kwannanki biyu kina wahalarnan, wane irin taurinkai ne wannan.......?”.
Dakatar dashi Momma tayi ta hanyar d'aga masa hannu, ta dafa k'afad'ar munaya dake kuka tana fad'in “y'ata dama kinmata alk'awarin zakije Nigeria ki haihu ne?”.
“Momma ba alk'awari namataba, amma kusan 2months kenan tacemin gida zanzo Na haihu ko? nikuma bance mata komaiba”.
Murmushi Momma tayi, ta kalli Galadima dake tsaye yanata kumbura dan haushi. “Muh'd anemi ticket d'in Nigeria yanzunnan”.
Da sauri yace “Momma amma......”
Hannu ta d'aga masa alamar bata buk'atar jin komai. ya had'iye wani k'ullutu daya tsaya masa a mak'oshi, shifa ba tafiyar tata bace matsalarsa, shima akwai tashi manufar da dalili, amma bashida ikon yin jayayya da Momma, waya ya zaro a aljihu. Ya lalubo wata number yay kira, ficewa yay daga d'akin.
Momma tacigaba da lallashin Munaya daketa hawaye, ga zufa Na cigaba da jik'eta dukda AC dake aiki a d'akin.
Kusan mintuna talatin Galadima yashigo shida doctor, dannan aka shirya Munaya, nurses biyu suka kaita mota.
Wannan karon harda Momma rakkiya Airport, tanata jerama Munaya addu'oi har suka isa.
Haka sukai wannan tafiya babu shiri, Galadima kayan tun safenema a jikinsa bai ko koma gida ya canjaba, hakama aunty Mimi.
A jirgi yana rungume da ita tanata murk'ususu idan abin ya motsa, wai danma waje Na musamman aka basu dankarta takura. idan nak'udar ta lafa sai barci mai dad'i ya kwasheta, da abin yamotsa kuma tata kuka kenan tana k'ank'amesa, dukta jimasa ciwo da farce, shikam tausayinta dukya cika zuciyarsa.

Yaa marwan ma cikin haushi yakira inna ya gaya mata abinda Munubiya tayi, inna taita fad'a tamkar zata ari baki, itada ta haifi su munaya ita tasan halin kowa acikinsu, tabbas a fili Munaya tafi Munubiya fad'a, amma a bad'ini Munubiya tanada ak'idar tsiya da tsatstsauran ra'ayi, lokuta da dama idan takafe akan Abu bata tankwaruwa, kuma dolene Munaya ta amince ayi kokuwa tasha wahala, dan idan Munubiya ta murd'e abin bazai ta6a ya yuwuba saidai idan Ubangiji ya juna mata ikonsa, to amma bata ta6a zaton shirmen nasu zai iya ta6a har lafiyarsu irin hakaba.

Dole inna tashirya zuwa asibitin da kanta, taita zubama Munubiya dake fama da kanta fad'a, su mama Rabi'a da Maman Fauziyya sunata bata hak'uri, tunda dai anrigada an aikata, saidai kuma a kiyaye nagaba.

Su Munaya sun iso Nigeria lokacin tsakkiyar ranane anan, dan irin 1pm d'innan ne, dayake yakira su sarkin mota ya sanar dasu time d'in dazasu iya isowa, tun wajen 11am ma suna airport d'in..
Tunda Galadima yafara sakkowa daga matakalar jirgin rungume da Munaya akan idonsune, hakanne yasaka sarkin mota matso da motar bisa alfarmar ma'aikatan wajen, suna gama sakkowa k'afarta ta rik'e, dole ya d'auketa daga ita har nauyin cikin ya k'arasa da ita motar, mutane duk tausayinta yakamasu.
Tunfa a mota labari yafara canjawa, dan Munaya tafita hayyacinta sosai, Galadima sai tsawa yakema sarkin mota, ALLAH daine kawai ya kaisu asibitin lafiya, aiko suna shiga dogarai suka shiga da gudu cikin asibitin kiran doctors.
Tunima Galadima ya kuma sunkutarta yayi ciki, a hanya yagamu da nurses da gadon d'aukar marasa lafiya, bai d'orataba, yawucesu abinsa, doctor Farida ta nuna masa d'akin da aka canjama Munubiya.
Gadon da aka tanada dan Munaya ya d'orata, Munubiya tashiga mik'o mata hannu tana kuka, itama a wahalce tamik'a mata nata, dan gadon kusa da kusa aka sakasu....
A tare suka dinga Neman yafiyar junansu suna kuka, sai tausayinsu ya kamasu Galadima.
Da k'yar doctor Farida tasamu Galadima ya fita suyi aikinsu, dama haka tasha dagama da Yaa marwan shima, saida ma Abbansu yamasa magana, Dan shima yana asibitin.

Munubiya da Munaya Haka suke rik'e hannun juna kowa nashan azabar nak'uda, (wannan k'auna dabance gaskiya, nak'uda ba abun wasaba amma suna son jin junansu a kusa, wato koma mutuwace tazo musu a tare?😽).
Haihuwar Munubiya ce tafara gadan-gadan, Dan haka Munaya ta k'ank'ame hannun y'ar uwarta tana kuka da kiran sunanta a galabaice, itama sai labarin yafara canjawa, Nurse da doctor Farida and doctor Zainab dake Kansu duk suka maida hankali ga Munubiya, cikin rahamar ubangiji saiga jinjiri yayi sallama duniya da kuka. tamkar jira itama Munaya ta kar6a, a time d'in Munubiya tayi shid'ewar wucin gadi, amma hannunta na cikin na Munaya datake shan azaba itama. Ba'a d'auki tsawon lokaciba itama tata mace tafito, saikuma sabuwar nak'uda ta tashi a tare suduka, yanzu Munubiya mace Munaya kuma namiji, na Munaya na fad'owa wani yakuma biyo baya😳.

Turk'ashi, ALLAH sarkin rahama da tausayi, maiyin yanda yaso kuma ga Wanda yaso, Munubiya ALLAH yabata k'autar tagwaye mace da namiji, yayinda Munaya keda uku, maza biyu mace d'aya.
Su doctor Farida duk sun kacame da murna da k'ok'arin gyara yaran, kaikace su akama haihuwar.
Dandanan aka shiga goge yara da zaitun, amma cikin hattarar kar a had'esu agaza ganewa..
Su Munaya ma dai kulawa ta musamman aka basu, amma Munubiya ta suma, kuma bata farfad'oba, hakanne ya tada hankalin su doctor Farida suka rufu akanta suna bata dukkan wani taimako, sama-sama Munaya ma kejin 'Yar uwarta tashid'a, hakanne yasata kuma k'ank'ame hannunta hawaye na zurara mata, itama bawani k'arfine da itaba, Dan ko idanu dak'yar take iya d'agawa, dishi-dishima take ganin komai.
Lamarin yana san zama babba, Dan saida wani babban doctor ya shigo dole, ganin shigi da ficinsu doctor Farida yayi yawa yafara ankarar dasu Galadima.
Nanfa suka fara turkesu da tambayar ko lafiya?, sukuma suna basu amsa da babu komai, kowa dai bai yardaba, dukda suna jiyo kukan jariran.
An d'auki wasu adadin mintuna kafin numfashin Munubiya ya dawo, ajiyar zuciyar da Munaya tasaki duk saida yasaka su doctor Farida kallon ta da tausayi, dukda tana cikin wani hali itama, amma hankalinta nakan 'Yar uwarta.
Sun kimtsasu tsaf, daganan aka musu allurar barci dansu sami Hutu, yara dai kam Alhmdllh, duk da sun lura d'aya daga cikin na Munaya bai cika kuzariba, kamar sauran mace da namijin sun fishi lafiya, amma basuda tabbas tunda basu bincikaba. Nurse d'aya tafito ta kar6i kayan haihuwar takoma, duk an saka musu, dukda basu zama iri d'aya ba tunda sunzo babu tabbacin miza'a haifa, musamman ma su Galadima, gara su Yaa Marwan sunsan ita Munubiya dama biyune.

Tunda su doctor Farida suka fito Galadima dake ta kaikawo shida Yaa marwan da Muftahu suka maido hankalinsu Kansu, Galadima bai iya matsawa ba, saisu aunty mimine suka k'arasa ga su doctor Faridan.
Kowa yana k'ok'arin tambayar abinda ke faruwa.
Doctor Farida tayi murmushi, tace, “to ai bakine bazai iya fad'a ba ma, inaga kawai angunan k'arnin su shiga daga ciki, idan sun fito kwaji komai”.
Yaa marwan da Galadima suka kalli juna, kowa yana fargabar abinda zai tarar d'in.
Aunty Mimi ce takama hannayensu tana fad'in “kuje mana, mi kuke tsorone wai?”.
Kowa tamkar an doke masa gwiwa haka suka nufi d'akin, Yaa marwan ne gaba Galadima a baya.. Duk sukayi sororo a k'ofar d'akin suna bin gadajen matan nasu da jariran kusa dasu da kallo.
Badan kowa yasan kayan jikin matarsa ba dabasu iya banbancewa ba (kunsanfa mu 9ja 'yan gargajiyane🤭, kod'an canja kayannan na asibiti bamayi🤣).
Galadima da Yaa marwan suka kuma kallon juna, kowa ya kasa cewa uffan, doctor Farida dake bayansu tamkar ta kwashe da dariya, tadai daure ta danne.
Ra6asu tayi ta shigo ciki sosai, ta tsaya tsakkiyar gadajen tana kallon hannun Munaya da Munubiya dake had'e da juna har yanzu, sunyi-sunyi su saki amma sunk'i, sai suka saka musu lokar asibiti a tsakkiyar aka d'ira hannayen Dan kar suyi sanyi.. Juyowa tayi ta kallesu da murmushi a fuskarta, tace, “wannan itace Munubiya ga babies d'inta nan 2 mace da namiji, wannan kuma Munaya ga nata 3 maza biyu mace d'aya. Ina muku fatan alkairi gaba d'aya, ALLAH ya rayasu akan sunna”. tana gama fad'a ta juya ta fita tabarsu.
Binta sukayi da kallo harta fice, sannan suka maido ga iyalan nasu, saikuma kowa ya k'arasa da hanzari ga matarsa.
Yaa marwan yasaki murmushi yana d'aukar macen, sanan ya d'auki namijin shima, dukya rungume.
Galadima kam durk'usawa yay gaban gadon yasa gwiywoyinsa a k'asa ko k'yank'yami bayayi, dukda angyara wajen tsaf tamkarma ba'a haihunba.
Hannunsa d'aya ya d'ora agoshin Munaya da duk yaga ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login