Showing 369001 words to 372000 words out of 382522 words
Chapter 124 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete
yace, “Bazaka gane bane d'an uwa, my mata tayi abincin salla, idan naci wannan cikina ya cika naje can kuma babu space ai sai a hanani.......”. Sai yay shiru bai k'arasaba.
Mi Matawalle da Muftahu zasuyi inba dariyaba, har mutanen dake d'an gefensu suka juyo suna kallonsu.
Galadima kam murmushi kawai yayi ya maida eyeglasses d'insa a ido yana kallon inda su Abie ke zaune.
Anci ansha kowa yay mak'il cike da godiyar Ubangiji, daganan aka fara gudanar da jawabai Na godiya ga ALLAH bisaga ni'imar dawowar Abie.
Mai martaba shine ya fara, sannan Abba hayatudden.
Maganarsu ta ratsa zukatan mutane da dama, domin sun nuna k'auna mai yawa da farincikin dawowar d'an uwansu, hakan ya k'ara musu kima, dan sunture zancen nan Na mutane a zuciyarsu, wato y'an ubanci dayafi komai ruruta wutar k'iyayya a masarautunmu Na Hausa Fulani.
An buk'aci ganin Galadima shima.
Ya mik'e cikeda takun izza da zagayawar jinin Mulki a dukkan sassan jikinsa, k'asaita da kwarjinin yarinta Na d'awainiya dashi. Yanda akaita zubama su mai martaba hototuna shima hakanne. Da yawan mutane dake wajen ya burgesu, koda haushinsa kakeji kwarjininsa ya Isa jin ka k'aunacesa lokaci d'aya. Ya gyara tsayuwarsa yana wani k'asaitaccen murmushi mai tsada da nuna halin dattako, cikakkiyar sallama ya musu suka amsa, sannan yacigaba da magana yana zare eyeglasses d'insa.
Hawaye cike da idonsa yace, “A watannin da bazasu cika shekara ba Na tsaya a gabanku kamar haka ina kuka da kausasan kalamai ga dukkan mai hannu a ciwon mahaifina, a ranar d'aurin aurena hakan ta faru, nasan kuma dayawanku dake nan suna a wancan zaman, sai dai bisa ga hukuncin Ubangiji yau nine tsaye a gabanku ina kukan farinciki da tausasa harshena Na Neman afuwa, na godema Ubangiji da yaymin dukkan sutura ta rayuwa, ina fatan samun ta gaba inda yafi gidan duniya, badan nafi kowaba yaymin wad'anan ni'imomin, sai Dan hak'uri da juriya da kar6ar k'addara aduk yanda tazoma bawa, bara nabaku wani labari kad'an, Wanda yana d'aya daga cikin babbar riba dabazan manta da itaba har k'arshen numfashina. Doctor Arjun shine likita na farko daya fara duba Abie, shine kuma yacigaba da kulawa dashi har nakai wayo, shi mabiyin addinin Hindu ne, sanann daga wannan k'abila ya fito, shekarar dazan shiga jami'a sai ALLAH ya jarabcesa da ciwo rana tsaka, yanama cikin aiki a asibiti ya yanke jiki ya fad'i, y'an uwansa doctors sun bashi dukkan taimakon gaggawa harya farfad'o, a daren ranar saiya buk'aci d'aya daga cikin doctors d'in daya kira masa ni. Ina tare da Momma da Jakadiya kiran ya iso gareni, munyi mamaki kwarai da gaske, dan bamu dad'e da duboshiba, lokacin salla dayayine yasakamu baro d'akin dayake ma. Haka Na tashi natafi amsa kiransa. Awajen doctor Arjun Na iya yarensu na Hindu, tunda Na shigo saiya shiga muk'omin hannu alamar nazo garesa, nabi umarninsa Na zama kusa dashi tareda rik'e hannayensa cikin nawa, muryarsa cike da rauni yace___”.
_“Sameer Kasan miyasa nace a kiraka kuwa?”._
“Kaina na girgiza masa alamar a'a. yayi murmushi idonsa Na cigaba da tsiyayar da hawaye, yakuma damk'e hannuna a cikin nasa yana cigaba da fad'in___”.
_“Sameer kune Muslims na farko dana ta6a mu'amulla mai tsayo dasu, daga gareku na fahimci wasu k'yawawan halaye da kullum duniya kefad'in baku dasu, lallai duk mai ambatar wannan addini da addinin y'an ta'adda ya jahilci fahimta da sanin halayyar d'an adam, kun kasance masu hak'uri wajen samu da rashi, kar6ar rayuwa a dukkan halin data zo muku, kun kasance masu yawan k'yautata zato, mutane da yawa sunsha zuwa duba mahaifinka, amma duk d'unsu ban yarda dasuba amma Ku sainaga babu wani kokwanto a Kansu, da zuciya d'aya kuke k'ar6arsu da mu'amulantarsu, dukda zukatanku sunada yak'inin dolene a samu mugaye a cikinsu, a duk daren duniya idan nashiga duba mahaifinka nakan iske mamanka tana salla ko karatun littafinku, ahankali sai wad'annan abubuwan suka fara kwad'aitamin wani abu daban, tun ina kokawar turewa harya fara zama babban 6angaren tunanina dayay tasiri mai girma a dukkan kuzarina, da farko tsoro nakeji, Dan kaf ahalinmu babu wani mabiyin addinin musulunci ko kiristanci. Amma kasan duk miye matsayar wannan labarin danake baka a yau?”._
“kaina Na girgiza masa jikina a sanyaye, yayd'an murmushi da cigaba da fad'in__”.
_“Inason biyan ko nawane domin Shiga addininku, a yau bana tsoron kowa yasani koya ganni a ciki, inason ribantuwa da k'yawawan halayenku”._
“A lokacin kunsan miya faru?”.
Jama'a suka amsa da a'a. Galadima yay murmushe da share hawayensa da Handkerchief.
“Na tsinci kaina cikin zumud'i da firgici dukda k'ananun shekaruna, Dan lokacin bazan wuce 17years ba nake tunani, hawaye Na zuba a idona nace da gaske zaka musulinta Doctor?. Cikim jinjina kai ya tabbatar min. Ban tsaya 6ata lokaciba nace doctor addinin musulunci ba'a biyan ko sisi domin kasantuwa a cikinsa, imani da ALLAH da yarda da manzonsa shine babban farashi mafi daraja a duniya. Yace to a ina zan samo imanin?. Nai dariya da fad'in ta hanyar ambaton Kalmar la'ilaha illallah muhammadurrasulullh. Yace to ya shirya. Duk da k'arancin shekarunan nawa baiyi Girman kaiba ya kar6a kalmar shahada yana mai jaddadata a harshensa har saida tari ya sark'esa, rikicewa nayi Na mik'e da nufin nemo doctor amma saiya hanani, yamin nuni dana bashi ruwa, haka nadawo na bashi ruwan, kur6arsa hud'u ya janye kansa yana fad'in___”.
_“Sameer, tabbas yauce ranar tafiya koda shiri ko babu, ina rok'onka koda sau d'ayane ka gudanar da salla a kaina, sannan karka yarda wani d'an uwana ya san da musuluntata, badon komaiba sai Dan gudun tozarta ku, ka sanarma Anania ina matuk'ar k'aunarta, karta manta dani”_.
Daga nan ya shiga maimaita kalmar shahada yana wata irin zufa maiban tsoro, na rik'ice inata ambatar sunansa da girgizashi, sai kawai naga jikinsa ya saki. Sakinsa nai Na fita da gudu kiran doctor sai mukaci karo da Momma dataji shirun yayi yawa tabiyo sawuna. Rik'eni tayi tana tambayar lafiya?, jikina Na rawa nasanar mata abinda yafaru da Hausa. Dan nasan mawuyacine asamu maijin yaren a kusa damu, hanani kiran doctor tayi taja hannuna muka k'oma d'akin tana share hawen farin ciki Dana kewar Dr Arjun, tai addu'a mai yawa akan gawarsa sannan tace Muh'd zaka iya masa wanka?. Bak'aramin tsorata nayiba, jikina Na k'yarma nace Momma wankafa?, nidai tsoro nakeji. Ta dafa kafad'ata cikin k'aramin kwarin gwiwa tace yarona karkaji tsoro, tunfarko ubangijine ya za6eka ya k'addara Dr Arjun ta hannunka zai zama musulmi, ka daure ka cika masa wasiyyar daya barmaka ta sallatar gawarsa, Dan kasandai su ahalinsa ba irin wannan jana'izar zasuyi garesa ba, ina tare dakai kaji. Bisa Umarnin Momma da koyarwarta naima gawar Dr Arjun wanka, itakuma tana bakin k'ofa tanamin gadi, Ubangiji kuma saiya ara mana dogon lokaci harna gama na maida masa Uniform d'in asibitin a jikinsa, sannan na sallacesa ina kuka. Saida muka gama komai sannan muka fito mukabar gawarsa cikin d'akin, bamukoyi nisa da k'ofarba mukaga doctor ya shiga d'akin da hanzari, mintuna kad'an da shigarsa maganar rasuwar Dr Arjun ta fara Shiga kunnuwan Mutane. Wannan rasuwa ta matuk'ar ta6a zuciyata, har a yau d'innan da nake gabanku ina jinta, kuma ban gaza wajen yimasa addu'oin samun rahama ba”.
Galadima ya share hawayensa dake zirara tamkar fanfo, ya kalli mutane yana fad'in “kakannina, iyayena, yayyena da k'annenna kunsan hikimar baku wannan labarin kuwa?”.
Jiki a sanyaye, wasuma hawaye sukeyi suka amsa da a'a.
Galadima yay murmushi yana kuma share hawayensa da gyara tsayuwa, “Wannan labarin yana mana nuni muzama masu nagarta aduk inda muka tsinci kanmu, babu irin k'yawawan halaye da addininmu bai koyar damuba, amma son zuciya da burukan duniya saisu sauyamu, miyasa muke mantawa damu su waye? Ina kuma zamu koma?, dalilin ruk'o da gaskiya mahaifina ya fad'a hali mai tayar da hankali na tsawon shekaru, babu wanda ya ta6a tunanin sake ganinsa anan, amma kuma sai gashi, kunsan wane irin hali mai firgici da ciwo da muka tsinci kanmu kuwa? Mahaifiyata itace silar komawata jarumi, da taimakonta nazama jajirtacce, a halin k'uruciya har tunani nake anya kuwa tana sona? Ajiye sosayyar nan ta d'a da uwa tayi ta kutsani cikin talakawan daba yarena ba, ba addinina d'aya dasuba, ba k'asa d'aya muka fitoba, naringa wahalhalun koyon sana'oi da gwagwarmaya ta fahimtar rayu, ga karatu, ga damuwa da ciwon mahaifina, ban fahimci gata taminba saida na iya d'aukar nauyin ciwon mahaifina da hidimomin ahalina, na kammala karatuna bisa bigiren danake buri, iyaye mata wlhy kuzamto masu koyi da halayen mahaifiyata, matasa y'an uwana kuzama masu koyi da rayuwata, dukda ana ganina d'an ganta ban zauna gata yamin komaiba, saina tashi da k'afafuna da gumina na gina kaina, muzama masu k'yawawan halayya koda daraja martabar addininmu ga wad'anda basu fahimcesa ba, Dan k'yawawan hallaya da nagarta yaja hankalin Dr Arjun kwad'aituwa da addinin Islam, Yakuma mutu a cikinsa bisa amincewar ubangijin al'arshi, da mugayen hallaya mukeyi saidai doctor Arjun ya k'yamacemu dajin kuma k'yamar addininmu, son zuciyoyinmu shike maidamu bayan baya a Kullu yaumin, ba tarin dukiya ko gata ko k'yawune abin birgewaba, Nagarta, nagartar samun k'yawawan halaye da d'abi'u shi ake kira jarumta, matata ta ta6a fad'amin Hak'uri shi ake kira NASARA, saida hak'uri ake zama jarumi, sai an jure zafi ake tsintar kai a sanyi. Kusan shekarunta nawa kuwa?, ashirin, inhar mace mai k'ananun shekaru irin wannan tanada hikimar zance da nazari mai amfanar da wani irin haka miyasa tunaninmu ke d'aukar mace mai k'aramar kwakwalwane?, nabaku satar amsa kaje ka mu'amullanci matarka ta nagartacciyar hanya kaga yanda zaka amfanu da tagomashin tunaninta, kunga mata biyunan sun zamema rayuwata wata ginanniyar Katanga, mahaifiyata da kuma matata da auren shekara d'aya kacal zamu cika, kakata yayata k'anwar mahaifiyata rumface su dake kare martabata da zamana cikakken mutum, ina mai farin ciki mai tsanani da samun lafiyar mahaifina, da godiya mai yawa ga wasu ke6antattun mutane wadda gudunmawar suce silar ganina a gabanku, ALLAH ya albarkaci rayuwar ahalinsu ya cika musu burukansu na alkairi, Yakuma had'amu a aljanna gaba d'aya”.
Duk suka amsa da amin suna binsa da tafi.
Daganan sauran jama'a sukaita bayani d'ai-d'ai, taro dai bai tashiba sai kusan 3:00pm.
Cikin farin ciki Galadima ya shigomin, ko kunyar su Ahmad dake zaune da Sarkin mota ya shigo dasu bai jiba ya rungumeni, saida na ankarar dashi sanann ya sakeni yana susar gefen wuya alamar yaji kunya, yayi farin ciki da ganinsu kuwa, yaran sun shiga ransa sosai, duk da abinda yayma mahaifansu basu tsanesa ba, saima zuminci mai k'arfi daya k'ullu a tsakaninsu.
Ranar sashenmu saiya koma na matasan samarin masarautar, Dan shima Sauban nan ya kawo gayyarsa cin abinci, gasu Yassar kuma, itama Samha saiga tata gayyar, saikuma ga matasan gidanmu da y'ammata da banyi zaton ganiba, harda Zarah da Siyama, dad'i tamkar xai karni kuwa.
duk yanda Galadima yaso ke6ewa da matarsa abin ya gagara, dansu Matawalle da Nuren da suka iso dawasu samarin masarautar suma duknan suka nufo, tsakaninsa da Munaya sai dai y'ar satar kallo, dan kwalliyarta tagama narkashi.
Baniba kosu Amaturrahman sunji a jikinsa raranar, d'auka dai sun shata harsun gode ALLAH, bankuma samu damar shayar dasuba sai madara suka sha. Har dare babu wata damar samun ke6ancewa da juna.
Washe gari kuma aka gudanar da hawan salla mai k'ayatarwa, wanda a tarihin masarautar gagara badau an dad'e ba ayi irinsa ba, saboda manyan sarakuna na garuruwa daban-dabanne da Governors harda uban gayya president da senators da sukazoma Abie barka da dawowa suka halarci bikin hawan sallar.
Misalta muku k'yawun kwalliyar jarumin naku Galadima ai 6ata lokacine, ammafa komai zamm, y'ammata da yawa sun k'yasa, balle yau fuskarsa washe take da murmushi na musamman Wanda jama'a basu ta6a ganiba.
Su Abbana ma sunzo gaida Abie, sun sami k'yak'yk'yawar karramawa mai ban mamaki, wadda tasani farin ciki mai tsanani dajin k'arin k'aunar Ahalin Galadima.
******
Saida shagalin bikin salla ya lafa nasamu zuwa gidanmu da zagaya dangi, kowa yayi farin cikin ganina, musamman ma Munubiya da Innarmu, su Aiyaan da sauran jama'ar gidanmu, jikin Innaro yayi tsanani, dan harma ana shirin kaita asibiti, ciwon k'afa ya takura mata ainun.
Sati biyu dagama bikin salla tawagar masarautar su Momma sukazo daga Niger, a masarautar gagara badau suka sauka, kasancewar harda uban gayya Sarki.
Wani k'warya-k'waryar biki zuwan nasu yazama a masarautar, tareda k'ulla alak'a mai matuk'ar k'arfi wadda ada babu ita, da safe Matan suka koma gidanmu akabar Sarki da jiga-jigansa anan.
A wannan zuwane aka nemi auren Ayusher, saima Abbansu ya tak'aita musu wahala akan a d'aura auren kawai baki d'aya kowa ya huta.
Kowa yayi murna da hakan k'wai da gaske..............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼
[8/21, 8:44 PM] 0mmer Farouk: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
______________________
*_My Ayusher Muh'd kema ga naki, a koda yaushe kina cikin zuciyar bilyn Abdull, alkairin ALLAH yakai gareki har gadon barci tawan_*😘😘😁👍🏻
*_Maman kadee kina ina, maza garzayo ki kar6i k'undumemiyar gaisuwa ga bilyn Abdull, ina yinki ever y'ar uwa rabin jiki, ked'in tadabance wlhy a gareni, ALLAH ya raya mana kadeen mu har lokacin aure mu kwaso shoki😂😘😘👍🏻🤸🏻♀🤸🏻♀._*
_____________________
*_BOOK 3_* 👉🏻3⃣1⃣
.................Randa sukaje gidanmu ai munsha kallo da mamaki, yau ga babban Sarki har cikin gida, dan Sarki cewa yay saiya taka har d'akunan y'an uwansa, hakan yayma Innarmu dad'i, koba komai jama'ar gidanmu zasu kuma ganin martabarta.
Aiko sun gani, dan ko rantsuwa nayi babu kaffara wasu saisunyi kukan fili bama na zuciya kawaiba. Ranar anguwarmu cika tayi mak'il da jama'a.
A wannan zuwane Innarmu ta fara taka nawa d'akin itama, dan tana zuwa gaida ahalinta masarauta saboda anan aka saukesu, dan haka Galadima yake sakawa a d'akkota duk bayan kwana 2 susha hirar zuminci, duk da Sarkine dawasu manyan y'an rakiyarsa ne kawai a masarautar, sauran mata dasu Badeerah duk suna gidanmu, wasu kuma gidansu Ayusher. Kwanansu goma ciff aka d'aura auren Yarima Issifu da amaryarsa Ayusher, wannan aure yasaka kowa farin ciki da annashuwa, anyi biki na kwanaki biyu anan muka shilla Niger kaita, a can kuma aka d'auro auren Badeerah da Yaa Fadeel, kwanakinmu Biyar anashan shagali maiban mamaki da birgewa, muka d'akko amaryar Yaa Fadeel muka dawo gida.
Koda muka dawo babu zama, dan kuwa hidimar bikin aunty salama muka shiga, Wanda yanemi had'ewa Dana Muftahu da Matawalle, zakusha mamaki idan nace Muku Samha Ce matar Muftahu😁, wannan had'i ALLAH yayishine bisa umarnin Momma, kowa kuma ya kar6a da hannu biyu yay addu'a, koda Samha taso bijirewa bisa ga soyayyar Gopal nice naita tausarta da mata nasiha harta kwantar da hankalinta.
Munsha shagali kam iya shagali, babu abinda zamucema ALLAH sai godiya dakuma bin amare da angwaye da addu'a.
Aiko wad'annan bukukuwa sai suka tada tsumin Nuren shima, yace aure shima yakeso, kai tsaye kuma ya kawo Farhat d'iyar Minister a matsayin za6insa, su Papi basuk'iba, domin nagartar mahaifiyar yarinyar ya cancanci a aureta, hakan kuwa akayi, shima aka sanya bikinsa kusa, mukasha biki kuwa cikeda nishad'i da farin ciki.
*************
Bayan kammala wad'annan bukukuwa mukajema Aunty Salamah gaisuwa, da tayata murna ta musamman ni da Munubiya, tarba tamana mai k'yau da mutuntawa, a hirar da muka gudanar nake mata tambaya gameda mitasani ga Galadima?, dan naga yaranta sun kasance yaransa na wajen aiki.
Murmushi tayi tana sakama Meenal pampas, “Babu wata alak'a tsakaninmu, Ameer k'aninane uwa d'aya uba d'aya, sanan mu y'ay'ane ga Baba Rabilu da zakiji yana fad'a, har akayi aurenki da Galadima bansan akwai alak'a tsakanin Mahaifina da shiba, duk da nasan kad'an daga cikin labarin mahaifina, sai a dalilin satar Muftahu da mukayi, ta wannan hanyarne kuma mahaifina baba Rabilu yasamu ganawa da Galadima ma, akuma wannan lokacinne duk muka San komai gameda abinda yafaru, ashema yanakan Sani ya saka Ameer aikin C.I.D, bisa tsatstsauran bincike daya dad'a yanayine ya gano Galadima yanama hukumar DSS aiki, shiyyasa yatura Ameer ga hukumar dan neman kusanci dashi, wannan shine kawai abinda na sani”.
Daga ni har Munubiya munsha mamaki da girmama hukumar Ubangiji, dan shine ya sanya alak'a tsakaninmu da aunty salamah batareda sanin junaba ko wani dalili, ni dai ALLAH yariga ya k'addara nice dama matar Galadima, shiyyasa ya kulla bisaga hikimarsa wadda wasu wawaye suka kalla a matsayin nasararsu.
Satinmu biyu da zuwa gidan aunty salamah mukaje India ni da Galadima, halattar bikin Akash da Doctor Erfan Fahad, abin mamaki da al'ajab saiga Radha a matsayin matar Akash, matan Dana ta6a had'uwa dasu a shagon kayan yara na Galadima, lokacim inada cikinsu Abdurrahman, masu yara Vishnu, Ashe ita k'anwar Maman Vishnu d'ince. Aiko muka rungume juna cikin tsantsar farin ciki da annashuwa, ashema munsan juna, vishnu ya k'ara girma abinsa, sai dai bai ganeniba ma😊.
Ana